RAINA KAMA (BOOK 2) 9
*_♦RAINA
KAMA......♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull Ce_*
~Book 2~ 👉🏻9⃣
Duk da kasancewata farin shiga, hakan bai
hanani gane Galadima Na daban bane, kamar yanda kuka sanshi mutum mai izza da
k'asaita, hakan bai canja ba ta wannan fanin, komansa a
nurse da izzar k'asaita
yake gudanar dashi. ban tashi farga nayi kuskure ba saida labari yafara nisan
zango, anzo wajenda tsorosa yafara tasiri a gareni, Sai dai kuma nayi sakacin
da Galadima yazama kurman dutsen dabaya ji baya gani. Sai lokacin hawaye suka
fara ambaliya ga fuskata, hannayena na k'ok'arin d'agawa domin rok'o, sai dai
ya hanani wannan damar gaba d'aya..........
🤥🙆🏻kai
babu ruwana, iya nan nagani nima🤫 aradu aunty Magajiya da aunty Ni'ima zasuci k'aniyata ne
idan na k'arasa fad'a😱🤭⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀.
Tabbas na gurzu, dan yau na banbance
tsakanin aya da tsakkuwa, banbancin baya cikin hayyacinsa da yau d'inma
kad'anne, dukda babu yanda za'ayi daren farko yayi dai-dai da kowacce rana ta
bayansa.
Duk ajiyar zuciyar danake saukewa yana
jina, amma yay luf a gefena, hakan ne Yakuma tunzurani, a zalinceka akasa
lallashinka saboda jin kai, wlhy kasaitar bawannan tayi masa yawa, duk randa
yazama sarki kam fadawa sunga takansu, dan magana dai idan sarki na uku a fada
toshi bazaiyi ko guda d'aya ba😏.
Galadima daduk yake sauraren kukan nata
da ajiyar zuciya ya juyo kad'an yana fuskantarta, hannu yasaka ya tallafo
fuskarta ta matso dai-dai da tasa, jinai kawai ana huramin iska saman ido, tsaf
na fahimmci iskar bakinsa yake huramin, amma saina dake nak'i bud'e idona.
Muryarsa can k'asan mak'oshi ya furta “my
friend are you okay?”.
Banza na masa, nakuma k'i bud'e odon,
lallai mutuminnan yacika d'an latsin rainin wayo number 1, yanzunan Galadima
har yanada bakin yimin wannan banzar tambayar?, idona a rufe har yanzu na bud'e
baki cikin salon tsiwa zan maka masa bak'ar magana, amma saiya d'ora yatsansa
saman bakina yana fad'in “shiiii!🤫” da bakinsa, shirun kuwa nayi kamar an rufemin bakin Dan
Nina Na tuna illar yin tsiwar.(😝😂)
Ya matso dani jikinsa ya rungume, hannunsa
na buga gadon bayana k'ad'an-k'ad'an, ya d'ora bakinsa saitin kunnena, “yanzu
kin gane banbancin Sameer da Munaya right?, idan kuma har yanzu baki fahimta ba
to bakinki ya cigaba d'amin tsiwa OK?, nikuma bazan gaji da punishment nashi ba
sala-sala yalla6iya💋”. ‘ya k'are maganar da sumbatar
cikin kunnena’.
Babu shiri na k'ank'amesa dan har cikin
kwalwar kaina naji sumbar nan.
Kad'an ya buga bayana sannan ya janyeni
daga jikinsa ya sauka daga saman gadon.
“hasbinallahu wani'imal wakil” na iya
maimaitawa kawai, na k'ank'ame pillows d'in gabana ina rintse idanu da cije
lips (copy copy😝).
Kusan mintuna 15 duk nazata yama
fitane, sai kawai jinai an d'aukeni. a razane na bud'e idanuna, kallon ido
cikin ido mukaima juna, da matuk'ar Sauri na maida nawa na lumshe.
Wani muskilin murmushi Galadima yayi
yana cije lips.
Ba shiri na bud'e ido, saboda jina
cikin ruwan zafi, yunk'urawa nayi zan mik'e cikin 6ata fuska ya maidani ya
zaunar yana fad'in “za6i ya rage naki, zama kiyi da kanki, kokuma ni nayi
miki..”
