RAINA KAMA (BOOK 2) 26&27
_Writer's namu ina mik'o gaisuwa da
babbar murya_.🙋🏻
*_(takwara) Bily s Fari, (mamana)
Maryam IG, (mamana) Ummu hanan, Hauwa'u A Usman (jidda😘) Rufaida Umor, Qurratul ayn, Ai'sha Alto, Leemat,
gwoggo😜
Asykhaleel, miss Xakss, Jameela Janaf, (takwara)
Ummie Garkuwa, Khadeeja Candy, Billy Sarki, Sister Naja'atu, Reefat yahya,
Sad-Naf, Maryam wasagu, Maman Shaheed, classic Feedo, Mzzdady._*
🙆🏽 _Yawane
da kufa. Alkairin ALLAH ya kai gareku aduk inda kuke, bilyn Abdull na nayinku
wujiga-wujiga🥰😘😘👍🏻_
___________________
~Book 2~ 👉🏻2⃣6⃣
...................MC
yafara shelanta cewa wannan bikin sunafa an had'ashi da bikin birthdays ne,
domin ranar haihuwar yaran tai dai-dai da ranar haihuwar iyayensu, dan haka
suka had'e wannan biki a yau guri d'aya, dan a waccan ranar murnar haihuwar
bata basu damar yanka cake ba😂.
Dariya aka sanya, saboda a yanayin
barkwanci mc yayi maganar, Galadima kam ai kod'an murmushin ma baiyiba, garama
Yaa marwan ya murmusa.
Galadima ya kalli munaya, cikin
maganar nan tasa mai kamada an masa tilas yace, “Kina da sa'a”.
“Sa'a kuma?”. ‘Munaya ta fad'a cikin
yanayin mamaki’.
Harya bud'e baki zaiyi magana sai kuma
ya basar. ganin haka itama Munaya saita sharesa, dan takula yau y'an mulkin ne
a kansa.
Saida ya gama shan k'amshinsa sannan yace,
“wannan ne karon farko da Sameer yata6a bikin birthday”.
Baki munaya ta d'an ta6e, tana fad'in
“Humm, kodai y'ay'anka suna da sa'a?, domin dai a dalilin haihuwarsu ne kayi”.
“ko kina jealous ne?”. ‘yay maganar cikeda
basarwa’.
tura baki tai gaba.
Idonsa akan yaransa yace “idan kika bari
na kama wannan bakin a wajennan humm.” ya cije lips d'insa.
Sanin k'aramin aikinsane ya akaita abinda
ya fad'a d'in ya sata saurin gyara bakinta , tad'an saci kallonsa, ya wani
Fiske tamkar ba shine yay maganar ba ma. ita dai tana mamakin kasaita da izza
irinna bawan ALLAH n nan, jinin mulki yana da matuk'ar k'arfi a jikinsa.
tunaninta ya katse lokacin da hankalinta ya koma kan abinda ke faruwa a hall
d'in
Khaleel da Aiyaan, Aryaan ne suka turo
cake mai k'yau da tsari, Wanda yasha kwalliyar White and Golden, an saka sunan
Galadima da shekarunsa 31years a sama, a jikinsa kuma daga can k'asa ansa
Muhammad Sameer (Dadyn Triples), an
d'ora candlestick🕯guda
uku, Sai hotonsa da yay k'yau sosai cikin shigar sarauta.
Galadima ya kalli Sauban da Samha, yasan
dai wannan aikinsu ne, k'in kallonsa sukayi sukam ballema suyi gamo da tsarabar
harara😅.
Ita Munaya ma sai yanzu taga Su Aiyaan,
batayi zaton anzo da suba, tunda bataga yaran gidansu k'anana ba a waje, sai
manya maza da matan Na ma'auri.
MC ya taso k'eyar su Khaleel har inda
su Galadima suke zaune, kowanne aka d'ora masa yaro d'aya, suma mik'ewa sukayi
bisa umarnin MC d'in, a tare suke takawa ita da shi, sai k'yastu ake zuba musu,
masuyi a waya da masu cameras, sai gidajen TVs d'in da aka gayyata suna nuna
live. Sun Isa gaban cake d'in hannunsa rik'e da sandarsa, kaikace sarkine da
kansa (gaskiyar Munaya Galadima akwai k'asaita, Kodai sarkin da Kansa ya shafa
masa lafiya🤭).
Bayan anmasa wak'ar happy birthday
yayma munaya nuni waita hura candles d'in.
Cikin k'asa da murya tace, “yalla6ai bafa
haka akeyiba, ka hura abinka da kanka”.
Hannunta ya kama ya matsa yanda zataji
zafi, yace, “zakiyi?”.
Ai baima kai k'arshen maganarba ta
risina ta hure wutar, hall d'in ya d'auki tafi. cake d'inma dan rigima wai
saidai su yanka tare.
“haba yalla6ai, saikace Na wani aure?”.
Cikin ta6e Baku yace, “wama ya sani kona
auren ne”.
Shiru tayi bata tanka ba, dan itadai
fatanta a rabu lafiya, hannunta ta d'ora kan nasa dake rik'e da wuk'ar suka
yanka taren. nanma dai tafin akayi. Ya lakata a d'an yatsa ya duk'o gasu Aiyaan
ya daddan gwalama yaransa a hanci da kumatu, sannan ya juyo ga Munaya da haushi
ya kamata, ai ita yakamata ma yafara sawa ba yaranba.
Itama akan hanci ya shafa mata
yana fad'in “yalla6iya haushi kikajine?”.
Kafin tabashi amsa yakuma lakata ya
shafama Aryaan Khaleel da Aiyaan suma.
Dole munaya ta had'iye maganarta. Amma ta
kudiri saita rama.
Itama itada Munubiya k'aton cake nasu aka
kawo kalar pink and White , Munu da Yaa marwan suka taso a tare.
Munaya da Munubiya suka rungume juna
suna maijin dad'in tunawa da ranar haihuwar su, shekaru 20 cif da kwana 7. Sun
yanka cake atare suka sakama juna abaki kad'an-kad'an, sannan kowacce cikin son
tsokana ta lakatama y'ar uwarta a fuska suka rungume juna suna dariya da
k'ananun hawaye, suncika shekaru 20 ranarda yaransu sukazo duniya suma.
Abin ya birge mutane, Munubiya ta matsa ga
mijinta ta saka masa a baki kad'an, cikin murmushi yace, “happy birthday my
heartbeat ”.
Tace, “Thanks you my luv” k'arasawa tayi ta
sakama yaran munaya dasu Aryaan a kumatu, sannan ta sakama nata yaran.
Munaya danta rama abinda Galadima
yamata, takai cake bakinsa kamar zata bashi, saida ya bud'e baki saita juya ta
shafama yaran Munubiya a kumatu, sannan nata.
Yanda Galadima yay shock akan abinda
Munaya tamasa sai mutane suka sanya dariya suna tafa mata, mai martaba da papi
ma dai saida suka Murmusa.
Munaya ta dawo ta dangwalama Galadima
akan hanci tana masa gwalo.
Shi kansa baisan k'asaitaccen murmushin ya
kufce masaba, ya saka handkerchief ya goge yana dawowa mazauninsu ya zauna.
Daga nan aka fara gudanar da wasa,
Comedian's sukazo sukad'an saka mutane dariya, saikuma mawak'a da suka bada
nasu salon.
Tun da Galadima ya fara yawaita kallon
agogon hannunsa su Muftahu duk suka sake shiri, dan lokaci yana gab kenan.
Galadima yay k'asa da murya batareda ya
kalli Munaya ba, yace “ki shirya, shirinsu na farko d'aukewar wutar hotel d'in
nan gaba d'aya, na gaba kuma shine banida tabbas. Yara dai ALLAH yana tare dasu, gakuma su Aryaan
suma”..
Cikeda mamaki Munaya ta kallesa, sannan
ta kalli yaran dake gabansu a wani d'an gado mai k'yau.
Jikinta har rawa yake tace, “yalla6ai mi
su Aryaan zasu iya? Please k.....”.
