Breaking News

DIJA QAYA 11

 🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋

            *DIJAH QAYA*

           *page* 1⃣1⃣

 A gefen Hanya suka faka motan suka shigo wurin da k'afa da hanu Malam Bukar ya nuna musu inda su KB suke,    Bak'aramin kad'uwa police d'in sukayiba musamman da suka lura Ba k'ananan mutane bane, Ogansu da kansa yaja mota ya tafi asbiti suka taho da ambulance akatafi dasu, 


     Nan likitoti suka rufu akansu sukaciremusu harsashi ajikinsu, Sani kusan bulet hud'u aka ciremasa, ga raunukan da yaji yayin da akacirema KB d'aya, sai dai ansameshi da karaya aduka k'afafunsa, 


       Har la'asar ana abu d'aya akansu, sai daf magriba suka kammala agajiye Doctors d'in suka fito, har lokacin police d'in sunanan babban likitanne ya mik'a ma police d'in hanu, suka gaisa, "yadai likita ansamu nasara? 



     "Eh to mundaiyi musu aiki amma dai ba wanda ya farfad'o acikinsu,

    

 Police d'in ya mik'a masa ID card  wannan a aljihunsa muka samu, ya karb'a ya duba 

*Kabir Mahmud tugga*  yagani ajiki da sauri ya d'ago ya kalleshi "oficer ai wannan Babban likitane kuma d'an shahararren d'an kasuwan nanne Alhji Mahmud Tugga,   



   Kai police d'in ya jinjina yace "shiyasa nanumaka kagani kasan jiya anyi taron manyan likitoti a Abuja, maybe can yanufa masu hamayya dashi kokuma "yan fashi sukamishi wannan aika aikan, so yanzudai zamu d'aukeshi mukaishi National Hospital Abuja, Inyaso kuyita treting d'in seceuritynsa anan inya d'ansamu releif sai amai dashi cikin Adamawa.



   🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

 

Gidan Mami na lek'a bak'aramin kad'uwa nayiba lokacin da na hango Mami zaune abakin gado ta jingina kanta ajikin gini, tanajiyo hargowan mutanen da suka cika gidan wasu "yan'uwanta ne wasu kuma "yan zuwa jajene, yau kwana uku kenan ba Kabir ba labarinsa, ko ataron da akayi na Abuja ma lbr yasamesu Kabir bai halacci taronba, bincike iya bincike kullum yinsa akeyi amma ba lbr,


 hanunta tasa tashare hawaye k'waya d'ayan da yagangaromata  Zuciyanta sai zogi yakemata, ahankali take tuno Abumda mijinta yagaya mata ranan da zai Rasu, *Fatima kikula min da Kabir Don nasan duk mainiman yaga bayana yanzu hankalinsa zai koma kan Kabir shima za'ayi k'ok'orin ahalakashi kamar yanda akaso amin abaya shiyasa akecewa dukiya fitinace, don nasan abumda suke nima kenan awajena dukiyata gashi kuma yanzu zai koma hanun sa* 


   "Kabir ta fad'a tana share k'walla dai2 lokacin akayi nocking sauda ce tashigo tad'an rusuna "Mami wai kije inji su Dady, sai da tashiga bayan gida ta wanko fuskanta sannan ta zira Hijabinta tafito acan babban falo tasamesu, su biyune Uncle Musa da Abban Habib, tazauna daura dasu suka gaisa cikin k'arfin Hali, ta kalli yayan nata "yaya har yanzu ba wani lbr?

    Ko boudy guard d'innasa ba'asamu lbrnsuba? 

    Uncle Musa yad'ago ya kalli Abban Habib, ya sauk'e ajiyan zuciya, dai2 lokacin wayan Mami ya hau ruri,

 Nafisa sunan da yabayyana akan wayan kenan, d'auka tayi tasa ahans free cikin matsanancin kuka Nafisa tafara magana "Mami ashe ankashe yaya KB tun ran Asabar amma ba wanda yagayamin? Cikin tashin Hankali Mami tace "waya gayamiki wannan magana Nafisa?

