Breaking News

DIJA QAYA 12

 🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋

            *DIJAH QAYA*

            *page* 1⃣2⃣


       Ranan juma'a shine Ranan da za'akai KB Rugan Juma, Basu samu flight ba sai wajen k'arfe uku,

 a airpot suna sauk'a dama sunyi bucking Amubulance kasancewan k'afan bayi ko lank'wasuwa,Basu suka isa cikin Rugamba sai da aka idar da sallahn isha'i, suna shiga cikin Garin suka tambayi Gidan *Malam Bukar Maid'ori* ba wani b'ata lokaci aka kaisu,

 ak'ofan Gida suka sameshi sunacin Abinci shi da mak'ocinsa Baban Jebu,

 Uncle Musa ne ya musu sallama Hanu biyu suka karb'eshi hami da bashi wajen zama, 


     Bayn sun gaisa Uncle Musa yace "Munzo wajen Malam Bukar ne, 

  "Ayyah nine Malam Bukar, nan yasanar dashi  abun da ke tafe da su,  Mik'ewa yayi da sauri yashiga Gida "Dijah! Dijah!! 

     "Na'am ta Amsa da sauri ta fito, 

      "Maza d'ibi taburmai kije can d'akin Bak'i ki shimdid'a ankawo mara lfy yana fad'an haka ya juya yafita 


  a jikin mota yasamu Uncle Musa yana tsaye, "Bismillah kushigar dashi Habib da Driver da Abban Habibne suka d'aukeshi, 

  Uncle Musa da Malam Bukar suka rufa musu Baya dama Gidan k'ofa biyu yake dashi d'ayan K'ofan shine zai sadaka da cikin Gidan inda su inna suke,

   sannan akwai k'ofan da zai sadaka da d'ayan side d'in ananne Baffa yake kwantar da marasa lfy, 

  kasancewan akwai wanda suke zuwa daga nesa,  


     D'akine ciki da falo wanda akayi da bluck d'in k'asa aka maasa Rufi da ciyawa irin dai d'akunan k'auye sai dai wanna yasha flasta sosai da flu na siminti uwar d'akinkuma har da Gadon k'asa a falo aka shimfid'a taburman 

    Suna ajiyeshi Habib yayi sauri yaje yad'auko blancket ya shimfid'amasa yasa pillow suka taimaka masa ya kwanta nan suka zauna aka sake sabon gaisawa Baffa yace sai  in Allah ya kai rai da safe zamu fara aiki, 


    Shiga cikin yayi yasa aka kawo musu Abinci, 

     Habib ya matso kusa da Habib yana kallonsa  "KB me kk son kaci? 

    "Nothing, 

    "to barin Had'ama tea 

     " bazan shaba kabarshi kawai

     "naga kaman bakaso zuwannan ba kayi hak'uri insha Allah daka samu lfy shikenan,  

   "Gaskiya ni bana iya zama a duhu wannan shine kawai matsalata, wlh yanzu jina nake kaman a kurku, 

   "a'a baza abarka aduhuba ka kwantar da hankalinka,


  Yauwa KB pls kayi magana da yarinyannan mana tadamu taji voice d'inka  wlh tadameni seriously,

 tsaki KB yayi ya kalli inda su Uncle Musa suke suna Hiransu,          

"ko zamuyi magana badai yauba sai ka bari da safe, daga haka ya mai da kanshi  ya kwanta,


    Washi Gari tunda safe Baffa yafara had'a magungunan da zai masa d'auri, 

    Bintalo da Dijah ne suka musu abun karya, Doya Baffa ya sayo akasoyamusu aka dafa musu Ruwan shayi da yasha kayan k'amshi, Inna ta jere ma Dijah a k'aton tray takaimusu, a falon ta samesu dukansu KB da Habib suna kwance Uncle Musa da Abban Habib suna zaune suna Hira, cikin kunya irin nata ta gaidasu dondai duk tsiwan Dijah takan ji kunya maza sosai, Uncle Musa yace meye Sunan ki "yanmata?  Dijah tafad'a tana mik'ewa, "a'a asai dai uwatace guda awajen, sannu ko uwata ita dai murmushi kawai tayi tafita, 


   Abban ya d'aga su KB ya gabatar musu da abun kari,  sunaci suna Hira KB kan Shayin kawai yasha, sosai yaji dad'in Ruwan shayin don Haka yasha sosai,


   Baffa yana gama karyawansa, yafito, yashiga wajensu tunda ga nesa KB yake kallon Baffa har yashigo yasamu guri yazauna, KB yana mamakin yanda hakan yakasance, ikon Allah,  Baffa ya Gaisa dasu Uncle Musa sannan yajuyo wajesu  KB, Baffa kam sake baki yayi cike da mamaki yana kallon sa "Likita!  Ikon Allah Dama kaine Mara lfyn?  

