RAINA KAMA (BOOK 2) 24&25
~Book 2~ 👉🏻2⃣4⃣
.............Kallonsa
Nuren yayi da y'ar dariya, “angon jego ai dole kake sauke numfashi, irin wannan
aiki dakayi haka? Y'ay'a uku fa a lokaci d'aya, a fuska dai kamar bazaka iya
komaib.....”
Nuren bai samu k'arasawa ba saboda filon
kujera d'aya daki bakinsa, wanda Galadima ya jefa masa.
Dafe baki Nuren yayi yana kallonsa cikin
6ata fuska.
Galadima ya cije lips yana fad'in “cigaba
mana parrot ”.
Nuren ya cire hannun yana kwafa da
jinjina kai, alamar zan kamaka ne.
Galadima ya ta6e baki yana hararsa,
“yaro aini yanzu na daina halin yara, sai dai kayi da wani kuma”.
Dariya Nuren ya kwashe da shi, “o manya
o manya, ai yakamata ma mai martaba yay murabus yabaka kujera kawai, kainefa
Wanda kafara kafa tarihi a masarautar nan, Sarki Salisu barde shi yak'in filin
daga yaje ya samo sunan gagara badau, kaikuwa yak'in kashe arna kaje kasamo
sarakunan gagara badau”.
Girgiza kai kawai Galadima yayi yana
fad'in “kai dai d'an iskane wlhy, yakamata papi sumaka aure kodan y'ay'an mutane
su samu lafiya ma”.
“ni wlhy dama zakaje kace amin auren
daka taimakeni”. Nuren ya fad'a cikin ta6e baki da d'aga kafad'a.
Murmushi Galadima yayi yana gyara zama,
“ALLAH ya shiryeka to, mike tafiya akan al'amura?”.
Zama Nuren ya gyara yana komawa serious,
“wlhy d'an uwa abubuwannan sun cika tsauri da yawa, a duka mutanen nan uku da
yarinyarnan ta fad'a da gaske fa babu SD, amma ga pictures d'in wajen mutum 30
ka nunama Mumcyn Triple's ko zata ganeshi a cikinsu. dukansu yaransu tanderu
ne, Sannan nifa inaga lokaci yayi da zaka binciki Muftahu face to face, dan
lamarinsa yafara birkitan tunani gaskiya”.
“kafad'i gaskiya Nuren, nima kuma ina
tunanin hakan shine mafita, dan ni kaina lamarin nasa yafara kaini ga dogon
nazari”.
“To ALLAH yasa muji alkairi”.
“amin dai”. Galadima yafad'a yana mik'ewa,
“nifa na shige zan kwanta, ka kwana lafiya”.
“ok ALLAH ya tashemu lafiya gwauro”.
Galadima yay dariya, batareda ya juyoba
yace, “duk lalacewar goma dai tafi biyar albarka tuzuru”.
Nuren ya kwashe da dariya, yana
fad'in, “oho dai, muma mun kusa zama gomar”.
★★★★★★★★★★★★
Zumid'i ya hana Momma komai, ta k'agara
Abie yafarka yasha kanu, hakama su Samha su dawo school suji babban labari.
Ana cikin haka saiga Sauban tamkar an
jehoshi, babu kunya ya rungume Momma yana fad'in “wayyo dad'i Momma y'ay'a uku
fa wlhy, kuma dai-dai da ranar haihuwar Yaa Sam, dan yau birthday d'insa wlhy,
ciwon aunty gimbiya ya mantar dashi”.
Itama rungumeshi tayi cikeda farin ciki,
“hakane wlhy my love, yau ina cikin farinci mai tarin yawa, tarihi ya maimaita
kansa da wani sabon salo mai banmamaki”.
“Wlhy nima haka Momma, kallafa pictures
d'in babies d'inmu”.
Dukda tagani itama bata katse masa
hanzariba ta kar6a wayarsa tana kuma kallo, harda na Munubiya.
Momma tace, “kai yau innarsu yazataji,
jikoki 5 a lokaci d'aya, baiwar ALLAH, dama mahak'urci mawadacine, tayi kukan
shekaru masu yawa ga lokacin dariya kuma yayi”.
“wlhy kuwa momma, nakira Yaa Sam
batajeba”.
“Ai yama manta wayoyinsa a nan, kasan sun
tafi hankalinsa ba kwance ba, nima da wayar Muftahu mukayi wayar”.
“wayyo Momma dan ALLAH kicema Yaa Sam
mutafi gobe, wlhy kamar nayi tsuntsuwa na ganni a 9ja nakeji”.
Dariya Momma tayi, tarasa inda zata saka
kanta dan dad'i.
Motsin da Abie ya farane yasakasu maida
hankali garesa, idonsa ya bud'e ahankali a kansu. ganinsu tsaye kansa sunata
murmushi saiya ma Momma alama da ido wai miya faru?.
Da sauri Sauban ya rungumesa yana fad'in
“Albishirinka Abie d'inmu, matar Yaa Sam y'ay'a uku ta haifa”.
Ba k'aramin shock bane ya kama Abie, ya
kalli momma alamar da gaske?.
Kanta ta jinjina masa tana murmushi.