Hannu ya d'aga mata alamar karfa ta ishesa
yace, “wani ilimin aduhuwar daji kawai ake laluboshi, kinsan kuwa dolene a gamu
da had'arurruka Aciki”.
batada za6i sainyin shiru, ta kalli su
Khaleel daketa wasa da abinci a teble da suke zaune hankalinsu kwance. Hawayene
ya cika mata idanu, yama za'ayi wad'an can sakarkarun yaran ace suna masu bama
yaranta kariya? Yaushe suka gama sanin ciwon Kansu ma balle na waninsu? gaskiya
wannan gangancine kawai, tasa handkerchief ta share hawayen da ke k'ok'arin
zubo mata.
Duk abinda take Galadima yana kallonta.
duk tausayinta saiya kamashi, ya tuna da wahalar datasha, amma bashida za6in
daya wuce hakan, kuma itace tabashi k'arfin gwiwa ai, yasaka aransa ko salwanta
yaransa sukayi zaiyi tawakkali insha ALLAH.
Duk Wanda yake cikin shirinsu
Galadima ya gama shirinsa, haka suma mak'iya masu buri a shirye suke.
Gaba d'aya saura mintuna 25 atashi,
saboda gabatowar sallar magrib, a kuma time d'inne Sarki Abdul-fatah da Sarki
jalalludden dadai duk wani babba Wanda sukazo tare suka mik'e domin tafiya,
ganin haka Galadima yama Yaa marwan sigina da ido akan ya fita da Ameen and
Ameena suma, yabi tawagar su papi, dan baya buk'atar a cuta musu..
Jikin Yaa marwan a sanyaye ya d'auki
yaran ya fita cikin dabara, yana kallon y'an uku, shidai dan kawai Galadima ya
dagene, amma bai kamata a saka yarannan a matsayin tarko ba.
Munaya ma dai ta danne zuciyarta tayi
shiru, tanason bama Galadima kwarin gwiwa.
Su papi na fita y'an rawar k'oroso suka
fara wasa, mintuna goma da aka basu ya k'are, sai wani mawak'i ya fara nashi,
nanfa y'an mata da samari aka samu nayi, dama ganin su mai martaba ne ya sakasu
nok'ewa, ana tsaka da cashewa hall d'in yay d'iff, wuta ta d'auke agaba d'aya
hotel d'in, mutane aka fara hayaniya kowa na k'ok'arin damk'e dukiyarsa a hannu
da k'ok'arin kunna fitulun waya.
Gaba d'aya jikin Munaya yahau 6ari,
ta fashe da kuka tana laluben gadon da yaran suke, ruk'ota Galadima yay yasaka
a jikinsa, muryarsa na rawa yace, “please ki nutsu”.
“bazan iyaba yalla6ai, karsu......”.
Yay saurin rufe mata baki, da tattausan
tafin hannunsa..... A dai-dai wannan lokacinne kuma wutar hotel d'in tadawo.
Hall d'in ya kuma kaurewa da hayaniya,
zaram Munaya da Munubiya suka nufi gadon da yaran suke ciki, wayam babu komai.
Munaya tayi luuu zata fad'i, saurin
ruk'ota Munubiya tayi, Galadima yataso daga inda yake shima zuwa garesu. hall
d'in yagama rikicewa da tsantsar hayaniyar rashin ganin yaran, sai kallon kallo
akeyi. Securitys d'in da aka baza sun rikice da wannan tashin hankali, dan sune
mutane na farko da za'a fara tuhuma.
Rufe hotel d'in akayi aka hana kowa shiga
balle fita,
Galadima ya shafama Munaya ruwa ta kawo
numfashi, fashewa tayi da sabon kuka ta fad'a jikinsa, hannu biyu ya saka ya
rungume ta shima yana had'iye kwallar bak'in cikin dake Neman zuboma idonsa.
Tausayinsu ya kama mutane da yawa,
innaro harda kukanta, hakama inno, abinda yabani mamaki shine tsantsar damuwar
da mama Fulani ta nuna, dan itacema tabama Galadima ruwa ya shafama Munaya ta
farfad'o.
Da farko Munaya ta d'auka ko Galadima wasa
yake mata yasan inda yaran suke, amma ganin
damuwar da yake ciki saita kuma rikicewa, dandanan numfashinta yafara
gagarar k'irjinta, ta mik'e a kid'ime, dan taji a jikinta kuka sukeyi, nononta
sai tsitstsirawa suke, wani jirine yafara hajijiya da ita da zuciyarta ta
k'iyasta mata zafa su iya kashe mata yara, luuuu tayi baya Galadima ya ruk'ota.
sume musu ta kumayi.
Hankalin Galadima kuma tashi yayi,
dole ya d'auki Munaya aka sakata a mota suka bar hotel d'in.
Sauran mutane kam kowacce mota zata fita
sai an binciketa.
Yayinda Securitys d'in suka bazu ko ina na
hotel d'in ana bincikawa.
Gida aka wuce da munaya, har suka isa tana
jikin Galadima, yanata murza tafin hannunta kozata farfad'o, har d'ora bakinsa
yayi akan nata ya jawo iskar numfashinta amma a banza, hakanne yakuma tada
hankalinsa.
Kai tsaye d'akinsa ya wuce da ita, ya
shimfid'eta a kan gadon ya cire mata alk'yabbar jikinta, Akash suka k'araso da
hanzari shima, taimakon gaggawa yafara bata shida doctor jalal, cikin amincin
ubangiji saigashi takawo numfashi, bama su bari tadawo dai-dai ba suka mata
allurar barci.
Suna fita Galadima ya cire rawani da
alk'yabbar jikinsa shima, ya sassauta bottom d'in wuyan rigarsa.
Safa da marwa ya shigayi a tsakar d'akin
yana Mirza agogon hannunsa Wanda daka gani kasan ba normal agogo bane,.
Wayarsa datai k'ara yay saurin d'auka,
d'agawa yayi yasaka a kunne, “Muftahu ya ake ciki?”.
Cikin hakki Muftahu yace, “komai yana
tafiya yanda ya kamata ranka ya dad'e, har yanzu gamu muna bin bayansu, amma
munkai inda yakamata ka fara Controlling namu, yanzu mun.......”
Da sauri Galadima ya katseshi ta hanyar
fad'in “karka damu ina kallon Ku, saidai kilometer's d'in dake tsakaninku dasu
fa yakai 1½, Saleem da Sauban sunfi kusa dasu, dan haka ku k'ara azama. daga
lokacin da suka farga da abinda nasaka jikin Amaturrahman tabbas zasu cireshi,
kuma zamu rasasune gaba d'aya”.
“Ok babu damuwa, ranka ya dad'e”.
Yanke wayar sukayi, Galadima ya bud'e
wani k'aramin akwati ya fiddo kayan aiki wanda a ready dama yagama had'a komai,
bajesu yayi akan gadon kusada Munaya, ya zauna yafara Control cikin matuk'ar
kwarewa.
Saleem ya kira aunty Salamah wadda itama
take tare dasu Ameer yaran da suka sace Muftahu, d'agawa tayi jikinta na rawa,
“Saleem kuna inane?”.
“Aunty Salamah gamunan bayansu kad'an,
amma mund'an basu k'afa saboda na kula sunfara fuskantar muna bin su, yanzu dai
haka mun ajiye motarmu mun samu mashin”.
“Hakan yayi, insha ALLAH indai ta Anguwar
da muke tsammanin zasu shigane kamar yanda kaji Harun d'in yay magana to tabbas
mu dai mun iso, saidai suzo su iskemu, ka kira yalla6ai ka sanar masa yakamata
ya fito yanzu”.
“no Aunty Salamah, bazai yuwu boss
yabaro masarauta ba yanzu, saiya tabbatar mun Isa, saboda dukma inda suka shiga
yana bibiyarsu, dan bazai saka yaransa a matsayin tarko ba babu tsaro k.......”
Tai saurin k'atseshi ta hanyar fad'in
“yauwa ina zargin kamar gasunan a wata bak'ar mota sun wicemu fa”.
“Alhmdllh, su Ameer Susan yanda zasuyi
su bisu bara na kira boss”.
“ok”. Kawai Aunty Salamah ta fad'a ta
yanke wayar.
