RAINA KAMA (BOOK 1) 1&2
_{Kaga gayya}_
*_BISMILLAHIR
RAHMANIR RAHIM!._*
👉🏻1⃣
*Matsanan cigar* hayaniyar dake tashi
agidan ce taja hankalina, cikeda bak'in ciki natashi daga barcin safen dana
koma, fitinar gidanmu dabance data kowane family House dana Sani kona ta6a jin
labarinsa a rayuwata, haka gidan namu yake kullum tamkar kasuwar 'yan danbe,
daga matan gidan zuwa 'yan mata da yara tamkar muna ganin hanjin juna, saika
rantse badaga tsatso d'aya muka fitoba.
Kururuwar danaji maman Safara'u ta kurma
yasani kuma jan dogon tsaki, sai kuma najiyo muryar gwaggon haleema Na fad'in
“kai amma wannan lamari baiyi dad'iba, kekuwa maman biyu ya kamata ki canja
wannan halin naki, dan tabbas inba wani abu kikayiba babu yanda za'ayi yaronan
Sadeequ yadage shi cikinsu *MUNAYA* yakeso, duka yaushe aka gama maganar nan
akan shafi'u amma shine zaki koma kan Sadeequ kuma yanzu?”.
gaba nane ya fad'i, cikin zaro idanu waje
nace, “ashema mu akanmu fitinar take yau?”. yink'urin sakko nake daga gadon
Munubiya tashigo tana share kwalla, binta nayi da kallo harta fad'a saman gadon
ta kwanta rufda ciki tareda fashewa da kuka mai ban tausayi. Hakan Yakuma
tabbatar min lallai mud'inne dai ake hargowar akanmu. a fusace Na dirgo daga
gadon na nufi k'ofar fita, (ko kad'an banida hak'uri, musamman akan cin zarafin
mahaifiyarmu da akeyi agidan lokuta da dama idan irin hakan ta taso), taku biyu
nayi naji an damk'oni, najiyo cikin masifa dan nasan Munubiya ce.
“wlhy ki sakeni kafin nafara huce
haushina akanki munu! yau saina gyarama kowacce 'yar iskar mata zama agidannan
dan kutu.....
Bankai ga k'arasawa ba Munubiya tai saurin
rufe bakina da tafin hannunta.
Kici-kicin kwacewa nafarayi amma nakasa, dan
bak'aramin ruk'o taminba, raina yak'ara 6aci ainun danjin irin rashin kunyar da
Safara'u ke zubama innarmu a tsakar gida, bansan na wancakalar da Munubiya gefe
ba nafice da gudu.
Babu Wanda yaga fitowata sai dai saukar
sautin marin dana zubama Safara'u a farar fuskarta sukaji.
Hakan yaja gidan yay tsit na wucin gadi,
sai kuma hayaniya takuma 6allewa, Safara'u da mamarsu sukayo kaina danufin
duka....
Tsawar da baba k'arami ya bugace tasaka
kowa dakatawa tsakanin ni dasu, hakama matan gidan sai suka fara jan k'afafu
danufin barin wajen.
A tsawace yace, “kar wadda tabar wajen!!”.
Tsitt kakeji gidan yayi, tamkar bashi
bane d'azun ya cakud'e da hayaniya tamkar ana biki ko suna.
Jarabar gidanmu ba bak'on Abu bane a
anguwarmu, danta rigada tazama tamkar ajininmu take (yo ajininmu mana zance)
tunda kullumne babu fashi sai anyi hayaniya, kodai matan gidan kokuma mu
'ya'yan gidan. Babu mai d'agama wani k'afa koda na second d'ayane kuwa, yanzun
zakaji gidan shiru, anjima k'ad'an kaji an doka gangar shaid'an, musamman ma
fad'an yara dayafi komai saurin had'a fad'an matan gidan da a kulum, a rana sai
ayi fad'a biyar akan yara kawai, innarmu ce kawai da Maman Fauziyya keda
k'ok'arin K'aucewa irin wannan fitintunun dasuka zama tamkar shan ruwa acikin
gidanmu.