Banma bari yakai k'arsheba na koma na
zauna ina kare k'urjina.
Kafad'a ya d'age sama yana ta6e baki da
fad'in “hummm”.
Fita yay daga bathroom d'in ya rufe mata
K'ofar.
Na kai tsawon lokaci a bayin ina Gasa
jikina, dan nasan idanma banyiba kaina nama mugunta, saida naji ko ina ya saki
sannan nayi wankan tsarki ina hawaye, bansan yanda zan fassara wannan muguntar
ta Galadima ba kuma, wannan karon kuma tsautsayin zaice kokuwa ba yin Kansa
bane?.
Haka dai na kammala na d'aura towel d'ina,
a zuciyata ina addu'ar ALLAH dai yasa ya fita, dan towel d'in guntune, bai gama
rufe cinyoyina bama baki d'aya.
Da sand'a na fito, yauma inajin zafi
kad'an-kad'an, amma ba kamar na ranar ba. ganin baya d'akin saina ida rufe
k'ofar na tako cikin d'akin sosai.
Ina neman kaya a wardrobe ina share
hawaye, indai rashin tsiwar dayake fad'ace na daina masa, dan bazan zauna ya
illatani a banza ba, wannan k'addararren cikinma daya hanamin gangar jiki
hutawa da ciwuka ya isheni, basai na cigaba da 6alloma kaina wata muguntar tasa
ba.
wata 'yar riga mai d'an nauyi-nauyi na
samo, na cirota dan sanyi nakeji, juyowar da zanyi saina gansa zaune bakin gado
yana danna laptop, hannunsa d'aya rik'e da glass cup yana shan fresh milk
hankali kwance.
Saida nad'anja baya, nakuma bud'e rigar
ina kare jikina.
Duk abinda takeyi yana kallonta ta gefen
ido, amma yawani share kamar baima San da itaba.
Da bin bango da sand'a na koma bayin, ta
gaba kuma ina karewa da rigar.
Saida ta shige ya d'ago kai yana kallon
k'ofar bayin, saikuma ya girgiza kai yana murmushin gefen baki. cigaba yayi da
aikinsa a nutse.
Barci nakeji, ga zazza6i yafara rufeni,
hakan yasa ina gama saka rigar na fito, naci serious kawai sannan na fito.
d'ago idanu yayi muka had'a ido, da sauri
nad'an rankwafa inajan rigar barcin k'asa wai danta rufemin cinya zuwa kwauri.
Baki ya ta6e yana wani janye ido cikeda
basarwa. Irin shi baiga abin kallo d'in nanba.
Ni kuma na dalla masa Harara ina k'ok'arin
hayewa gadon.
“ji mana”. ‘yafad'a cikin izza’.
Banza na masa zan haye gadon.
Yace “iyim, bakije daddarawa ba kenan
yarinya, saina sake kaiki yanzunnan....”.
Kafin ya rufe baki nama iso gabansa na
tsaya.
d'agowa yayi yana kallona yana kur6ar fresh
milk nashi, ya d'agamin gira d'aya.
Baki na turo masa ina share hawaye.
Ya kamo hannuna ya zaunar kusa da shi,
“nikam yalla6iya karki haifomin abin cikin kwan da halin kuka, bana son ragwan
taka, 'yata ko macece jaruma za'ayi, irin wadda labarinta zai zaga lungu da
sak'o na duniya”.
Harara na balla masa, yay saurin rik'e cup
d'in hannunsa dayake zuba frash milk a ciki, “eh me, malama karkisa hantar
cikina fitowa, irin wannan harara haka”.
Kad'an yarage banyi dariya ba, da
gaskiyar Momma, halin Galadima d'aya da Sauban, tsantsar harmutsine da sanya
damuwa a rai ya lullu6e halinsa na barkwanci, hakan kuma yanada nasaba da
rashin samun mai jansa a jiki yana d'auke masa kewa da rage masa rad'ad'in
damuwarsa. Momma hankalinta nakan jiyyar Abie, Aunty mimi kuma rainon Sauban,
mom kuma tayi aure lokacin dayake buk'atar makusanci, s.......
Firgigit nayi saboda hancina da yaja, na
kalleshi ina tura baki.
“maida wuk'ar yalla6iya, abin bana fusata
bane, wace duniyar kika tafi hakane da nisa inata magana?”.
