RAGGON MIJI 46-50
4⃣6⃣
*another
page for you rukayya haroun(maman nour)* *and erminatou*
Ummi tace
"gaskiya alhaji bazan kai diyata gidan kishiya ba "
Abba yace
"haba asiya be kamata kina magana irin haka ba, ita ai ba budurwa bace
jawara ce kinga mawuyacine tasamu saurayi, dan Allah kibarta tunda tanasonshi
karki sage mata gwiwai "
Ummi tace
"ni ban iya kishi ba bare ita hakanan kaje aimaka wani mugun abun kana
zamanka lpya "
Abba yace
"shikenan tunda zancen kikeso bari nabaki wuri inkingama mitar kikawomin
fura ta "
Ya tashi
yabata wuri, ummi tace "shikenan se inki magana, yanzun intayi auren ko
nima hankali na ba kwanciya zeba bare ita, tunda taji tagani shikenan Amman
dole na dage mata da gyara na musamman in inaso tai daraja "
Ta tashi ta
nufi dakin abba,
Faseelat
nashiga daki ta haye gado ta kunna data cikin farin ciki,
Messages
nagama shigowa tabude na maman amira wanda yanzu ta meda number ta da my anty ,
ta bude message nata "wai antyn amira kinmanta danine?ko duk zawarcinne ya
boyeki?har munyi tafiya mundawo, in bazaki zoba kibani address naki zanzo ni
saboda yarki ta matsamin "
Faseelat tai
dariya ta tura mata "zanzo insha Allah zuwa jibi de nima ina missing naku
"
Tafita
tashiga contact na fahad ta turamishi "masoyi naji dadin kyautar ka, Allah
yakara maka budi ya kareka daga sharrin makiya, kanata kara kyau miye sirrin
ne?"
Ta turamishi
tana murmushi ta kashe datar se barci,
Da laasar
fahad ya kirata suka kara shan vedio call sannan sukai sallama,
Se dare ta
samu tabude data bayan sunyi bankwana da habibinta, ta shiga message din maman
amira "💃🏼💃🏼💃🏼thank
se kinzo inanan ina zuba eyes"
Faseelat ta
tura mata "don't mind"
Tafita
alokacin fahad ya turomata reply kamar haka "amin cutie karki damu da
kyauta da namiki bakomai bane danko raina kikeso zanbaki, kinason kisan
sirrin?"
Faseelat tace
"thanks eh inaso inji "
Cikin zolaya
yace "aisha ce sirrin tana kula da service dina duk lokacin dana bukata
ana bani "
Faseelat ta
tura mishi "😏 To yayi kyau ,tunda ta isheka me
zakai dani "?
Yace
"I'm joking fa naga kinhau I just test you kinga kema kishinne dake zuwa
zakuyi kuyita hadamin zafi "
Faseelat
tace "aini bazanyi kishi da anty ba "
Yace
"hmmm Allah yasa, gobe inanan zuwa fa, don kullum zanzo sekin gaji dani
"
Tace
"ai bazan gaji ba kazo yanzu ma "
Yace
"kina tsoron nawa da rana ma yaaka kare? "
Tai murmushi
ganin ya sauya zancen tace" good night sleep well 😘"
Yanagani
yayi murmushi ya cigaba da aikinshi.
Da safe abba
yaje yasamu baba babba akan maganar fahad yace zesa amishi bincike akansa,
Da marece
faseelat taci gayu sosai tasaka kayan da ya siyomata, tafito ummi tace"
kinyi kyau gaskiya ina zuwa halan? "
faseelat
tace "fahad ne yace yana kan hanya "
Ummi tace
"to waike bazaki ce yarika shigowa ba kullum fira a mota? "
Faseelat
tace "to ummi zanmasa magana "
ummi tace
"kibada asiyomiki dan juice mana kitafi mashi dashi yadansha "
faseelat
tace "to bari nabawa Mubarak "
Ummi tace
"sekinfa dage yarinya, don ba khalil bane wannan awaye yake kuma yanada
mata "
Faseelat
tace "nasani ummi bari naje "
Ta juya ummi
tabita da kallo rigar duk tafito mata da shape dukda tanada fadi, kuma faseelat
dan mayafin rigar kawai ta yafa,
Karfe 5 yazo
ya mata waya tafito, be fito daga mota ba ta cikin glass yake karemata kallo,
harta zo tabude marfin motar ta shiga,
Yaja
numfashi ya sauke ta kalleshi tana turo baki,
Ya lumshe
ido ya bude yace "cutie wannan kwalliyar fa?"
Tace "i
did it just for you "tana marmara ido cike da jan hankali,
Yayi
murmushi yanabinta da ido yace "thank you I'm happy, kinyi kyau sosai
"
Tace
"thanks ga ruwa"
ta mika mai
water melon juice yana kallon kwalin yace "ni bazansha ba sede kibani a
baki "
Ta bata
fuska tana hararanshi yace "abinda aisha keyi kenan komi yimin take taimin
wanka, tasmin kaya, ta bani abinci abaki, amma ke just kiban drink yagagara
"
Ta harareshi
tace "kabari kaga muyi auren ba wanka ba har goyonka ma zanrika yi
"ya kyalkyace da dariya yace "sure? "
Ta daga mai
kai yace "to fara tundaga yau mana mugani inda gaskene"
Ta tunzuro
baki gaba tace "open ur mouth"
ya wage baki
yana jiran tafara bashi,
Tai dariya
ta bude marfin ta dora mishi kwalin abaki, ya dage yayita kwankwada, tai sauri
zata janye caraf ya rike hannun alamun ta cigaba da bashi,
Ta dora mai
yayi ta sha ta fiddo ido tana kallonshi tasss ya shanye yana meda numfashi
,tana mamaki ta sadda robar Kasa bakomi ciki ta dago tace "amma yau anty
batai maku girki ba ko? "
yayi dariya
yana goge bakinshi da handkerchief yace "yau nidakaina nashiga kitchen,
bawani yunwa nakeji ba jindadin juice dinne yasa na shanye shi duka, kinsan duk
abinda ya fito daga gunki dole yayi dadi "
Ya kashe
mata ido daya,
Ta rufe
fuska tana dariya,
ya dauko
waya yace "kigyara nai miki pic, badani zaaiba bare kice danna samu na
tabaki ne "
tace
"OK, amma zamuyi da kai a wayata "
Ya saki
murmushi yanajin dadi,
Ta dan fiddo
ido ta matse baki ya dauketa, pic din yayi mugun kyau kalar rigarta purple da
baki ,
shiru be
dagoba yanata kallon bakinta da ta matse kamar zatai kisss,
Tana
kallonshi tace "muyi atare mana "
cikin rashin
sanin abinda yake yace "wait for me "
Ta turo baki
ta matsa ta leka wayar yayi zooming bakinta yanata kallo ta fashe da dariya,
yayi sauri
ya dago cikin dawowa tunani,
tana nunashi
da yatsa tana dariya tace "Allah kacika jaraba dubi duk yadda idanunka
suka koma "
Yayi
murmushi ya jingina da seat ya juya ya kalleta yace "kamar kinsani kima shirya
"
Ta canza
maganar da matsawa kusa dashi ta dauke su pic,
Tana dauka
shiko hankalin nakanta tana samu tadauka ta matsa tana dubawa tace "yayi
kyau sosai, kasan wani abu zan dorashi a status da insta "
Yayi
murmushi yace "idan kuma bakisaka ba ni zan saka akan nawa "
Ta rufe baki
"rufani kasayani ban shirya abinda zancewa anty ba, gobe ma zanzo ganin
yata anty ma tace tayi missing dina "
yace
"gobe munada special guest kenan Allah yakaimu "
Tace
"amin bari natafi se munyi waya"
Yace
"ammmmm"ya fiddo 1000 rafas biyu daga gaban motor ya mika mata yace
"kibawa yara "
Ta girgiza
kai tana murmushi tace,"bana son kudinka kai nikeso"
Yaji dadin
maganarta ya lumshe ido ya bude kafin yace wani abu tabude tafita tana mai
murmushin dauke numfashi,
ya rumtse
ido gam yanajin yadda zuciyarshi ke harbawa saboda tsananin sonta,
sannan ya
bude yana kallonta har ta shiga gida, seda ya dau 10 mnt sannan ya tada mota ya
tafi,
Yana kan
hanya yamata transfer na 500,000,
faseelat
mamaki ya cikata da tagani tanata tambayar kanta koshi bejin wuyar fidda kudine
oho, ta nunawa ummi, ummi tace
"duk kan gyaranki zasu kare ai"
faseelat tai
dariya
Next day
tunda wuri faseelat tagama aikinta tatafi super market, ta kwashi kayan kitson
yara danginsu beads ,robber band,robar kitso ,Brazil wool dasauransu sannan
taje wurin kayan wasan yara,
Wata big
teddy me kyau ta baby ta burgeta ta dauka taje tabada ATM suka cire kudinsu
