TARAYYA 25-26
Page 25
Haske writers association +
Abu 'daya tasani shine tana
tsananin qaunar rumanah kamar itace ta haife musamman a yanxu datake hango
soyayyarta mai tsanani a idanuwan Maheer 'dinta saidai duk wannan qaunar da
yardar zata rushe tazama qiyayya da tsana mai tsanani idan sirrin rasuwarsu
asma'u da bulama ya bayyana ga rumanah abinda bazatasoba kenan. 3
Qarfe goma da mintuna goma
sha biyu suka farka yatashi zaune tareda tayarda ita zaune yana gyara mata
gashinta daya barbaje.
Kallonsa tayi tareda sakin
kasalallen murmushi
Ya shafi gefen fuskarta
tareda bude baki yace,
Yaya?
Lumshe ido tayi cikin laushin
murya tace,
Yayi sauki yanxu banajin
ciwon kan.
Lumshe ido yayi tareda
jinjina kai kafin yakalli agogo yace,
Ya salam" yana sauka
daga kan gadon.
Tare suka shiga toilet din
dakinta sukayi wanka Wanda yadaukesu dogon lokaci sbd tsayawa shiririta.
Koda suka fito kan cinyarsa
ya zaunar da ita tana goge masa ruwan jikinsa yana kallon gashinta dake 'digo
masa ruwa sbd wasan dasukai acikin bathtub yasa dole suyi wankan tsarki.
Riqo hannunta dake goge
gashinsa yayi tareda Shafo gashinta har zuwa fuskarta ya zarce cikin towel
dinta ya shafo cikinta dake lafe yana kallonta cikin wani irin yanayi da
galabaita da zuciyarsa ke ciki.
Daqyar ya bude baki cikin
wani irin taushin murya yace,
I have something precious inside
you so daga yanxu bazaki sake ganin albinon malaminkiba sbd gudun daukar
jajayen ido da qaton baki. 4
Murmushi zancensa yasa tasaki
tareda zare hannunta taci gaba da goge masa gashi batareda tace komaiba.
Sake riqe hannunta yayi yana
tsareta da ido yace,
I will miss this smile
dakikeyi danki hanawa suhailat mijinta. 2
Kallonsa tayi gabanta na
faduwa sbd jin sunan suhailat yasatajin faduwar gaban ta sunkuyar dakai tareda
tashi daga jikinsa ta dauko hand dryer ta jona tafara busar masa da gashinsa
mai tsananin laushi.
Shidakansa ya shiryata cikin
pink gathered neck top da black straight skirt ta Sanya black hula ta fito ta
nufi dakin sa ta dauko masa kayan dazai saka takawo masa yasaka suka fito palon
hannunta na cikin nasa tanata 6anbare hannunta amma takasa ahaka yajata har
gaban ammy dake sintiri a tsakiyar bedroom dinta tana ganinsu tasaki murmushin
qarfin hali tana qarajin tausayinsu dan ko ayanxu datake ganin yanayinsu bama
zasu iya rabuwa da junaba saidai duk soyayyarsu qila basuda rabon hada zuria
sbd bazata so rumanah ta zamto itace zata fara haifarwa maheer namijiba gwara dai wata kokuma
suhailat duk da itama bazataso wani Abu yasametaba saidai so sone amma sonkai
yafi. 2
Cikin kulawa tace,
Rumanah yajikinki?kan yadaina
ciwo ko?
Kai ta daga tana sake janye
hannunta amma Sam kamar bashine riqeda hannunba.
Abinci sukaci a dining ammy
madai hartafi rumanar jin kunyar abinda maheer din kemata kuma ko ajikinsa
tamkar bashine yakeyiba. 1
Daqyar sukaga sungama ammy
tarigasu barin gurin tana girgiza kai sbd batasan haka 'danta yake 'dan
duniyaba. 1
Ammy na barin gurin takallesa
kamar zatayi kuka yazuba mata ido tareda sakin wani miskilin murmushi kafin ya
miqe tsaye ya ranqwafa yayi kissing kanta yace,
Ki kula.
Ya fice yana duba agogon
hannunsa sbd lokacin tafiyarsa yayi sosai.
Bayansa tabi da kallo hawayen
datake riqewa suka gangaro tasa hannu ahankali tashare tareda miqewa ta nufi
dakinta ta zauna bakin gado sai kawai siririn kuka ya kufce mata. 1
Yini tayi adaki kwance bayan
sallah babu abinda ke tayarda ita ko abinci yau ammy daki tasa aka kai mata sbd
ta fahimci halinda take ciki na tafiyar maheer 'din.