Baba k'arami yafara fad'a tamkar zai ari
baki, inda yake shiga bata nan yake fitaba, kowa yayi tsit yana saurarensa,
(saboda kasancewar masifaffe shima) sai da yayi mai isarsa sannan yajuya yafita
yana fad'in nida Safara'u mu sameshi falonsa. harda iyayenmu mata.
Duk abinnan da akeyi innarmu na kicin tana
had'a Karin kumallon safe, kuma kalma
d'aya bata tofaba a zancen nasu, datasan ma zan fito bazata barniba nima.
A falon baba jafaru yanemi jin ba'asin
tushen fitinar, cikin d'aga muryar da hargowa maman Safara'u tafara fad'in
“Alhaji wlhy kashiga tsakanina da maman biyu a gidannan, idanfa tanama sauran
matan gidannan Yanda taske so, suna barinta nibazan bartaba, tasanni tasan waye
ubana ehe, kum.......
Hannu yay saurin d'aga mata, “kinga
Suwaiba nifa ba wannan ne yasani kiranku ba, sonake naji minene ya kawo
hayaniyar?”.
Cikin jin haushin an tareta tace,
“Alhaji akan yaronnan Sadeequ ne, kowa yasan wajen Safara'u yake zuwa a
unguwarnan, amma jiya da yamma sai ya aiko kiran Munaya, dayake ALLAH yatashi
tonon asirinsu sabida bayaune na farko ba sai d'an Aiken ya kwatsa maganar a
tsakar gida, babu dai Wanda yace komai, dan azatonmu ba Sadeeq d'in Safara'u
baneba, goshin magriba saiga Safara'u tashigo tana kuka. Na tsareta da tambaya
da k'yar tacemin cikinsu 'yan biyu tagani da Sadeeq a zauren gidan Malam halilu
suna hira da dariya, kuma hardama mata gwalo akayi. Saboda na gaskata zancenta
na sake aiken Rahma taganomin da idonta, harma taji Sadeeq d'in nafad'in ai
koma miza'ayi bazai auri Safara'u ba, cikin wad'an nan munafukan yaran daba
ganesu akeba zai aura, saboda darene yasani d'inne maganar a raina har safiyar
yau d'inan, amma wlhy Alhaji da k'yar na iya barci nida Safara'u jiya.
“hummm” kawai nafad'a ina dafe kaina,
saboda jin Yanda aka canja maganar.
Babak'arami ya kalleni yace, “Munubiya ce ko
Munaya?” (dan basa ganemu saboda tsananin kamata da hassana ta).
Zuciyata cikeda bak'in ciki nace, “Baba
Munaya ce”.
“yauwa Munaya, ina 'yar uwarki?”.
“Tana ciki baba”.
Baba ya kalli Safara'u daketa matse kwallan
munafurci tun d'azun yace, “k! Safara'u tashi kiramin Munubiya ”.
Batareda ta amsaba tatashi tafita, mintuna
kad'an saigata sun dawo tareda Munubiya datasha kuka idanu sukayi luhu-luhu.
tsaki naja a raina ina hararta ta gefen ido, rashin jarumtar ta na bani haushi,
ta cika hak'uri da sanyin hali tamkar innarmu.......
Maganar baba ce tadawo dani daga tunanin
dana tafi. nad'ago ina kallonsa saboda kiran sunana dayayi, muryar a dake na
amsa da “na'am baba”. kallonsa ya maida kan Safara'u yana fad'in “wacece
acikinsu kika gani tareda Saddik'un?”.
Binmu da kallo Safara'u tayi, cikin matse
kwalla tace, “baba niba ganesu nakeba, sai sun banbanta min Kansu sannan”.