Wasu hawayen dad'ine suka gangaro a
kumatunsa, fuskarsa d'auke da k'ayataccen murmushi, A hankali yaketa jero
Alhmdllh. Yace, “Mafarkina na shekaru da yawa yazama gaskiya Zeenah, tabbas
ubangiji shine masanin gaibu, ya ALLAH na gode maka, godiya marar yankewa balle
gajiyawa”.
A hankali yake maganar Amma su Momma naji
saboda sun matsar da kunuwansu.
Dad'i duk yakuma lullu6esu, Abie yakuma
fad'in “Zeenah wannan yarinya ta zama alkairi ga Ahalinmu, ALLAH ya albarkaci
rayuwarta da abinda ta Haifa daku ma gaba d'aya”.
Sauban da Momma suka amsa da amin.
Yace a kira masa Galadima.
A time d'in sunta neman Number Mom amma
bata wuceba saboda Network, hakama ta Nuren da Muftahu, daga k'arshe dai sun
hak'ura ne sai wani lokacin a sake gwadawa.
Yau dai kam har doctor's d'in Abie sun
shaida yana cikin farinciki, dan jikinsa ma ya nuna haka, k'arfin muryarsa ya
k'aru, hakama bugun zuciyarsa dawasu yankunan halittun jiki dake bama d'an adam
garkuwa, sun tabbatar a kowanne lokaci ALLAH zai iya gwada ikonsa ga wannan
bawa, bayan tsawon shekaru daya d'auka a kwance sai an juyashi.
Wannan albishir ya k'ara yalwata farin
cikin wannan ahali, saima dasu Samha suka iso, duk sun rikice da ihun murna,
yau d'in ta dabance a ransu.
Isowarsu ce ta tunama Galadima da ranar
haihuwarsa dai-dai da haihuwar yaransa, kuma dai-dai da haihuwar su Munaya ma😳😜.
Wannan abin al'ajab da yawa yake, ita
kanta munaya sai lokacin ta tuna, wayar Ayusher ta kar6a ta kira Munubiya tana
mata tuni da ranar haihuwarsu. dad'i ya kama Munubiya ma, dan itama ta shafa'a,
sai murna kan murna ta k'aru🤸🏻♀.
**************************
Uban gayya dai Galadima da k'yar barci
6arawo yake sace sa a kowace rana, daya rimtse ido 'y'ay'an sa kawai yake
hangowa, badan kar aga rashin hak'urinsa ba shikam da dasu zai ringa kwana.
O baban zumud'i😘😘😽.
A 6angaren yalla6iya ma hakane takan
kasance, da taga laraba tayi barci dash Ayusher da Samha, (dayake itace take
kwana dasu) saita tashi ta dinga d'aukarsu d'ai-d'ai tana runguma da musu
addu'oi, jitake kamar ta had'iye kayanta ta huta kawai, takan dad'e tana Abu
d'aya kafin barci yaci k'arfinta take kwantawa.
Tosu yalla6iya anaso ana kaiwa kasuwa😂😜.
*************************
Fad'a muku yanda abubuwa suka cigaba da
kasance ga y'an barka ai 6ata lokacine ma, dangin Munaya ma sun taka rawar
gani, Ayusher ma dai ta dawo nan zata zauna har ayi suna, hakama madam Innaro
Galadima da kansa yaje ya kwasota🤣😜, aiko baki har kunne.
Gaskiya fans sannunku da k'ok'ari, irin
wannan tururwa haka, lallai kunma Galadima halacci shida yalla6iya, ALLAH ya
saka muku da alkairi dai my sweetness🥰🥰🥰😘😘😘😘❤🤝🏻.
Dole Galadima ya nemi waya da sim card
ya lalubo su Abie da Momma d'insa da jakadiya dabasu samu zuwaba, suna
shan hira a kullum shida su Abie ta
video call, ga jarirai aita jera musu sunata shan kallo abin birgewa, Abie
jiyake kamar yay tsuntsuwa ya gansa a 9ja, tsakanin nan yana cike da kewar
k'asarsa ta haihuwa, yana fatan yakuma takata ko sau d'ayane kafin yabar
duniya.
“Insha ALLAH zaka taka da yawa Abie😭”.
Mu tafi ran suna kawai😨⛹🏻♀⛹🏻♀.
Abubuwa da yawa sun faru a kwanakin
bakwai d'innan, sai dai Alhmdllh bamasu tayar da hankali bane, dan jinjirai
suna cikin k'oshin lafiya da kariyar ubangiji.
Samha dai konan dacan bata matsawa, duk
wani motsinta nakan yaranan, tazama bodyguard d'insu itada Ayusher da hajiya
innaro, dan itamafa ta kafa ta tsare🤣.
Mama Fulani dai ta danne zuciyarta tazo
har sashen Galadima taga babies, harma suka samu k'yauta mai tsoka daga gareta.
Ana gobe suna masarautar gagara badaufa
tayi dank'am da jama'a, dan bikin suna na ban mamaki Sarki ya shirya, abin ba'a
cewa komai. Inno ma dai wannan karon ba'a barta a baya ba, tazo masarautar su
sunan tatta6a kunnenta, kuma 6angaren mama Fulani ta sauka😳😜.