    "Dady ne yak'irani yanzu yake gayamin wai ahanyarsa ta zuwa Abuja aka kashwshi, kuma wai bai yarda inzoba wlh sai nadawo ko zai kasheni nabar England har Abada, Mami kam kusan suman tsaye tayi awajen, idonta taf k'wala, ahaka wayan yasulale yafad'i ta zube akan kujera tanayima yayanta kallon tuhuma, 

    "Yaya meyasa kuka b'oyemin Mutuwan Kabir?  Bani na halliceshiba don me za ab'oyemin mahaliccinsa ya karb'eshi? Uncle Musa ya katseta da fad'in Fatima ki kwantar da Hankalinki wlh bamu samu lbrn mutuwan Kabirba amma bari muk'ira wanda akaji abakinsa, yalalub'o no. Alokacin Alhaji ya'u suna zaune da su Kila awani tafkeken Hotel suna pertyn samun nasara ganin mai k'iranshinne yasa shi tashi awurin dayake ya canza waje, bayan sungaisa Uncle Musa yace "Ashe kasamu lbrn mutuwar d'anka KB? Shine bakasanar damuba? Cikin firgici  Alhaji ya'u yace "ni ni kuma? Ta ta ina kennan? 

     "mhmm yanzu "yarka Nafisa tayi waya take sanardamu kuma tace kai kagayamata, 

    Arud'e yace "no no bata fahimceniba bahaka nagaya mataba, 

  Kallon Kallo Uncle Musa da Abban Habib sukayi  sannan yakashe wayan yana kallon Mami data zuba masa ido, dai dai lokacin Habib ya shigo bako sallama yazauna yana kallonsu "mmn  Dady nasmu lbrn KB na yanzu  akak'ira asibitinmu akasanardamu KB yana Yana national Hospital Abuja ai gaba d'ayansu mik'ewa sukayi suna k'ara tambayansa Mami kam sauk'ar da kanta k'asa tayi tana kirari ma mahaliccinta tana hawaye, bata majin mesuke fad'a ita dai taji yayanta yana waya murya k'asa2  


  "Fatima kitashi kishiga ciki yanzu zamu Je Asibitin garinnan muduba Sani daga nan kuma zamu wuce Abujan ajirgi  sannan kuma ki iya ma bakinki, karkisanar da kowa cewa ansamu lbrn Kabir harsai mun gano masu hanu akan son salwantar dashi, 

  Asanyaye tace "wasune ko? Suka mishi wani abun?  


  "Ranan lahadi da azahar masu tsaronsa suka zo gidana suka shaidamin wasu sun tsaresu ahanya sun kashe mutum biyu acikinsu sauran sun kub'uta da k'yar da raunuka wasu kuma ba raunuka, amma basuga uban gidan nasuba shiyasa bazasu iya zuwa gidannan ba shine sukazo su sanarmin,  nikuma nasanar masu Ibrahim, yanzu haka wanda suka samu raunin suna asibiti muna kula dasu sukuma ma matan munje ga iyayensu munsanardasu munmusu ta'aziya harda d'an ihsani,


Cikin tashin hankali Mami tace muje tare inga Sanin, 


Tumdaga nesa da Mami ta hango Sani ta rud'e, kallonta yakeyi har ta matsoshi, sai mirmushi yake mata ta dafa jikin hadonsa tana kallonsa harsu uncle Musa suka gaidashi da jajan tawa, sam Sani baiji dad'in ganin hawaye afuskan Mami asanyaye ya k'irata tad'an sunkuyo tana kallonsa "laifin Kabir yashafeka ko Sani sunyi niyan kashe Kabir kaima sun nakasaka duk wannan gurbin harsashine haka ajikinka? Ta k'arasa maganan cikin kuka,   Sani ya ya marairaita fuska yana kallonta yace "Haba Mami don ALLAH kidaina kukannan dagaske oga KB yana raye? Yafad'a da muryan kuka, Habib yadafa kansa yace "ka kwantar da hankalinka Sani nacemaka yana raye bak'arya namakaba yana Abuja yanzu haka wajensa zamuje, "Don Allah inkaje kak'ira wani da kasani a asibitinnan yabani wayan kahad'amu inji muryansa, "insha Allah zanyi yanda ka fad"an Allah yabaku lfy "Ameen mami ta amsa Abban Habib yace mata tazo amaidata gida tunda akwai masu kula da Sani, tak'i tace anan zata zauna, ahaka suka tafi suka barta har dare tana wajen sai wuraren 1:00 ta koma gida,


Awannan dare kam sam Mami bata rintsaba juyi kawai takeyi akan gado data rufe idonta Hoton Kabir take gani, gashi tun da rana a Asibiti tayi ta k'iran su uncle Musa Amma wayansu baya shiga sosai ta k'ara razana, washi gari kuwa tun safe tagama shirinta taje taduba jikin Sani daga nan tawuce air pot, tana shiga Abuja kai tsaye Hospital ta wuce, 


