RAINA KAMA (BOOK 2) 10&11
*_♦RAINA
KAMA......♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull Ce_*
_Duk marubucin daya kafa
alk'alaminsa bisa takarda tabbas yagama tanadar yanda labarinsa zai kasance ne,
amma
sai wasu wabubuwan mamaki kaga sun gaza k'arewa a social Media, ban saniba
ko samunmu available ne yakesa a kullum kuke mana kallon marasa aikinyi?, ni
dai nasan time d'in dana shirya labarin RAINA KAMA ban zauna tebirin shawara da
kowaba a online, inkuwa hakane tayaya wasu har suke tunanin nafara sauka akan
layin labarin?, to magana d'aya zanyi a wannan ga6ar, ban gina labarin Raina
kama akan kwanciyar aure bane, dan haka masu maganar munaya bata da aiki saima Galadima rashin
kunya saisu jira saina kai k'arshen labarin kafin su k'alubalanceni, abin
dariya, (wai aikina kenan daga nasa munaya ta murgud'a baki sai ta harari
Galadima da masa k'unk'uni) tunda aikina kenan babu lallai wajen 6ata lokaci
karantawa, haka Na tsara labarina tun farko kuma haka zanyi, duk wanda yaga bai
masaba zai fara iya rubuta nashi shima kawai. wannan abun da kukema writer's
yana 6ata mana rai, bai kamata ku dinga k'alubalantar writer's ba, bayan su
suke da masaniyar yanda suka shirya labaransu, idanma zakuyi saiku ringa
tanadar lokaci har zuwa bayan mun kammala, hakan zaifi tasiri fiyeda
katsalandan a tsakkiyar labaran mu, akoda yaushe kuzama masu kula kafin Ku
k'alubalanci mutum🤷🏻♀._
*Ba akan kaina kawai nayi wannan
bayaninba, harda sauran writers da yawa da akema makamancin hakan koma fiye da
nawa.🙅🏻*
_____________________________
~Book 2~ 👉🏻1⃣0⃣➖1⃣1⃣
...................Koda motocin suka tsaya
sarkin mota ya bud'e masa k'ofa yakai tsawon lokaci baiko motsaba, saboda tsantsar
tunani da zuciyarsa ta lula, aduk sanda zuciya take cikin matsanancin matsi
gangar jiki ma gazawar karfin ikon jini dana 6argo sukan mata k'aranci, shi
kansa yasan yanada buk'atar mataimaki a kan wannan lamarin, amma k'arancin
rik'on amana Na d'an Adam ne yake yawan gargad'arsa da taka masa birki, ba
kowane zai fahimci ma'anar nok'ewar tasaba, sai mutum daya tsinci kansa a
makamancin halin da yake ciki.........
“Ranka ya dad'e mun iso”. Sarkin mota
yasake fad'a cikin taraddadi da taka tsantsan.
A hankali Galadima ya bud'e idanunsa da
suka koma launin jaa saboda damuwa a kan sarkin mota, batareda yace uffanba ya
ziro k'afarsa k'asa yana cije lips da had'iye wani kududun damuwa a mak'oshi.
Tunda ya fito ma'aikatan wajen suketa masa
sannu da zuwa, dan tunda ya shigo k'asar sai yanzu ne zai shiga cikin plaza
d'in.
Hannu kawai yake iya d'aga musu, amma
bakinsa yay masa nauyi, kallo d'aya kuma zaka masa ka nazarci damuwa da
buk'atar hutun dake tartare da kuzarinsa.
A cikin plaza d'in ma bata sauyaba, d'aga
hannu agaresu shine yazama linzamin amsa gaisuwar dasuke masa.
Da hannu yayma d'aya daga dogaransa nuni da
amso masa key.
Da sauri dogarin ya amsa yana mai nufar
sashen da zai kaishi office d'in Saleem mai kula da CCTV camera's.
Sai dai kafinma yakai ga k'arasawar suka
had'u da saleem, Wanda tun shigowar motocin Galadima ya gansa.
Keys d'in ya damk'ama dogarin, sannan ya
k'araso domin mik'a gaisuwa ga ogansa na wajen aiki kuma magajin garinsa.
Shima d'in dai hannu Galadima ya d'aga
masa, hakan kuma ya saka Saleem fahimtar akwai damuwa kenan.
Koda aka bud'e ya shiga saiyayma
dogaransa nuni da suje kawai, sannan ya maida idanunsa ya lumshe tareda
kwanciya jikin kujerar yana lilawa a hankali.
Shi kansa baisan tsawon lokacin daya
d'auka a hakanba, amma tabbas yasan yashiga kudin nazari mai zurfin gaske.
Knocking d'in k'ofar da akayi yasakashi bud'ar baki da k'yar ya bada izin a
shigo.
Nuren daya shigo ya maida k'ofar ya kulle,
kafin ya ida takowa cikin office d'in, idonsa nakan d'an uwannasa.
Zama yay a d'aya daga kujerun dake
fuskantar Galadima, “brother what
happen?”.
“Northing”. Galadima ya fad'a batare da
ya bud'e idonsa ba.