Marairaice fuska nayi ina shirin fara
kuka, “please ka barni na kwanta barci nakeji”.
Kofin hannunsa ya mik'amin, na waro
idanu ina girgiza masa hannu alamar a'a”.
Shima saiya waro nasa idanun yana fad'in
“why?”.
“kawai ni bazan sha bane, aje a zubamin
wani abu”.
“hakane kuma”. ‘ya fad'am yana kamoni ya
jawoni jikinsa’.
Saman cinyarsa na zauna, da hanzari nafara
k'ok'arin mik'ewa. shima saiya kama hannayena ya maidasu baya yanda bazan iya
kata6us ba, madarar ya d'auka ya guntsa da yawa a bakinsa.
Waro idanu nayi ganin ya nufo bakina
gadan-gadan, duk yanda naso kauda fuskata ya gagara, na datse hakwarana da
sauri, shi kuma saya toshemin hanci, hakan yasa ni bud'e baki dole, dan ina
buk'atar shak'ar numfashi. Tas ya juyemin fresh milk d'in abakina, sannan ya
kuma rufe hancina saida na shanyeta sannan ya janye bakin, ni dashi duk muka
hau sauke numfashi, kuka na sanya masa, amma hakan bai hanashi kuma guntsar
madarba ya kuma juyemin a baki na, haka yayta min, ya kuma k'ara rabin kofi
kuma, saida yaga ta kwalin ta k'are sannan ya sakarmin hannu na tashi zaune.
Bansan kawai na fara kaima k'urjinsa
k'ananun dukaba, ina fad'in wlhy sai ALLAH ya sakamin, kai bama zan yarda ba
fa, saboda k'azanta kaita had'a yawunka da fresh milk kana d'uramin, ni bazan
yardaba”.
Shagala kawai yayi yana kallona, yakasa
kare kanshi balle yunk'urin hanani, saida nayi mai isata sannan na fad'a
k'irjin nasa ina raira kuka.
Lumshe idanunsa yayi yasaka hannayemsa ya
zagayeni sosai yana kuma sakani jikinsa sosai. Nima sainayi luf Ina shak'ar
k'amshinsa da yariga ya mannema fatarsa.
Munja wasu times a haka, ni ina kuka shi
kuma idonsa a lumshe yana shafa kaina da saurarena.
Jiyay kawai jikinta ya saki, alamar barci
ya d'auketa, sai ajiyar zuciya da take ta saukewa, bud'e idonsa yayi, sannan
yakai bakinsa a hankali ya sumbaci sumar kanta dake tare da danshin ruwa har
yanzu. zafin zazza6inta dake ratsa 6argon jikinsa ya sakashi fidda huci yana
kuma sumbatar kanta.
Dr Farida ta sanar masa babu abinda zai
hanata wannan zazza6in, koda tasha magani ya sauka saiya dawo, sai idan cikin
yayi kwarine maybe ta daina ma gaba d'aya, amma mai juna biyu ba'a rabata da
k'ananun ciwo makamantan haka. jiyay ya kuma k'aunar Momma d'insa a ransa, a
hankali ya furta I love you my Momma”.
Tashi yay d'auke da Munaya a hannu, ya
kwantar da ita sannan yaja bargo ya lullu6a mata. tare da sunkuya wa ya sumbaci
goshinta ya shafa cikinta da hannunsa sannan ya mik'e ya koma inda yake.
Ya cigaba da aikin dayake a laptop Wanda
ban fahimci komaiba a ciki, tsawon lokacin yana aikin, saida ya fara hamma
sannan ya kashe. bayi ya shiga ya d'auro alwala, ya gabatar da nafila kafin yay
shafa'i da wutiri yaja doguwar addu'a da kirari wa Ubangijin talikai, harda
hawayensa sannan ya mik'e.
Ya kuma daidaita hasken fitilar d'akin
sannan ya hau gadon shima ya kwanta, yay musu addu'a ya shafe cikin munaya (😂Galadima saboda tsaro ba tsoroba ko🥺).
a zatona zai rungumeta, sai naga ya
gyara kwanciyarsa kawai a gefenta yaja bargo shima.