    Gadajen word d'in take bi da kallo can tahango sojoji da police ajikin wani gado k'ura musu ido tayi, abayanta taji ance Fatima tana juyowa ta ido biyu da yayanta yana dariya yace "kin kasa hak'uri ne?  Duk da k'in nimanki danayi awaya, to zo muk'arasa ga gadonsa can jami'an tsarone ke gadinsa, suna k'arasawa da uncle Musa yagabatar da ita amatsayin mahaifiyarsa gaba d'aya suka watse suka basu guri, ahankali Mami take d'aga k'afa kaman wanda k'wai yafashe ma aciki, Kabir kuwa sai k'ok'arin k'ak'alo murmushin k'arfin Hali, yana kallonta duk yanda Mami taso ta daure abun ya gagara hawayen da taso b'oyewane suka hau sintiri afuskanta ta dafa goshinsa da d'ayan hanunta tana share k'olla da d'ayan tace "Sannu Kabir irin jarabawan da mukuma aka jarrabe mu dashi kenan, juya kanshi yakeyi ahankali ya d'ora Hanunsa asaman hanunta kaman zaiyi kuka yana kallo idonta, yace "Pls Mami ko mutuwa nayi bai kamata kimin kukaba, Addu'anki nake buk'ata Mami wlh wannan hawayankin yafi min raunukan jikina Mami, 


    Cikin sheshshek'an kuka Mami tace "wayene Kabir? Waye yake son ganin bayanka? Meka musu Kabir? 

       Kabir ya tura hanunsa ya jawo kujera yasaka mata ta zauna tana shafa gashin kanashi,


 "araunane yace Mami wlh bawanda ya isa ya kasheni sai kwana na ya k'are,  


Da son ransune da yanzu bana nan, amma kinga da Allah bai soba gani araye pls kikwantar da hankalinki Mamina yafad'a yana sharemata hawaye,


   Mami ya lbrn Sani? 

     " yana Asibiti jikinsa da sauk'i har yafi naka,

     "su Bala fa? 

       "Duk jikinsu da sauk'i, sai Alokacin Mami ta kalli su Habib da Abbansa suka gaisa, 

           




     Sannu sannu Su KB suke samun sauk'i da ikon Allah,


      Acikin watanni Biyu duk wani raunuka ya warke Sani kam tuni har Ansallameshi Uncle Musa ya d'auleshi yakaishi Gombe campanin KB yace masa yazauna anan don haryanzu mutane basu san Ansamesuba,



     Alokacinne kuma aka kunce karayan KB amma wani abun tashin hankali shine sam karayan bai d'oruba ba k'aramin tashin hanlali suka shigaba, 


       Ahaka aka sake wata d'aya aka kunce Amma baiyuwuba, ganin haka yasa Uncle Musa yace Asallamesu kawai zasu kaishi amasa na gida haka Kuwa aka sallamesu aranda zasu tafi police d'in da case d'in yake hanunsa yazo, cike da girmamawa yagaida Mami, ya tambayeta jikinsa,


     Mami ta jinjina kai "jiki da sauk'i saidai karayanne bai gyaruba shiyasa zamu koma gida agwada na gidan agani ko Allah zaisa Adace, shiru yayi nad'an lokaci yace "kunada wanda ya iyagyarane?  

       "a'a gaskiya saidai zamu bincika

        "acan k'auyen da nake aikinnan kuwa akwai wani datijjo wanda yazo yasanar mana lokacin da yagansu acikin mummunan halinnan ya iya gyaran karaya sosai don naji ance har daganan akan kaimasa masu karaya, ko zaku gwada kukagani?

     "Abban Habib yakarb'e da cewa "Eh sai kawai mukaishi can awani garine? Wani Rugan fulanine can k'arshen Adamawa sunan Rugan Juma sunan mutumin kuma *Malam Bukar maid'ori* nan yagaya musu tanda akayi kafin akawo KB nan Mami tajinjina kai to Allah yasa Adace, 


    Uncle Musa yace "Ameen, tunda hakane kawai sai mufasa zuwa gidan ke Fatima Gobe in Allah yakaimu sai  ki koma gida mukuma jibi sai mushirya mukaishi, 



*Tirk'ashi masu kartu ga Dr KB fa yana shirin zuwa gidansu Dijah k'aya abokiyar Hamayyansa cab ga Shi wai ita Dijah bata mantuwa wai wani wainan za'a totane?*..........................






*HAUSA NOVELS* 📚

*HAUSA NOVELS* 📚📚

*HAUSA NOVELS* 📚📚📚

No comments