Da daddare ma kasa bacci tayi
harsai kusan asuba ya saceta koda ammy ta leqo taga bacci takeyi bata tadataba
sbd tasan balallaine tasamuyin bacci da daddare ba.
Koda gari ya waye sosai
guraren qarfe goma ammy tadawo ta tararda ita cikin wani zazzafan zazzabi nan
hankalinta yafara tashi musamman yanda jikinta yayi wani mugun zafi banda amai
babu abinda takeyi
Ganin abin na girmama yasata
sanarda s salma nan aka kirawo Dr faduwa tazo tadubata tareda fara mata
pregnancy test dan karta maganin da baikamacetaba awon farko ciki ya tabbata
nan ammy taqara shiga damuwa ga farin ciki ga fargabar abinda zai iya zuwa
yadawo. 3
Magani tarubuta tareda Wanda
zaita tasamu dan bacci kota huta daga aman.
Kallonta ammy tayi bayan
fitar Dr faduwa tasauke ajiyar zuciya tareda mata sannu cikin tsananin kulawa
da qaunarta.
Abinci ammyn tasamu taci
daqyar kafin tayi sallah tayi wanka ta kwanta wani sabon baccin yayi gaba da
ita.
Tunda yatafi bata sake lafiya
ba sosai ciwo ya kwantarda ita komai taci baya zama cikinta
Duk inda hankalin ammy yake
ya ninka tashi drip kuwa tasha ledoji qarshemadai daina samata ruwan akayi.
Batasan 'daga masa hankali
kokuma shiga haqqin suhailat shiyasa bata fada masa saidai duk yanda taso tare
alamarin fin qarfinta yayi dan yanxu wata biyu da tafiyarsa ga mamakinta cikin
harya fara tasawa gashi har lokacin ko zaman arkiqi bata iyayi koyaushe akwance
take. 1
Gyara zama tayi ta fuskanci
Dr faduwa cikin nutsuwa da damuwa tace,
Yanxu wata hudu kenan cikin
yake?
Abinda scanning dina yabani
kenan"" dr faduwa tafada tana sake kallon takardar scanning din. 1
Cikin tsananin damuwa sultana
takalli Dr fadwa tace,
Inason axubarda cikin tunda
yaqi bata lafiya wuyardatake sha tayi mata yawa banason wani Abu yasameta tunda
mijinta baisan dashiba. 5
Kallonta Dr tayi cikin
nazarin zancenta sbd tanaga idan anyi hakuri duk wannan wuyar zata wuce duk da
itama tana tsananin tausayin rumanah din.
Cikin nutsuwa tace,
Inaga tunda haryakai wata
hudu aqara hakuri idan yakai wata bakwai duk wannan wahalar zata rage sosai.
Girgiza kai ammy tayi cikin
damuwa tace,
Acire kawai shine abinda
nakeso yanxu. 2
Kallonta Dr tayi cikin nazari
kafin ta bude jaka ta fiddo takarda ta rubuta allura tace aje yanxu akawo
zatayiwa rumanah din sai zuwa dare idan ciwon mara yataso idan tafara zuba sai
akai mata ita asibiti.
Cikin qanqanin lokaci ammy
tasa akaje aka kawo allurar nan suka nufi dakin rumanah dake kwance tana baccin
datasamu yadan dauketa.
Yawu masu 'dacin damuwa da
wasi wasi ammy ta hadiye cikeda tsananin tausayin rumanah dakuma takaici da
baqin cikin abinda zatayi 1
Bude ido rumanah tayi cikin
wani irin laushin ciwo suna hada ido da ammy
Ammyn tayi saurin sunkuyar
dakanta sbd tasan haqqoqan rumanah bazasu barsuba komai daren dadewa saidai
idan har zubar mata da ciki shine abinda zai kare mata ita daga masifar
mineelik to ashirye take data ringa zubar mata da ciki idan tasamu. 3
Cikin tausayawa Dr ta kalli
rumanah tace,
Sannu rumanah,
Allura za'ai miki kisamu 'dan
qarfin jiki.
Murmushi qarfin hali tasaki
daqyar tareda 'dan muskutawa tabada bayanta cikin nutsuwa tasoka mata allurar
tayi mata tana mata sannu. 2
Saurin barin dakin ammy tayi
sbd hawayen dake qoqarin ciko idanuwanta
Cikin tsananin sanyin murya
takalli Dr faduwa data fito dakin tace, 3
Awa nawa allurar zatayi kafin
cikin ya lalace yafara zuba sbd........