Galadima asuba ta gari, (ni dai rungume
nawa mijin zanyi aradu🤫🙈⛹🏻♀).
Ga bannin asubahi zazza6in munaya ya
sauka, hakanne ya sakata samun dad'in barci sosai, ta kuma kanainaye Galadima,
wanda shi da kansa ya mirgino har inda take cikin barci ya rungumeta, dukda
zafin zazza6inta nata ratsa nashi jikin yakasa barinta. ahaka kiran sallar
farko ya riski kunnuwansu.
Kusan a tare suka farka, ganinsu manne
da juna yasaka kowa barin jikin d'an uwansa da sauri, munaya dai kunya ta
sakata juya baya, amma boss ko a kwalar rigarsa, saima tashi da yayi yana wani
ciccin Magani ya shiga toilet.
Alwala ya yo, baiyi mata magana ba ya fice
abinsa.
Munaya ta raka bayansa da harara tana
fad'in Girman kai dai rawanin tsiya wlhy. tashi tayi itama ta shiga bayin, amma
sa6anin shi ita harda wankan gasa jiki (lallai kinji basawa Munaya🤭, wannan gasa jiki dabaya k'arewa
haka🤥😂).
Fitowa tayi tanata kumbura fuska, ni
dai na lalla6a na shige bayinta danna dandalo arzik'i😝 lol (koya kukace fans🤷🏻♀😂?).
****************************
Ban sake jin d'uriyarsa ba sai around
9:30am.
Tashina a barci kenan na rarrafa
zuwa bayi da k'yar nayo wanka, dan banajin dad'in jikina gaba d'aya, danan ya
saki sai nan ya kama ciwo.
Motsin mutum naji a bayana dan haka na
waiga, Galadima ne cikin Farin wando da t-shirt itam fara tas, ya d'aure
k'ungunsa da Navy blue d'in belt, sannan ya kawo jacket navy blue itama ya
saka, babu takalma a k'afarsa, sai dai k'afar fes tamkar ba'a takata a k'asa,
sai agogon azurfa mai k'yau d'aure a tsintsiyar hannunsa.
hummm dan k'yau kam dai yayishi, sai dai
ni bawai ya birgeni bane😏 (ho Munaya banda zuk'i ta malli dai🤥🤣😝🙆🏻).
Janye idona nayi na maida kan gyaran
gashina da nakeyi.
Shima baice uffanba ya wuce wajen
frigate, fresh milk ya d'akko yatako gaban mirror inda nake zaune. a saman mirror ya ajiye kwalin madarar ya
jingina bayansa shima, idonsa a kan gashina danake gyarawa. ya d'au madarar ya
zuba a cup d'in daya d'akko tare da mik'omin.
“ni ba ita zan shaba”. na fad'a ba tare da
na kalleshi ba.
“mikenan?”. shima yafad'a cikeda
k'asaita.
Yanzunma ban kalleshi ba nace “tea”.
Kofin ya dire saman mirror yana tattare
hannun rigarsa, “salon ki k'onamin idon abin cikin kwan kenan, to za6i ya rage
naki, sha da arzik'i ko kuma d'ura”.
Babu shiri na d'auki kofin na kwankwad'e,
dama iyayine inajin yunwar.
Kofin na mik'a masa ina 6ata fuska tamkar
zan fasa ihu.
Ya d'agamin gira yana fad'in “taimakon
kai my friend”.
Gefe nayi da fuskata ina fad'in “kai duk
salon mugunta ka sani ai”.
“martabar gudan jinina nake karewa”.
yay maganar yana k'ok'arin ficewa.
Baki na na ta6e ina harar bayansa, su
gudan jini anji jiki kuwa.
Ganin zai fice nai saurin cewa “nifa inason
zuwa kitso, kuma zan koma school”..
Tsayawa yay cak daga yunk'urin fitar
da yakeyi, Batare daya juyoba yace “babu wannan tsarin a masarautar gagara
badau”.
Yana gama fad'a ya ida ficewarsa.
Tamkar zan fasa kuka nayi jifa da cumb d'in
hannu na ina fad'in “ina ruwana dawani tsarinku ni, makaranta ta nakeson komawa
ehe”.
Yana jiyota amma ko'a jikinsa yaci gaba da
k'ok'arin fitarsa hankali kwance.