Baice komaiba dan shima yasan da hakan, (ta
hallaya ne kawai kowa ke banbantamu agidan, hatta da innarmu kuwa). Baba yabimu
da kallo alamar son sanin wacece acikinmu.
Da sauri Munubiya tace, “baba nice”.
Nima na kar6e da fad'in “baba k'arya
takeyi nice jiya Sadeeq ya aiko kira, kuma babu wata alak'a dake tsakaninmu,
hasalima ya kirani ne akan Safara'un, sune dai suka maida zancen haka”.
Daga Safara'u har mamanta harara suka
ballamin, babu ragi nima na rama kuwa.
Baba ne yakatsemu da fad'in “miya faru to
Munaya?”.
Janye idona nayi daga Kansu na maida
gareshi, kaina ak'asa Nace,
“baba ya kirani ne yana tambayata minene
abinda Safara'u tafiso a rayuwarta, dan yanason yabata gift na birthday d'inta,
kuma soyake yayi mata bazata. shinefa nake lissafa masa muna dariya saboda ina
cewa ya had'o mata da gyad'a soyayya dan ita mayyarta ce, a dai-dai lokacinne
kuma na hangota zata shigo gida, nifa dama tsokana namata gwalon, Ashe ita ta
d'aukeshi wani Abu. Kuma wlhy Rahma k'arya takeyi, lokacin data fito tareda yaa
Hameed ta ganni yana bani kayansa nakai masa ciki shi zai shiga masallaci
salla. Wannan shinefa abinda yafaru, shine suke cewa nakwace mata Sadeeq, har
ana cin zarafin innarmu da farar safiyar nan”.
Ajiyar zuciya innarmu ta sauke a hankali,
taji dad'i daba abinda suke zargin baneba.
Wata uwar harara baba jafaru ya watsama
maman Safara'u, “kai Suwaiba kedai ALLAH ya gyaraki, dan ALLAH kuringa bincike
akan Abu idan yara sun fad'a muku, tokinji dai abinda yafaru, kekuma Safara'u
dayake bakida tarbiyya har bakinki yana iyama Ai'sha rashin kunya ko, ki
tabbatar saina saka Abdulhameed yacimin ubanku keda Rahama yau a gidannan.
Ai'sha kiyi hak'uri dan ALLAH ”.
Innarmu ta yink'ura zata mik'e tana
fad'in babu komai babansu, ALLAH ya kauda fitinar gaba”.
“Amin” muka fad'a muma muna mik'ewa
mukabi innarmu a baya.
Koda muka fito, sai matan gidan suka zubo
mana ido suna kallo tamkar yau suka fara ganinmu, a raina nace munafukai, haka
zaku k'are.
Ran innarmu ya6aci matuk'a a wannan karon,
amma kasancewarta mutum mai hak'uri da shanye damuwa sai bata nunaba.
Nida Munubiya kam kasa shanye 6acin ranmu
mukayi, munsan koma wace irin wulak'antawa za ai mana agidan *KAKARMU* ce taja
mana, itace tabada kowacce iriyar k'ofar tozartamu, idan kaga abubuwan da ake
mana saika d'auka ba jinin gidan baneba, tunda muka taso a haka muka tsinci
kanmu, hakama mahaifiyarmu a wannan halin muka risketa tana fuskantar
k'ask'anci da wulak'anci daga Kakarmu da matan Abban mu, harma da matan
k'annensa, bamuda 'yanci irin na 'ya'ya, mahaifiyarmu batada kima irinta matar
gida (Uwargida), hakan yasamo asaline dalilin................✍🏼
👎🏻
Tofa masu
karatu dalilin mi? Dani daku duk muna buk'atar jin wannan dalili a bakin
MUNAYA!, saiku kasance dani danjin Yanda wannan labari mai d'unbin harmutsi da
tsalle-tsalle zai kaya, miye manufarsa? ina kuma ya dosa?.
Amsa d'aya zan iya baku.👇🏻
*_LABARIN
MAI TSAWONE_*
saikun kasance dani a hankali zancigaba da
warware muku lauje cikin nad'i.