Koba komai zata kafa zata tsare, takuma
raka ta jira🤸🏻♀😂 mana ga Mama Fulani.
Harun da baya k'asar yayi tafiya a
fannin aikinsa yau ya diro a Daren suna cikin masarautar, dama tun yana can
labari yagama Isar masa Galadima ya samu y'an uku, Muftahu da kansa ya kirashi
ya Sanar masa haihuwar, Yakuma tura masa hoton babies😽🤥
*****************
Wajen 8pm Galadima suka dawo daga
masallaci sallar isha'i, shikad'ai ya shige falonsa, dan yana son magana da
Munaya, gaba d'aya yinin yau tun safe daya Shiga bai samu komawa wajensu ba
saboda hidimomi sun masa yawa.
Ayusher ya kira, dan itama Munaya batazo
da waya ba, lokacin da su Sauban zasu taho kuma basusan inda ta saka layinta Na
Nigeria ba, sai sukaga babu amfanin d'akko wayarma.
d'agawa Ayusher tayi, Galadima yace ta bama
Munaya.
Murya k'asa-k'asa tace bata da lafiya.
Tashi yay daga kwanciyar da yayi, yace,
“ciwon cikin ne dai?”.
“eh shine wlhy Yaa Galadima ”.
Dukda kunyar shiga mutanen yake dole ya
mik'e ya fita, sashen nasu kam Alhmdllh
da yawan jama'a babu laifi, ga yawan bayi da suka k'aru saboda inno da
tawagarta, dukda ba'anan ta sauka ba.
Tunda ya fito suketa gaisuwa da jama'a,
wad'anda ma basu sanshiba yau sun gansa, musamman wasu a y'an uwan Munaya.
cirko-cirko ya iskesu tsaye, Munaya Na kwance a gado ta cure waje d'aya da
alama tanajin ciwon sosai, Aunty Mimi nata faman jijjiga yaron d'aya dake kuka.
Duk kallonsa sukayi, cikin damuwa yace,
“ciwon cikinne?”.
Da eh suka amsa masa, ya taka zuwa gaban
gadon ya zauna kusada ita, har zai ta6ata Mom tamasa nuni da a'a ya barta.
dakatawa yayi shima ya zuba mata ido cikin tausayawa, gaba d'aya fita
hayyacinta take idan cikinnan yana ciwo, kuma saida ta kwana biyu da haihuwa
sanann yafara. ya tsira mata idanu ganin yanda take zufa, dukda garin akwai
sanyin ruwan da akayi da yammaci.
Yakai tsawon mintuna 30 a zaune kafin ya
lafa mata, ahankali tafara gyara kwanciyarta tana mik'ewa sosai, da Galadima
suka fara had'a ido, yace, “sannu”.
Kanta ta d'aga masa cikin murmushin k'arfin
hali, suma duk sukai mata sannu sauran.
Nanma ta amsa cikin d'aga kai. Maganin da
laraba ta tace a Kofi ta mik'o mata, Na gargajiyane, kar6a tayi ta shanye tana
yamushe fuska, ta mik'a mata kofin sannan ta zauna sosai.
Tausayinta ya kama Galadima, iyaye mata
nashan wahala akan y'ay'a, ALLAH ne kawai zai biyasu.
Ganin ta dawo dai-dai duk sai suka fita
suka basu waje, bayan Aunty Mimi ta d'ora masa babyn a cinyarsa.
Sannu ya kuma mata yana gyarama yaron
kwanciya, murya a hankali tace, “ya daina ai, amma wlhy ciwon cikinnan yamafi
haihuwar zafi”. ‘ta k'are maganar idonta cike da kwalla’.
Tausayi ta kuma bashi, ya matso kusada ita
sosai yana ruk'o hannunta, yace, “insha ALLAH Akash zai zo miki da Magani zuwa
gobe, zai daina gaba d'aya ”.
Kanta kawai ta d'aga masa amma batace
komaiba.
Kukan da macen tayi yasakasu kallonta su
duka, nuni yamata ta d'auketa.
Batayi musuba ta d'auketa ta saka a
acinya, kamar jira suma sauran suka farka harna hannunsa, kai Munaya ta dafe
tana fad'in “ni jikar fharuk ku shikenan da d'aya ya tashi kowa saiya tashi”.
Murmushi yayi, “to basu birgeki ba ma,
sunyo gadonku ne keda Munubiya, Ku ba haka kukayiba?”..
“a'a mukam ba irin wannan mukayiba
yalla6ai”.
“humm, ai inna ta sanarmin komai
yarinya”.
Da mamaki Munaya ta waro masa ido, ya
d'aga mata gira yana kashe ido d'aya.
'Dauke idonta tayi cikeda basarwa.
Shima saiya mik'e tsaye d'auke da yaron
d'aya, ya kalli agogon dake a hannunsa sannan ya kalleta “inason ganinki”. daga
haka ya sunkuya ya d'auki macen ya juya zai fita.
“wai ina?”. ta fad'a da saurin dan
karya fice.