kusan 50 thousands teddyn yakama tana dauke daita ta hau napep zuwa gidansu
Aisha,
Me napep na
ajiyeta ta biya tai knocking ta gaida baba tsoho ta shiga,
Amira na
wurin wasanta ta hango faseelat da gudu taje ta rungumeta,
Faseelat na
dariya tace"daughter I really miss
you "
Amira tai
dariya tanakai hannu kan teddy faseelat tabata tace "dama nakine gashinan
"ta mika mata amira ta rungume babyn,
Faseelat
tace "ina anty? "
Amira
hankalinta na kan teddy dukda tana da wadanda suka fisu setaga wannan tafi mata
tace "she's inside "
faseelat
tace "OK zo mushiga ciki "ta jawota suna tafiya tana kallon kitson
kanta da yadan tsufa,
Suka tsaya
bakin kofa faseelat ta danna door bell shiru takara dannawa seda akai 15 mnt
sannan aisha tazo tabude tana murmushi tace "maraba da anty "tana
kallon kayan jikinta,
Faseelat ta
shigo tana murmushi,
faseelat ta
gaida aisha, ta amsa tana mata kallon up and down tace "a, a! Jawara
kinfaso gari kinga yadda kika kara kyau kuwa? "tana dariya
Faseelat
tace "anty bawani kyau kina zaulayata ne "
Maman amira
tace "Allah kinsauya gaskiya bazawarinki na kula dake "
Faseelat tai
dariya tace "anty very soon de zanyi aure nahuta da kirana jawara da kike
"
Aisha tace
"Allah yakaimu muna murna ai, saboda mune kirjin biki "
faseelat tai
murmushi,
Aisha ta
mike "baride nakawomiki drinks, inkoma ciki daddyn amira nanan, bacci ma
muke kika tadamu "
Faseelat
tace "ok"
Aisha tatafi
kawo mata drinks ita kuma ta bude jaka ta fiddo kayan kitson amira ta dauki
wasu da zatai amfani ta ajiye sauran ta ajesu a kasa, tafara wa amira tsifa,
aisha
nadawowa tagansu tace "yau ranar ta amira ce kenan naga harda katuwar
teddy aka siyomata "
Faseelat
tace "eh dan ita nazo "
aisha tace
"to Nagode "ta ajiye mata ta haura sama,
Seda tagama
mata tsifa ta danzuba drink tasha, ta daga kai tana kallon benen jin aisha
shiru, wani malolo yatsaya mata a makoshi ta daure ta farawa amira Twisting,
Irin manyan
nan ne masu guda ukku shaf shaf tagama mata aisha shiru bata fito ba, abun
yabata mamaki kusan 1hr,
Cikin dabara
ta kalli amira tace "kitsonki yayi kyau jeki gwadowa mommy "
Amira ta
gudu tana taka step,
Ba jimawa
segasu sunfito Aisha rike da hannun
fahad shi kuma ya dauki amira yana tambayarta wa ya mata kitso dan besan
faseelat bace har tazo,
Har suka
sauko falo ahaka faseelat tunkan bene take kallonsu tanajin haushi,
Fahad na
dago ido yaga faseelat,
Tayi kyau
tana sanye cikin milk hijab da brown atamfa ya dan dauke ido daga kallonta,
Aisha tace
"yaya kaga teddyn da faseelat ta siyowa amira nan gashi harda kitso tai
mata "
Faseelat
cikin jin haushi tace "inayini "
yace
"lpy thanks for your care for our child "
Tai banza
dashi ya juya yacewa Aisha "sena dawo "
Ta matsa tai
masa kisss a cheek tace "take care of yourself"
Faseelat ta
cika tai famm yana satar kallon faseelat ya fita,
aisha tazo
ta zauna tajawo amira tana duba kitson tace "gaskiya kinyi kokari har
kingama cikin sauri kiyi hakuri nabarki ke daya wlh se yanzu mukai wanka
tundazu muna kwance "
Faseelat
tace "badamuwa "tana yamutsa fuska tace "tafiya ma zanyi "
aisha tace
"tunyanzu kitsaya mudanyi fira mana "
Wayar
faseelat tahau ruri ta ciro ta duba taga fahad ne batare data dauka ba ta kalli
Aisha tace "jirana akeyi dama nacika alkawari ne kawai "
Aisha tace
"to shikenan Nagode kwarai faseelat Allah yabarki da masoyinki naga yanaji
dake har iPhone 8s kike riko yanzu "faseelat tai yake,
Aisha tace
"bari nakawomiki tsarabarki "
Faseelat
tace "dan Allah anty kibarta ina sauri "
aisha tai
dariya tace "aikuwa har gida zan kawomiki wasu English dress ne masu kyau
nasiyomki naga zasuyi kyau da jikinki dan Allah kima bari nakawomiki daukosu
kawai zan yi "
Faseelat
tace "tom"
Aisha ta
juya faseelat taja tsoki,
Can zuwa
aishar ta dawo da ledar ta amsa tai godiya shaf shaf ta fita daga gidan,
Tana fita
taga motar fahad awaje tana sauri tai gaba yabi bayanta da motar,
haryakai
setin ta ya rage glass yace "kishigo in kaiki "
Tai banza
takara sauri,
Yakara binta
yana cewa "meyafaru ne wai? Kishigo mutafi "
Takarayin
gaba, cikn fushi yakashe motar yafito yabita yajawo hannunta tana ta kokarin
kwacewa ya sakata motar yaja yabar unguwar,
Faseelat ta
duke tafashe da kuka me cinrai,
kujimin iko
seta hanashi soyewa da matarshi 😎
team
faseelat de 💋
[7/12, 11:01
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*SHALELE🤸🏼♀*
✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
We are
bearer's of so golden a pen🖊
We write
assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative
golden pen🖊
Be hold our
words
A product of
our pen🖊
Savour our
words
For it will
cause you no pain.✍🏽
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
4⃣7⃣
Yana tuki
yana jiyowa yana kallonta saboda mamakin abinda yasakata kukan kawai yake,
Ta cigaba da
kuka tana sheshsheka, cikin jin ciwon kukunnata ya gangara gefen titi yatsaya,
ya kifa kai jikin sitiyarin motar zuciyarshi na zafi,
Faseelat
batabar kukan ba don wani mugun kishi takeji yanda suka fito tareda aisha says
it all sunacan suna soyewarsu ne,
Ya dago yana
kallonta cikin jin haushi yace "wai me yafaru ne?hakanan sekita kuka
ninasan banmiki komi ba, kifadamin mekikewa kuka "
Ta cigaba da
kukanta tana rage volume din,
Ya matsa ya
dago fuskarta yana kallonta,
Bata
kalleshiba ta cigaba da zubda hawaye,
Yana
nazarinta yace "cutie kifadamin damuwarki plsss banajin dadin kukanki
"cikin rarrashi,
Ta daga ido
ta kalleshi tana ajiyar heart tace "bakome kaina ne ke ciwo "
Ya
girgizakai kawai yafara share mata hawayenta da hannunshi sannan yace
"kishi ko cutie?"
Taki cewa
komi ya kwantar da kanta kan kafadarshi ya jinginar da kanshi jikin seat din
motar ya rumtse ido zuciyarshi na harbawa dasauri,
Bayan 3mnt
tanata ajiyar heart tadena kukan cikin jin tausayin kanshi yace "faseelat
meyasa zakimin haka? yakamata ace kina boye kishinki kefa kikace min bazaki
kishi da aisha ba yanzu me kike? Aisha ce fa ,aisharki haba for god sake ni
yazan da rayuwata, faseelat akwai kalubale da yawa akaina, kullum cikin tunani
nake taina zamfara fadawa aisha wannan batun, momy zata amince koko?ga shawarki
data addabeni inason aurenki nankusa na rasa taina zanfara komi ya jagulemin
hakanan kike ganina Amman ni nasan me nake ciki, yanzu bazaki temakamin ba ?ki
kwantar da hankalinki kicire kishinnan ko nasamu kwanciyar hankalin yin abunda
yakamata, saboda inkina fushi dani wlh duk tunani akanki yake tafiya "
faseelat ta
daga kanta daga kafadarshi tanajin tasayinshi ta saka hannunta cikin nashi ta
damke ya bude ido yana kallonta,
Tace
"kayi hakuri plsss bazan sake ba"
Yana ta
kallonta yace "yanzu haka zamuyi auren faseelat? I'm not going to take you
to somewhere agida daya zaku zauna ya kenan, I want to build a peaceful
family,idan kina haka yazaku zauna lpya keda aisha? Itama fa bansan ya zata
dauki abun ba fa "
Faseelat tai
fuskar tausayi tace "I'm really sorry nadena kishinka are you happy now?