Shiru kawai Nuren yayi shima, ya d'akko
laptop a briefcase d'in daya shigo da ita, kunnawa yay, kusan mintuna biyu ya
d'ago ya kalli Galadima, sai kuma ya maida kansa ga laptop d'in. “Sameer nasan
kaga cigiyar da akeyi takowacce kafar yad'a labarai ta k'asarnan akan d'iyar
minister, sannan jami'an tsaro tsaye suke akan binciken inda take. yakamata
musan abinyi kafin lokaci ya k'ure mana”.
Guntun murmushi Galadima yayi, batareda ya
bud'e idanunsa ba yace “Nuren indai har babu wata waya datake aiki inda kakai
yarinyarnan, kuma ka cire sim card d'in phone nata a lokacin daka d'auketa, to
babu wata hanya dawani jami'in tsaro zai ganota, dama hanya d'ayace da kuskure
zai basu damar bibiyarta, na d'aya lokacin daka d'auketa yazam wayarta na aiki,
tabbas zasubi ta wannan hanyar su gano har iya inda ka kashe wayar, hanya ta
biyu itace ka kashe wayarta baka cire sim card d'in ta ba daga phone nata, koda
wayar a kashe take zasu bibiyeta ta hanyar 📡 su ganota” ya tashi zaune sosai yana bud'e idanunsa akan Nuren, “wannan
hanyoyin biyu kawai ke garesu saikuma idan da camera tare da ita, idan duk babu
wannan basuda wata hanya, ka kwantar da hankalinka my brother, komaina da
tsarinsa right?”.
Murmushi Nuren yayi, kafin ya salute
d'in Galadima yana fad'in “I thrust to you my dear broth”.
Shima galadima salute d'in Nuren d'in
yayi yana murmushi.
Komawa yay ya sake kwanciya jikin kujerar,
“yanzu inaga time d'in turama minister Massage yayi?”.
Cikin zaro idanu Nuren yace “baka kallon
hakan a matsayin ganganci kuwa?”.
Baki Galadima yad'an ta6e yana crossing
k'afarsa, cikeda izzarsa yace “sai idan nabama wani damar hakan ai”.
Nuren baice komaiba, dan yagama sanin
hatsabibancin Galadima wajen iya sarrafa Computer, dan haka ya bar wannan
zancen ya d'akko wani. “yauwa to maganar Malam Saminu fa? Kasan yana hannunmu
fa har yanzu?”.
“wannan barsa saiya kuma magantuwa, dan
da alama yasan wani Abu, saidai akwai abinda ya sakashi za6ar 6oyewa. ni yanzu
damuwar 6atan Muftahu yafi damuna, nasaka camera's jikin mutane 10 danake iya
zargi a masarauta amma banga alamun da hannun koda mutum d'aya ba, hakan ya
tabbatar min da gaske Muftahu na bibiyar lamarina, sai dai bansan dalilinsa ba,
ko kuma waye sakashi?”.
Nuren ya jinjina kansa, “brother aini
da Harun dama mun dad'e da zargin Muftahu, Kaine kawai kake masa kallon mutumin
kirki daman”.
Lips kawai Galadima ya cije, amma baice
uffanba, Nuren yaci gaba da 'yan danne dannensa a laptop d'in, zuwa wasu
mintuna batareda ya d'agoba yace, “maganar Sirikinka fa?”.
Shiru Galadima ya masa, saida ya mula dan
kansa sannan ya murmusa tareda maida idonsa ya lumshe, “a daren jiya nagama da
wannan matsalar, sim card d'insa 3, akwai Contact 300 da 38, mtn yanada mutum
172, ya fara saka credit a layin shekaru 15 kenan, ranar 3/6/2005, glo 107, ya
fara amfani dashi shekaru 8 kenan, wad'annan sune Sim card d'insa da yake
mu'amulla da kowa a ciki, kuma anfi saninsa da su, akwai 6oyayyen layinsa Na
mtn shima, yafara aiki dashi shekaru 13 kenan, kuma mutane 59 ne kawai
acikinsa, sannan ba kowane yasan layinba, dan dukkan family nashi basu San da
zamansa ba, ita kanta mahaifiyar su
Munaya batasan anyi saving number a phone nata ba, suma da suka kirata basusan
da number a wayarta ba, dan baita6a kiranta da shiba, akwai matakan tsaro dake
tattare da Layin, hakanne ya tabbatar min da akwai abinda yake 6oyewa a Sim
card d'in, dan sai time to time yake amfani da shi, kiran matarsa da sukayi da
layin wannan shine kuskuren farko da suka tafka da Sameer ya samu hanyar musu
takun sauro. zan fara aiki akan layin na shigesu ta hanyar da basu zataba”.
Jinjina kai kawai Nuren yakeyi dan
mamaki, Galadima da banne, kamar yanda basirarsa take daban, ya sauke ajiyar
zuciya yana kama hannun Galadima da idonsa ke a lumshe har yanzun, cikin
karsashi yace “lallai kai RAINA KAMA ne Sameer”.
Murmushi kawai Galadima yayi, amma baice
uffanba.