Kiran Galadima Saleem yayi, bugu biyu ya
d'auka, “Saleem mike faru yanzu?”.
“Ranka ya dad'e gamu dai biye dasu, amma
Aunty Salamah tacemin gasu tagansu”.
“wacece Salamah? ”.
Gaban Saleem ya fad'i, dan ya manta
Galadima baisan Salamah ba, “Am sorry sir, idan komai ya dai-daita zan maka
bayani”.
“Saleem!!!”. Galadima ya kirayeshi a
tsawace.
Saida Saleem ya janye wayar akunnensa,
muryarsa na rawa yace “ka yarda dani sir, wlhy itama ta kwarai ce”.
Ajiyar zuciya Galadima yayi, muryarshi
cikin tsantsar damuwar yace, “wannan anguwar da kuke tanada hanyoyi da yawa,
dan haka Ku fara amfani da live GPS navigation maps naku, yanzu zanyi settings
komai yanda zaku ringa ganinsu duk layin da zasu shiga insha ALLAH, waye yake
driving d'in a cikinku?”.
“nine sir”.
“ok bama Sauban wayar”.
Saleem ya mik'ama Sauban wayar,
Galadima na fad'a masa yanda zaiyi, shikuma yana Controlling maps App d'in dake
cikin System d'in cikin kwarewa, (dan shima Galadima bai barsa hakaba, dukda
bashida ra'ayin karantar wannan fannin saida ya tsaya tsayin daka ya koyan
saboda irin wannan ranar).
Saida Galadima ya tabbatar komai ya
dai-daita, sannan ya kira su Nuren ma, suma suka dai-daita komai nasu, cikin
sauk'i duk suka koma ganin inda yaran suke, saboda Galadima ya saka Abu jikin
Amaturrahman, dukda bawai hotonsu ko video suke kalloba kai tsaye.
Duk da haka Galadima ke fad'a musu su
shiga layin haggu, ko dama, kosu canja hanya dadai sauransu.
Duk Wanda yake a wannan masarauta yau
hankalinsa a matuk'ar tashe yake, saifa kallon kallo da hasashen juna ake a
zuciya, kowa yana zargin Wanda ya raina.
Hankalin Abie a matuk'ar tashe ya
nemi ganin Galadima, koda sarkin k'ofa yazo yana knocking Galadima bai amsaba,
kuma yana kallonsa ta CCTV.
d'an aike ya koma ya sanar Galadima ya
kulle kansa a d'aki yak'i bud'e k'ofa.
Papi inno ya kira, yace maza taje sashen
Galadima taga mike faruwa.
Ko kuyangi inno batajira sun mata
rakkiyaba, hasalima babu Wanda yaga fitowarta a sashen mama Fulani, dan kowa a
rikice yake da wannam bak'on lamari na satar yara.
Galadima daya ga sarkin k'ofa yabar
wajen ya mik'e shima daga gaban kayayyakin da yake aikin, shaddar jikinsa ya
cire yasaka bak'in wando da t-shirt, ya kawo bak'ar jacket mai k'yalli kamar
rigar sanyi ya ajiye gefe, a bakin gadon ya zauna yana d'aura takalminsa yana
cigaba damasu Sauban da Nuren bayanin hanya, a dai-dai lokacinne Inno ta iso
sashen nasa, da hanzari Sarkin k'ofa ya bud'e mata k'ofar, bata jira wani isoba ko masa sallama ta turo
k'ofar falonsa ta shigo, babu kowa a falon, komai ma a kashe yake. Bedroom
d'insa ta nufa, nandai saida tayi knocking kam, saidai kafin yay yunk'urin
tasowa ya bud'e mata ta turo k'ofar ta shigo, mik'ewa yay yana kallonta da
d'aukar jacket d'insa zai saka.
Ajiyar zuciya inno ta sauke,
saboda ganinsa normal.
“Ranki ya dad'e da kanki? lafiya
dai ko?”.
“Inafa lafiya Muhammad? takawa ya aiko a
kiraka ance ka kulle kanka, gashi baka sanar mana halinda yarinyar nan take
cikiba”.
Galadima yace, ba kulle kaina nayiba,
bansan kuma d'an aiken daga papi yakeba” ya juya yana kallon Munaya da cigaba
da fad'in, “itama ta farfad'o, amma sun mata allurar barci”. ‘ya k'are maganar
da daidaita zaman kwalar rigar jacket d'insa’.
Ajiyar zuciya inno ta kuma saukewa, tace,
“to Alhmdllh. ina kuma zaka naga kana shiri?”.
Wani murmushin takaici yayi zuciyarsa
dake gudun daya wuce kima da suya ya dafe, Inno dai ta zuba masa ido, takowa
yay inda take ya kama hannunta ya rankwafo (dan yafita tsaho) ya d'ora bisa
kansa, cikin murya mai nuna tsananin karsashi da alwashi yace, “kisamin albarka
inno, zanje farautane”.
Da sauri ta janye hannunta daga kansa tana
matsawa baya, “Muhammad mikake nufine? kana ganin tashin hankalin da muke ciki
shine zaka k'irk'iro mana wani kuma? kana tunanin wad'annan mutanen zasu
barkane? dama kai suke fako, shiyyasa sukayi tarko da bayin ALLAHn dabasu ji ba
basu gani ba, su takawa cikin k'ok'arin d'aukar mataki suke, yanzu haka naga IG
da kansa gashican ya iso bisa umarnin kiransu”.
Galadima dake tattara abinda zai amfani
dashi yana zubawa a aljihu, yace, “inno Muhammad Sameer d'inku ba ragon namiji
bane da zai zauna jiran Police d'in da suka gaza gano wad'anda suka durk'usar
masa da mahaifi tsawon shekaru a yanzu kuma nayi tunanin zasu iya dawomin da
gudan jinina har uku, ba sune sukamin tarko ba nine namusu tarko, idan tsoron
na mutu kuke, Ku cire inno, ko babusu mutuwa tabbataccen abune rubutacce a
kundina, kimin addu'a saina saina dawo”..
Biyosa inno tayi har babban falo tana
Kiransa amma yak'i dakatawa, saima d'aga mata hannu da yakeyi, yana gab da zai
fita ya juyo yana fad'in “karki d'aga murya da yawa ranki ya dad'e, dan kunnen
magauta a bud'e yake”.
Yana fitowa Sarkin mota ya taso, dan
suna zaune jigum-jigum a rumfar bunun dake sashen na Galadima, duk gaisuwar da
suke masa babu ta wacce ya amsa, yau kam ko d'aga hannun basu samuba ma.
Basu damuba dan dolene kowa yamasa uziri.
Da kansa ya bud'e mota ya shiga mazaunin
driver, Sarkin mota daya k'araso yace, “ranka ya dad'e ka gafarceni gani”.
Da hannu yamasa nuni da gefen mai zaman
banza batareda yace uffan ba.
Sarkin mota bashida za6in daya wuce
zagayowa ya shiga.
A 360 Galadima ya ja motar, kamarma ya
manta yana cikin masarautane, saida suka fito gaba d'aya sannan ya bud'e baki
da k'yar yace, “ka dinga kallon bayanmu, dan nasan dole za'a samu masu binmu”.
Da “to” sarkin mota ya amsa cike da
girmamawa.
Sarkin mota yace, “tabbas ranka ya
dad'e ana binmu”.
Cije lips Galadima yayi, ya canja hanya,
cikin salon iya taku suka 6acema su Harun dake bin su tundaga masarauta.
Hankalin Harun ya tashi kwarai da gaske,
dan bai shirya fito na fito da Galadima ba yanzu, saiya cimma burinsa, daga nan
komai ta fanjama fanjam, iya zagaye-zagayensu baiga ko motar datai kama data
Galadima ba.
Shima yana 6ace musu ya dawo kan titi
sosai, Maps d'in GPS ne yazama jagoran Nuna masa hanya, da taimakon Sarkin mota
kuma dayasan gari. Danshi Galadima ba tuk'i yakeba idan yazo 9ja, saidai idan
ta kama tilas babu yanda zaiyi kamar irin haka.