"
Ya juyar da
kai yace "I'm not, ai bacewa nai kidena kishina ba, cewa nai ki rage ai u
have to hide it now "
Ta cire
hannunta daga nashi tace "naji nabari, kuma badole naji ciwo ba, nazo
kunbarni a palo kuna ciki kuna...... Sannan kunfito harwani kisss zatai maka
dan iskanci "
Yayi
murmushin takaici yace "to miye aisha cefa maman amira "yaida yana
dariya,
Ta harareshi
tace "nasan kunayi basekafada minba ai"
Yayi
murmushi ze kamo hannunta ta janye tace "kakaini gida ni "
yayi
murmushi "ke yarinya kincika wayau time dinda kinason kiji dadin hannu na
keda kanki kika rikoni nikuma in inaso seki hana? "
tai murmushi
ta rufe fuska tace "kuskure ne akasamu "
Yayi dariya
yana tada mota yace "inason irin kuskuren nan,"
yana hawan
titi yace "bari muje na kaiki kidanyo shopping ko se nakaiki gida "
Tace
"nide kakaini gida kawai banison shopping din "
Yace "I
insisted "
Tai shiru
yana tuki har suka isa big mall yayi parking ya fita ya budemata tafito suka
shiga ciki,
Duk yadda
yaso tadauki abunda takeso taki, sede shi yazabar mata kayan makeup da
different perfumes dasu kayan tea ,
Yaje yayi
payment suka fito suka kama hanyar gida, sunata labari kamar ba yanzu tagama
kuka ba,
Suna zuwa
kofar gidansu ya tsaya ya kashe motar ya kalleta yace "kigaidamin da kowa
se nazo gobe "
Tace
"tam Nagode hubby Allah yabiya maka bukatunka na alheri "
Ya lumshe
ido ya bude yace "inason adduarki kicigaba damin addua "
Tace
"karka damu ahakan bakomai bane akan wacce nakema aduk salla ta"
Yace
"thanks Allah ya amsa "
Tai murmushi
tafita,
Ya bude back
seat din ya dauko ledojin yaji da nauyi yace "muje narage miki aiki banso
ki expanding "yana dariya,
Tamai harara
irinta masoya ta juya sunatafiya tare har bakin kofar gidan ya mika mata yace
"bye"
Ta daga
mishi kai kawai ta shiga, yana juyowa abba naiso wa akan mashin,
Fahad ya
dakata har abba ya sauko ya zukunna har kasa ya gaidashi,
Abba ya amsa
yana kallonshi, sannan fahad ya tashi ya tafi,
Bayan abba
yashiga gida suna daki da ummi yace "anyi bincike kan yaronnan"
Ummi tace
"to lpy de ko? "
Ya
girgizakai yace "akwai matsala gaskiya ,wato shi mahaifiyarshi sun rabu da
babanshi da dadewa kuma ba rabuwar arziki ba, shi yataso ne awurin matar
babanshi, lokacin da babanshi na raye yahana mahaifiyar shi koda ganinshi
saboda wulakanta yaron da tayi lokacin tana neman Saki, yanzu da yamutu tanata
bibiyar yaron ya yafemata yaki ,saboda ancusa mishi kiyayyarta,yafison matar
babannashi akan mamanshi sannan diyar ita matar babanshi yake aure, kinga akwai
matsala kenan ace mutum na fushi da uwa, kuma yana tareda diyar ita wadda
yakeso kinga faseelat zatasha wuya ne, kuma bazata hada kanta da kishiyartan ba
tunda sunfi mu hali ganinake abun zezo da matsala, nima dazun alhaji ke fadamin
Amman yace wannan duk ba matsala bace tunda suna iya sasantawa da ita mamanshin
nangaba "
ummi tace
"a, a gaskiya ni dama banason gidan kishiyarnan, bare ita wannan da
yaruwarshi ce ,wlh da maganar da zanmaka ince kungama binciken ace yaturo dan
naga ita faseelat ta haukace kanshi yanzu ma daga zuwa unguwa ta dawo da
nikinikin kaya yasiyo mata "
Abba yace
"Allah sarki ainima mungaisa yanzu har Kasa ya zukunna ya gaisheni "
ummi tace
"ai yanzu sede ta hakura don abunnan bazeyiwuba"
faseelat
dake bakin kofar daki kan tabarma tana kwance duk tanajin abunda ake wufff
tatashi ta shiga dakin abba ta durkushe gabanshi tana zubar da hawaye tace
"dan Allah abba karku rabani dashi, wlh inasonshi ni aganina shi abun
tausayi ne, ansa mishi tsanar mamanshi kuma bayada wanda ze nuna mai gaskiya,
dan Allah abba kayarda in aure shi kodan na temaka mishi "
Daga ummi
har abba sukai kasake suna kallonta saboda mamaki, itako she don't care
batamasan kunya ayanayin da take ciki ba ,
abba yace
"faseelat karfa ai abunnan azo ana danasanin yinshi"
ta girgiza
kai "insha Allah abba baabunda ze faru "
Ummi
hannunta kan baki tana zaro ido tace "kajimin ikon Allah dama kina labe
kinajinmu kenan, kuma yanzu faseelat tunda kinfara soyayya kin tattara kunya
kin aje gefe kina ta zuba rashin kunya, bama agabana ba hargaban abbanku ko?
"
Faseelat ta
girgiza kai "ummi dan Allah kubari na aureshi "
ummi tace
"ahaf tunda kinji kingani ai shikenan Allah yasa alheri iyakar abunda zamu
ce kenan "
Abba yana
kallon faseelat yace "tashi kije "ta tashi tafita,
Ya kalli
ummi yace"mutayata da addua kawai Allah yasa hakan ne alheri"
hannun ummi
kan gemu tana mamaki tace "amin ya Allah" tana kadakai dan mamaki,
akan hanya
fahad se tunanin yadda yaga gidansu faseelat yake duk da ginin cement ne amma
ya tsufa, acikin ranshi yake shawarar canzamusu gida daga cikin gidajenshi,
Se marece ya
koma gida, kodayaje aisha batanan tafita, yakada kai kurum dama da mommy
takirata inde baya gida tafiyarta kawai takeyi sede ya samu batanan,
Se dare ta
dawo amira ahannu tana bacci ,yana cikin balcony ya taso ya amsheta suka shiga
ciki se akan hanyar shiga takecewa "mommy ce takirani anty kulsum ta haihu
shine muka tafi tundazu muna asibity se yanzu muka dawo ,ta samu baby boy
"
Yanata
tafiya yace "Allah yaraya "tace "amin"
Tunda
tashiga take ta kai kawo tai wanka ta
shige salloli,
shiko yana
saman bed yajawo computer dinshi yana aiki, yana cikin aikin faseelat ta turomishi
pic Data dauka da dayan color da yasiya mata ,ya bude pic din yana kallo rigar
is maroon irin robar nan ce irin kayansu na yan can tabi jikinta sosai ta mata
dasss kamar dan ita aka yisu ga pic din andauketa from head to toe ta dan juya
kadan wanda har hips nata ana gani,
ya kure pic
din da kallo yanajin many emotions, yana tunanin kila dan takarasa shi ta
turomishi pic din,
Yanata
kallon pic din bako kyaftawa gabadaya ya rikice hannunshi biyu adunkule akasan
habarshi,
Har Aisha
tagama sallolinta taje gaban mirror ta shafa perrfumes dinta tasaka rigar
baccinta da wando ta juyo tana kallonshi taga baaikin yakeba tunani ma yake,
yadda taga yakure system din da ido dukda bata cika bin aikinshiba amma yasa ta
zagaya ta bayanshi tai tsaye tana kallon computer din,
Abinda
idonta yagani ne ya tada mata hankali gabanta ya rika harbawa fat fat!!!
Jikinta
yadau rawa koina tafara ja da baya tana jawo numfashi da karfi,
Jin nishi
nishi yasa fahad ya juya yaga aisha nata kyarma tana ja baya,
Cikin tsoro
ya mike yana kallonta ,
Har takai
karshen bango tanajinta jikin bango ta zukunna ta dora hannu biyu tafasa
tsuwwar da fahad besan lokacin da yakai wurinta ba yariko ta yana "sorry
Aisha take it easy please "
Jikinta na
cigaba da rawa cikin rarrabuwar harshe tace "fa..fa....see.... Lat....
Ce..... Fa......A...com. ..pu.. Ter...dinKa.... KaKe.....