Knocking akayi, Nuren ya kalli k'ofar
yana bada izinin a shigo, Sauban ya shigo da sallama, su duka idonsu a kansa,
Nuren yace “lafiya kuwa?”.
Zama Sauban yayi yana sauke Numfashi da
k'yar, cikin magana d'ai-d'ai da alamar a birkice yake yace, “wlhy Yaya binmu
aka ringayi da wata bak'ar Jeep, da k'yar mukasha wlhy, ni dai yau zanbar
k'asarnan gaskiya”. Sauban ya fad'a tamkar zaiyi kuka’.
Gani kawai sukai Galadima yana dariya,
saida yayi mai isarsa sannan ya tsagaita.
Nuren da Sauban suka tsaya kawai suna
kallonsa.
Tashi yayi tsaye yana takawa cikin izzar
k'asaita, ya dafa bango yana lek'en waje ta window d'in office d'in, yakai wasu
adadin lokuta a wajen, sai kuma ya juyo yana kallon Nuren d'in da Sauban da
suma suka zuba masa idanu.
“my dear brother! daka tsaya sun kamaka
ai, tabbas da wannan shine kuskuren da zasuyi Wanda bazasu ta6a mantawa da waye
Muhammad Sameer Saifudden ba a tarihin rayuwarsu. Waya gaya maka kana yawo
cikin 9ja ne batareda idon Sameer ba a kanka?”.
Sauban ya sauke ajiyar zuciya yana share
gumin daya jik'a fuskarsa, “wlhy yaa Sam daka fad'amin da bazan tsorata ba”.
Daga Galadima har Nuren dariya suka kwashe
da shi, Nuren ya dafa kafad'ar Sauban yana fad'in “matsoracin banza”.
“uhm-uhm yaa Nuren bazaka ganeba wlhy,
tsoro halak ne fa”..
Galadima dai baice komaiba ya koma ya
zauna yana murmushi.
★)))*(((★)))*(((★)))*(((★)))*(((★
Ganin har anyi sallar Magriba babu baba
k'arami balle Dady ya saka Innaro d'aukar gyale ta fito, lokacin gwaggo Safiyya
tana salla, shiyyasa batasan innaro ta fitaba, habiba da Naja'atu dake tsakar
gida suna tattare kaya saboda hadari na farkon damina dayake nuna alamar zai zubda
ruwa. suka kalli juna, Naja'atu tace “yaya habiba tsohuwarnan fa bata da dama
wlhy”.
Dariya habiba tayi, “ai kad'anma kika gani
Naja'atu, yanzu dai zataje ta tadama baiwar ALLAH hankali”.
“to ALLAH ya k'yauta”. ‘cewar Naja'atu
tana rik'e ha6a’.
Lokacin da Innaro ta shigo gidan d'akin
Innarsu Munaya ta nufa kai tsaye, sai dai ta iskeshi rufe, kwala kiran sunanta
ta shigayi cikin masifa, “Ai'sha!! Ai'sha!! Nasan kina jina, wlhy ki fito kafin
yau d'innan igiyar aurenki ta tsinke”.
Mamansu yaa Hameed da gwaggon Haleematu ne
suka fito, mamansu yaa hameed tace “aiko tafita fa inna, dan gab da magribar
nan naga Fadeel ya shigo sun fita, bansan mike faruwa ba dai”.
“yaza'ayi kusan mike faruwa tunda anyi
k'ulle-k'ullen munafunci, lallai jafaru, wai yau da kaine za'a muzantani hannun
mak'iyana, to nikuma naga ta yanda Ai'sha zataje wata k'asa jiyyar Auwalu da
raina”........ haka taita zuba banbamin masifa matan gida na saurarenta, daga
daddy har baba k'arami suna gidan amma sukak'i fitowa. Jarabar Innaro ta saka
kowa na gidan fahimtar mi ake ciki, nanfa hassada da bak'in ciki suka kume
zukatansu, dukda kuwa sunsan tafiyar bata dad'i baceba, maman fauziyyace kawai
hakan yamata dad'i, koba komai inna ta huta da cin zarafin Innaro koyayane.
Sai da Gwaggo Safiyya ta shigo tama
Innaro magana sannan ta tafi gida, su matan gidanma sai yanzu suka San da zuwa
gwaggo Safiyya d'in.
Amma sunso ace innarsu munaya na gida
Innaro tayi wannan rashin mutuncin.
Hummm😕.
****************************
Bayan fitowar su Galadima daga birnin
gayu, sun wuce gidane, Nuren kuma yakoma hotel d'in daya sauka.
Galadima kawai ne ya shiga sashensu,
amma Sauban 6angaren mai martaba ya nufa neman yarima Mahfuz.
Munaya na zaune a falon farko tareda sabbin
kuyanginta guda uku, (dan bata amince su shiga falonta ba, saita gama tantance
su sannan) ba wani hira sukeyiba, d'ayace a cikinsu ke sak'a shine abin ya
birge Munaya take kallo, tana kwance cikin doguwar kujera ne, yayinda su kuma
su ke zaune a k'asan lallausan carpet d'in falon.
Dogarai biyune suka fara shigowa hannunsu
d'auke da ledoji, sai kuma mai gayya mai aiki Galadima.