Juyowa yayi ya d'an kalleta, kamar
bazaiyi magana ba sai kuma yace, “sashena”. bai jira cewarta ba yay ficewarsa.
Kanta ta dafe tana sauke ajiyar zuciya,
shi bama ya ganin gida cike da mutane, fitinar yalla6ai yawane da ita wlhy.
batayi yunk'urin binsa ba, saima zaman shayar da Wanda ya bari tayi, harsu
Samha suka dawo ganin ya fita.
Shikam yanacan kwance a gado ya d'ora
yaran saman cikinsa yana shafa bayansu, yayinda zuciyarsa ta tafi wata nahiyar
tunani, ganin lokaci yaja bata zoba ya kalli a gogon hannunsa, shidai bazai
kuma kiranta akan tazo ba, idan ta gadama kartazo.
Mom data lura babu sauran yaran ta
tambaya, cikin kunya Munaya tace, “suna wajensa”.
Banbancin babba da yaro saurin fahimta,
mom ta fahimci d'an nata yana buk'atar ke6ewa da matarsa, shiyyasa ya d'auki
abinda dole tabishi inda yake ta kar6o..
Tace, “to aiko jeki ki kar6osu, dan shirin
barci zan musu nima Na kwanta, gobe ba zama za'a samuba hidimomi zasuyi yawa”.
Kamar Munaya tai ihu haka taji, to a
aiki Ayusher da Samha su kar6osu mana, ai ba dole sai itaba, amma babu yan da
ta iya, dan bazata iya sa6a umarnin Mom ba dai.
Dogon hijjab ta d'auka ta zumbula, Mom
kamar tayi dariya, a ranta tace, Munaya shi namiji ai ba'a hanashi yanda yaso,
balle naku na yanzu da suke a fetsare ma.
Harzata fice mom tace, “shima zoki
d'aukesa”.. Ta kalli mom d'in
tana fad'in “mom aikuma zasuyi yawa wajen d'akkowa”.
“eh d'auka, basai ya tayaki ku d'akko ba”.
Babu yanda Munaya ta iya dole shima ta
dawo ta d'aukeshi, sai wani k'yallo idanu yakeyi Lamar yasan mi akeyi.
Babu kowa a afalon, harma television an
kashe, babu yanda ta iya dole ta nufi bedroom d'in, saida tayi sallama yabata
izinin shiga sannan ta shiga.
Harta zauna idonsa a kanta itada
babyn hannunta, saiyaga ta k'ara masa k'yau ma da girma.
Yace, “kin gama jan ajin? ai saki bari
sai randa nazo tad'i ki jamin bawai yanzu ba”.
Munaya ta ciza lips d'inta kawai
batare da ta tanka masaba,
Yaran ya kwantar gaba d'aya, sannan
yatashi zaune yana fad'in “taso”.
“intaso kuma, ba magana kace zamuyi ba?
please ka fad'a a haka”. ta fad'a kamar zatayi kuka, (Dan hirar innaro da
laraba ta tuna da sukace jiya wata yarinya sati biyu da haihuwa ta yarda da
mijin saiga ciki ya fito yaro Na wata uku, ciki wata biyu da sati biyu🤣, itama fa yanzu kaffa-kaffa zatakeyi
da Galadima, inma baka badaba sai'a saka maka k'arfi🤭😂).
Tsaf Galadima ya fahimceta, dan haka
yay wani miskilin murmushi yana fad'in “oh kina min bak'in cikin sake ajiye
abin cikin kwan ne?”.
Sosai Munaya ta waro idanu, a firgice tace,
“ban ganeba?”.
“Zaki gane lokacin da kika zo hannuna”.
Ta yunk'ura da sauri ta mik'e, ita tama
manta da yaro ajikinta, ALLAH dai ya kiyaye tai saurin tarboshi, Galadima ma
dirgowa yay daga gadon, saidai kawai ta gansa kusada ita.
Rungume yaron tayi tana sauke ajiyar
zuciya, gashi mai kamar mara lafiyarne.
Shima Galadima had'ata yay itada yaron ya
rungume, ganin haka saita mik'a masa shi ita ta janye jikinta. hannunta ya
rik'o ya maidota, daga k'arshema janta yay zuwa gado, ya zaunar da ita shima ya
zauna, fuskarsa babu walwala yace “Munaya badai haka kikemin ganganci da
yaraba?”.
A tsorace ta girgiza masa kai idonta Na
cika da kwalla, “wlhy yalla6ai a'a, yanzu ma Na shafa'ane”.
Taune lips d'insa yay tayi yana
kallonta, haushima ya hanashi samo amsar bata, jima yake kamar ya maketa, anya
zaibar yarinyarnan zuwa wani wankan banza can, taje tamasa wasarere da yara?.
Yanda ya koma duk saitaji babu dad'i, shi
yaronma bafa kuka yakeba, yad'an dai firgita ne kawai yay kamar zai shid'e.
Saida ya gama cikarsa da batsewa sannan
yay kwafa, ita shima abin yabata mamaki, shikenan yanzu y'ay'ansa kawai ya
Sani, mutum bazai ta6a iya kuskure ba a Kansu saiya hauma mutane bala'i, shin
ya fita sonsune itada tasha wahalar d'aukar ciki da haihuwa?.