Kallon....pic......nata "tadora hannu abaki tana fiddo ido,
Ya rumtse
ido ya zukunna gabanta yahade hannu biyu yace "kiyi hakuri Aisha ki
saurareni "
Itako
kojinshi batayi tana ta tariyo maganganun faseelat, "harna fara son wani
daban , anty soon de zanyi aure nima nahuta dakirana jawara da kike "sune
maganganun datake ta tariyowa, that means tun tanada aure suke tare, kuma shine
Wanda zata aura.
ya jawota
jikinshi yana fadin "listen to me aisha "
Tai kukan
kura ta tunkude fahad daga jikinta tai waje da gudu tana kuka , yabita yana
kiran "Aisha wait plss kitsaya karkifita dare ne "
Koda yafita
har tabar gidn ko takalma babu bare dankwali,
Kusan karfe
10:40 tana fita tasamu mashin ta haye tana kuka da rawar jiki tafada mai
yakaita malali quarters ,
mashin na
ajiyeta ta dira tafara buga gate din gidansu da karfi tana kuka,
megadi yazo
yabude da katuwar gorar shi ahannu,
Tabanka
aguje ta shiga cikin gidan,
Me mashin ko
kotsayawa amsar kudi beba yajuya, don ya tausaya mata
Kannenta
biyu na kallo Tawuce su dagudu tafada dakin mommy, mommy na zaune tana waya kan
bed aisha tafada jikinta,
Jikinta na
rawa tace "mommy mommy kitemakamin faseelat ta cuceni zata auremin miji... ......"
tohwa ana
wata ga wata 🏃🏽♀
inga ruwan
comments woooo 🤣🤣🤣🤣🤣
Shalele
takuce fans🤗
[7/12, 11:01
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY
SHALELE*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN
WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven
No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of
our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
4⃣8⃣
*dedicated
to firdausi, F🧕🏼kinsanme? Inasonki sister😍, kina sona kinga ko dole naso ki hausawa na cewa kaso
me sonka,shiyasa nakamu over, fans kutayani son firdausi don nima inasonta,
tadamu Dani matuka da zanwuce 9am bana online seta kira taji ko lpya nake, I
love you F🧕🏼,my masoyiya*
Mommy tarika
kallonta hankali tashe takamo fuskarta tace "ban fahimta ba, ki kwantar da
hankali sosai kimin bayani"
Tana
sheshsheka tace "mommy yaya aure zeyi kuma kawata ce, wlh faseelat ta
cuceni ban cancanci haka daga gareta ba"
Momy tafara
tafi tana salati tace "nashiga ukku ni faiza, yanzu yazanyi ne? Ke dan
ubanki har wata kawa kikasamu wadda bansaniba? "
Ta daga kai
tana kuka tana jijjiga mommy tace "dan Allah mommy kice karyayi aurennan
wlh zuciyata bugawa zatayi, nide nashiga ukkuna faseelat ta gama da rayuwata
"
Mommy tace
"keda harkina da guarantee kan kawa? da har zaki saki jiki daita? To yanzu
gashinan de kinaso kijamin asara inyi renon banza, nasaki jiki zansamu kudi
Amman kinjawomin tsiya, kafin mahaifin fahad ya rasu ya mallaka mishi gidaje da
filaye da gonaki da bansan adadinsuba, su ramlat su ukku bazasu samu rabin
gadonshi ba shiyasa nasamu nahadaki dashi kinga komi de nawa ne akarshe Amman
kinyi sakaci zekawo wata ta ragemin lissafi "
Aisha tace
"mommy kihanashi plsss wlh bazan iya sharing dinshi ba da wata "
Mommy tace
"aiko sede ki hakuri sanin kanki ne nariga nasaba mishi da goyon bayanshi
akan komi, yanzu innace aa to matsala zaasamu saboda yana iya bijiremin gwara
na yarda din yafi "
aisha tafasa
kuwwa tadora hannu saman kai mommy ta jawota tana rarrashi tace "ki
kwantar da hankalinki diyata baabinda ze faru a aurennan kede kirika bin
shawarata sannan kirika fadamin duk abinda ake ciki "
Aisha ta
cigaba da kuka mommy nata rarrashi tace "dole ki hadiye kishinnan ki nuna
mishi kinason abunnan kinga zeji dadi yakara sonki kuma ko tazo ki kauda kai ga
alamuransu seki zauna lpya, inkika yi haka se yakara ganin girmanki fiyeda da
"
tana kuka
tace "mommy wlh bazan iyaba ni ina kishin mijina sosai bazan iya dannewa
ba "
Mommy tace "to
hauka zaki tayi duk kisure mishi, ?kowane namiji fa inde zaiyi aurennan seyayi
doki, kuma yanada damar auren mata hudu in yaso, kita hauka yadena sonki bahaka
kikesoba, kinade gani yanda nazauna da babanshi komi atafin hannuna "
Takara
volume na kuka "wlh faseelat setayi danasani inta auri mijina "
Mommy tace
"aure kam kamar anyi angama ne, kedai kinyi kuskure, yanda mazannan sukai
karanci bare naki da kowa zeso kikabari har tasanshi, kiyi hakuri kinji nasan
kome zanyi akai "
aisha takara
volume itafa inba auren akace anfasa ba bazataji dadi ba,mommy nata bada baki
Amman ina,
Jiki sanyaye
fahad yakoma cikin gida yana shiga amira tazo ta rungume tana kuka tana kiran
mommy ya dauketa yana rarrashi ya dauko Key yasaka riga suka nufi gidan mommy
tunkan hanya amira tai barci, shiko yanata sakesake,
Yana zuwa
yayi parking ya sabi amira awuya suka nufi ciki
Yana shiga
su sadee suka tashi sukai saman bene da gudu don sunajin kukan aisha su
azatonsu ko jibgarta yayi ,
Bedamuba ya
kwantar da amira kan kujera yana sauraron kukan aisha daga sama,
Ya kama
hanyar benen cikin sanyin jiki, dama yasan bazaa kwashe da kyau ba,
Mommy nata
bata shawarwari koji batayi tanata kuka ya shigo dakin, yana kallon fuskar
mommy yaga yanayinta ya zauna gefen gadon yafara magana "dan Allah mommy
kiyi hakuri bazan kara aurennan bane don inci mutuncin aisha ba, inason
yarinyar ne kawai"
Mommy fuska
a sake amma deep down tanajin zafi tace "rabu daita dana ai kai mijin mata
hudune, ni nagoyi bayanka kaje kayi aurenka karka biyewa Aisha kishine ya rufe
mata ido "
Yayi shiru
cikin jin nauyi zaaiwa diyarta kishiya Amman bata damu ba ya kalli aisha ya
sadda kai kasa,
Mommy tace
"gobe nidakai na zanje naiwa kawunka magana ayi komi in time akawo maka
matarka "
Yayi shiru
bece komiba sede yana jinjina irin son da mommy ke mishi, ya matsa ya rungumo
aisha jikinshi yana cewa "kiyi hakuri Aisha, zanyi aure ne kawai amma
ketadabance kinada special place in my heart, ki kwantar da hankalinki plss
honey"
Mommy na
zaune na kallo shiyasa aisha bata fizge ba daga rikon da yamata,
Tana ta kuka
taji hannun mommy ta tsunkuleta ta dago ta kalleta mommy tai mata alamun tai
shiru da ido,
Aisha tadan
rage kukan, mommy tace "kutashi kutafi Allah yamaku albarka diyana, kiyi
hakuri aisha kishi jihadin mata ne se andaure "
Ya mike tana
jikinshi yace "seda safe mommy "
Mommy tace
"ka kara bata hakuri plsss ka kuma hakuri daita har ta sakko "
Yace
"Nagode mommy "yanajin sonta da kaunarta yaja aisha sukafita,
Ya dauki
amira suka tafi gida,
Aisha
naganin amfito takara saka kuka hannuwa biyu saman kai tanayi tana dumumuwa
"ni nabani na lalace ni aisha, wayyo Allah na ancuceni an ci amanata
"
yana tuki
sede yajuya kai ya kalleta yana mamakinta wasu dumuwan dashi takeyi sam bata
bashi haushi ba har suka karasa gida,
Yana parking
tabude ta banka cikin gida da gudu, ya girgiza kai ya dauko amira ya medata
dakinta ya kulle yafito ya shiga dakin aishar,
Ya sameta
tana ta wurgar da pillows tana hauka, cikin rarrashi ya rikota cikin kwantar da
murya yace "Aisha plss stop all this kar kanki yayi ciwo, faseelat ba kowa
bace in zan kwatanta ta dake, inasonki sosai Aisha kuma u knew it ki yi hakuri
nasan namiki laifi plss pardon me my love "
Yazo ze
kaimata kiss ta kwace daga rikonshi tana kuka tace "ni zakuciwa amana? Ni
faseelat zataiwa haka after all I did to her? "
Taja tsokii
tai wurin mirror tabude Jakarta ta fiddo waya, yana tsaye yana kallonta ta
dannawa faseelat kira hannuwa na rawa,
Wajen 1am ne
faseelat tayi barci bata kashe wayar ta ba kiran aisha ya shigo, cikin magagin
bacci ta lalubo wayar takara akunne,
ganin
andauka aisha tafara balai tace "marar mutunci marar amana faseelat ni
zaki ciwa amana? Kirasa wanda zakiso se mijina? Dan kina diyar akuya ko azatona
ke diyar arziki ce ashe bansaniba da katuwar karuwa nake tare kinci amanata
kuma wlh bazan barki haka ba, kishigo cikin gidan se naci kutumar uwarki jakka
yar iska "
Faseelat
tuni ta wartsake tafara kuka cikin kukan take cewa"anty dan Allah kitsaya
ki saurareni kiji me zance "
Aisha tace
"bakida hankali da kike tunanin zan tsaya in saurareki karuwar banza
karuwar wofi me bin mazan mutane... "
Kafin taida