Da sauri bayin suka mik'e tsaye, saida ya
ida shigowa sannan suka d'urk'ushe a k'asa suna kwasar gaisuwa.
A la66ansa ya amsa yana d'aga musu hannu,
yayinda idanunsa ke kan munaya da itama ke satar kallonsa
Duk d'insu kowa janyewa yayi, yayinda
bayin da dogaran suka fice bayan sunkai ledojin falon Galadima.
Baice da ita uffanba yafara takawa zai
shige, tamkar mai tsoron fad'a tace, “sannu da zuwa”.
Ysayawa yayi cak, sannan ya juyo da kansa
tamkar mai ciwon wuya ya kalleta, bata yarda sun kuma had'a idoba takuma fad'in
“nagode sosai”.
“for what?”. ‘ya fad'a cikin isa’.
Shiru munaya tayi, ta kasa cewa komai.
Shima bai sake cewa komai ba ya taka ya
shige abinsa.
Harara munaya ta raka bayansa da shi, sai
kuma ta sauke numfashi tana tashi itama, bedroom d'inta ta koma, a saman sofa
ta zauna tana dafe kai, sosai take buk'atar zuwa sake duba mahaifinta, amma ta
kula Galadima bashida niyyar cemata taje, kai itako wannan wane irin abune
haka? shi dama gidan Sarautar haka yake bakada 'yancin kanka?, komai saida
k'a'ida. tun d'azu kuma take kiran number inna bata d'agaba, tadai kira baba
k'arami da daddy sun gaisa ta tambayi jikin Abba, shine ma har suke kuma sanar
mata k'ok'arin da galadiman keyi. tabbas hakan da yayi yasata jin farin ciki,
koba komai tasan shi adaline, ko anan gaba ragamar shugabanci ta riskesa
zaiyima na k'asa da shi adalci.
Galadima daya shiga tun a falo yafara
k'ok'arin cire navy blue d'in jacket d'insa, ya wullata saman kujera, sassauta
belt d'in yayi shima amma bai cireba, ya zauna cikin tsantsar nuna gajiya yana
furzo iskar bakinsa, remote ya d'auka ya kunna tv, tamkar ya saita lokaci saiga
hoton d'iyar minister mai amsa sunan Farhat ana nunawa, an saka 2.5 millions ga
dukkan wanda ya kawota koya bada bayanan sirri akan wanda yasan wani Abu akan
6atanta.
Wani mugun tsaki Galadima yaja a zuciyarsa
yana fad'in wawaye, saiku k'ara yakai 100millions ba 2 ba, idan ubanta ya
shirya kawo kansa gareni nima a shirye nake nabashi shashashar 'yarsa mai zubin
ta6arya, ya kashe TV d'in kawai ya mik'e ya shige ciki.
Ko ina fes da shi, yasan baida Matsala da
Sauban a 6angaren tsafta dama. kayan jikinsa ya ida cirewa ya shiga wanka.
Bayan ya fito samu yay yad'an kwanta, dan
ya samu Hutu kona 2hours ne, dan yanzu akayi sallar zuhur. aiko kwanciyarsa
babu dad'ewa barci yay gaba dashi.
Munaya ta jawo wayarta da nufin kuma kiran
inna, amma sai taga Ashe credit d'inta yama k'are, kanta ta dafe dan haushi,
zuwa can tamik'e domin bin shawarar zuciyarta. turare ta kuma fesama jikinta ta
d'auki gyale ta yafa.
Ta d'an dad'e a k'ofar d'akin tana
tunanin idan kuma ta shiga hasashenta bai zama gaskiyaba ya kenan?, wata zuciya tace kije abinki
k'ilama wanka yake.
Da sand'a na ida shiga tamkar wata
6arauniya, sai kuma na tuna ai yanada CCTV camera, nutsuwa nayi na daidaita kaina,
na koma normal saboda tsaro. Ganin babu abinda naje nema d'in a falo saina
zarce bedroom ina wani ciccijewa.
Mamaki ya kamani ganinsa kwance a kan gado
yana shak'ar barci hankali kwance, hakan yamin dad'i kam.
Saida nabi ko'ina na bedroom d'in da
kallo, ganin babu alamar akwai camera a nan saina ida shiga, wayoyinsa biyu na
ajiye gefen filon dayake kwance, rabin hannun damarsa ma nakan d'aya ya d'ora
cikin barci halan?.
Dole saina hau saman gadon, dan haka na
tsaya tunanin yanda zanyi, banida wata mafita dan haka nahau a hankali, kai
kace wata hawainiya ce.
Cikin rintse ido da cije la66a nakai
hannu zan d'auki wayar d'aya.
Caraf aka rik'emin hannu, babu Shiri na
bud'e idona zuciyata nawani tsitstsinkewa.
Fisgoni yayi na fad'o jikinsa, zafin
danaji ya sakani sakin k'aramar k'ara.
Ya matseni a jikinsa batare da ya
kula miya aikata ba. nikam jikina sai rawa yakeyi, tsorona karya d'auka ko
cutar da shi zanyi ma........ maganarsa cikin yanayin barci ta Sani kallonsa.