Sunyi tafiya mai tsawo, yayinda yake
Communication dasu Nuren dasu Saleem. A haka ya iso inda suke, duk fitowa
sukayi daga motocin, shima Galadima ya fito, idonsa akan agogon hannunsa,
yad'an kallesu sannan ya koma kan waya yana fad'in, “maps d'in ya nuna suna a
wajennan, kunga kenan tsakanin gidajennan guda hud'une dake kallon juna?”.
“kwarai da gaske suna nan”. cewar
Muftahu yana furzar da iska.
Galadima yace, “Sauban da Saleem zaku
cigaba da Control namu”. ‘yay maganar yana ciro agogon hannunsa ya mik'a musu,
“ga wannan kuci gaba da using dashi”.
Suka amsa da “to” suna kar6a. ya mak'ala
abinda zai taimaka masa yaji magana, suma su Nuren duk yabasu suka saka.
Har zasu bar wajen ya dakatar dasu ta hanyar
d'aga musu hannu, takawa yay gaban k'ofar gidan farko ya haska gaban gate d'in
da fitilar wayarsa, babu abinda yake nema, ya matsa na biyu ma haka, komawa yay
d'ayan 6angaren, yana haskawa saiga sawun tayar mota data shiga gidan, duk'awa
yay ya d'iba k'asar wajen ya shinshina, ya d'ago ido ya kalli gidan yana jizar
lips, saiya zubar da k'asar daya d'iba ya mik'e, da hannu yayma Nuren da
Muftahu nuni nan ne.
Tahowa sukai garesa, Aunty Salamah datun
d'azun suna daga cikin mota suna kallonsu suma suka fito ita da su Ameer.
A tare suka rissina suna gaida Galadima ya
amsa yana bin su da kallon mamaki.
Da yake su Saleem sun sanar dasu Muftahu
su Aunty Salamah d'in sai Nuren ya kuma yima Galadima bayani.
Aunty Salamah tace, “ka gafarcemu ranka ya
dad'e, nasan zakayi mamkin mun shigo abinda ba'a gayyacemu ba, insha ALLAH
zakaji dalilin shigowar tamu nan gaba. game da shiga gidan nan mungama komai,
maza 5 ne da mata biyu, wad'anda shigarsu ta tabbatar min suna cikin hadiman
masarauta su matan kenan”.
Kai kawai Galadima ya iya jinjina masa.
daga nan yaymata nuni da zasu iya farawa.
Da taimakon su Ameer suka shiga gidan.
★★*★★★*★★★*★★
Fitar Galadima da kusan awanni
hud'u, around 2am Munaya ta farka a
firgice, Inno dake zaune akan Sofa, mom da Aunty Mimi kuma a gefen gadon suka
kalleta, tashi Mom tayi da sauri ta nufeta tana rik'eta, itama Aunty Mimi ta
taso.
Kuka munaya ta sanya tana fad'in “Mom sun
mutu ko? Nasan dama kashesu zasuyi,
Aunty Mimi dan ALLAH miye laifinsu su? kwanansu 7 fa kacal yau a duniya, mi
suka sani game da abinda ake tuhumarsu? An durk'usar musu da kakansu, an hana
mahaifinsu nutsuwar zuciya data rayuwa, shin wannan tabon bai Isa a barsu su
taso da shiba a rayuwarsu? Har sai an had'a da salwantar dasu kenan?”. ta fashe
da kuka maiban tausayi.
Tasowa inno tayi ta zauna a bakin gadon
itama, kamo hannun Munaya tayi ta kwantar da ita a jikinta tana shafa kanta,
yayinda itama kwallar kebin nata kumatun.
Aunty Mimi da mom ma duk hawayen sukeyi,
kalaman Munaya sun ta6a zukatansu.
Lallashinta da magana mai dad'i suka shiga
fad'a mata, sai sauke ajiyar zuciya takeyi, ga jikinta yayi ringim da zazza6i
saboda nononta sun mata hak'e-hak'e, rabonsu da shansa tunda rana, tausayinsu
ya kuma kamata, tasan yunwa da k'ishi ma kawai sun Isa su k'arar da
numfashinsu, hawaye masu d'umi suka kuma gangaro mata a kumatu suna sauka jikin
inno dake shafa kanta.
Shayi Aunty Mimi ta had'o mata, amma fir
tace ta k'oshi, da k'yar inno ta samu ta lalla6ata tasha Quarter d'in kofin.
Mom tace, “wannan nono kid'an matsesu
kozasu rage miki nauyi, dan shine yakawo wannan zazza6in”.
Bata musaba aka kawo k'aramin bowl ta
matse aciki, Aunty Mimi ta zubar a bayi”..
Tanason tambayar ina Galadima tanajin
kunya, sukuma babu Wanda ya sanar mata komai, kodan gudun k'ara tada
hankalinta.
Magani suka bata tasha takoma ta kwanta,
yayinda sukuma suka mik'e duk suka d'aura Alwala suna mik'ama Ubangiji kukansu,
danshi masanin sirrin 6oyene, yana kallon komai, kuma shine zai kawo iyakar
komai d'in.
★★★★★★★
Duk wannan abun dake faruwa su Momma babu
Wanda ya sanar musu, saidai sukaji a jikinsu tamkar akwai matsala, sunta kiran
numbers amma daga wadda zasu samu a kashe sai wadda network zai hanata shiga.
Sai suka d'aura ko shagalin sunan ne yakawo
hakan.
*******************
Tunda Munubiya suka koma gidan kuka
takeyi, ko kad'an tak'i sauraren yaran da keta tsula kuka suma, balle tabasu
nono.
Ba itaba hatta su Ayusher dasu feena kukan
sukeyi, hakama Samha harda shid'ewa, dan itama su tabi bata koma masarauta ba,
Yaa marwan da mama Rabi'a ne kawai ke k'ok'arin danne nasu suna lallashinsu.
Yayinda dare yay nisa duk sai suka
d'aura alwala suka zo suna mik'ama Ubangijin talikai kukansu da k'ok'on barar
bama wad'annan k'anan alhaki kariya da fatan ku6ta.
A 6angaren gidan su Munaya kam duk
hassadarsu yau dai sun tausayama gudan jininsu da yaranta, sundawo gidane kowa
yana sharar kwalla da addu'ar ku6tar yaran.
Ita innarsu Munaya ma ai ba'a magana, ALLAH
kad'aine yasan halin datake ciki, ta shige d'aki ta rufe kanta tana jera
nafilfili, dan wannance kawai gudunmawar dazata iya bayarwa a garesu akan
wannan lamari mai sark'ak'iya da yawa.
Abban su munaya ma yau harda hawayensa,
dukda bashi da tabbas akan hasashensa yasan komai zasu iya, saboda SD yanada
kusanci da wannan masarautar sosai, duk abinda ke hannunsa da bayanan daya
ajiye ya shiga tattarasu waje d'aya...............✍🏻
😿Duk nisan jifa dai k'asa zai fad'o, kwana 99 na 6arawo, 1 kuma tak namai
kaya.👎🏻
Fans insha ALLAH dai abuwa sun fara warwarar
zare, sai mubi su Galadima muga yanda zasu dawo mana da triplets d'inmu gida😭, yau Munaya tabani tausayi daga ita har Galadima, dan
shima dai dannewa kawai yake saboda jarumta, ALLAH ya rabamu da sharrin mak'iyi
komai k'an k'antarsa, Harun da sauran munafukai MAZA BISA KANKU🏇🏻🏇🏻🏇🏻🏇🏻🏇🏻.
Barkanmu da
dawowa my sweet fans🤕😡.
Yau bana cikin yanayin dariya😡
*_ALLAH ya
gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA
KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~Book 2~ 👉🏻2⃣7⃣
................Tunda
suka d'akko yaran suketa kuka, musamman Abdurraheem dahar shid'ewa yakeyi,
ALLAH dai yabasu sa'a ne saida suka fito suka fara kukan, neman haukatasu ma
sukaso yi tun amotar, jisukai tamkar su rufesu da duka, saidai babu damar
hakan, dan basuga abin duka jikin wad'annan kwad'unan yaranba.
Da farko sunga kamar ana binsu, sai daga
bisani ne sukaga ba haka baneba, har dai suka iso gidan y'an uku basu barsu sun
shak'i iska ba.