★★★★★★★★★
Tunda Aryaan
ya shigo da gudu inna ta tareshi tana fad'in “kai lafiya? minene na gudu?”.
“innarmu wlhy Uncle ne yace ki shirya
mana kayanmu ni da Aiyaan zai aiko gobe a kaimu wajen Auntynmu”.
Inna tayi d'an murmushi kawai, dan ita bata
d'auki maganarma serious ba.
Su dai su Aiyaan sunata murnarsu, sun tafi
d'aki sun hau had'a kaya.
Babu dad'ewa da yin haka saiga daddy ya
shigo da sallama, inna ta amsa masa tana gyara zama, shima zama yay kujerar
dake kusada k'ofa, ganin haka inna ta fahimci da magana yazo, dan haka ta maida
dukkan hankalinta Kansa.
Bayani yamata dalla-dalla akan zancen da
su Galadima sukazo dashi, ya d'ora da fad'in “saiki shirya dan zamuje ai miki
passport”.
Inna tace, “amma dadynsu nake ganin ai da
kud'in kukaje kamar zaifi”.
Murmushi Dady yayi, yace “Ai'sha nasan
miyasa kikeso zamewa, to ai kaf cikin matan yayan kece ya cancanta kije koda
ace bawai Galadima ne ya biyaba, maganar ciwo Muke bawai jin dad'i ko gutsiri
tsomar wasu ba, ki shirya dan zai turo wanda zamuje immigration office d'in”.
daga haka ya tashi ya fice.
Shiru kawai inna tayi, itadai inda ta
itace da antafi da ko innaro, dan tasan wannan tafiyar dukda ta ciwoce sai ta
janyo 6acin rai a gidan.
Aiko tamkar inna tasani, dan ana fad'ama
innaro tace “bata amince ba, ita ta haifi auwalu kuma da ita za'aje tayi jiyyar
yaronta, bazata bama kowacce mace acikinsu wannan ragamarba.
Shiru baba k'arami da daddy sukayi, taci
masifarta ta gama tayi shiru.
Baba k'arami yace, “amma dai inna kinsan
jinyar Yaya sai da matarsa a kusa, kekuma k'arfinki ya k'are ya za'a d'ora miki
d'awainiyar da matansa ne keda hakki a kai?”..
“yo d'awainiya ba tare da kai za'a
tafiba? Kai basai kamasa ba. ni dai fa ban amince Ai'sha tajeba, dan wlhy bazan
ta6a son Ai'sha ba komi zata zama, tunda dai ta silar jikokinane balle amin
ilimi. k'ilama itace ta jefeshi dan taga ta kama k'asa 'yarta Na auren d'an
Sarki, t........”.
“innaaaa! haba mana, dan ALLAH karma ki
bari maganar nan ta fita, waishin minene laifin Ai'sha a gareki? duk cikin
matanmu banga wadda take girmamaki da d'aukarki matsayin uwaba irinta, inna ya
kamata wannan k'iyayyar ta koma soyayya hakanan, a baya kince dan basuda asali,
kin dawo kince juya ce bata haihuwa, gashi kuma yanzu har ALLAH zai fidda
jikoki daga tsatsonta, to miye kuma matsalar?”.
“toko zaka shak'eni Na fad'a makane
Hameesu?”.
“a'a inna, ALLAH yabaki hak'uri”.
“kaidai ka Sani, ni yanzu bara Na tashi
Na shirya Ku kaini inama kace, imagesa nema ko uwarmi oho”.
Daga Dady har baba k'arami babu Wanda ya
tanka mata, tana shigewa baba k'arami ya mik'e yana cema dady “yaya ka jireta,
bara naje mutafi da maman 'yan biyun, kota fito kace naje shiryawa ne”.
Kai Dady ya kad'a masa yana murmushi, baba
k'arami ya fita da hanzari.
Bayan wasu mintuna saiga innaro an fito
ana warware gyale za'a yafa, “yauwa jafaru muje Na shirya”.
Habiba dake kitchen tana girki duk diramar
da ake tana saurare ta tuntsure da dariya, lallai tsohuwarnan akwai daru, mama
Na hanya ai, itace maganinki (gwaggo Safiyya mamarsu).
Kallonta Dady yay yana murmushi, yace “to
inna mu jira jafar d'in yaje shiryawa”.