Kad'an ya bud'e idonsa dake jajir, alamar da gaske barci yakeyi,
muryarsa a sark'e irinta barci yace, “sata kika koma?”.
Baki na tunzuro ina marmar da idanu da
suka cika da kwalla, nace “ALLAH ya kiyaye, arafa zanyi”.
Kuma matseni yayi har saida na rik'e
hannunsa,, yace “wannan ba aro bane sata ce yalla6iya, dan haka dolene ki kar6i
punishment”.
Jin ya ambaci punishment saina kuma
rikicewa, nahau k'yarma ina rantse-rantae da matso kwallan idona.
Bai wani saurareni ba ya hau sumbatar
wuyana, tureshi nafarayi amma saina gaza, dan haka na koma mintsini, shima a
banza man kare😩.
Dukna d'auka wasa yakeyi kawai
farfaganda Ce danna tsorata, amma saina tsinci ya fara sakin layi, iya yina da
rok'o, yakushi, mintsini, ban samu ku6uta ba, saima salonsa yafara tasiri a
kaina, nima nai luf harda k'ok'arin maida murtani. saida naji zai kama wata
tashar nai azamar tsaidashi ta hanyar fad'in “please yalla6ai camera”.
Maganinki ai baby😝, su Galadima akwai bak'in wayo dai🤥😂, idan ta gaskiya za'abi ni banga abin punishment anan
ba🤣, dama yadawo 'Yar matsalarsa dai
tsautsayi ya kawo mai karanbani dason banza ta fad'a tarko😜🥳😆.
**********★********
Koda inna ta dawo saita had'ama su Aryaan
kayansu, da nufin su koma wajen mamansu yaa hameed harta dawo.
Amma suka tibire akan bazasu jeba, su
Uncle yace zaizo ya kaisu wajen Auntynsu.
Tun inna na lallashinsu harta kai ga
mammakesu suka fara kuka, daga nan sukai barcin dole.
Bata fasa had'a kayanba, tagama tsaf ta d'auki
akwatin zuwa d'akin mamansu yaa hameed.
Su Bintu kawai ta iske a falo suna kallo,
Aminu ne yace “innar 'yan 2 ina zaki da daddare?”.
Murmushi inna tamasa tana fad'in “kayansu
Aryaan ne Aminu........”
Bata gama rufe bakiba mamansu yaa hameed ta
fito. ganin innarsu munubiya da kaya saita had'e fuska. Inna bata damuba tace
“ga kayansu Aiyaan, saisu dawo nan da zama kafin na dawo”.
“to”. Kawai mamansu yaa hameed tace tana
kauda kai gefe.
Ran inna ya sosu, amma sai batace komai ba
ta ajiye ta fice jiki a sanyaye.
Da murnar Haneeff ya tashi zai d'au jakar
yakai d'akinsu, amma sai Maman ta watsa masa harara. babu shiri ya koma ya
zauna. Jakkar dai sai anan ta kwana, bata d'auka ba, bata bar 'ya'yanta sun
d'auka ba saboda bak'incikin inna zataje jiyyar Abba ba itaba.
ALLAH ya k'yauta😡.
****************************
Dakatawa yay daga abinda yakeyi, ya bud'e
idanu a hankali akan fuskata, murya k'asa-k'asa ya furta “camera?”.
Kaina na d'aga masa batareda na bud'e
idoba.
Bai
kuma cewa komai ba ya koma ya kwanta yana furzar da huci mai zafi daga bakinsa,
sai kuma ya cije lips yana gyara kwanciya da sake rungumeni kawai.
Idona na bud'e a tsorace, azatona zai
cigaba ne, sainaga ba haka bane.
A cikin kunnene ya furta “barci please”.
Kallonsa nayi ta gefen ido sai naga idonsa
a rufe, nima banida za6in daya wuce na rufe nawan, dan haka na lumshe kawai.
Ni sai barcin ya d'aukeni, amma shi ya
k'auracema idonsa, mamakin furicina ya dami zuciyarsa, dama yadad'e yana zargin
akwai camera a d'akin nan nasa, sai dai bawai ya tabbatar bane, kuma bai ta6a
yunk'urin dubawa ba. da wad'annan tunanin ya cinye lokacin barcinsa har aka
kwala kiran sallar la'asar.
Bud'e idanunsa yayi akan fuskata, yad'an
tsuramin ido nawasu time's, sai yaga barcin yamin k'yau, kauda idonsa yayi
cikeda basarwa, saikuma ya janyeni daga jikinsa yana yunk'urin tashi, hakanne
ya sakani farkawar nima, na tashi da hanzarina ina gyara rigata, sai kuma na
sauka na fice batareda nako waiwayoshi ba.
Bina yay da kallo harna fice sannan ya
janye yana ta6e baki.
Ban kuma jin labarin Galadima ba har
dare yayi, nafito wanka ina shirin barci ya shigo, yau dai babu laptop d'in
kaddara, dagashi sai phone guda d'aya ma, yana sanye da kayan barci kalar
gwaiduwar kwai masu duhu.