ALLAH yasa zaku bani had'in kai,
tabbatarwata shine yanda zaku kar6i wannan labarin.
Dan haka
kumuje zuwa🥺✍🏼✍🏼
Zamu cigaba
Monday insha ALLAH, wannan d'and'anone.
Sannan
wannan karon zandinga typing ne Monday to Friday kawai insha ALLAH, kunga banda
weekend kenan😊.
One luv🥰
*_ALLAH ka
gafartama mahaifanmu😭👏🏻._*
[4/16, 9:53
AM] +234 811 277 0720: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
*_♦RAINA
KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
_Ban yarda
wani yaymin amfani da labarin nanba tako wace irin hanya, idan hakan tafaru ban
yafeba gsky, ALLAH yabani ikon fad'ar abinda zai amfanar dani da Ku, ya tsare
harshena daga fad'ar abinda zai cutar damu baki d'aya._
*_ALLAH ka
gafartama mahaifina da dukkan sauran musulmai dasuka kwanta dama, kabama marasa
lafiyarmu lafiya👏🏻._*
👉🏻2⃣
...........Zan iya ce muku fitinar gidanmu ta
farone daga tushe, dan kuwa ginannen abune tun zamanin k'uruciyar iyayenmu...
Malam Faruku shine kakanmu, matarsa d'aya
Marwa'natu (Innaro), 'ya'ya hud'u suka Haifa a duniya, maza uku mace 1. Auwal,
Hameesu, Saffiya, Jafaru.
ALLAH yayi Innaro mace mai mugun son abin
duniya, arayuwarta tanason ace komai daga gareta aka fara ganinsa, kokuma wajen
'ya'yanta, sun tsayama 'ya'yansu duk
sunyi karatun addini dana boko, sai dai Safiya iyakarta primary aka mata aure. Sukuma mazan duk sunkai
matakin babar makaranta (jami'a). wannan yasaka Innaro d'aukar burin duniya ta
d'ora akan 'ya'yan, harma matan dazasu aura.
Auwal shine yafara kammala karatunsa, dan
haka Malam faruku mahaifinsu yace ya fiddo matar Aure.
Bai wani tsaya Jan rai ba ya gabatar da
Ai'sha amatsayin wadda yakeso.
Kai tsaye innaro tace sam bata aminceba,
d'anta bazai auri d'iyar buzayeba kuma 'Yar iska, Auwal yayi lallashin yayi
rok'on akan fahimtar da ita sonda sukema juna shi da Ai'sha, amma Sam tak'i
saurarensa balle ta fahimcesa.
Da farko Malam faruku yasaka musu ido,
azatonsa innaro zata sakko cikin sauk'i, amma ganin yanda ta kafe akan bakanta
saiya sanya baki da tambayarta dalilin k'in amincewar.
Kai tsaye tace batason su Ai'shar ne, Dan
ba'asan asalin suba, sannan kuma 'Yar iskace, shima kuma yasani ai. cikin
hikima Malam yaso fahimtar da ita halin k'addara kowa da irin tasa, itama
Aishar bayin kanta bane ba, amma tak'i saurarensa shima. ganin abin zai tasamma
rashin mutumci yace to aure tsakanin Auwalu da Ai'sha kamar anyi an gama. A
wannan lokacin ba k'aramin birkicewa innaro tayi musuba, amma Malam faruku yace
tayi tagama, dan hujjarta batada muhimmancin dazai haramta auren Auwal da
Ai'sha. babu 6ata lokaci kuma aka fara shirin bikin.