Suna shiga suka danna musu wasu
allurai, cikin mintuna k'alilan jikinsu dukya saki sukayi luf.
ganin lokaci yaja har kusan 10pm
babu alamar wani motsi hankalinsu ya kwanta, dan sunsan dai tabbas sun tsira,
wayar wadda ta sakasu aikin suka kira, amma tak'i yin picking.
Cikin matan d'aya tace, “kusan dai
bazata d'aga ba, saboda nasan masarauta a haukace take yanzu, saidai mubari
zuwa safiya”.
Tsaki d'aya yaja, “kai nifa gaskiya a
tsorace nake, gara ta d'auka asan mafita, bana buk'atar gawar yarannan takwana
a hannunmu, kunsanfa babansu mayene wlhy, tsaf zai bibiyemu”.
“kai dalla ai yanzu bashida wannan
damar, caza'ayi a fad'ama police, sukuma aikinsu zai farane zuwa safiya, kafin
sannan munma gama binne gawar yaran mun kama gabanmu”.....
“eh kumafa hakane”.
Suna tsaka da wannan hirarne su Galadima
suke shigowa, gidan k'aton gaskene dan haka suka kasa fahimtar INA zasu dosa,
Galadima Yakuma danne abin kunnensa da d'anyatsa d'aya cikin murya k'asa-k'asa
yake fad'in “Sauban kufara muje”.
“yauwa Yaya zaku shiga hannunku Na
haggu, duk sunajin maganar dan haka sukabi hannun haggu, yayinda su Ameer ke
binsu a baya suma. Galadima dake gaba ya bud'e k'ofar a hankali duk suka shiga,
daga can Saleem yace, “duk Ku rarrabu sir, dan abin ya nuna yaran suna ainahin
tsakkiyar gidanne”.
Batare da sunyi magana ba duk suka
rarrabu.
'Daya acikin 6arayin yace, “kai nifa
kamar motsi nakeji gaskiya”.
“to sannu mai kunnen maciji”. cewar
d'aya aciki.
Cikin matan d'aya tayi dariya tana
fad'in “nakula kaidai bibo matsoracine halan?”.
Hannu ya d'aga zai kwad'eta, a harzuk'e
yana fad'in “k wlhy kacaccalaki zanyi, bar ganin kinfito daga masarauta,
kubadan ma an had'amu aiki dakuba kun Isa saninmu ne? jimin y'ar iskar mara
kunya”.
Hak'uri y'an uwansa suka bashi, ya
mik'e yana jan tsaki ya fito danya duba.
Galadima dake la6e cikin labule yay
saurin fitowa, abinka da dogon mutum dan danan yasamu damar shak'osa ya shaka
masa abin hannunsa, tun yana k'ok'arin kare kansa har jikinsa ya saki ya
kwantar dashi a k'asa.
Jinjina Muftahu dake kusa dashi yamasa,
sannan suka cigaba da shiga.
'Dayar baiwar tana kitchen tare da wani
suna iskancinsu Nuren yasamu damar sad'ad'awa, (kunsan dai shahararren
kidnapper ne🤭😂) yauma tsiyar ya aikata wajen jefa ma namijin
handkerchief a fuska, macen tai yunk'urin zuba ihu yasa k'afa ya tad'ota ta
fad'in, sannan ya danne bakinta da ya shak'a mata itama.
K'arar fad'uwarta taso fargar da sauran,
dan haka duk suka mik'e suna fara lek'e-lek'e, aikam Muftahu yasamu ya tad'e
d'aya ya fad'i, Ameer dake bayansa shima ya shak'a masa, harda mangareshi yana
fad'in “kwallon shege taka ta k'are, inakai ina satar sarakunanmu insha ALLAH”.
dariya taso kufcema Muftahu amma ya danne
bakinsa da hannu yana girgiza kai saboda tsiyar Ameer.
Fad'uwar wani da suka juyo ya sakasu
kuma saurin waigawa wajen, Galadima ne ya sakeshi ya fad'i, “shegen k'arfin
jinine dashi dak'yar abin yay masa tasiri”. Galadima ya fad'a yana halbinsa da
k'afa.
Gaban d'ayar baiwar dake la6e jikin
labule ya fad'in, dan tabbas wannan muryar Galadima ce, kowa yasan bai iya R
ba, zuface tashiga keto mata jikinta na 6ari, ta to she bakinta saboda kuka
daya kufce mata, saigata tana tsilala fitsari saboda ganin Galadima yanufo ta
wajen, shikenan itakuma tata tak'e, wannan zakin gagara badau d'in binneta
kawai zaiyi da ranta.
Waige-waige Galadima ya fara saboda jin
numfashin mutum dayakeyi kad'an-kad'an ta wajen, har yayi gaba ya dawo baya
yana yaye labulen wajen. shi da farkoma ya zata aljanace saboda yanda ta
zazzaro masa ido. fincikota yayi ya Watso tsakar d'akin, mamaki ya kamashi
ganinta da kayan manyan kuyangin gidansu.
“tashi tsaye”. ya fad'a cikin matuk'ar
d'aure fuska, kad'an yarage kashi ya kufcemata.
“ina suke!!!”.
Yafad'a
cikin matuk'ar tsawa daya firgita hatta su Sauban dake saurarensu a waya.
Wannan tsawar tasa ce ta saka d'ayan fitowa
a tsorace da gun a hannu, Aunty Salamah dake bayansa bai saniba ta hankad'ashi
yay gaba zai fad'in, Nuren ya ida tad'eshi da k'afa.
Gun d'in data fad'i ta silalo gaban
Galadima ya taketa da k'afa yana huci da taunar lips. Handkerchief d'in
hannunsa yasaka ya d'auki bindigar, ya saita namijin da ita.
Mazari jikinsa ya fara yana d'aga hannu
sama, “dan ALLAH ranka ya dad'e karka kasheni, wlhy bansan komaiba, oganmu ne
yasan komai da wannan baiwar”.
Kunamar bindigar Galadima ya d'ana, nanfa
su Muftahu duk suka rud'e, Nuren yace, “Brother please karkayi harbi, nasan
zasu fad'a mana, dan ALLAH kayi hak'uri”.
Gaba d'aya jijiyoyin kan Galadima sun
mimmik'e, sai fidda huci yakeyi a wahalce.
Muftahu ma yashiga rok'onsa, Su Saleem
dake sauraren komai dagacan duk suka rud'e, Sauban yace “yaa Sam ALLAH ya huci
zuciyarka, amma idan ka aikata haka a wajenwa Zamu samu hasken sauran
abubuwan?, dan ALLAH kayi hak'uri badan mun isa mu saka ka ba, saidan halin da
mahaifinmu ya tsinci Kansa tsawon shekaru, gakuma dama tazo mana ta Sanin
sirrin 6oye, muyi amfani da ita ta sauk'ak'ak'iyar hanya....”
Sakin gun d'in Galadima yayi ak'asa yana
dafe k'irji, wani mugun bugawa zuciyarsa keyi, da baya-baya yanemi zubewa a
k'asa, cikin hanzari Nuren da Muftahu suka taresa, da taimakonsu ya zauna akan
kujera. Yana nuna baiwar da d'ayan hannusa.
Aunty Salamah data fahimci mi yake nufi
tace, “ina yaranne?”.
Jikin baiwar Na 6ari ta nuna k'ofar wani
d'aki, shiga Aunty salamah tayi itada Ameer suka d'akkosu.
Saidai duk a firgice suke, dan yaran babu
alamun rai tare dasu, zufa ta shiga ketoma Aunty Salamah, haka ta fito rungume
da Abdurraheem da Amaturrahman, shikuma Ameer ya d'akko Abdurrahman yana fad'in
“Aunty kamarfa yarannan sun mutu”.
Wannan kalma caraf a kunnen Galadima.
Wata muguwar zabura yayi yamik'e
tsaye, sai ya kuma dafe k'irjinsa da sauri hajijiya tafara katantanwa dashi,
basu fargaba sai jinsa sukayi kawai a k'asa.
Gaba d'aya suka kuma rikicewa, sukayi
kansa.