Zama yay a kujerar dake cikin d'akin,
yayinda ni kuma na k'arasa saka hijjab d'in dana jawo, babu walwala ko alamar
wasa kwata-kwata a face nashi, dan haka nima saina kama kaina.
cikin k'asaitarsa yace “muyi magana mana”.
Kallonsa na d'anyi, saikuma na amsa da
“ina jinka”.
d'ago ido yay muka kalli juna, da ido yay
min nuni da bakin gadon.
Ban musaba nazo na zauna, amma sai nayi
k'asa da kaina ina wasa da zoben hannuna.
Maida kallonsa yayi ga zoben danake
jujjuyawa, kusan mintuna 4 harna d'auka ya ma fasa maganar, na d'ago na
kalleshi.
Ya kauda kai gefe yana fad'in, “waya
fad'a miki da CCTV camera a d'akina?”.
Nima ban kalleshi ba na bashi amsa a
tak'aice, “bakai ka saka kayarka ba danni?”.
Da mamaki ya kalleni, sai kuma ya kausasa
muryarsa, “Munaayaa seriously nake miki magana!”.
nad'an razana, amma saina dake, nace
“kana nufin bakasan da itaba?”.
“idan nasan da ita mizai sani aikata wani
Abu na sirrina a d'akin”.
da
mamaki na kalleshi domin tabbatarwa, tsantsar gaskiya na hanga a idonsa, dan
haka na danna yatsun hannuna da k'arfi suka bada sautin “k'asss!, k'asan
zuciyata na tunanin minene sirrin nasa?”.
Idonsa a kaina ko k'yaftawa bayayi, nima
na d'ago mukaima juna kallon ido cikin ido, dukda tsorata danai da hango masifa
cikinsu ban janyeba, nafara fad'in “tabbas naga camera a falonka, tana nan
saitin hotonku kaidasu momma, inda flower d'in nan take, hakanne yasani zargin
kai ka saka kayarka saboda tsaro”.
“hummm”. kawai yafad'a yana janye
idanunsa, sai kuma ya taso ya dawo inda nake zaune, ganinai kawai ya rungumoni
jikinsa, na waro idanu dan mamaki, shikuma ya lumshe nasa tareda sumbatar
goshina a hankali, shigar sumbarce tasakani lumshe nawa idanun nima tareda
k'ank'ameshi.
Cikin kunnena ya furta “i'm proud of you
my friend”.
Da sauri na waro idanu ina kallonsa,
saiya d'agamin gira d'aya yana wani miskilin murmushi, sannan ya tadani zaune
shima ya tashi ya fita.
Baki da idanu da hanci duk na saki ina
binsa da kallo, a k'asan raina ina tambayar mike damun guy d'innan ne wai?.
Banida mai bani amsa, dan haka na mik'e
na cire hijjab d'in nai kwanciyata.
d'akinsa ya koma ya d'akko wani Abu
kamar k'aramar ball🎱 ya ajiye saman table d'in gaban
gadon, sannan ya manna wani dogon Abu a jikin 'Yar ball d'in, ya d'akko laptop
d'insa ya kunna. shiru na kusan mintuna uku ya k'urama abinnan ido, zuwa can
yafara wata k'aramar k'ara d'i! d'i! d'i!, sai kuma k'aramar danja ajikin
abinda ya manna d'in shima tana kawo haske
jaa da d'aukewa.
Murmushin takaici kawai yayi, a zuciyarsa
yanama ALLAH godiya dabai ta6a kusantar Munaya a d'akin nanba. dan tabbas ga
CCTV camera ya gani a d'akin, an sakatane can ta saman wardrobe, yanda ko alama
hankalinsa bazai kaiba, baiyi yunk'urin cirewa ba, ya d'auki kayan aikinsa ya
koma parlour, dan yaga itakuma tanan a ina take?. yanama shigowa tun'a k'ofar
tsakanin bedroom da falon ya gani, baima k'arasaba ya koma ciki, kashe laptop
d'in yayi ya d'auke k'aramar ball d'in ya 6oye.
Duk wannan hidimar da Galadima keyi Sauban
na kwance bisa gadonsa yayi d'ai-d'ai yana kwasar barci.
Gyara masa bargo yayi saboda tasowar
hadarin farkon damina da iska tafara kad'awa sanyi ya busa. daga nan ya kashe
masa fitila ya fita zuwa d'akin Munaya.
Ita harma tayi barci, tana k'ank'ame da
fillo saboda sanyin hadarin dake busawa, gadon ya hau tareda warware bargon ya
lullu6a musu. dai-dai iska ta taso mai azabar k'arfi, a rikice Munaya ta juyo ta
k'ank'amesa saboda tsorata.
Rik'eta yay sosai yana fad'in “uchh!
Karki karyani”.
Babu shiri munaya ta bud'e idonta, tana
k'ank'ame da shi tace, “wai miyasa bazaka ke kwana naka d'akinba ne?”.
“k miyasa time d'in da kikaje India kika
gajemin d'akina?”.
Shiru tamasa bata amsaba, amma yanajin
alamar murgud'a bakinta akan k'irjinsa.
“punishment ya tabbata agareki
yalla6iya”.