*Wacece Ai'sha?*
Ai'sha
d'iyace gawasu buzaye 'yan k'asar Niger wad'anda k'addarar rayuwa ta jawosu
zuwa k'asar Nigeria, su biyu kacal iyayensu suka Haifa, Aisha itace babba, sai
k'anwarta Rabi'atu, wurjanjan suka
shigo k'asar Nigeria, sun fara rayuwane awata tashar mota, inda anan tsautsayi
ya fad'ama Ai'sha wani mara imani yamata fyad'e anan cikin tasha da daddare,
randa abin yafaru Malam faruku yaje tashar zai bada sak'o akaima wani d'an
uwansa dake garin Maiduguri, ya taras anata cecekuce atashar, yayinda Ai'sha da
iyayenta ke rungume da d'iyarsu sunata kuka da kururuwa.
Malam faruku yatambayi abinda ke faruwa
daga wajen mutanen dasuka zagayesu suna kallo, babu 6ata lokaci matashin
saurayi yafad'a masa komai.
Hankalin Malam faruku yayi matuk'ar tashi,
danshi mutumne mai kishin al'umma, anan ya d'auki Ai'sha da iyayenta suka nufi
asibiti, saboda jinin daketa zuba daga jikinta (Dan bazata wuce 15 ba sannan),
duk wata kulawar da yakamata anbama Ai'sha a asibitin, har tsawon kwanaki hud'u
tasamu lafiya sarai, kamarma komai bai faruba, sai dai tabo Na zuciya da aka
bar mata itada iyayenta. tun suna zaman asibiti Malam faruku ya fiskanci iyayen
Aisha basuda wajen zama, dan haka yak'udiri niyyar taimakonsu.
Akwai wani d'aki k'arami ciki da falo dake
gidansa, saiya zagaye musu shi da Katanga yamasa gyara.
Tunda aka fara aikin innaro ta tada
hankalinta, duk zatonta aure zai k'ara, ganin tana neman tara masa k'asa ya
zaunar da ita yamata bayani dallah-dallah, maimakon ta kwantar da hankalinta
tunda ba kishiyar bace saima takuma tadashi, tace bazata zauna da iyayen Aisha
ba.
Malam faruku yace bata isaba, Dan gidansane
babu mai hanashi ajiye Wanda yakeso akuma lokacin dayaso.
Dole badan innaro tasoba su maman Aisha
suka zauna agidan, sai dai ko kad'an basajin dad'in zama da ita, kullum gori da
cin mutunci take musu, su Aisha kam basuda sakat awajenta, saita koma sakasu
aiki tamkar boyi-boyinta. Malam faruku ne ya koyama mahaifin su Aisha sana'a,
har shima yasamu rufin asirin rik'e iyalensa dai-dai gwargwado, amma ko kama
k'afar Malam faruku baiyiba, lokuta da fama ma shine ke taimakonsa dawasu
abubuwan Na rayuwa, musamman d'inkin sitturar su Aisha da wasu matsaloli Na yau
da kullum dasukan taso. tun zuwansu gidan Auwal yafara k'aunar Aisha, duk da
mahaifinsu ya Sanar musu da komai akan k'addarar da ta fad'ama Aishan kuwa,
shekararsu biyu suna soyayya, tun Aisha Na d'ari-d'ari dashi saboda tsoron
abinda aka aikata mata har tazo tasaki jikinta dashi, sai dai babu Wanda yasan
suna soyayyar sai Rabi'a k'anwarta.
Ana haka kuma Auwal yazo da zancen Aisha
zai aura.
To haka dai akayi auren Auwal da Aisha
badan innaro tasoba.
Wannan kuma yasakata d'aukar Karen
tsana ta d'orama Aisha, kullum cikin zagi da cin mutuncin Aisha take, sosai
tazamar mata Uwar miji mai kishi da sarakuwa, ga gorin datake mata akan ita
'Yar iskace, babu wani fyad'e da'aka mata, taje tayi iskancinta an fake da
fyad'e an dawo an lik'ema d'anta da asiri, tujara dai iri-iri dai ta innaro.
Aisha tanada hak'uri, ko kad'an abinda innaro
kemata bai hanata girmamata ba da bata matsayi irinna uwa, amma innaro bata
gani.