maganar fahad da kejin kalmar karuwar nan kamar ana zuba mishi wuta ya fige
wayar yanajin kamar ya kai mata mari,
Ta riko hannunshi
cikin kwaratsi take cewa "kabani waya ta kabani wayata in kara zagin
shegiyar can, yanzu daddyn amira ni zakaiwa kishiya? Nice fa aisharka ur honey
"
yazo ze
rikota tai kasan bene tana kuka ya zauna dabass kan bed ya dafe kai da hannu
biyu saboda tsananin sara mishi da yake,
Faseelat
najin aisha takashe wayar tafashe da kuka me karfi, ummi da jin maganar
faseelat tafito tai tsaye jikin window tanajin abinda aishar ke cewa,
ummi ta tura
dakin tashiga tace "ke dama kinsan matarshi ne? "
Faseelat ta
daga kai tace "eh inazuwa gidanta "
Ummi tace
"amma baki kyauta ba faseelat ai wannan cin amana ne, yakuna tare daita
kuma kizo ki auremata miji baki kyautaba gaskiya "
Faseelat
cikin jan numfashi tace"ni aganina kowa da yadda Allah yatsara haduwarshi
da wani, nita sanadiyarta ne Allah yasa nasanshi be kamata tayimin irin wannan
wulakancin ba, saboda banida niyyar cutar daita ko na aure shi, inaganin
girmanta bazan manta alherin da tamin ba"
ummi dake
tsaye gefen bed tace "to Allah ya kyauta, tundade kinji kingani aishikenan
amma kinde fara fahimtar yaki zakijeyi kenan, ita kuma bewar allannan kisamu
bayan kwana biyu kikirata kibata hakuri in Allah yasa tayi shikenan, "
faseelat ta
daga kai tana kuka, ummi namata kallon tausayi saboda batasan me diyarta zata
tarar ba tace "kidena kuka ki kwanta seda safe munyi maganar "
Faseelat ta
koma ta kwanta amma takasa bacci tanata tunani ta yanke shawarar gobe taje
tabawa aisha hakuri su dedeta,
Duk yadda
fahad yaso ya bawa Aisha hakuri taki hakura a karshe ya barta falon tanata
wurge wurge ya shiga dakin amira ya kwanta ya jawota jikinshi, tunani be barshi
bacci ba yana ta tunanin ita faseelat ya take ciki yanzu,
Se asuba
bayan yayi salla bacci ya daukeshi itako aisha tana gama salla ta dawo falo ta
zauna har tagaji da kukan sede azabar zafin da zuciyarta ke mata ta mikar da
kafa tadan kwanta itama bacci ya dauketa amma ba me dadi ba,
Tun asubar
farko faseelat tafito tana aiki ko tarage jin damuwa amma ina hankalinta yaki
kwanciya tanata tunanin miake ciki yanzu,
Ummi na
dakin abba dan befita da wuri ba,
Faseelat tai
wanka tasaka doguwar rigarta orange color tasaka farin hijab ta duba wayarta
karfe 9 dede ,batare da ta fadawa ummi ba tai wufff tabar gidan tanufi gidan
aisha,
Aisha cikin
dan gajeren baccinta taji karar door bell tana yamutsa fuska taje ta bude ,
Ganin
faseelat tsaye tai mutuwar tsaye tanajin kamar ta shakota ta daba mata wuka
kotaji daman abinda takeji,
Ganin tayi
tsaye tana kallonta faseelat ta kutsa kai ciki tana tunanin kila su dedeta, ta
zukunna gaban aisha kanta Kasa tace "anty nasan ni me laifi ce agunki dan
Allah kiyi hakuri bansan taina zan fara fadamiki bane tuntuni cewar muna
soyayya da mijinki....."
Bata bari
takara saba cikin tsawa tace "keeee dan uwarki harkin isa kifadamin kina
soyayya da mijina, karuwar banza kawai wato tunda kikaganshi kika like masa ko?
To ki san dasanin nidake har abada wlh nayi danasanin saninki a cikin rayuwata
"
Faseelat
tafara hawaye tace "anty kitsaya ki saurareni plsss "
Aisha tace "kimaza
kibarmin gida wlh kafin inci ubanki "
Faseelat ta
dago zatai magana aisha ta rufeta da bugu ta koina, jikake fas! tab!duf!duf ,
Jin Azaba
faseelat tafara ihu, cikin barci yaji ihu, ya farka zaune yakasa kunne inyaji
da kyau muryar faseelat ce ,yace "oh my God "ya fita dasauri,
Tunkan bene
ya leko yaga yadda aisha tahaye faseelat tana jibga ya kwatsa tsawa
"keeeee aisha"
Koji batayi
tana ta jibgar faseelat cikin sauri ya sauko daga kan benen ya janye aisha ya
dauketa da mari a duka kumatunta, jikake tasss! Tassss,
Aisha ta
dafe duka kumatun da hannu biyu tana kallonshi dan saura kirisss ta kife
awurin,
Cikin sauri
ya tada faseelat tana ta kuka ya rungumota jikinshi yana.........
*inajin
dadin comments naku jiya anyi ruwan comments godiya lodi lodi, nima inasonku
masoyana*💋💋
Wani sabon
salo har team aisha ke da kwai yanzu 😂🤔
Team fahad 💋
Team
faseelat 😘
team khalil
bodari😂
Team Aisha 😍
Yayin team
team ake saura team hajiya da team jamila 😂
luv u always
my fans dake koina 🤗
[7/12, 11:01
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
We are
bearer's of so golden a pen🖊
We write
assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative
golden pen🖊
Be hold our
words
A product of
our pen🖊
Savour our
words
For it will
cause you no pain.✍🏽
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
4⃣9⃣
*dedicated
to those lovable group's*👇🏾
*RAGGON MIJI
FANS*
*RAGGON MIJI
FANS 2*
*RAGGON MIJI
FANS 3*
*UMMYN
YUSRAH NOVELS GROUP*
*MUKARU DA
JUNA BY MOMYN SAUBAN*
*NOVELS
ZAFAFA BY DR FATEE*
*MY FORUM
GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*
*MOMMY'S
NOVELS GROUP BY SHALELE*
*THIS PAGE
IS ALL YOURS FRIEND'S ACIGABA DA COMMENTS KAWAI*⛹🏻♀
*MANZON
ALLAH (S. A. W) YACE :-lalle Allah ya rubuta kishi akan mata, da jihadi akan
maza wadda tai hakuri acikinsu tana da lada kwatankwacin wanda yayi shahada.*
Yanajin wani
irin ciwo a zuciyarshi, jintana ta kuka ya dagota yafara duba jikinta duk yayi
ja abunka da farar fata ga gashinta duk Aisha ta yamutse shi cikin jin tausayi
yakara rungumeta yana shafa bayanta,
Kwata kwata
kuka yaki zuwa ma aisha tazuba mishi ido tana ta kallonshi ganin yadda ya
kwakume faseelat kamar ze medata ciki yasa ta sauke hannuwa daga kumatunta tai
hanyar kitchen da gudu ko seconds goma baaiba ta fito da sharbebiyar wuka
ahannu tai kukan kura zata sokawa faseelat a baya, fahad yayi sauri ya rike
kaifin,
Aisha tafara
jujjuya wukar tanaso ta kwace ta sokawa faseelat shi kuma ya rike kuma still
yana rungume da faseelat daketa kuka,
Dandanan
jini yafara diga Kasa kan farar hijab din faseelat, ganin jininshi yana zuba
amma yaki sakin wukar Aisha ta saki wukar ta dora hannuwa biyu akunne ta kwara
baki ta saki kuka tai saman bene da gudun tsiya,
Fahad ya
Saki wukar tafadi kasa ya bude tafin hannunshi yana kallon yankan da ke jiki,
Faseelat ta
zare jikinta tana kallonshi cikin tausayi ta duka ta dauki kallabinta dinta ta
kama hannun fahad tana nannada mishi tana kuka, shi ko kallon fuskarta kawai
yake yana ganin wautar ta na zuwa gidan a yanzu,
Suna haka
aisha tafito tana kuka sabe da amira awuya tafita tabar gidan, duk sukabita da
ido,
Seda tafita
faseelat ta medo kallonta gareshi tana sheshsheka tace "I'm sorry bansan
haka anty take ba nazata zata saurareni ne dana sani banzo ba "
Ya riko
fuskarta da hannu biyu yana kallon cikin idanunta yace "aisha zata iyayin
fin haka, karki sake irin gangancinnan cutie yanzu da bani nanfa? Wlh aisha har
kashe ki tana iyayi saboda gabadaya ta haukace,"
Ya riko
jikinta "jibo yadda taimiki da jiki"
Faseelat
takara zubo da hawaye dan ta jibgu ba karya ,
Ta riko
hannunshi tana fadin "it's hurting ko? "ta kalleshi cikin jin
tausayi,
Ya rungumota
jikinshi yana kwantar mata da gashin kanta yace "it's not idan nahadashi
da zafin dukanki da Aisha tayi "
ta kwantar
da kai kan kafadarshi tana hawaye,
Yana ta
shafa gashin kanta tai breaking hug din tace "zan tafi gida "
Ya jawo
hijab dinta da take dauke da drops na jininshi yasaka mata, sannan ya kalli
jikinshi daga shi se boxer ya dago ido yace "bari na dauko key na kaiki
"
Ya juya ya
haye bene few minutes ya dawo cikin jallabiya da keys a hannu ya kamo hannunta
suka fito daga cikin gidan ya bude mata
motor ta shiga ya zagaya yaja sukabar gidan ,shide baba tsoho yanata kallon ikon
Allah yadda yaketa ganin Aisha na ficewa da kuka yasan akwai matsala,
Suna kan
hanya yana tuki da hannu daya hannunshi daya kan cinyar faseelat, tunda suka
fito take ta kara zubda hawaye,
Ya kalleta
ya meda kai kan titi yace "kiyi hakuri cutie ki dena kuka ,Aisha bata isa
ta hanani aurenki ba inasonki sosai fiyeda yadda zaki harsaso, ki kwantar da
hankalinki aisha zata sauko insha Allah "
Faseelat
zuciyarta zafi kawai take yadda Aisha ta wulakantata ga zafin yankan da taiwa