Da sauri nace “wlhy a'a, inba hakaba zaka
koma saman sofa ne, ai kaima haka kamin a d'akinka”.
“uyim Madan tsiwa, to ai nima dankar ki
murk'ushemin abin cikin kwan cikin barci yasani kwantawa anan?”.
Zan bashi amsa aka kwad'a wata tsawa data
sakamu ruk'unk'ume juna babu shiri, sai kuma ruwa ya 6alle.
Da wannan damar Galadima yay amfani wajen
canja salon kwanciyar tamu, tun ina nuna banaso har salonsa ya sakani sakin
layi, (😆anya munaya wannan cikin naki bashine tarkon da
Galadima ya d'ana miki ba?😜).
Da asuba tashi nayi inata
zum6ure-zum6ure, baice dani uffanba yashiga toilet ya tsarkake jikinsa. Bayan
yafito nima na shiga.
Baki ya ta6e yana wani d'age gira d'aya
tamkar ina kallonsa ya fice.
Saida nasha kukana sannan nayi wankan
tsarki, narasa mike sakani biyema Galadima? insha ALLAH zan d'auki mataki (🤣idan babu abin cikin kwan ba😂, nasan inhar yana nan babansa zaita samun bonus😜).
Bayan na
idar da sallar ban koma barciba, saina gyara d'akin nayi wanka, shirin fitarma na sake yi yau, dan baba k'arami yacemin k'arfe
goma na safe zuwa 11 zasu tafi.
Kammalatawa kenan ya shigo, ko kad'an banji
alamar shigowarsa ba, saida na gama fesa turare ina k'ok'arin ajiyewa na hango
kamar mutum tsaye a bayana.
Da sauri nayi azamar juyowa, dayake yana
gab dani kad'an ya rage na fad'a masa a jiki, na dai samu nad'anyi baya na
jingina da mirror ina tura baki.
Ko motsi baiyiba shikam, bai kuma janye
idonsa daga kallona da yakeba.
Haushi ya kamani, nima nabi jikin nawa da
kallo kozanga abin da yake kallon, ganin babu wani Abu daya faru na d'ago na
kuma kallonsa, “wai yalla6ai mi kake kallone haka?”.
d'an yatsansa d'aya yasaka yad'an shafi
girarsa yana gyara tsayuwa, “abin cikin
kwan mana”. ‘ya fad'a cikin basarwa’.
“ta gefensa na ra6a zan wuce ina fad'in
“ai lokaci kad'an ya rage maka ka bar ganin nasa”.
Da sauri ya rik'o hannuna, na juyo muka
kalli juna, mayun idanunsa ya saka cikin nawa, “kina zaton idan nabar ganinsa
kema za'a cigaba da ganinki?”.
Guntun murmushi nayi ina janye idona daga
cikin nasa, nace “kana zaton kasheni zakayi nima?”.
“cire maganar ma zato”.
Kallonsa na kuma yi, cikin yanayin da shi
kansa bai ta6a zaton ina dashiba nace “saika fara shiri”.
Shima a dake yace “dama a shirye nake
kullum”.
Na murmusa ina k'ok'arin cire hannuna daga
cikin nasa, amma ya hanani damar hakan, kallonsa na kuma yi nace “ko har
lokacin yayi ne?”.
Fisgoni yayi na koma da baya, ya mannani
jikin mirror d'in tare da maida hannuna baya ya rik'e, ya matseni da jikinsa,
fuskarsa gab da tawa tamkar zai had'a bakinmu, yayinda idonsa ke cikin nawa,
wani miskilin murmushin gefen baki yayi, yasaka yatsansa yana zagaya janbakin
dake kan la66ana a hankali, cikin muryarnan tasa mai kama da an masa dole ya
fara magana cikin karsashi “ko Ubangiji yakanyi hukuncine ga bawan daya
bijirema umarninsa, koda ace zubarda wannan cikin kikayi dolene saikin kuma
d'aukar wani, zubar da shi na dai-dai da haihuwar yara goma anan gidan kafin na
aikaki inda shima ya tafi” ya matsa la66ana da k'arfi, wani zafi ya ratsani
saiga hawaye a kumatuna, murmushi yayi, yasaki la66an ya dangwali hawayen a
d'an yatsansa, nunamin yay yana fad'in “lallai momcyn abin cikin kwan kin
cancanta 100%, amma bayan abin cikin kwanfa akwai k'annensa, please bar kuka my
dear friend”. ‘ya k'are maganar da sumbatar la66ana sannan ya sakeni yaja baya.
Koda ya sakeni sainayi murmushi kawai,
sannan na juya ina fuskantar mirror, foda na d'auka na gyara fuskata, na sake
saka jambaki kad'an kamar yanda na saka d'azun.
Tsayawa yay cikeda mamakin abin da nayi na
ko inkula yana kallona, mi wannan yarinyar take shiryawa ne haka?.....
Kafin ya samu amsa Na juyo gareshi, fuskata
d'auke da murmushi na ra6a zan wuce sa, bina kawai yay da kallo, naje gaban
wardrobe na bud'e, alk'yabba na d'akko na sanya, sannan na d'auki handbag ina
kallonsa har yanzu fuskata d'auke da murmushi.