Watan aurensu 7 kacal innaro ta samoma
Auwal wata yarinya mai suna Mero, mero d'iyace ga wani matashin d'an kasuwa,
tun alokacinma ana lissafashi a masu kud'in yankin balle yanzu daya zama
shahararre, Auwal bayason Mairo, amma dolensa ya aura saboda innaro tace zata
tsine masa.
Shigowar Mairo Yakuma k'untata Aisha a
gidan, dan tunkan ta shigo innaro tagama 6ata sunan Aisha dana iyayenta
awajensu mairo, shigowar mairo da wata 1 kacal kuma tasamu ciki, wannan fa
yakuma k'ara ta6ar6arewar al'amura, gashi sannan ALLAH ya yalwatama Auwal d'in
babu laifi, harma yasayi wasu filaye uku shida 'yan uwansa anan cikin anguwar
kusada su innaro, amma ba'a ginaba, dan babu kud'in ginin lokacin.
A wannan lokacinne kuma k'addara ta afkama
iyayen Aisha, ranar wata alhamis da daddare aka maka ruwa Na tashin hankali,
Wanda yay sanadin fad'awar d'akin dasuke ciki suka rasu.
Aisha da Rabi'a sunshiga matuk'ar tashin
hankali, hakama Malam faruku, innaro kam ko'a jikinta.
Rasuwar iyayen Aisha yasaka rabi'a
k'anwarta dawowa hannunta da zama, akuma lokacinne Hameesu shima yace Rabi'a
yakeso da aure. tashin farko innaro ta taka masa birki da kukarin zata tsine
masa kuwa. dole yabar maganar auren Rabi'ar yasamo wata Ruk'ayya ya aura.
A lokacinne Mairo ta haihu namiji, zokaga
murna wajen innaro da mairo, Malam ma yayi murna, hakama Aisha, dukda innaro tace Na munafurcine.
ranar suna yaro yaci Abdulhameed, koda wasa mairo bata ta6a yarda Aisha ta
d'auki hameed ba, dan innaro tahana, Auwal yayi fad'an shida Malam harsun gaji.
Rayuwa tacigaba da tafiya tsawon shekaru,
zuwa sannan su Auwal sun had'a hannu sun gina filinsu, kowa da 6angarensa,
gidanmu yafara yawaita da 'ya'ya, dan matar Hameesu ma ta haihu Namiji Shafi'u,
hakama matan gidanmu sun k'aru, dan jafaru ma yayi aure, hakama Hameesu yak'ara
aure shima, ga iyayenmu sun kuma bunk'asa, dansu wuce buk'atun yau da gobe,
dai-dai gwargwado akwai rufin asiri agaresu, alokacin kuma sai Auwal yakuma
auro ta uku, auren iyayenmu yakoma tamkar gasa wajen za6o 'ya'yan manya, dan
kuwa Aisha ce kawai d'iyan talakawa acikinsu, tana zaunene kawai da k'arfin
ALLAH dakuma Na Malam faruku, saikuma soyayyar mijinta Auwal, amma da dan ta
innaro ne da tuni Auwal ya saketa.
Akwaima randa fada ya had'a mairo da Aisha
akan Rabi'a ta doki hameed saboda yamata rashin kunya, dukan da mairo taima
Rabi'a saiya sa Aisha kasa hak'uri a ranar ta tanka mata, nankuwa mairo tafara
zuba mata gori da cin zarafi, da innaro tazo danjin ba'asin rigimar saitace
dole Auwal yasaki Aisha, dukda kuma mairo ce mai laifi, Auwal yayta magiya amma
innaro tace yaza6a ko ita ko Aishan, babu yanda zaiyi yasaki Aisha saki d'aya
alokacin. Hankalin Aisha yatashi matuk'a, dan batasan inda zasu dosaba, tunda
basuda kowa a Nigeria, ga innaro tsaye akanta tace atake saita bar mata gidan
d'a.