fahad da takeji kamar ita akaiwa,
Ta Kalli
hannunshi dake kan cinyarta
Tasa hannu
ta rufe fuska jin kukan da ya taho mata tafarayi tana jan numfashi,
Fahad ya
dauke hannun daga kanta ya shafi kanshi zuwa sajenshi ya fitar da iska me zafi
daga cikin bakinshi gabadaya Sun caza mishi kai yace "cutie ya kikeso nayi
ne? Yanzu kina ganin zan bari kitafi gida kina kukannan? Kiyi hakuri
plsss"
Ta daga kai
ta jawo hijab dinta tafara share hawayen dake zubomata tana sharewa wasu na
zubowa,
Ya girgixa
kai ,har suka kawo kofar gidansu, Ta bude zata fita yace "kode nakaiki
asibity ne ko akwai inda ke miki ciwo? "
ta girgiza
kai cikin muryar kuka tace "thank you "ta bude tafita ta shiga gida
dasauri,
Yakara
murmuxa gashin kanshi kanshi na zafi sannan ya tada motar ya nufi gidan mommy,
Faseelat
dasauri ta shiga gida ummi da tundazun ta duba bataga faseelat ba ta ga wulgin
faseelat dasauri tafito daga dakin abban tabi bayan faseelat da kallo kayan
jikinta a cumumuye ga jini saman kan hijab din zuwa kasan hijab din,
Hankalinta
ya tashi tabi bayan faseelat, lokacin faseelat ta yaye hijab din tahaye can
karshen gado ta hade kai da gwiwa tana kuka,
Ummi ta
shigo dakin tana kallon gashin kanta cumimiye tace "kee daga ina kike
"
Faseelat ta
dago tana raba ido tafara nazarin me zatacewa ummi,
ummi tace
"dan ubanki ba magana nake miki ba? "
Faseelat ta
fara yarfa hannuwa tana kuka,
cikin zafin
rai ummi ta haye kan gadon ta shakarota cikin tsawa take cewa "bazaki
fadamin ba ne dan ubanki daga ina kike? "
Abba yafito
daga daki jin kakari da fadan ummi yayi sauri ya shiga dakin ummi ganin ta
shakare faseelat yayi sauri ya je ya janye faseelat din yana kallon ummi yace
"haba asiya kibari mana aibata haka zaki tambaye ta ina tajeba "
Ummi tace
"alhaji yarinyarnan harta san
takwasa taje wurin saurayi? Yaga ma tumurmusarta ta dawo tana kuka, jibi hijab
dinta "ummi tajawo hijab din tana nunamasa tace "duk jinine jiki wlh
faseelat ta iskance tunda har taiya bashi kanta kafin aure "
Faseelat ta
dago tana zare ido jin abinda ummi ke cewa,
abba cikin
mutuwar jiki yakebin faseelat da kallo duk ta harmutse,
ummi tace
"nikam nagaji alhaji dan Allah kasamu yaronnan kace ya turo tunkan ta jawo
mana abun kunya"
Abba bece
komi ba yabar dakin ummi tazo zata kawowa faseelat bugu faseelat ta kauce tana
zare ido tace "wlh ummi banyi komi ba, naje bawa anti hakuri ne, shine ta
yankeshi a hannu amma wlh baai komi ba "
Ummi cikin
rashin yarda tace "gafara can da Allah ni zakiwa karya, ko ni makauniya
ce? ke kikasani dan wlh ko aurenki yayi bazaki wata daraja ba sakarai kawai yo
miki so hauka ne da zaki je kibashi kanki, kin kyautawa kanki ai "
Fuuu tabar
dakin faseelat ta fashe da kuka ta jawo pillow ta danne kanta dashi ta cigaba
dayi,
ummi nafita
bataga abba ba har yabar gidan takoma dakinta ta buga tagumi zuciyarta na zafi,
tundazu maganar da sukeyi da abba akan faseelat ne don yaji abinda yafaru jiya
Sunata neman mafita sega sabuwa ta billo,
Aisha
nashiga cikin gida takara sakin kuwwa da mommy dasu ramlat sukayo waje, sadiya
tai sauri ta amshi amira daga hannunta,
Aisha ta
rungume mommy tana kuka,
Mommy tace
"wato Aisha bazaki bi shawarata ba ko? Yanzu mi yakawoki da
safennan?"
Aisha na
kuka tace "faseelat dince wai tazo bani hakuri shine nahauta da duka ina
cikin dukanta shine yazo ya mareni shine na dauko wuka zan soka mata shine
yarike da hannunshi duk yaji ciwo ahannun "
Hjy tace
"wato de bakijin magana ta kenan ko? yanzu da kin kasheta fa? Kema ba
barinki zaaiba, nace kiyi hakuri kibar lura da abubuwansu kinki, inaji miki
tsoron ya sake ki dan masu irin wannan haukan da saki suke karewa, kinga
shikenan se ita wasila take kowa tasami yadda take so"
Aisha tace
"wlh bataisa ta rabani dashi ba "ta cigaba da kuka,
Ramlat dake
gefe tace "kinyi dede anty gwara da kika ci ubanta da kyau "
Mommy ta
banka mata harara tace "tashi kiban wuri "
Ramlat
tatashi tabar wurin dama sadiya bata zauna wurinba tunda ta amshi amira ta wuce
daita ciki ta kimtsata,
Mommy ta
medo hankalinta kan Aisha taja ta tazaunar daita kan cushion tace "haba
Aisha inafada miki abinda yakamata kiyi kina kaucewa, kiyi hakuri kibari ayi
auren karkimanta fahad a tafin hannuna yake ya daukeni tamkar uwa, ba abinda
waccan zata fiki awurinshi inde zakibi shawarata "
Aisha takara
saka kuka mommy nata ban baki amma taki denawa,
Seda fahad
yafara zuwa hospital akai mishi dressing sannan ya taho gidan mommy,
Yana shigowa
ya gansu main pallow yaude fuskar mommy ba walwala dan taji zafi da ya mari
diyarta akan wata,
Yazo ya
zauna gefen kujera Aisha ta dago ido tana kallon hanninshi da bandage ta cigaba
da kuka kanta kan cinyar mommy,
fahad yace
"Aisha kiyi hakuri kizo mutafi gida banso na dakekiba "
Aisha batace
komi ba mommy na kallonshi tace "inaganin kabarta anan ta danyi kwana biyu
tadan samu natsuwa sannan se ta koma don naga duk tafita hayyacinta, kayi
hakuri daita da duk abinda zatayi anan gaba, nide namata duk nasihata taki ji
"
Fahad
gabanshi ya fadi don be tunanin zeiya 2days batare da matarshi ba wannan nema
yasa yake tafiya daita duk inda zashi,
Cikin rarrashi
yace "Aisha kiyi hakuri mukoma gida, kinsan bazan iya kwana nikadaiba
"
Ta dago
fuska ta watsa mishi harara ta meda kai kan cinyar mommy,
Mommy ta
canza maganar tace "dama inadawowa daga gidan kawunku se gata ai naso
nakiraka tazo ta hargitsamin lissafi, naje nasameshi munyi magana yace kaje
kuyi maganar kasameshi a office "
Aisha
tatashi ta haye bene dagudu jin abinda mommy tace
Fahad Yace
"Nagode mommy bari naje nasameshi "
Ya tashi
yafita yaja motar zuwa gidan kawunshi rabiu,
Yana fita mommy
taja tsoki, tace "dole fa intashi tsaye kar abinda na raina yazo yafi
Karfina "
Fahad har
cikin office din alhaji rabiu ya shiga ya zauna suka gaisa alhaji rabiu yace
"danbaba mommynka tazo mun da maganar kanaso ka kara aure, naji dadi sosai
ka girma kazama babban mutum ai karin aure sunna ce kuma mutum nakara
girma,sede bata fadamin gidansu yarinyar ba nace ta turoka muyi maganar"
fahad yayi
murmushi yace "Daddy sunanta faseelat gidansu a kofar durbi yake bazawara
ce babanta sunanshi alhaji maaruf "
Alhaji rabiu
yayi dariya yace "ai zawarawannan ma sunfi hankali da dadin shaani yanzu
yaushe ka ke ganin zanje na musu maganar mommynka tace bataso bikin yafi wata
amma inaso naji ta bakinka "
Fahad yayi
dariya yasan kawunshi dama da barkwanci yace "yau nikeso inde akwai damar
hakan, kuma su zasu zabi tym sede banson komi daga garesu kuma inaso ayi komi
kamar auren budurwa "
alhaji yayi
dariyar manya yace "to maganar kudi fa? "
fahad yace
"zan rubuta maka chek kaje kacire yanzu de kafara zuwa tukun, anjima zan
kawomaka kudin "
Alhaji yace
"to yayi Danbaba Allah yasa ayi damu "
Fahad yace
"amin se nazo anjiman ya tashi yafita "
Shiko abba
gidan baba babba yawuce dan suyi shawara dan bayayin komi seda shawarar shi,
bayan an
mashi iso ya shiga alhaji yace "lpya kake naganka somehow kamar kana cikin
damuwa "
Abba yace
"tunda safe asiya tazo takecemin bataga faseelat ba se yanzunnan gata
tadawo jikinta duk jini wai taje wurin yaron sunyi lalata inaga, ni tundazunma
muna ciki muna tattaunawa da ita akan batun saboda jiya matar yaran takira ita
faseelat taci mata mutunci d daddare har mungama yanke shawarar tirsasata ta
rabu dashi sega wannan abun "
baba babba
yace "subhanallahi ashsha abu be dadi ba "
abba yace
"shine nayi shawarar fadama yaron ya fito amma yakace? "
Baba babba
yace "hakane dede ayi mishi magana yafito inda gaske yake, tunda gashi har
yayi mata fyade, tunda ai tataba aure this means dakarfi ya kwata "
abba yace
"to Allah masani nima abun ya dauremin kai amma tunda tana sonshi zanmasa
magana yafito ayi musu auren suje can su cinye kansu tunda da kafarta tabar
gida ai "
Baba babba
yana jimami yace "Allah ya kyauta "suka cigaba da labari, sannan
sukai sallama abba yawuce wurin kasuwancinshi.