     Allah Sarki D'annan meyasamekane haka? Ya fad'a yana kallon k'afan da ya kumbra suntum,  Uncle Musa yace "Ayyah acnce mana kuma kai kasamesu abakin kogi ka k'ira Hukuma "innalillahi wainna ilaihirraji'un kanason kacemin Likitane na tarar dasu abakin kogi jinajina?  "Eh haka dai police d'in yagayamana, ikon Allah asai kasanshi,

    Baffa yayi ajiyan zuciya cike da tausayi "wannan yaro ai bazan tab'a mancewa dashiba, 

  Ya kwashe duk abunda KB ya musu lokacin da yakai Dijah Asibiti, 

     "Rayuwa kenan da kakai masa mara lfy, yau gashi shima ankawo maka shi amatsayin mara lfy, 

   Shiyasa arayuwa akeso kazama nakowa saboda bakasan yanda wataran zaka kasanceba, cewan Abban Habib,

    Baffa yajuyo da kallonsa ga Kabir da shimad'in shiyake kallo yana murmushi, KB yace "Ashe anan kake? ai inayawan zuwa tanan,  "Allah sarki shiyasa kasan mutuncinmu kasan mutanenmu sam basa mutunta fulani,  

     Dukansu suka sa Dariya "ai dole yasan darajan fulani don Uwarsama bafulatanace, inji Uncle Musa Baffa ya matso Kabir yana cewa a kace bazamu samu matsala wajen aikin k'afanba tunda ya had'a zuriya da fulani, kasanmu akwai dauriya, Habib ya kwashe da dariya "ah Baffa kar ka zugashi don naciro wayata zan masa vidio, kabir ya harareshi " yaro ancemaka ni kaine? Allura mafa inza'amaka sai katara mana mutane, 


    Baffa yana dariya yakamo k'afan Kabir yafaramasa aiki, sosai Baffa yatausaya masa don har da tsagewan k'ashi ak'afan gashi yayi tsami, 

    Kabir kuwa tunda Baffa yakama k'afanshi yakamo lip d'insa na k'asa yana tsotso ya rufe idonsa gam sai zufa yakeyi, duka d'akin bawanda bai tausaya masaba, 

   Har aka gama duka biyun bai ko bud'e idoba, yanajin Angama ya kwanta tuni bacci yayi gaba dashi,


Godiya suka mishi sosai, Uncle Musa yanisa "to Malam nawane kud'in aikin?


    Baffa yad'anyi murmushi yace "ai koda bani namishi aikinba nizan biya amishi Balle kuma ninayi, wlh tun zuwana Asibiti abunda yaronnan yamin nake jinsa kaman d'an dana haifa, 


    Inzakuyar da kubarni da Kabir zan masa duk abunda yakamata fatana dai Allah yabashi lfy,


     Godiya suka masa sosai sannan Abba yace "mu yau zamu koma zamu barshi da d'an'uwansa, 

   Saidai kayi  Hakuri zamu saka Generator agidannan don munga ba kuwani samun wuta sosai, 

    "A'a wannan bawani abun damuwa bane, yafad'a yana mik'ewa, "nizan d'an fita sadai inaga zan dawo kafin kufita,

  "to Allah ya kare muma zamuje cikin gari midawo, tare suka fita, suka koma cikin gari donyin sayayya, 


       Inna tana zaune agindin murhu tana Raba Abinci Bintalo tayi sallama, ta Amsa mata tana kallon bayanta, ina Dijah?  "mhmm Dijah suntsaya can ita da Jebu wai zasu daki wata yarinya, inna rafka salati tana rik'e baki yanzu duk fad'an danayima yarinyannan Shekaranjiya batajiba, kenan nayi asaran yawun bakin? "Mhmm inna waifa akan lado ne, wai ancemata anganta da Lado adandali shine tunda akatashi a makaranta suka sha d'amara ita da Jebu ba irin maganan da ba mumusuba nida Ma'u basu kulamuba, cikin takaici Inna tace maza kije kice mata tazo injini intak'i kuma ranta zai b'aci,


     Bintalo kan tsayawa tayi cike da mamki tun isanta gun,


     Dijah ta haye kan wani itace ta hard'e k'afa tanagani k'awayenta Jebu da Har, da sude suna ta  dambe da larito da k'awatanta, 


    Cikin zafin nama ta cafko jebu tana mata fad'a "yanzu fisabilillahi Jebu ku wasu irin marasa hankaline,  Dujah ta maidaku sakarkaru, tanimo fad'a tabarku da dambe ita masifa ga tsoron tsiya, kukuma ga k'arfiko? 