Gira ya d'agamin shima yana wani
k'asaitaccen murmushi, ya juya ya fita batareda yakuma magana ba.
Yana fita na sauke ajiyar zuciya ina dafe
k'irji, wlhy ni kad'ai nasan dukan da zuciyata takeyi, kad'an yarage ya ranfo a
tsorace nake, kalamansa ne suka shiga dawomin cikin zuciyata, mi wannan yake
nufine wai..........?
“Shin bazaki bane?”.
Muryarsa ta daki dodon kunnena, da sauri na
gyara yanayina na d'ago muka had'a ido, Ashe yana bakin k'ofar bai tafiba.
Bance komai ba na biyo bayansa.
A falon farko na iske kuyangina suna
gaidashi, hannu kawai ya d'aga musu ya fice abinsa.
Tsayawa nayi muka gaisa, d'aya a cikinsu ta
yunk'urin k'ar6ar handbag d'ina.
Na iske harya shiga mota, nima aka bud'emin
na shiga, handbag d'ina ta mik'omin tana fad'in “ranki ya dad'e ana buk'atar
rakkiyarmu ne?”.
Murmushi namata, na juya na kalli Galadima
danjin mizaice, kansa ya girgiza alamar a'a.
Juyawa nima nayi na girgiza mata kai,
tamana addu'a tana rufe k'ofar.
Tunda muka tafi babu wanda yace uffan,
yanata latsa wayarsa.
Airport muka nufa kai tsaye.
Bayan motocin sun tsaya sarkin mota na
yunk'urin fita yace “2 minutes ”.
Sarikin mota yace “to ranka ya dad'e”.
Ni ban fahimci mi suke nufiba, naga dai
sarkin mota ya fita mukuma ba'a bud'e mana ba, sai kawai nakai hannu zan bud'e.
Hannuna ya rik'o, na juyo ina kallonsa,
har Yanzu idonsa nakan waya,, ajiye wayar yayi ya juyo yana fuskantata, ina
yunk'urin tambayar lafiya naji la66ana cikin bakinsa.
Ya salam, na fad'a a zuciyata, saida ya
shanye janbakin la66ana tas sannan ya sakeni. yanda kukasan gunki haka na koma
masa, ya buga yatsunsa biyu saitin fuskata suna bada k'arar d'as d'as yace
“gargad'i, first and last dazanganshi abakinki yayin fita”.
Harya fita ban iya motsawa ba, saida aka bud'e
murfin 6angaren danake sannan na iya sauke numfashi, na kasa fahimtar damuwar
guy d'innan kwata-kwata. fita nayi nima, yana tsaye yana jiran fitowata. a tare
muka jera muna tafiya, yayinda dogaransa ke take mana baya. ya wani miskile
fuska tamkar bashine yagama ta6argaza ba a mota yanzun.
Mutane sai kallonmu suke, masu gulma nayi
masu nunamu nayi, ni dai duk sainaji wani iri, shima tsaki yayi danya tsani
kallo.
A mamaki na duk sai naga 'yan gidanmu ma a
wajen, gaggaisawa muka shigayi, muka rik'e hannun juna nida munubiya muka
k'arasa inda innarmu take, gaisheta nayi, nace “su Aiyaan fa?”.
“suna gida zasu zauna da mamanku mana”.
“kai innarmu, ya zaki barsu wajen
muguwarnan, bama gara Maman fauziyya ba komu suzo wajenmu”.
Murmushi kawai innarmu tayi, tace, “ashe
bazaki canjaba Munaya?”.
6ata fuska nayi, ina fad'in “kai inna,
duk canjawarnan danayi”.
Murmushi sukayi itada Munubiya. akuma
dai-dai time d'in Ambulance ta shigo airport d'in, sai mota biyu a bayanta sai
motar police guda d'aya.
Gaba d'ayanmu hankalinmu saiya koma can,
Galadima ya k'arasa wajen Ambulance d'in, yayinda sauran motocin biyu Sauban da
Nuren baba k'arami Dady ya Shafi'u da yaa Naseer yaa hameed suka fito.
Zuwansu baifi da mintuna 15 ba aka fara
kiran sunan wad'anda zasu tashi a jirgin.
Sai kuma ma'aikatan wajen mutum uku suka
iso wajen Ambulance d'in aka fara k'ok'arin fidda Abba. Hankalin jama'a da yawa
ya tashi a airport d'in nan saboda tausayin Abba, mukam kuka ma wasunmu sukeyi
ai, muna kallo aka gungura gadon da aka d'oroshi har zuwa ga jirgin.
Suma su innarmu suka shiga itada baba
k'arami da Sauban.
Rungume juna mukayi nida munubiya muma muna
kuka.
Galadima bai fito cikin jirginba saida yaga
komai ya dai-daita. yana fitowa babu dad'ewa jirgin ya d'aga zuwa sararin
samaniya, yayinda mukuma muke binsu da addu'oin fatan alkairi da samun
sauk'i.................✍🏼
🤥kutt harda na gobe nayi🙄⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀.
*_ALLAH ka
gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
No comments