Muftahu yace, “bamuda isashen lokaci,
asuba ma ta gabato, dolene mubar gidannan dan ko yaushe zamu iya gamo da abinda
bamu shirya masaba”.
Duk sunyi na'am da wannan maganar tashi,
nan fa suka fara kwasar wad'anda suka sumar suna kaiwa mota, sannan suka tasa
k'eyar d'ayar baiwar da wancan, suma.
Yayinda Nuren yad'an bincika gidan, ganin
babu wani abunda zasu k'aru dashi yazo suka kama Galadima daya Suma suka fita
dashi.
Hankalin Sauban ya tashi matuk'ar tuk'ewa,
ya fito yana nufarsu da ta6a jikin d'an uwansa, “Yaa Nuren miya farune? miya
faru da Yaa Sam?”.
“Sauban bamu hanya, ba lokacin wannan
baneba yanzu”.
Sole Sauban ya matsa baya hawaye Na
kwarara a idonsa, suka shinfid'ar da Galadima a bayan mota, sai lokacin Sauban
yaga yaran a hannun Aunty salamah da Ameer, da hanzari suma ya nufesu, Aunty
salamah ta bashi Abdurraheem, jujjuya yaron yayi yaji kamar baya numfashi,
“innalillahi....” yashiga maimaitawa zufa Na keto masa, dolene Yaa Sam ya suma,
hawaye yafarayi yana rungume yaron a jikinsa, Tausayin dukkan ahalinsa da suka
kwallafa rai ga yaran ya kamashi, musamman ma iyayensu, ya ALLAH nasan bazaka
jarabcemu da abinda bazamu iyaba, ALLAH kabamu juriya”.
Muftahu yace, “su shiga mota, duk shiga
sukayi, Nuren dasu Ameer suka wuce da wad'ancan sauran wani waje daban, Muftahu
kuma ya kira police d'in da suka shirya komai dasu, a hanya suka had'u, sai
sukai joining d'insu tamkar tare sukayi aikin, suka kira manyansu suna sanar
musu gashifa sun kama wani matashi da baiwar masarauta da yaran....
Wannan labari yama su d.p.o dad'i ya kira
IG shima ya sanar masa, yaji dad'i shima, koba komai mai martaba zai yaba
k'ok'arin dasukayi, akace yanzu suna inane?.
Amsawa sukai da gasu a masarauta, dan
harda Galadima sukayi aikin, yana kuma cikin wani yanayi shida yaran yanzu
haka.
Basuda za6in daya wuce suce musu to suma
gasunan zuwa masarautar.
Tun'a mota su Muftahu sun gargad'i baiwar
nan da d'ayan mutumin akan suce su biyune suka sacesu, inhar sukace basu kad'ai
bane wlhy saiya kashesu, sannan su tanaji fad'ar wani abun ba ainahin gaskiya
ba, (dan Galadima baya buk'atar police su shiga cikin aikinsa yanzu, yafison
saiya kama kowa sannan, dan inhar police suka shiga aikin mutane da yawa zasuyi
escape ne) shiyyasa Muftahu yayma wad'ancan gargad'in tunma kan su k'arasa
cikin masarauta.
Da yawa wasu basu rintsaba a masarauta
gagara badau yau.
Munaya dai dole aka sake d'irka mata
allurar barci mai k'arfi, dan kusan kuma haukace musu tayi gabannin asuba,
dalilin wani barci daya figeta tayi mafarki mai matuk'ar tada hankali.
Su inno Na zaune har yanzu suna kai
kukansu ga ALLAH Muftahu da Sauban suka shigo d'auke da Galadima da suka kamo
tamkar gawa, sai Saleem da police biyu dake falo d'auke da yaran sukuma.
Zaram duk suka mik'e suna tambayar
lafiya? Miya sami Galadiman?.
Basu sami wata amsaba, saida suka kwantar
dashi a gadon sannan Sauban ya share hawayen fuskarsa yana fad'in “suma yayi
inno”.
Aunty Mimi da mom sukayi kan Galadima
suna kuka, inno tace, “kun samo yaranne?”.
“eh gasu can a falo tareda police,
saidaifa duk sun mutu, shiyyasa ma Yaa Sam ya suma”. yak'are maganar yana kuka.
Hawaye suka zuboma inno, waya ta d'auka
ta kira papi, Wanda shima dai a zaune suka kwana dagashi har Sarki jalaludden.
A time d'in dama har ankai musu bayanin
shigowar su Muftahu d'in.
Yau dai kam tilas Manyan Sarakuna biyu
suka nufo sashen Galadima da Kansu, abinda waninsu bai ta6a yiba kenan.
Maganar ganin yara yafara baje
Masarautar tun'a daren, dan kowa kunenensa a bud'e yake, da masu fatan a gansun
da masu fatan kar'a gansun.
Lokacinda papi da mai Martaban suka iso
Inno Na rungume da yaran duka tana hawaye, sukuma su Aunty Mimi suna bedroom
wajen Galadima.
Kusan a tare Akash da Dr jalal suka iso
dasu papi.
Mai Martaban da papi suka kar6i yaran daga
hannun inno, Suna zama bisa kujerun.
Akash wajen Galadima ya nufa, dukda ba
shine likitansa Na zuciya ba zai iya bashi taimakon gaggawa, shikuma Dr jalal
ya fara kar6ar Abdurraheem dake hannun inno, yan d'ube-dube, yayi Na tsawon
lokaci kafin ya ajiyeshi ya kar6i Na hannun mai Martaban, shima yagama duk
abinda ya dace ya kar6i Amaturrahman a hannun papi, ajiyar zuciya ya sauke yana
fad'in “Alhmdllh duk basu mutuba, allurar barci mai k'arfi sosai suka musu,
shiyyasa numfashinsu yay nisa sosai, danta musu k'arfi da yawa, amma idan kuka
saka kunne nawasu mintuna saitin jikin zuciyoyinsu zakuji suna motsawa
kad'an-kad'an, sai dai ta wannan tafi yin k'asa sosai gaskiya”. Ya nuna
Abdurraheem dake hannun inno.
Su mai Martaban suka sauke ajiyar zuciya
suna hamdala ga ubangiji.
A
cikima Akash nata iya bakin k'ok'arinsa ganin Galadima ya farfad'o, Ahaka su
mai Martaban suka k'araso cikin d'akin d'auke da yaran a hannun, Munaya Na
gefen Galadima an lullu6a mata bargo batasan wainar da ake toyawa ba, dan
barcin nata shine mafita fiye da zama ido biyu.
A gadon suma yaran duk aka shimfid'esu,
Dr jalal yad'an musu dabarun likitoci sauran kuma aka barma ubangiji ikonsa Na
jiran farkawarsu.
Hankali kuma duk saiya koma ga Galadima
da aketa fama.
Har aka kirayi sallar Asubahi babu amo
babu labari akan farfad'owar tasa. daga k'arshe dai Akash saida ya kira likitan
Galadima na zuciya. Shiya dunga fad'ama Akash d'in yanda yadace yayi, lokacin
shiga salla ya saka su mai Martaban fita masallaci dole, sukabar Akash da Dr jalal
dake taimaka masa suna aikinsu, saisu Aunty Mimi da suka kasa matsawa ko nan da
can, Sauban ma da k'yar su papi suka lalla6asa yabisu salla.
Har gari ya waye sashen Galadima ya cika
da manyan masarautar irinsu mama Fulani matan Sarki da sauransu Galadima babu
wani bayani, zuwa yanzu ma wasu sun fara tunanin kodai yama mutu ana 6oyewane
kawai.
Wajen 8:00am Dr Yaseen Ali Modibbo
babban likitan zuciya da akeji dashi ya iso, bisa kiran da Dr jalal ya masa
yafad'a masa, dan abubuwan da sukaima Galadima bai farfad'oba Akash yakuma
sanarma likitansa, shine yace tofa gaskiya Kodai asamo ainahin likitan zuciya
ko kuma su taho dashi kafin cikar awanni 12, idan ba haka ba komai zai iya
faruwa.