ALLAH ya tak'aita abunne dai-dai sanda
Aisha ke fitowa rik'eda hannun Rabi'a
kuma saiga Malam faruku yadawo daga kasuwa, nanfa ya tambayi ba'asi,
Aisha tasanar masa komai, maidata yayi gidan, yakuma saka Auwal ya maida
aurensu atake awajen, sannan ya tabbatar masa ko bayan babu ransa yasake sakin
Aysha bai yafeba, kuma inhar innaro tasake sakashi ya saketa itama abakin
aurenta.
Wannan shine dalilin dayasa auren Aisha da
Auwal bai sake rawaba. rayuwa kuma tacigaba da shurawa. Matan gidanmu 7.
Auwal matansa uku, Aisha (innarmu) Mairo
(mama) Sadiya (gwaggon haleema)
Hameesu nada biyu, Ruk'ayya (umma) Hadiza
(momy)
Jafaru Nada biyu shima, Suwaiba (maman
safara'u) Hafsatu (maman Fauziyya).
Kowacce ta haihu acikinsu, amma banda
Aisha, wadda saida sukayi shekara 20 da aure itada Auwal sannan ALLAH yabata
ciki, zokiga murna wajen Auwal da ahalinsa, saidai banda matan gidanmu da
innaro, dan aganinsu duk sunfi Aisha matsayi, (maman fauziyya) Ce kawai babu
ruwanta, dan suna d'asawa da Aisha sosai, ita kad'aice bata raina innarmu ba,
dan Yaya ma take cemata.
Babu irin wahalar da Aisha batasha agidanba
acikin shekarunan, kullum cikin mata gorin haihuwa dana talauci ake, harma dana
batada asali, tundaga kishiyoyinta har matan k'annen mijinta basu raga mataba,
kowacce jitake ina wuta tasaka innarmu a gidan, dama ga d'aurin gidi daga
innaro suna samu. innarmu bata cemusu komai, saidai tashiga d'aki tasha
kukanta, 'ya'yan maman fauziyya ne kad'ai ke shigowa d'akinta, amma sauran duk
an hanasu, gashi ta aurar da Rabi'a tuni, itama harta haihu uku ma.
to saikuma ga Aisha da ciki rana tsaka,
bayan tagama fidda ran haihuwarma gaba d'ayanta. cikin ikon ALLAH cikinta yakai
haihuwa, ranar data haihu saiga 'yan biyu k'yawawa kamarta duk mata, A zahiri
matan gidanmu suna k'untatama innarmu ne saboda yanda innaro tagama 6ata Aisha
awajensu, a bad'ini kuma suna k'in Aishane saboda tafisu k'yau da komaima Na
halittar jiki, (dan cikakkiyar buzuwa Ce) mai k'yawu Na asali, dirarriyar
macece doguwa, fara tas, gashin kai, idanu da komai ALLAH yabatasu. Sa6anin su
daba haka sukeba. cikin ikon ALLAH kuma saigashi ta haifo 'ya'yanta masu
tsananin kama da ita.
Hassana (Munubiya) da Hussaina (Munaya)
wad'anda suke matuk'ar kama da juna, kamar Munaya da Munubiya ta 6aci matuk'a,
ko Aisha saitayi da gaske take banbancesu, saida suka fara girmanema ake d'an
banbantasu tawajen halayya shima ba kowaba, amma Aisha ita tana ganesu kai
tsaye a sanan.
Munubiya tanada hak'uri tamkar Aisha, duk
wahalar dasukesha wajen yaran gidan bata iya ramawa, saidai tasha kukanta
tashare hawaye. sa6anin Munaya da take fitinanniya, bata bari a cuceta, koda
anfi k'arfinta saitabi tawata hanyar tarama kuwa, wannan yasaka matan gidan da
yara sukafi tsanarta, sai dai kuma basa iya banbancesu itada Munubiya,
sometimes Munaya takanyi laifi akama Munubiya a daka, itakuma Munubiya bazata
ta6a fad'in ba itaceba.