Wani wawan jiri taji yayi
mata muguwar diba tana kallon qofar palon saida Dr ta riqota tareda juyawa
itama sukai ido biyu dashi tsaye yana kallonsu babu mai iya gane yanayinsa
acikinsu shiya mugun tayarda hankalinsu.
Manage wlh ciwon kai ke
damuna yau.
#mamuhgee
Page 26
Haske writers association💡
+
Dan Allah daga yanxu yanzu
idan kasan labari baya maka dadi zaifi idan zaka daina bi sbd wata maganar
batada dadi kuma kowane marubuci idan harya fara rubuta labari to shi yasan
saqon dayake son isarwa kuma idan har
mai karantawa yayi hakuri ahankali zai riqa fahimatar abinda akeson isarwa
dan haka pls mu riqa sanin maganar dazata fito bakinmu,
Nidai nasan abinda nake
rubutawa idan kasan baka iya magana mai dadiba to zaka iya tsayawa daga nan sbd
bazanso kaci gaba dabiba dan abinda zaizo agaba. 14
Not edited.
Ammy ya qureda idanuwansa
dasuka mugun qara sanyata damuwar abinda tayi muryarta na rawa takira sunansa
daqyar.
Ya lumshe idanuwansa yasake
kallonta Dr faduwa na ganin haka ta sulale ta fice dan ita ko kallo bata
ishesaba.
Gaban ammy yaqaraso ya tsaya
cikin wani irin yanayi na tsananin 6acin rai da bata ta6a ganinsa acikiba yace,
Bantaba samun tarba irin
wannan ba ko sakin fuska babu bare murmushinki da murnarki.
Da mamaki ta kallesa da sauri
zuciyarta na qara tsinkewa dan kuwa abinda take hangowa acikin idanuwansa ta
tabbarda yajisu.
Murya cikin sanyi da tsananin
damuwa tace,
Maheer nasan kaji komai amma
dan Allah inaso ka fahimci manufata tayin hakan dan nikaina ba'ason raina nayi
hakan ba wlh zanfi kowa farin cikin ganin rumanah ta haifa maka 'yaya saidai I
can't risk her life.......
Oh please ammy karki fara
kawo maganar risking life anan sbd babu Wanda ya isa yahanawa bawa shiga
qaddararda Allah ya dora masa,
Ammy kinsan meyasa kuke wahala da masifar mineelik
haryansu shine sbd kuna sake qarfafawa abin ne,
Meye alaqar 'yayana da wannan
tunanin naki dazaki min haka?
Meyasa zaki rabani da abinda
ko hannuna bai shigaba?
Shin ammy ina iliminki da
saninki yayi dazakiyi tunanin namiji zata haifa bayan bakida masaniyar
hakan...... 4
Cikin 'daga murya da takaicin
abunda ke faruwa ayanxun tace,
Kana tunanin ina nuna kamar
nasan zata haifi namijine shiyasa nayi hakan?
Amatsayina na uwa nayi hakan
sbd sanin matsayin dazata hau idan ta haifi namiji Wanda kasan mezata zama idan
harta zauna wannan matsayin musamman da jinininta bai zamto na sarautaba
saitafi wainda suka gabata zama baraza da abin fargaba......
STORY CONTINUES BELOW
Cikin tsananin baqin ciki ya
katseta da cewa,
Rumanah har abada bazata ta6a
hawa wannan kujerarba koda ta haifi namiji koda hakan na nufin ni nakar6i mulkin
zan karba ni nazama masifar...... 2
A tsawace tace,
Ka riga karasa wannan damar
ta zauna throne 'din mineelik tun lokacinda kace baka karbi magajin mineelik ba
dan haka ko kanaso kabaka ayanxu atarihince 'dankane yanxu yakeda cikakken ikon
karbar mulkin mineelik kuma kafin ya girma mahaifiyarsace kawai takeda ikon
bawa duk Wanda taga damar riqon qwaryar mulkin 'danta idan kuma taso ta itace
dakanta zata.......
Idan angansu kenan a mineelik
'din...yafada zuciyarsa na qarasa daukar zafi.
Itama cikin zafi tace,
Wannan ne baka isaba sbd
labarin cikin na isa a kunnen sultan bazata qara ko kwana biyu ba'a mineelik ba
dan haka zabi ya rage naka kodai acire wannan cikin kodai rumanah ta rasa
rayuwarta amatsayin rumanarta......