A k'iyasin da sukayi cikin awanni 12
bazasu Isa india ba, tunda duk tsiya sai an samu jirgi mai tafiya, sannan ma
kafin komai ya biyo baya. Hakkane yasaka Dr jalal kiran Dr Yaseen Ali Modibbo
d'in, cikin amincin ALLAH kuma ya amsa zaizo d'in, saikuwa gashi ya iso.
Canjama Galadima d'aki akayi, dukkan
kayan aikin da Dr Yaseen yazo dasu aka shigo dasu, rufe d'akin sukayi suka
duk'ufa su uku kansa suna taimakon Dr Yaseen d'in.
Sun jigata kwarai da gaske kafin zuciyar
Galadima tafara bugawa k'asa-k'asa, sai numfashinsa yafara fisga yana k'ok'arin
fita. Duk ajiyar zuciya suka sauke. Suka cigaba da aikinsu, ana sakama Galadima
wani abu a k'irji kamar dutsin guga, saiya girgiza sannan a cire, akuma
maidawa. Basu barsa ba saida yasaki wata ajiyar zuciya mai matuk'ar sauti,
harsu mai Martaban dake falo saida suka jiyosa kuwa.
Wannan ne yasaka zukatan doctors d'in uku
sanyaya, Dr Yaseen da Dr jalal suka had'a baki wajen fad'in “Alhamdulillah!”.
Numfashin Galadima ya dawo dai-dai, amma
sun masa allurar barci danya samu nutsuwa.
Yaranma an kawosu ne Dr Yaseen ya kuma
bincikawa, shima dai yace suna da ransu, amma Abdurraheem yanada ciwon zuciya
shima, shiyyasa yafi sauran y'an uwansa jigata, ALLAH nema dai yay rabon yanada
sauran numgashi, amma allurar tamasa k'arfin da zata iya dakatar da bugun
zuciyarsa. Suma dai sun kuma samun taimako, musamman ma dai Abdurraheem da
tausayinsa ya kama mutane da yawa a wajen.
*_2:00pm_*
Zuwa wannan lokacin Munubiya da mama
Rabi'a da Ayusher Feena duk sunzo masarautar, Hakama baba k'arami da daddy, dan
an sanar musu samo yaran da halin da galadima yake ciki.
Amma saboda kara irinta Abba da innarsu
Munaya sai suka bar su Baba k'arami da maman Fauziyya da mamansu yaa Hameed,
maman Safara'u suka taho, sai innaro da gwaggo Safiyya.
Ba'a barin wani bak'on fuska shigowa
masarautar a yau, amma su sai mai Martaban yasa aka shigo dasu, basu samu ganin
ko d'aya a cikin su Munaya ba, saidai Munubiya da aka shigar d'akin galadima
inda Munaya ke kwance, Sauran kuma sun shiga ayarin y'an zaman jigum-jigum da
jiran tsammani.
Har zuwa wannan lokacin Galadima da
Munaya babu Wanda ya farka, Amaturrahman da Abdurrahman dai sun farfad'o, sai
dai suna kuka ko fita bayayi.
Wanka laraba ta musu aka gasa musu jikinsu sosai, yau dai
dole aka nemo madarar da Galadima bayason susha d'in, ita aka dama aka basu
sukasha, aiko sun shata sosai dan yunwa sukeji, bayin ALLAH, rabonsu da abinci
tun jiya da rana kusan I war haka d'in.
Tausayinsu ya kama Munubiya dake basu
madarar, tana yi tana sharar hawaye, da da farko nono inno tace ta basu, sai
papi yace, “a'a kar ayi wannan gangancin, dan ba'asan abinda ALLAH zaiyiba
wataran, ko akwai k'addarar aure a tsakanin yaransu, kar azo ayi Dana sani a
watarar da baza'a iya maido wannan ranarba balle a gogo 6arnar da akayi”.
Kowa ya gamsu da wannan magana, dan haka
Muftahu yafita suka nemo madara shi da Saleem.
Shine aka basu.
Baiwar da
aka kami da mutumin kuma suna hannun police, kuma kowa yaji cewar tana cikin
bayin gidan wad'an da aka aminta dasuma sosai, saidai ba'asan ta wane sashe
bace.
Wannan Abu ya tsurar da zukatan Sauran
bayin, dan dolene ya shafesu.
Hankalin Uwargidan Sarki Sarauniya
Zulfah (mahaifiyar su matawalle) a tashe yake, amma dayake ta iya takunta
bazaka ta6a fahimtar haka ba, saima nuna tsantsar damuwarta akan lamarin da
tayi fiye da sauran matan Sarki. dama kuma tafi nuna kulawarta ga Galadima kowa
yasan wannan, shiyyasa babu Wanda yakawo wani Abu game da ita, saima wasu daban
ake zargin.
Munaya da Galadima sun farfad'o ne kusan
time d'aya, amma Galadima ya riga Munaya, dama allurar awanni 4 kacal aka masa,
da Sunan ALLAH a bakinsa ya farka, sannan yafara kiran yaransa d'aya bayan
d'aya yana fad'in karsu tafi su barsa..
Rik'eshi Dr Yaseen yayi yana fad'in “ka
kwantar da hankalinka ranka ya dad'e, dan zuciyarka tana cikin yanayin jiran
k'iris ne, inamaka albishir da cewar yaranka suna raye, yanzu nan zakagansu
insha ALLAH”..
Galadima ya sauke nannauyar ajiyar
zuciya yana kallon Dr Yaseen, ya lumshe idonsa a hankali sannan ya bud'e,
hanunsa ya d'ora akan saitin zuciyarsa saboda wajen yamasa matuk'ar nauyi.
Ana haka Dr jalal ya shigo d'auke da
yaran biyu, dan Abdurraheem shi yanan a d'akin kusa dashi bai farfad'o ba.
Tunda Galadima yaga yaran sa suna a
raye saiya kuma rungumesu a k'irjinsa da Dr jalal ya d'ora masa, wasu hawaye
masu zafi suka gangara gefen kunnensa.
Dr Yaseen yaji dad'in kukan da Galadima
d'in yakeyi, dan zai rage masa rad'ad'in da yakeji da nauyin zuciyar, hakan ya
nuna aikinsu zaiyi k'yau insha ALLAH.
Galadima ya dad'e rungume da yaran,
saidaga baya ya farga babu guda d'aya.
A hankali ya bud'e baki yana fad'in, “ina
d'ayan?”.
Murmushi Dr Yaseen yayi, yace, “gashi a
gefenka yana barci shima”.
Juyawa Galadima yay ya kallesa, ganin
d'an cikin yaron Na motsi alamar fitar numfaahi sai dad'i ya kuma ratsashi, ya
lumshe idonsa yana yun k'urawa zai tashi zaune, taimaka masa. Dr Yaseen yayi,
yatashi rik'e da yaransa, kwantar dasu yayi sannan ya matsa ga Abdurraheem
hannunsa dafe da k'irjinsa har yanzu, rankwafawa yay kan yaron ya sumbaci
goshinsa da kumatunsa, sannan ya shafa kansa la66ansa suna motsawa alamun yana
masa addu'ar fatan samun lafiya a garesa shima.
A 6angaren Munaya Itama tana farkawa da
kuka ta farka, tana kiran yaranta, itadai afad'a mata idan sun mutu kawai saita
hak'ura.
Rungumeta Munubaya tayi tana lallashi da
mata albishir d'in dawowar yaran garesu, hakan yasaka Munaya d'agowa da sauri
tana kallon Munubiya, “Sweetheart da gaske kikeyi?”.
“da gaske nakeyi Sweetheart, yanzu haka
suna tare da mahaifinsu”.
Dad'i ya ratsa Munaya, ta kuma k'ank'ame
Munubiya suka rungume juna suna kuka da dariya lokaci d'aya.
Hakan kuma saiya sanya su inno kukan tausayinsu
da sha'awar wannan k'aunar juna nasu.
Saboda su mai Martaban sun shiga wajen
Galadima sai akace ita Munaya tayi wanka kozataji k'arfi kafin su fito.
Bata musaba ta amince, ruwa mai zafi laraba
ta had'a mata, tashiga wankan. Tanayi tana kukan farin ciki. bata cuci kantaba
tayi wanka sosai ta gasa jikinta.