Ganin hakan yasaka Aisha yima Munubiya
shaida saboda aringa banbantasu, amma Munaya Na k'yalla ido tagani sai itama
tayima kanta irin ta Munubiya komai da komai, idan sau dubu akama Munubiya
shaida ajiki Munaya ma zataje taima kanta, hakama Munubiya takanyi idan anyima
munaya, hakan yasa Aisha ta hak'ura kawai harma suka Shiga makaranta, nanma
rikicin Munaya bai k'areba, dan saima abinda yay gaba, tajawo fad'a akama
Munubiya adaka, hakan kuma bazaisa gobe ta fasaba.
Shekarar su goma Aisha takuma haihuwar
'yan biyu duk maza, Aryaan da Aiyyaan, tundaga lokacin kuma bata sakeba.
Sai dai Munaya da Munubiya suna matuk'ar
k'aunar junansu over abinma har saiya Baka mamaki, sannan suna k'aunar
mahaifiyarsu da k'annensu, Munaya ce kan shiga idan ana cin zarafin mamansu,
amma ita Munubiya saidai taita kuka.
Yanzu haka zancen danake muku shekarunmu
19 nida Munubiya, muna matakin farko a jami'a, munzama 'yan mata, k'yawunmu da
tsananin kamarmu da innarmu yasake fitowa, mun fita daban a gidanmu, dan
mukad'aine kamarmu daban, Ayyan da Aryan ma duk Abbanmu suka kwaso, wannan
yasaka suke kama da 'yan gidanmu.
Tabbas bamajin dad'in zaman gidanmu, saboda
k'unci da hantara damuke fuskanta muda mahaifiyarmu awajen Innaro da matan
gidan, harma dawasu yaran gidan 'yan uwanmu, amma wasu muna shiri dasu sosai,
musamman ma mazan yayyenmu manya, dansu babu ruwansu da gutsiri tsomar cikin
gidan.
Gidanmu gidane tamkar gidan hayar daya
had'a k'abilu daban-daban saboda yawan rikici, kullum cikin fad'a muke, ba
iyayenba ba yaranba, kai kace muna ganin hanjin junane.
Gwargwadon iko akwai hali a gidanmu, dan
iyayenmu sun rik'e gidanmu sosai da buk'atinmu, dukda yawa da ALLAH yabamu,
bamu rasa ci da sha ba da situra, hakama matsalolin karatunmu, dan kai tsaye
zance gidanmu gidan 'yan bokone, kullum cikin gasa da juna ake, burin kowa ace
shine gaba, batun ilimin addinima kam Alhmdllh, dan tsaye iyayenmu suke akanmu,
har gobe yaa hameed bai daina zama gaban malamai ba balle mu 'yan baya-baya.
ak'alla yaran gidanmu munkai mu 43 kuma.
ALLAH yayma Malam jafaru kakanmu rasuwa
shekara biyu kenan, innaro Ce dai tana nan daram, al'amuranta sai abinda yay
gaba, dan har gobe bata k'aunar innarmu, kuma bata daina cin zarafinta ba
agaban kowa da mata gorin rashin dangi.
Hakan yasa kullum cikin buri da k'udirin
binciko dangin Innarmu nake, ko itama zata samu 'yancin kanta kamar kowa😢.
Wannan shine labarin gidanmu, sai ahankali
zaku cigaba da fuskantar ainahin halayen jama'ar gidanmu da aiyukansu, harma da
sunayensu😊.............✍🏼
To masu
karatu, sai nace yanzufa za'a fara, saiku kasance dani danjin labarin *_RAINA
KAMA.... kaga gayya_* dan akwai babban al'amari a gaba, bawai gidan su Munaya
kawai labarin ya shafaba, akwai wani lauje cikin Nad'i daga d'ayan 6angaren
labarin Na Raina kama.....😉 suga gayya ba👎🏻😄.
No comments