Ayau da wanine agabana bake mahaifiyata
ba da bazai sake ko minti 'daya da kansa a gangar jikinsaba,
Zuciyarsa tariga tagama
'daukar wuta bazai iya cigaba da maganaba ya wuceta ya nufi dakin rumanah dake
kwance lamo tanaji mararta na murda mata ahankali saidai ko wani qwaqwaran
motsi bata iyayi saidai jikinta dayayi mummunan sanyi hakanan takejin
maraicinta na taso mata. 2
Qamshinsa taji yashiga
hancinta ahankali ta bude idanuwanta dasukai laushi takalli qofa tagansa tsaye
cikin yanayin dabata ta6a ganinsa ba ta lumshe ido sbd tasan idanuwanta ne
kawai ke ganinsa sbd zuciyarta tasamu sukuni.
Qarasowa yayi baice komaiba
ya dauketa cak ya nufi qofa da ita ya fito ammy dake zaune palon ta rafka wani
mugun tagumi cikin tsananin damuwa da zullumi
ta miqe tana kallonsa yazo
yatsaya gabanta cikin danne halinda yake ciki yace,
Komawa zanyi idan ta sauka
zankawo miki ita. 1
Kafin tayi wata magana ya
wuce yabarta da baki bude idanuwanta dasukai jajir suka ciko da qwallan damuwa
ganin tun yanxu alamura na neman ca6ewa. 1
Wani babban private hospital
ya nufa da ita tun ahanya yasa akai musu booking flight koda suka isa harta
fara fita hayyacinta sbd jinin daya 6alle mata sosai.
Cikin gaggawa aka fara dubata
dan tsaida jinin dayake suma doctors din asibitin qwararrine yashiga cikinsu
dan baibari kowa yataba masa itaba,
Cikin ikon Allah suka samu
nasarar tsaida jinin batareda cikin ya zubeba saidai kwata kwata baza'aso
taringa babban motsiba sbd anriga antaba lafiyar cikin dole saiya kwana biyu
yasake qarfi.
Adakin datake kwance yashiga
toilet ya wanke jikinsa tareda canxa shirt sbd sosai jini ya 6atasa.
Sunsamu ticket din da asuba
jirgin zai tashi shiyasa yasake mata wasu injections sbd motsin daza'ai da ita
Yana zaune sofa din dake
dakin akai kiran asuba ya tashi yayo alwala yayi sallah yana idarwa babu bata
lokaci akai rubuce rubucen daza'ai suka nufi airport cikin ambulance ko mintuna
ashirin basuyi da isaba jirginsu ya 'daga.
Da rana tsaka suka isa
Georgia direct motar asibitinsa tazo ta daukesu suka nufi asibitin nan aka fara
bata sabon treatment likitocin basu zaunaba saida suka sake tabbatarda komai is
back to normal.
Baibar asibitin ba saidata
farka ta bude idanuwanta dasukai nauyi takallesa tareda lumshe ido sbd ba qwari
ajikinta sosai.
Matsowa gabanta yayi yatsaya
tareda kallon cikin idonta ya riqo hannunta tareda sakar mata siririn murmushi
ahankali ya furta,
Hey yene konjo(my pretty) 1
Kallonsa tayi fuskarta na
bayyanarda farin cikin ganinsa dakuma sunan daya kirata dashi.
Da kansa ya dagata yadauketa
yakaita toilet yayi mata wanka yacanza mata kaya patients sabbi ya rasa yanda
zaiyi ya daure mata gashinta dole yahaqura yabarshi asake yabata tea tasha
yabata magani da sauran injection dinta kafin yayi kissing goshinta yafice.
Koda ya isa gida qarfe tara
na dare lokacinda suhailat tagansa bude baki tayi tana kallonsa cikeda mamakin
ganin jiya yatafi amma yadawo yau bayan batasaka ran dawowarsa da wuriba.
Rungumesa tayi cikin danne
mamakinda tace,
Hey welcome.
Rungumeta yayi tareda sakin
ajiyar zuciya da 6oyayyan numfashi sbd shikadai yasan halinda zuciyarsa ke ciki
ayanxu sbd tabbas yasan akwai rigima agaba saidai bazai ta6a bari rumanah ta
Shiga abinda kakannin kakanninsa suka aikatoba koda hakan na nufin shi yafadawa
abinda yayi gudu tun qurciyarsa matuqar hakan shine zai kare rumanah da abinda
zata Haifa so be it. 1
Bedroom dinsa suka nufa ya
tube yashiga wanka itakuma ta nufi kicin tacewa Carolina ayi abincinda akasan
maheer din naci.
Daga haka takoma dakinsu amah
tasanardasu dadynsu sundawo suka fito da tsallen murnarsu.
Sakin fuska da jiki yayi
sosai dan gudun shiga haqqin suhailat 'din da yaransa saidai cikin zuciyarsa
damuwace mai tarin yawa duk da kasancewar cikin ya tsaya damuwa batabar
zuciyarsaba musamman dayasan dole zasu koma mineelik sbd ammynsa takoma
'dakinta badan hakaba bayajin rumanah zata koma mineelik.