Kafin ta fito an gyara d'akin tsaf, sai
k'amshin daddad'an turaren d'aki yakeyi, babu kowa duk sun fice.
Su mai Martaban suna tare da Galadima,
sunyi farin cikin tashinsa, hakama yaran. sunkuma yima Abdurraheem addu'ar
tashi shima. Sun d'an jima a d'akin, dan har saida aka shigo dasu Dady da baba
k'arami, Yaa marwan, Yaa Hameed suma suka gaidashi da masa jajen ALLAH ya
kiyaye gaba sannan suka fita gaba d'aya.
Daga nan manyan irinsu mama Fulani, inno
matana Sarki da sauran su duk suka shigo suma, harda su innaro da akaita kuka.
Galadima dai Kansa kawai yake iya d'agawa,
idonsa a lumshe. Baya buk'atar kallon kowa a cikinsu.
Su inno duk tausayinsa ya kamasu.
Innaro aka share hawaye tace, “barka da
arzik'i kaji, ALLAH ya kiyaye gaba, ya shiga tsakanin nagari da mugu, ya tona
asirin duk makirin dake cikin wannan satar yara”.
Duk da amin suka amsa. Galadima ma yace
amin akan la66ansa. sai tunani yake ina Munaya take?, dan hankalinsa yafara
tashi da rashin gilmawarta, musamman daya tuna a halin daya tafi itama ya
barta.
Yadai kasa daurewa ya bud'e baki da
k'yar yace, “Mom ina Munaya wai?”.
Saida mom ta matso da kunnenta sannan
tajishi, tasan yana lafiya ma ya aka k'are da k'asaitar magana balle yanzun. Murmushi tayi, tace, “tana
d'aki, itama sai yanzu ta farka, dan dole aka sake mata allurar barci bayan
tafiyarka, waccan bata dad'eba ta saketa”.
Tausayin Munaya ya kuma kamashi, ya
jinjina kai yana yunk'urawa zaune sosai.
Cikin yamutse fuska yace, “Mom nima
yakamata nayi wanka Na rama sallolin dake kaina”.
Mom tace, “to bara a kira su Muftahu su
kamaka ”.
Kansa ya girgiza mata da mata alamar, zai
iya da kansa.
Mom tace, “Alhmdllh”. Rigarsa ya jawo
yasaka, dan da dagashi sai best. d'aukar Abdurrahman da Amaturrahman yayi ya
fito, yabar mom tana gadin Abduraheem dabai farko ba. babu kowa a falonsa Dan
duk sun fice.
Da k'afa ya turo k'ofar, Munaya Na zaune a
bakin gadon rik'e da mansa zata shafa amma dukta kasa, burinta taga halinda
Galadima da yaranta suke ciki kawaine damuwarta, gashi har yanzu babu Wanda
yazo yakirata akan su papi sun fita. bud'e k'ofar ya sakani d'ago ido. Zummbur
na mik'e tsaye ganin Galadima rungume da yaran, ai yau nama manta dawata kunyar
towel na d'aura, hawaye suka shiga zarya tsakanin idona da kumatu, Galadima ya
tako a hankali zuwa gareni idonsa a kaina. Da sauri namatso garesa nima,
nahad'ashi shi da yaran na rungume ina sakin kuka mai k'aramin sauti.
Shiru yay kawai ya zubama gashinta ido
yana tausaya mata daga ita har yaran, ansakasu a yak'in dabasu San mafariba, ya
godema ALLAH da yarannan sunada sauran numfashi a duniya. Da baisan yanda zaiyi
da munaya ba. Ganin kukan nata zaiyi yawa ya bud'e baki da k'yar yace, “ya isa
mana”.
d'ago idanu nayi na kallesa, cikin
muryarta data dishe saboda kuka nace, “Nagode yalla6ai, dasun mutu nima mutuwa
zanyi”.
Murmushin gefen baki yayi, cikin d'age
gira d'aya yace, “dama ana sonmu haka?”.
Sai
yanzu kunya ta kamani, nai k'asa dakai ina kallon k'afafunmu.
Bai sake cewa komaiba ya ra6a ta gefena
yaje ya shimfid'e yaran akan gado.
bathroom ya nufa yana cire rigar
jikinsa, nidai Na k'arasa gadon Na rungume yaran ina sumbatarsu, wani dad'i da
tsantsar farin ciki Na ratsani, Na d'aukesu Na fara shayar dasu ko zasu rage
nauyin da sukamin, aikam kamar jira sukeyi suka kama sha. Hannun rigar namijin
Na d'aga saboda tanan muke gane shaidarsu, ganin Abdurrahman ne saina fara
tunanin ina Abdurraheem shikuma?, hankalina yaso tashi amma saina daure ina
jiran Galadima ya fito naji daga garesa.
Galadima dake kallonta bata saniba ya
d'an cije lips, ya tabbatar yanzu tana son yaransa, amma baisan miyasa take
ignoring d'insu ba idan yana waje? Kokuwa tsabar jan ajinne oho?.
Har Lokacin daya fito wankan tana shayar
dasu, ta shafa kan wannan ta shafa Na wannan, sosai suka birgeshi itada yaran,
jin kamar motsi yasakani kallon wajen, da sauri na janye yaran daga bakin nono
naja towel d'in na rufe abinna ina turo baki gaba.
Baki ya ta6e yashiga takowa inda muke, ya
rankwafo kaina ruwan fuskarsa yana d'iso min a jikina, a kasalance yace, “wane
darene jemage bai ganiba malama, tunkan su sha ni........”.
Da sauri na saka hannu na toshe masa
baki.
Zama yayi yana janye hannunna, cikin waro
idanu yace, “to mikike tunanin zan fad'a? lallai kinfi k'arfina, niba can Na
dosaba to”.
Sosai naji kunya, na sauke yaran a kan
gadon na sakko, zuciyata cikeda mamakin sa, ya d'aure fuska yana basarwa yayta
sakin magana kuma kamar bashi yayiba.
Ficewata nayi bayan na d'auki bathrobe
d'insa na d'ora akan towel d'in jikinna.
Wani kallo ya bita dashi yana ta6e baki,
kafin ya maida ga yaransa daketa kalle-kalle, ya shafa kumatunsu sannan ya
mik'e zuciyarsa na tunanin su Momma, addu'arsa d'aya kar wani ya sanar musu.
Kasa fitar nayi saboda jin kamar da mutane
a falon da zanbi ya sadani da 6angarena.
Badan nasoba tilas Na dawo baya.
Galadima dake gaban mirror yana shafa mai
yana kallonta ta ciki, amma sai yayi biris tamkar bai gantan ba.
Komawa nayi na zauna a bakin gado ina
tunanin mafitar yanda zan samu kaya, da jin haushin sharenin da yayi.
Ana haka mukaji knocking, saida ya kalli
Computer d'in yaga Mom Ce d'auke da Abduraheem sannan ya mik'e yana amsawa..
Zuwa yay ya bud'e mata, bata shigoba ta
mik'a masa yaron da har anmasa wanka Ashe, ta mik'a masa kaya a leda tace na
Munaya ne.
Galadima yace, “mom ya tashine?”.
“ya tashi, tunma fitowarka babu dad'ewa,
harma an masa wanka”.
Sumbatar kumatun yaron yay yanama mom
sannu
Idonsa akan yaron yana kuma sumbatar
goshinsa cikin lumshe idanu ya k'araso inda nake dana zuba musu idanu cikeda
sha'awa.
Kusa dani ya zauna ya d'ora minshi akan
cinya. nima rungume kayana nayi na sumbaci goshinsa, inason bashi abinci amma
inajin kunyar Galadima, gashi ya zubamin ido yak'i tashi.
Lura da hakan dayay ya sakashi yin
miskilin murmushi ya mik'e yabar wajen.
d'an hararan bayansa nayi ina fad'in
mugunta dai babu k'yau a kan la66ana..................✍🏻
“Hummm fans nasan kwace wai ina Harun ne?🤔, kumuje zuwa dai danjin ina ya shige
haka? Ita kuma sarauniya Zulfah (uwar gidan Sarki mike matsalarta)?.😨😏
*_Ya Rabbi
ka gafarta ma iyayenmu_*😭👏🏻
No comments