“ato shikenan bara kafin ya dawo nad'anci
abinci, k! Habiba zubomin idan abincin nan ya tsotse, gara Na fita cikina da
d'an nauyi”.
Habiba ta had'iye dariyarta sannan tace
“innaro bai tsotseba, amma nanda kamar dai minti 5”.
“babu damuwa ai, nasan jafaru ma bai
dawoba harnaci, kinsan shi da dak'undar shiri, ya tsufa amma kullum kallon
kansa yake sa'ar Abdul-hameedu”.
Dariya Dady ya had'iye da k'yar, yasa
handkerchief yana toshe baki dan karta fito.
★★★★★★★★
Tsaf na kammala shiryawa sannan Na kimtsa
d'akin, ni dukfa a nufina nayi shirin asibitine.
Fitowa nayi dan naga ko yana falone, wayam
babu kowa, sai sallama da nakeji a bakin k'ofar, amasawa nayi na bada izinin
shigowa saboda naji muryar matane.
Su 10 ciff suka shigo, k'asa suka zube
suna gaisheni, Na amsa musu da 'yar sakewa, “lafiya dai?”.
“lafiya lau ranki ya dad'e, mune zamu
kasance hadimanki, masu miki dukkan hidima.
Nifa wlhy banason wasu bayi, amma dolene Na
barsu tunda wad'ancanma Galadima ne yace su tafi, yanzu kuma baya wajen, ni
kuma banida ikon korarsu tinda bansan kan abinba.
Amsa musu nayi da “to” sannan nawuce Na
zauna a kujera.
Tasowa sukai suka biyoni, a tsanake suka
dinga fad'amin sunansu da aiyukan da zasuyi.
Wad'anda naga bazan iya yarda suyiba Na
canja musu aiki. Sallamarsu nayi, Ina k'ok'arin tashi Na shige ciki saiga
Sauban ya shigo, duk zubewa sukayi suna kwasar gaisuwa a gareshi, ya amsa musu
yana wani yatsine face, sai kuma ya basu izinin tafiya, fita sukayi harabar
sashenmu.
Na kalleshi ina murmushi, “ashe kaima dai
sarautar Na jininka yaa Sauban? Wanda bai saniba saiya d'auka duk bazaka iya
wani Abu daya shafi sarautaba”.
Dariya yayi yana zama, “aunty gimbiyar mu
kenan, wannan ai sai mijinki”.
Nima murmushi nayi kawai.
Ya mik'omin kayan hannunsa yana fad'in
“ga break fast d'inki”..
“wayyo yaa Sauban, nikam dai nagaji da
ciye-ciyennan ma, zuwa zanyi Na fara abinci da kaina”.
“wlhy dakin taimakemu Aunty gimbiya,
mijinki shiya saba da cin abincin waje shiyyasa bai damu ba, ya kamata kafin Na
wuce gobe naci girkinki”.
“kamarya gobe? Kana nufin zaka koma
kenan?”.
“tab da gudu kuwa, aini bazan iya zaman
k'asarnanba Na tsawon lokaci, tarema zamu wuce da Abba ai, harma da innarmu,
yaa Sam bai sanar dakeba kenan?”.
Baki bud'e Na girgiza masa kai alamar a'a.
Sauban yay murmushi, “kinsan halin
Galadiman namu ai, soyake yamiki surprise maybe, yanzu hakane yaje cuku-cukun
visa d'insu ne. waito miyasa bazamu koma tare da kubane?”.
Murmushin yak'e nayi, nace, “maybe akwai
ayyukan dabai gamaba shiyyasa”.
“inaga hakanne kam, ni bara naje, yace
Na iskeshi birnin gayu, ga mahfuz can Na jirana”.
“ok sai kun dawo” Na iya cewa, danni daga
'yan matan masarautar har samari ba kowa Na saniba, tunda time d'in daya kamata
nad'an San mutane sai muka tafi India. ni bama nason Na saba da kowa, ni da ba
zama ya kawoni ba.
Maganar fita da Abba da Galadima yakeyi
sai yayta cin zuciyata, kimar Galadima da darajarsa saita cika zuciyata, inason
mahaifana, kuma dukkan Wanda zai nuna musu kulawa bazan manta da shiba, harda
'Yar kwallata Na share, Na tashi Na koma bedroom ba tare da nayi break fast
d'inba ma.