Kafin sha
biyu zazzabi da ciwon kai me zafi ya rufe faseelat, ummi Takoma dakin da niyyar
takara cin ubanta ta sameta cikin bedshit dukunkune taja tsoki tafita tana ta
maganganu ita kadai ta dora bagaruwa da karamfani da dankumasu da ganyen
magarya saman wuta ta dahu sosai ta tace
ta cika uwar robar wanka takai toilet tazo ta yaye zanin gadon da faseelat ta
rufa dashi tace "kitashi ki tube muje nagasa miki jiki in Iskanci dadi ne
gobe seki kara zuwa sakarai wadda batasan ciwon kanta ba, "
Faseelat
dakyar jikinta yayi tsami ta mike zaune tafara jijjiga kai, zataiwa ummi
magana,
Ummi tace
"karki cemin komi anan kitashi ki abinda nace "
faseelat ta
sunkuyar da kai cikin tausayin kanta ta tashi ta daura zane tana dafa bango
zata fara tafiya ummi ta kamata tajata har cikin toilet ta zame mata zane cikin
bacin rai tace wa faseelat ta shiga ciki,
Faseelat
tafara matso kwalla ganin yadda ruwan ke suraci,
Ummi ta daka
mata tsawa jiki na bari ta shige ta zauna ciki tanata cije lebo Tana rumtse ido
saboda zafi.
Bayan wani
lokaci
Ummi tajawo
karamin towel ta rika tsomashi tana mammatsa wa faseelat jiki tanayi tana mata
fada hawayen azaba yarika wankowa daga idon faseelat .
Team
faseelat kuje ku fadawa ummi ba abun bane tukunna 😂
all teams
ana tare 💋
[7/12, 11:01
PM] Maman Mamy: ➰➰➰➰➰
*RAGGON
MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELENKU)*💃🏼
✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
We are
bearer's of so golden a pen🖊
We write
assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative
golden pen🖊
Be hold our
words
A product of
our pen🖊
Savour our
words
For it will
cause you no pain.✍🏽
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
5⃣0⃣
*🎶🎶ashe haka soyake shiga zuciya
yake,yasamu wurin fake cireshi wuya yake 🎻🎻🎸araina kena rike ,kimance komi kirike, koina kin
mallake, nakine amshi kirike🎼this page is for you lady my habibaty Nagode da alherin da kikamin
Allah yakara budi, thanks once again lady*
*Dedicated
to lady*😘😘
Ummi nagama
gasa mata taja tsoki tace "shasha kawai seki tashi ki wankan abinda kukai
kizo ki amshi magani "
Tafita tabar
mata toilet din, faseelat ta rufe ido da hannu daya tana kuka, ranta na mugun
baci idan ummi taimata mummunan zato ,bare na yau da har abba seda yaji, ta
share hawayenta tafito tai wanka saboda ruwan da ummi tai mata gashi sunyi duhu
dan haka tasaka soso da sabulu ta wanke jikinta ta fito ta koma daki tasamu
tasaka vest ta koma ta kwanta,
Wajen 2:00
ummi ta dawo da abinci da paracetamol and ibuprofen tana kallon ta tace
"kitashi kisha magani seki koma ki kwantan"
Faseelat ta
tashi zaune tana yamutsa fuska tai spoons biyu na jelop din pasta din ta dauki
maganin tasha, duk ummi na tsaye na kallonta ta koma ta kwanta,
Ummi tadade
tsaye tana kallonta sannan ta dauki plate din tafita,
Karfe 3:00
abba ya dawo, bayan ummi takawomishi abinci yaci yake bata labarin yadda sukayi
da baba babba,
Ummi tace
"ai gwara dakamishi maganar dan faseelat tayi nisa inajin yadda takeson
yaran nan koni bataso haka "
Ana haka
akaiwa abba sallama ya tashi ya fita, ganin sabuwar fuska dabe taba ganiba
sukai musabaha da alhaji rabiu,
Sannan
alhaji rabiu yace "nasan baka sanniba nine kanin mahaifin fahad yaron dake
neman yar wajenka, nazo ne neman izini muzo neman aurenta "
abba
yace"to alhamdulillah sede banine madaurin aurenta ba, don haka zan baka
number din yayana shi medaura mata auren se kuyi magana dashi"
Alhaji rabiu
yace "to masha Allahu badamuwa "
abba yabashi
number din baba babba tareda yimishi kwatancen gidanshi,
Alhaji rabiu
gidan baba babba yawuce sukai kicibus kofar gida dede shi kuma ze fita, bayan
Sun gaisa yafadi abinda yakawoshi, baba babba yace "bamatsala zakuiya
turowa amma zuwa gobe don zan danyi tafiya zuwa niger,"
Alhaji rabiu
yace "alhamdulillah haka ma yayi insha Allah munanan zuwa goben"
Baba babba
yace,"Allah yakaimu lpya "
Alhaji rabiu
yace "da karfe nawa zamuzo?"
baba babba
yace "zuwa de 10 to above"
Alhaji rabiu
yayi godiya ya tafi,
Fahad bayan
ya bar wurin alhaji yawuce gida ya kimtsa yafita aiki, zuwa 3 ya dawo tunda ya
shigo gidan yaji gidan ba dadi, yanata kallon falon da yanzu amira nanan na
wasa, tunanin Aisha yafado mai da yanzu tazo ta tarbeshi ,ya samu kujera ya
zauna ya fiddo waya ya kira Aisha tana ta ringing taki dagawa, har ta tsinke ya
ja tsoki besan haka aisharshi take ba sedaga jiya zuwa yau,
Ya tashi ya
haye sama ya watsa ruwa yayi sallah, ya shiga kitchen ya hada ruwan tea ya dawo
dashi ahannu da snack ya zauna yana ci yana latsa waya ya shiga gallery ya
latso pics din faseelat yana binsu one by one yana kallo besan meyasa ba ko
kallon pic dinta kadai yayi seyaji yana samun natsuwa sosai,
Aje tea din
yayi dukda bawani abu yaci ba rabonshi ma da abinci tunjiya amma yakasa shan
tea din saboda rashin kwanciyar hankali,
Yayi dialing
number faseelat yanabin screen din da kallo yaji tana kashe abun yabashi mamaki
jin wayarta kashe ya tashi yakoma bedroom yana aiki da system dinshi yaji
yanajin bacci ya kwanta ,yana baccinshi har 4:30 sannan yatashi yana duba agogo
yayi sauri ya tashi ya shiga shaf shaf yayo alwala ya dawo ya kabbara salla ,
aisha ko tasha kuka har tagaji, mommy de
batako leko taba tunda batajin magana ta shareta,
ramlat
tashigo dakin tazauna gefen Aisha tace "anty maganar da mommy ke fadamiki
fa gaskiya ne, yanzu an waye kishi da kissa ake baa fitowa aita haukannan nide
kinmun dede da kika jibgi shegiya Amman tunda kin rage zafi seki hakura kinga
har mommy tayi fushi tafita har karki ,kiyi yadda tace kurum tun kafin asamu
matsala dan kinga fayanzu har marinki yayi akanta nangaba Allah abinda yafi
mari ze miki, kirika daurewa de hakanan"
Aisha tana
kallonta tace "yanzunnan yaya har seya iya kwana da wata baniba ?"