Sosai suhailat ta lurada
akwai abinda yake ransa na damuwa duk da abune mai wuya ka iya gane yanayinsa.
Batason tana shiga abinda bai
shafetaba musamman yanxu dayakeda wata matar kuma 'yar 'dakin ammynsa dan haka
shishigi kan abinda babu ruwanta ba nata bane sbd kartajiyo abinda zai sakata
damuwa. 1
Fruits kawai yaci koda suka
zauna dining kuma harsuka gama bai yiwa kowa maganaba duk da ko yaransa sunsaba
da miskilancin daddyn nasu sbd kosu wani lokacin idan abin ya motsa baya iya
yimusu doguwar magana saidai idanuwansa dake ladaftar da mutum.
Da daddare koda yakira wayar
Dr olie yasanar masada tasamu bacci tundazu.
Kallonsa suhailat dake kwance
jikinsa tayi still taqi tambayarsa meke faruwa bayan taji da hospital yake
magana batai la'akari da ko ammynsa ceba dayake yasaba da haka take shiyasa bai
tsaya tunanin banxa akan hakanba da haka tai bacci cikin jikinsa ya qurawa
kyakkyawar fuskarta ido hakanan yakejin tausayinta sbd ba ita yakeji cikin
tsakiyar zuciyarsaba,
Bayajin fitar kowane
numfashinsa da ita aciki saidai tanada wani irin girma da qima a idanuwansa ta
yanda bazai iya barin ta quntatu akan abinda yake tsananin so ba.
Rufe idanuwansa tareda dakin
6oyayyar ajiyar zuciya.
Qarfe bakwai yafito wanka yakalli
suhailat data shigo dakin batareda yakalletaba yana gyara gashinsa yace,
Carolina ta hada breakfast na
mutum 'daya a basket and it should be something light.
Kallonsa tayi tana zaunawa
gefen gadonsa tace,
Ok amma pls who is the
patient?
Batareda yabar abinda
yakeyiba yace,
'Yar ammy.
Da mamaki ta kallesa tace,
Bansan waye haka ba.
Then kibarshi idan anyi
discharging nata zaki ganta.
Miqewa tayi tazo gabansa ta
tsaya tana kallonsa yana saka rigarsa tace,
Ok zanbika muje tare nadubata
ko waye tunda hanyar zuwa office dina ne.
Baice komaiba yagama shirinsa
suka sauko tana maqale da hannunsa.
Da gudu su amah dake qoqarin
zama a dining sukayo gurinsa yasaki fuska cikin kulawa yayi pecking kowannensu
yana cewa,
Good morning to sweets
angels.
Good morning to you too
daddy""suka fada suna kissing kumatunsa both sides.
Dining suka nufa dukkaninsu
sukai breakfast
Shidai daqyar ya iyacin
toasted bread one slice da black tea yamiqe
Suma dai dayake sun gama suka
dauki school bags dinsu suka fito dukkaninsu Carolina tabiyosu da basket 'dinda
aka shirya breakfast dinda yace.
Motarsu amah daban driver
yafara wucewa kafin yashiga Lamborghini dinsa suhailat tashiga yaja suka fice
daga gidan.
Koda suka isa asibiti suna
shiga reception yatsaya batareda yajuyo gefentaba yace,
Kije room 36 zanzo idan naga
dr Andrew.
Ok tace tareda kissing
hannunsa ta wuce da basket din ahannnunta.
Shikuma kai tsaye office
dinsa ya nufa.
Tana isa qofar dakin ta tsaya
tareda Sauke ajiyar zuciya dukda batasa waye acikiba ta murda qofar tashiga.
Zaune take tsakiyar gadon
nurse na gyara mata kanta daya barbaje yana damunta.
Tsayawa tayi tsakiyar dakin
qafafunta na rawa gabanta yayi mummunan faduwa ganin rumanah ce,
Ahankali tasauke idonta kan
qaramin cikinta daya fito ga wani haske mai firgitarwa dataga tayi.
Fita numfashinta yafarayi
dasauri wani irin zufa ya karyo mata amma saitayi saurin kiran sunayen Allah
acikin zuciyarta kafin tasauke numfashi mai sanyi tasaki murmushin qarfin hali
tareda qarasowa bakin gadon inda rumanah ta tsareta da ido itama numfashinta na
fita da sauri amma ganin tasaki fuska yasata qaqalo murmushi tana cewa,
Sannu da zuwa.
#mamuhgee.
No comments