*****************************
Innaro dai tun ana jiran dawowar baba k'arami harta fara gyangyad'i,
habiba data kammala abincin ta d'ebo ta kawo mata, nuni Dady yay mata akan ta
koma.
Habiba ta koma da baya ba tare da ta
k'araso falonba.
Tun tana gyangyad'i harta 6ingire a kujerar
barci mai nauyi ya d'auketa (ho innaronmu ta mutunci🤸🏻♀😜).
Baba k'arami da innarsu munaya kam tuni
sunyi ficewarsu, dayake Abu Na kud'i dandanan aka gama cuku-cukun komai, Nuren
ne tsaye, saida komai ya daidaita suka samu visa d'insu a hannu sannan suka
fito.
Har gida ya maidosu ya koma suna jera masa
godiya da addu'a shi da Galadima.
Innaro daga gyangyad'in jiran abinci ya
tsotse aka zarce da barci mai nauyi, shima Dady lalla6awa yay ya fito dan
asibiti zaije.
Tafiyarsa babu dad'ewa saiga gwaggo Safiyya
ta iso da yaranta biyu.
Hayaniyar su Dahiru ita ta tada innaro, ta
mik'e zumbur tana fad'in “yauwa Jafaru kadawo mu tafi ko? Habiba bar abincin
kawai idan muka dawo naci.
Mi Dahiru da Naja'atu zasu ba dariya
ba, suka shiga shek'ama innaro dariyar shak'iyanci. Wai kota kwanta da yunwa
ne.
Zaginsu ta hau yi ta d'auki filon kujera
tana dukansu.
Sai da gwaggo Safiyya ta musu magana sannan
suka nutsu, “inna ina zakuje da Jafaru ne?”.
Gyara zama innaro tayi tashiga bama
gwaggo Safiyya labari.
Murmushi kawai gwaggo Safiyya tayi, danta
gane wayo suka mata suka gudu kawai, itama sai tace “to inna ki cigaba da
jiransu, k'ila dan sunga kina barcine suka jira ki tashi sannan Ku tafi.
Da wannan gwaggo Safiyya ta rufe bakin
innaro ta zauna jiran su dady.
Aiki🤣🤣😝.
**********
Galadima daya fita kai tsaye asibiti ya
nufa, su yaa hameed kawai ya iske can, dan dady ya hana matan gidan zuwa sai
anjima, doctors Na complain akan suna cika wajen da yawa.
Cikin mutunta juna Galadima ya gaisa dasu yaa
sabi'u sannan yashiga yaga daddy.
Yau kam Alhmdllh dan ba barci yakeba,
kumbirin fuskarsa kuma yad'an sa6e kad'an, saidai baya iya magana sai dai yayta
bin mutane da idanu.
Dukda bazai iya amsawa ba haka Galadima ya
risinna ya gaidashi, tare da masa fatan samun lafiya sannan ya fita office d'in
doctor.
Bayan sun gaisa doctor ya bama Galadima
file d'in bayanan Abba dasuka tattara.
Kar6a Galadima yayi ya duba, dukda bawai ya
fahimci bayanan bane, ( kusan dai rubutun doctors sai su). Suka d'an tattauna
akan cigaban da aka samu sannan Galadima ya fito.
Ya iske daddy ya iso, suka gaisa sannan
yamasa dukkan bayanan da doctor yamasa shima. Dady ma yaji dad'in cigaban da
aka samu.
Galadima yay musu sallama ya fito.
Guntun tsaki yaja saboda yanda jama'a suka
wani zuba masa idanu tamkar sunga magiji, da sauri wani dogari ya bud'e masa
motar ya shiga, sannan suma suka shiga.
Daga asibiti Galadima yace su wuce birnin
gayu plaza.
Cike da girmamawa sarkin mita ya amsa da
to.
Maida kansa yayi jikin seat ya kwanta
tareda lumshe idanu ya fad'a duniyar tunani................✍🏼
Barkanku da juma'a💋💋💋🤝🏻.
Musha
weekend lafiya sisters⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀😄.
*_ALLAH ka
gafartama iyayen mu_*🙏🏻😭
No comments