Kwantar da yaron yay yanata wani had'e
fuska, itama tasha kunu ta shareshi.
K'aton akwatin dake gefensu ya matso
dashi, kayane Na jinjirai masu k'yau da birgewa, Wanda kallo d'aya zaka musu
Kasan Na musamman ne, kala-kala ne amma kowanne set uku ne, abinda ya banbanta
su wannan Na macene wannan Na mazanne. kowanne da takalma abindai masha ALLAH.
tsaf Munaya ta gama gani, ta kallesa tana
fad'in “Sunyi k'yau”.
Yana basarwan nan tasa yace, “wanda
zakuyi amfani dashi gobe ne, idan akwai abinda bai yiba saiki fad'a da safe a
nemoshi, ga naki nan kema”. ‘yay maganar yana nuna mata d'ayan akwatin’.
Jawowa tayi ta bud'e, duk an d'inka kayan,
kayane masu tsadar gaske Na mace y'ar gata, bama tasan ta rungumeshi ba Dan
dad'i, sai jero masa godiya da addu'oin fatan alkairi takeyi.
Shima tuni ya manta da fushin ya rungume
kayarsa yana murmushi. cikin kunnenta yace, “kinfi k'arfin komai a wajena
friend dan kin gamawa Muhammad Sameer komai”.
Munaya ta murmusa tana d'an dukan
k'irjinsa, tace, “kana shamin k'amshin ne nagama maka komai?”.
Hannunta ya rik'e yana murmushi, yamatso
da fuskarsa gab da tata, murya k'asa-k'asa yace, “ke d'ince Zuma ce...... ”
Harar data dalla masa ta sakashi fasa
k'arasawa ya wani basar yana kashe mata ido d'aya, “dad'ina dake akwai mazurai,
gaki babu k'arfi ga tsoron tsiya”.
Munaya tayi dariya, “aka gaya maka
banida k'arfi? kabari nakuma samun lafiya sai a gwada kwanji”.
Wata dariyar mugunta Galadima yayi yace
really?”.
“yes” ta fad'a cikeda karsashinta.
Ya mik'a mata d'an yatsansa alamar su
k'ula.
Babu musu tabada nata itama suka k'ula.
Murmushi yaytayi saboda muguntar dayasan yana shiryawa, wadda ita Munaya bata
fahimci komaiba a ciki saboda wauta.🤣
*_Washe gari_*
Ta kasance safiyar suna, inda aka rad'a
sunan yara bayan sallar Asubahi, *_Abdurrahman, Abdurraheem, and Amaturrahman_*
masha ALLAH Babies ALLAH ya raya Ku akan sunnah da tafarkin addinin Islam.
Yara sunsha Addu'oin fatan alkairi
sosai, tun kuma a safiyar shagalin suna ya fara, dan kowa yana cikin walwala da
farinciki, mai jego munaya ansha k'yau itada babies har an gaji, kamar ka
sacesu ka gudu, hotuna dai suna shansu kala-kala a yau d'inan, Su Momma ma da
basa kusa anata sambad'a musu, dan duk wani motsin da za'ayi Sauban da Samha
basa gajiya da tura musu, sai sukaji tamkarma suna nan suma, saboda kallon
komai suke tamkar live, farin ciki da walwala sun yalwatu a zuciyar Abie,
bakinsa yakasa rufuwa dan tsabar nishad'i daya tsinci Kansa yau aciki.
Hummm babbar magana, kayan barka dai sun
iso, fans yaufa nasha kallo, kaga Inda akeyi don ALLAH, ta bakin Munaya tace
INA zasu da wad'annan kaya haka, lamarin tamkar fariyya, gashi kowanne sashe
sai kawo nasu sukeyi, gidan sarauta manya, babu Wanda zaiso aga kasawarsa,
ballema wannan kana k'inyi za'a CE bak'inciki kakeyi, shiyasa mama Fulani aka
ware aka zuba kayan barka Na gani Na fad'a, daga gidansu Munaya ma su inna sun
taka rawar gani dai-dai k'arfinsu, daga ita har Munubiya komai iri d'aya aka
musu, kayan babies ne kawai Na munaya yafi Na munu saboda su su uku ne ita kuma
Nata biyu.
Nanfa y'an gidan suka Shiga k'us-k'us
d'in gulmar Ina inna ta samu kud'in yin wannan hidima haka? dansu basuyi zaton
hakanba, musamman da abin yazo da yawa ma, itadai inna ma ko kallo basu isheta
ba, hidimar gabanta da farincikin datake cikine a gabanta, bakinta yakasa
rufuwa saboda farinciki da godiyar ALLAH mai sassauya al'amura a yanda yaso a
kuma lokacin da yaso, idan ALLAH ya jarabceka karkayi bak'in ciki, hak'urinka
zai iya zama sauyin alkairi a gareka, inama iyayensu Nada rai suga wannan
k'yak'yk'yawar rana, ta share hawayenta tana murmushin farin ciki, sannan ta
kira y'ar uwarta a waya suka cigaba da tattaunawa.