Ramlat tace
"namiji nefa, cabb bare yaya da dama can beda wata kunya sosai, kinagani
agabanmu se ya rungumoki ko yamiki kiss fa ,aikede ai shaani kawai "
Ramlat
tacigaba da dorawa Aisha darasi, tana budurwa amma ba makircin da bata iyaba
don tafi aisha wayau,
Har marece
fahad nata trying number faseelat amma bata shiga duk se hankalinshi ya tashi
ya rasa me zeyi,
Itakuma
faseelat jikinta ne yayi tsanani dan amai tarika yi ma daga baya, ummi duk ta
rude ta dawo jinyarta,
Da daddare
fahad yaje gidan alhaji suka zauna alhaji yafada mishi yadda sukayi yace
"yanzu de in Allah yakaimu gobe zamuje nida su alhaji yunus "
Fahad yace
"Nagode daddy ga kudin nama cirosu daga banki one million kudin neman
auren se 200,0000 taka "
Alhaji yace
"to godiya nake insha Allah goben zan nemeka idan mundawo "
fahad
yatashi yafita cikin farin ciki, koda yakoma gida yata kiran faseelat amma
akashe itako wayar har ta mutu saboda rashin caji da bata saka ba,, ya hakura
ya dena kiran yanajin ba dadi dan yariga ya saba da jin muryarta, ya danyi aiki
a computer shi ya kwanta da niyyar gobe zeje gidansu faseelat tunda wuri ko
hankalinshi ya kwanta, yadade da kwanciya amma yakasa barci, gabadaya desire ta
hanashi baccin he's missing Aisha yanata juye juye har kusan 2 nadare yatashi
ya jawo laptop dinshi ya cigaba da aiki saboda ta dauke mai hankali,
Wan safe da
karfe 10:30 su alhaji rabiu su ukku sukaje nemawa fahad auren faseelat, baba
babba ya karramasu sosai sannan suka mika mishi kudin a leda 1 million cifff,
batare da alhaji yasan adadin kudinba yace "faseelat deba budurwa bace don
haka base kunkara ba kanku wahala ba munbashi ita idan kun shirya nan da 1
month ma seayi biki "
Alhaji rabiu
fuska a sake yace "shi yaron yace bayason amata komi zeyi duk wata hidima,
inde babu damuwa alhaji munason a ragoshi ya koma 3wks "
Alhaji babba
yace "ba matsala mu ashirye muke Allah yakaimu nanda 3wks din Amman muma
iyaye zamuyi mata abunda yakamata ace munyi"
Su alhaji
sukayi godiya aka rufe taro da addua aka tashi bayan ansaka rana nanda 3 wks,
fahad ko se
10 yatashi ya kimtsa cikin sauri ya kama hanyar gidansu faseelat yana kan hanya
ne alhaji rabiu ya kirashi danhaka ya juyar da motar zuwa gidan kawunnashi,
Yana zuwa
yakirashi alhajin ya fito a harabar gidanshi, suna kan resting chair alhaji
yace "to alhsmdulillah yanzu de faseelat ta zama taka, munje munyi magana
da iyayenta sunbaka ita kuma sunsaka ranar aurenku nanda 3wks"
Fahad ya
rumtse ido yanajin mugun dadi na ratsa dukkan gabar jikinshi, ya bude ido ya
Saki kayataccen murmushinda besan yayi ba ya kamo hannun alhaji yace
"Nagode daddy I'm very proud of you ,naji dadin wannan labari sosai da
sosai "
Ya saki
hannunshi ya fara shafar sumar kanshi da ya saba,
alhaji yace
"badamuwa danbaba, yanzu seku fara shiryeshirye kafin lokacin "
fahad yayi
zumbur ya tashi tsaye yanzu ba abunda yake son gani sama da faseelat yafada
mata wannan gud news din, ya kalli alhaji yace "daddy zantafi semunyi waya
thanks you so much"
alhaji yayi
murmushi ganin irin farin cikin da fahad ke ciki yace "welcome son "
fahad ya
juya ya fita daga gidan ya shiga mota ya kama hanyar zuwa gidansu faseelat
cikin farin ciki.
Yana zuwa ya
bude mota ya fito don samun yaronda ze tura yakira mishi ita don haryau wayarta
kashe take,
Sega Mubarak
yafito daga gidan fahad yayi sauri ya rufe motar ya karasa kofar gidan yacewa
Mubarak yakira masa faseelat,
Mubarak yace
"yaya batajin dadi tunjiya bata lpy "
Fahad ya
zaro ido ya dafe kai yasan bakomi yaja ba se dukan da Aisha ta mata, ya dafa Mubarak yace "tana gidan ne?
"
Mubarak yace
"eh dazun suka dawo daga asibity "
Fahad yace
"to kashiga kacewa ummi fahad zeshigo gaidata kaji? "
Mubarak ya
gyada kai ya juya cikin gidan, fahad ya fitarda iska daga baki ya cusa hannaye
cikin aljihun wandon,
Mubarak
yashiga ummi na cikn aikinta na yau da
kullum Mubarak yafada mata abinda fahad yace ,ummi tace "to jira karka
fita bari na saka hijab na kimtsa waccan tukunna, aibawani gaidani dayazoyi
faseelat de yazo gani yazo duba barnar
da yayi "
Ta juya ta
shiga daki ta sako hijab dinta ta shiga dakin faseelat tana barci ko hijab da
suka dawo daga hospital bata cireba ta kwanta,
ummi tafita
tacewa Mubarak "jekace ya shigo "
Mubarak
yafita har lokacin fahad na tsaye yace mishi ya shigo, fahad ya taka zuwa cikin
gidan ,
Da sallama
ya shiga ummi tafito ta amsa ta masa iso zuwa dakinta, tana kara kallon
kyawunshi ya shiga ya zauna akasa ya tankwashe kafa daya dayar kuma ya tsaidata
cikin sanyin murya yace "ina wuni"tareda sunkuyar da kai,
Ummi
tace"lpya lau ya iyali? "
Yace
"alhamdulilah ya me jiki? "
ummi tace
"dasauki "
Yace
"Allah yakara sawwakewa, ayi hakuri ummi haukansu ne na mata bana kusa
lokacin da abun yafaru "
Ummi na
kallon hannunshi dake nannade da bandage tace "ai bakomi Allah ya kyauta
gaba "
Cikin jin
nauyi yace "zaniya ganin faseelat din? "
Ummi tace
"eh bismillah "tatashi ta fita,
ya tashi
yabi bayanta,
Ummi ta
shiga dakin faseelat ta dan bubbuga gefen gadon faseelat ta bude idanunta da
sukai ja ta kalli ummi, ummi tace "ga fahad nan ze shigo ku gaisa "
Ummi na rufe
baki fahad ya shigo dakin faseelat tafara kallonshi daga Kasa zuwa sama tana
akwancen yana sanye da white shirt da golden trouser,
shima
kallonta yake tunda ya shigo room din fuskarta kadai yake iya kallo duk tayi ja
saboda kuka da yar ramar datayi daga jiya zuwa yau,
Ummi na
gefe, fahad ya tsaya daga nesa yana kallon faseelat baruwanshi da ummi da
takafa ta tsare yace "cutie ya jiki? "
Tadan Saki
murmushi kawai yace "I'm sorry "
ta lumshe
ido tabude alamun OK,
ganin ga
ummi tsaye yace "ina wayarki I have call you several times "
murya dishe
tace "banida chargy "
yace
"alright Allah yabaki lpya "
yacewa ummi "Allah yabata lpy "
Ummi tace
"amin "
Ya juya
yafita,yana fita ummi tace "Ashe de faseelat bakida hankali wani lokaci
idan kikai abu se inga kamar kece yar farin, inba rashin wayau ba ki kwasa ki
tafi gidan ta dankina sakarai? To Allah yatemakeki dan wlh inda nice ko
fuskarki bazata ganu ba "
Faseelat
lumshe ido kawai tayi, kashi biyar na ciwonta ya tafi taga habibinta da kuma
gaskiyar da ummi ta gano,
fahad
nashiga mota ya dauko power ban ya ba Mubarak yakaiwa faseelat tareda bashi
2000, Mubarak ya amsa ya shiga cikin gidan,
Yashiga
dakin faseelat ummi nata surutu ya mikawa faseelat power ban din, Ta mike zaune
dasauri kamar ba Marar lpy ba ta dauko wayarta ta jona chargy, ummi tace
"hmmmm Allah ya kyauta "tatashi tabar dakin saboda takaici,
Faseelat
takoma ta kwanta bayan ta saka chargyn danba warkewa simul tayi ba,
Fahad bebar
kofar gidanba ya dauki wayarshi yakira daya daga cikin yaran dake aiki a plaza
dinshi yace mishi yana bukatar engine good quality kuma ai masa full tank, da 2
cartoons of peak milk ,2 cartoons of maltina kwalin holandia ya fadawa yaron
address din gidnsu faseelat,
sannan ya tada mota yana tuki Ahankali yana ta
tunanin faseelat ya kama hanyar gidan mommy.
No comments