    Dijah ta jawo hanun Jebu daga cikin na Bintalo, ta hankad'ata cikin fad'a,

     " Jebu har yanzu bakin Larito baiyi jiniba kifasa mata baki sai mutafi, tafad'a tana zabga ma Bintalo harara 

     "wlh BIntalo nasha gayamiki kifita ahanyana bafa tsaoronki nakejiba,

    Cike da talaici Bintalo tace "sai ki wuce mutafi Inna tana k'iranki, 

    zaro ido Dijah tayi tana kallonta, "sharri kikaje kikamin? 

   Bintalo batace mata komiba,

   Ta rik'o hanun Jebu "zo mutafi ta kalli Larito wlh karki aza kin tsirane zan kamaki,

     Suna tafiya tana ta surutu ma Bintalo      ko kulata Bintalo batayiba har suka shiga cikin gida, arumfa suka samu inna ta rafka tagumi,

     Asanyaye Dijah ta iso ta tsiguna agefe, 

       "wai Dijah meyasa ne baki jin magana, ban hanaki tsayuwa bayan kuntaso daga makarantaba?  Wai yau harkece da fad'a akan saurayi Dijah? Yaushema kk kula Lado? Yaron da sai yazo yayi aika so goma baki fitaba, naga ko sunansa aka fad'a sai kin b'ata rai, shine don tsaban iyawa harda tare "yar mutane akanshi, 

     Wani irin kunya mai tsananine ya rufe Dijah, ji take kaman k'asa ya tsage tashiga ada tasan Bintalo takan rufa mata asiri, kotayi wani abun awaje batacika fad'a agida ba tabbasa da tasan Bintalo zata mata haka bazata bari taji ba, wani irin zufa taji yana bin jikinta, tsaban takaici sai kawai tasaki kuka, 

     Sosai Bintalo tayi nadaman fad'a ma inna da tayi, musamman ma yanda taga Dijah tana kuka, ba makawa tasan bashi taci awajen ta sai dai fatanta Allah yasa kar Dijah ta mata mummunan ramuwa, 

    Kuka takeyi bil hak'k'i ahaka Baffa ya shigo yasameta dasauri, ta tashi ta rik'e kekensa "Sannu da dawowa Baffa tagad'a tana share hawaye, Ran Baffa bak'aramin b'aci yayiba, Don in Akwai Abunda Yatsana kukan Dijah ne, 

     Tana sauk'e kayan Abincin da ya shigo dashi akan keke tana kukanta, har tagama sauk'ewa, 

       


        Hanunta yakamo rai b'ace yanufi inda Inna take, 

       "me kukayi mata? Ya tambayi inna yana mata wani irin kallo, aza bure Dijah take kallon inna tana juya kanta, inna ta fahimci Dijah bataso Baffa yaji, murmushi tayi "katambayeta tayi maka bayani da kanta, Bak'in halintane inaga ya motsa, 

 


  Nan dai yayi ta fad'an dayasaba sai da yayi yagaji don kansa,  


     Ya shiga d'aki Inna tace "ki wuce kije kicire kayan makarantan kizo ki kwashi Abincin Bak'innan kikai musu, 



    Su biyune ad'akin  Kabir da Habib,  suna Hiransu Habib yana rik'e da Hanun KB yana d'an matsamasa,  


    Ta shigo da tray d'in Abinci tunda ta shawo kwanan d'akin Kb yake Kallonta, sallama tayi Habib ne kawai ya Amsa, ta dire tray d'in a gefe ta d'ago ta kalli Habib akunyace tace ina wuni, lfy Beatiful girl yana murmushi,

   Ta juyo ga kabir "inawuni, caraf idonsu suka had'u, Dam taji k'irjinta ya buga ta tsaya baki bud'e tana kallonsa yamurtuk'e fuska yana hararanta, yace "Malama Kallon ya isa haka ko, ai sai kitashi ki k'ara wuta, dama d'an k'auye ako ina sai yanuna k'auyancinsa, bandahaka meye Abun kallon?, mtss yaja Dogon tsaki, cikin zafin Nama ta mik'e saida tafita tasa takalmin ta tayi taku Biyu ta juyo Rik'e da kunkuminta, ta zabga mishi Hararan sama da k'asa sannan taja tsaki ta tafi, Habib ya kece da dariya har yana rik'e ciki shi kuma gogan ji yake kamar zuciyansa tafito din takaici, arayuwansa  yatsani raini,







   *Tofah Anya KB kasan waye Dijah kuwa? 🤔    ka takalota kuma kace bakason raini?* 😳








Ku biyoni..........................






*HAUSA NOVELS* 📚

*HAUSA NOVELS* 📚📚

*HAUSA NOVELS* 📚📚📚

No comments