*****
K'arfe uku da rabi kuma za'a gudanar da
gagarumar walima da aka kama babban hall Na musamman.
A wannan rana yara dai har fada aka kaisu
sukayo gaisuwa da hotuna da mai martaba da gayyar y'an uwa da abokan arzik'i,
su Harun dai sune gaba-gaba, uban gayya kuwa Muhammad Sameer Saifudden Galadima
Baban y'an uku😂 ai ba'a cewa komai, koma ganinsa
ba'ayi saboda tsabar shiga hidima, wannan suna ko bikidai iyaka kenan.
Nasan kuma fans duk kunyi shirin wannan
walimar baje dad'i😋😋. Nifa buhu Na tanada walle😆, saura kuce
Bily tacika zari da son banza kuma🙄, har y'an anguwarmu saina kar6oma gifts d'insu😜😂🤸🏻♀.
****************
Alhmdllh yaran Mununbiya ma an rad'a
musu suna bayan sallar Asubahi, Namijin
*_Aminudeen macen Ameenatu_* ALLAH ya raya wad'annan yara masu albarka😘😘🥰.
Yau daikam farin cikin da Abba da
innarsu suke ciki 6ata lokacine ma, kai da dukkan masoyansu irinmu, masu
bak'inciki kam Ku k'ara himma, hassada ga mai rabo takice😏🤷🏻♀.
Kowa nabashi dama ya k'iyastama zuciyarsa
yanda bidirin suna yake guna, dan Alk'alamin Bily yau yayi k'ank'anta wajen
wallafowa, sai mugama Na wannan satin bikin sunan bai k'areba😁.................✍🏻
Kuyi manage da wannan yau inada uzuri🤦🏻♀.
☺my Guy's a kafta kawai danjin yanda
bikin suna zai gudana gobe idan ALLAH ya kaimu, kowa dai ya k'ure adaka dan
karfa a kawo mana raini😕, kunsan dai halin mama Fulani, tana
iya hanawa abarmu shiga😩🥺.
*_ALLAH ya
gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
*_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA
KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~Book 2~ 👉🏻2⃣5⃣
................Aunty
Salamah da kanta tazo yima Munaya kwalliyar zuwa wajen walima, saida tafara
biyawa tama Munubiya sannan ta wuto nan, ta iske su duk a damuwar kukan da
Abdurrahman ketayi, sai faman jijjigarsa akeyi amma yaro yak'i yin shiru, an
basa nono yak'i kar6a, innro ta kar6esa ta hura masa kunne, ya kuma
k'yak'yacewa da sabon kuka yana dunk'ulewa waje d'aya, tace “inaga kunnensa ke
ciwo yaronnan”.
Munaya Na gefe zaune ta zuba tagumi
kawai tana kallonsu, ita kad'ai tasan suyar da ranta ke mata, gashi Galadima
baisan wainar da ake toyawa ba, yanacan tareda su Akash da suka iso yanzu.
Innaro ta dungureta, d'ago idanu tayi ta
kalleta, ta mik'a mata Abdurrahman daketa sauke ajiyar zuciya, “d'iga masa
ruwan nono kad'an acikin kunnen insha ALLAH idan aka dace zai daina”.
Kar6arsa tayi, ta d'ora kan cinyarta,
dukma ta rikice ta rasa yanda zatayi, saboda sai mimmik'ewa yakeyi azaba na
cinsa, ga Amaturrahman itada Abdurraheem suma sun d'akko nasu kukan, laraba ta
rik'e matashi ta samu ta d'iga masa, ruwan nonon Na shiga yakuma mimmik'ewa
yana kwalla ihun sabon kuka.
Saiga hawaye a na zuba a idon Munaya,
tasaka hannu ta toshe kunen ta kozataji sassaucin jin kukan nasu dake d'aga
hankalinta.
Tausayinta saiya kama laraba, tasan indai
wannan ne yanzu ma aka fara, yaro d'aya ma ya kake k'arewa balle yara uku.
Cikin amincin ubangiji kuma duk sai
sukayi shiru, innaro da laraba sunata faman jijjiga, itama Aunty salamah ta
kar6i Na hannun munaya, tun suna ajiyar zuciya har barci ya kwashesu. Munaya ta
shige bayi tana share ragowar hawayenta.
Baki innaro ta ta6e tana fad'in “lallai
aiki yasamu mata, yo indai kukane yanzu ma kika fara”.
Daga Aunty salamah har laraba dai babu
Wanda ya tanka.
Munaya kuwa data jiyota daga bayi tace
“aniyarki ta biki, mai mugun fata kawai”.
Wanka tayo ta fito, Aunty salama kawai
ta tarar a d'akin sai bayi biyu dake morping, suka durk'ushe k'asa suna gaida
Munaya.
Hannu ta d'aga musu kawai dan
batasonyin magana, har yanzu raunin tausayin Abdurrahman baibarta ba. ta
kallesu duk suna kwance kan gado barci ya d'aukesu, yayinda Aunty Salamah ke
zaune kan sofa tana warema yaran kayan da za'a saka musu.
Ta d'ago ido tana kallon Munaya,
“haba auta kuka kikayi da gaske? Please kidaina musu kuka, ba'ason uwa Na
zubarma d'a hawaye dukda wannan Na tausayine kinji”.
Munaya ta had'iye abinda yamata tsaye a
mak'oshi tana gyad'ama Aunty salamah kai.
Saida Aunty salamah ta gama ware kayane
sannan ta taso suka fara kwalliyar, anutse sukeyin komai, dan da sauran time,
hakama Munubiya a nutse aka mata tata, anama Munaya tana kallon hotunan
Munubiya, taji dad'in yanda y'ar uwarta tasha k'yau, dukda ma batakai ga saka
kayaba.
★★★★★★★★★★★
Muftahu nata kai kawo a tsakar d'akinsa,
tunanin tawace hanya zai fargar da Galadima kawai yakeyi, dan dolene saida
hannunsa zaiyi wannan aikin, saboda had'arinsa, gudun kar reshe ya juye da
mujiya, sannan aikin yana buk'atar takune da sirri.
Fitowa yay yanufi can cikin k'aton lambun
masarautar indasu Galadima suke tareda mafi yawan y'ammata da samarin
masarautar.
Wasu sunata hirarsu in group, wasuko
hirar tasu ta masoya ce, Muftahu ya k'araso inda su Galadima suke, sun baza
babbar darduma anata hira, Bama zaka ta6a Sanin suna lambun ba saboda sunacan
ciki nesa da sauran yaran.
Galadima na zaune a gefe cikin kujera,
ya d'ora k'afafunsa a wata kujerar, sanye yake da farar shadda d'inkin boda,
fuskarnan babu walwala ko kad'an, gaba d'ayan hankalinsa yanaga system d'in
daya d'ora bisa cinya yana latsawa.
Muftahu ya mimmik'a musu hannu sukayi
musaba cikin fara'a. Amma tsakaninsa da Harun ba hakan baneba, kowa murmushi
mai cikeda ma'anoni yay ma d'an uwansa, kafin su saki hannun juna. Muftahu ya
matso kusada galadima shima ya bashi hannu sukayi musabaha, k'aramar takardar
dake mak'ale a hannunsa ya sakarma galadima a hannu.
Kallonsa galadima yayi, sai yay masa
murmushi yana signal da ido alamar ya duba.
Galadima bai ce komaiba ya cigaba da
abinda yake ya basar da takardar. Muftahu kuma ya koma cikin su Harun aka d'ora
hira, tamkar babu abinda ke damunsa.
Galadima baibi takan takardar da
Muftahu ya basaba har tsawon wasu adadin mintuna, sannan ya bud'e ya duba.
_Ranka ya dad'e ina buk'atar muyi magana
kafin a zauna wajen walima, magana mai muhimmanci please._
Iya abinda ke jikin takardar kenan.
Galadima ya d'an ja eyeglasses d'insa
k'asan ido ya kalli Muftahu, cije lips nashi yayi yana janye idonsa.
Ya sauke k'afafunsa yana d'ora laptop d'in
saman kujerar, ya d'auki ruwan gabansa yana sha da maida hankali garesu. jin
hirar tasu ta y'ammata ce sai ya zuba musu ido kawai bai saka bakiba, dan shi
dama ba'a wannan hirar dashi tun can da, suma duk sunsan haka, shiyyasa ko suna
shirmensu basa sakoshi.
Ganin zasu saka masa cinwon kai saboda
hayaniyarsu Na Neman yin yawa saiya mik'e d'auke da Laptop d'insa.
Duk kallonsa sukayi, Zayyan yace, “ina
zuwa daddyn Triple's?”.
K'aramin tsaki yaja, da k'yar ya bud'e
baki yace, “zaku samin ciwon kaine, zanje nad'an huta kafin time yayi”. ya
k'are maganar da kallon agogon hannunsa.
Matawalle yay murmushi yana salute
nashi, shima murmushin ya masa yana kaimasa rankwashi, ya kauce gefe yana
murmushi, (dayake shima bai cika hayaniya ba).
Wuce warsa yay cikin takun nan nasa Na
izza da k'asaita, da sauri wasu yaran masarautar dasuka had'a tasu dabar agefe
biyu aciki suka taso suka k'ar6i laptop
d'in hannunsa saboda girmamawa, ya mik'a
musu yana murmushi, yana gaba suna binsa a baya, sai zuba masa surutu suke akan
shagalin daza'a sha yau, shidai murmushi kawai yake musu babu magana, basu
damuba, dan kowa yasan halin galadima a masarautar nan, haihuwar nan ma wasu da
yawa zasu iya cewa sunga hak'oransa a waje. duk inda suka gitta ana kwasar
gaisuwa, bayi kam zubewa suke domin girmamawa a garesa.
Har sashensa suka masa rakkiya, sarkin
mota ya kar6a laptop d'in ya k'arasa masa da ita zuwa ciki..
Baibi ta ainahin k'ofar da zata kaishi
babban falonsu ba, saiyabi wata k'aramar k'ofa da kai tsaye nasa sashen zai shige
basai mata y'an suna sun gansa ba.
A falo ya iske Sauban kwance yana
barci, da alama yagama yawonsa ne gajiya ta makesa, da kallo Galadima ya bisa,
amma dan ya tabbatar da lafiyarsa saiya d'ora yatsunsa biyu a wuyan Sauban
d'in, babu zafi, ya maida goshinsa saiyaji zafi sosai, Galadima ya girgiza kai,
yasan dama ba lafiyace zata saka Sauban barci a irin wannan lokacin ba ana
wannan hidimar.
Bai tasheshi ba ya shige cikin bedroom,
zama yay a bakin gadon yana cire bottom d'in rigar guda uku, ya huro isaka daga
bakinsa yana zamewa ya kwanta batareda ya cire rigarba, zuciyarsa tana ta
jujjuya mi Muftahu yake nufi ne? wace magana zasu tattauna?. waya ya jawo da
nufin kiransa, sai kuma ya fasa, jefar da wayar yayi yamik'e yana ida cire
kayan gaba d'aya. ya shige wanka.
ya ja adadin wasu mintuna masu tsayi
kafin ya fito sanye da bathrobe fara sol, sai k'aramin towel a hannunsa yana
goge fuskarsa zuwa wuyansa.
Yana tsaye gaban mirror zai fara shafa
mai ya jiyo ana knocking d'in k'ofar falonsa, Computer d'in daya ajiye wadda
yake kallon kowane 6angare na sashen daga cctvs cameras d'in daya zagaye ko
ina, tun zuwan dayayi Na k'arshe ya saka akayi masa wannan aikin, sannan ya
d'auki mataki akan waccan cctv d'in da Munaya tamasa hannunka mai sanda da ita.
Sarkin k'ofa ya gani, sai kuma Muftahu
daga can waje alamar yana jiran iso ne.
Guntun tsaki Galadima yayi, ya fito zuwa
falo, Sauban dake barci ko motsi baiyiba balle yasan ana knocking d'in. yana
daga tsaye yabama sarkin k'ofa izinin shigowa.
Cikin girmamawa yace, “ranka yadad'e
yalla6ai Muftahu ne ke Neman iso”.
Da hannu Galadima ya masa nuni da ya
shigo.
Sarkin k'ofa ya amsa da to sannan ya fice.
Komawa Galadima yay ciki yacigaba da
shafa mansa, saida ya gama tsaf sannan ya zira jallabiya Brown ya fito.
A falo ya iske Muftahu zaune yana control
d'in television da remote.
Galadima ya zauna a kujera mai zaman
mutum d'aya, sai wani d'aure fuska yake.
Muftahu bai wani damuba, dan yariga ya
saba da wannan ai.
Kallonsa Galadima yayi cikin lumshe ido
yana fad'in “Mike faruwane?”.
Ajiye remote d'in Muftahu yayi, ya kalli
Sauban dake barci.
d'an ta6e baki Galadima yayi, yace,
“karka damu, kayi maganarka kai tsaye kawai”.
Cikin jinjina kai Muftahu yace, “Ok, babu
abinda ke faruwa saidai shirin faruwar kam, Ranka ya dad'e bamuda isashen
lokacin wata magana mai tsawo yanzu, saidai ga wannan takardar ka duba, so
yanzu wannan ne akan ga6a, shine yakamata mu d'au mataki akansa, daga baya komi
kenan namaka alk'awarin warware makashi, fatana dai ka fahimci wannan d'in
saboda had'arinsa”.
Kar6ar takardar Galadima yayi, ya
d'auki medical glasses d'insa daya ajiye a teble glass d'in dake gefen haggunsa
ya saka, duba takardar yay a tsanake, cikin wani yanayi dake nuna tsantsar
tashin hanki yace, “Muftahu wannan
maganar gaskiya ce kokuwa? karkamin wasa da hankali a wannan karon dan bazan
d'aga maka k'afa ba a wannan ga6ar alwashi nane”.
Murmushi Muftahu yayi, ya sauke ajiyar
zuciya yana fad'in “Nabaka wannan damar, inhar kayi gamo da sa6anin hakan karka
barni da numfashi ranka ya dad'e”.
Wani shegen Murmushi Galadima yayi,
yamik'e d'auke da takardar ya koma bedroom batare da kuma kallon Muftahu ba.
Tausayin Galadima ya kama Muftahu,
mik'ewa yay shima ya fice.
Jefar da takardar Galadima yayi akan
gado yana taune lips nashi tamkar zai huhhudashi, wata irin suya zuciyarsa ke
masa, lallai dolene ya jinjinama Munaya, dan ta taka rawa wajen shagaltar dashi
wanene shi? minene burinsa?, ganin tunani bazai masaba yatashi jikinsa Na rawa
yafara wasu had'e-had'en abubuwa, waya ya d'auka ya kira Ayusher, ta d'aga
cikin hanzari tana mik'ama Munaya dake shayar da Amaturrahman data tashi daga
barci tana kuka.
Kallonta tayi da mamaki tace, “wace Ayusher?.......”.
Galadima ya katseta da fad'in “ki kawomin
kayanda su Abdurraheem zasu saka”. iyakar maganar da yay kenan ya yanke wayar
yana cigaba da latse-latse, zuwa can kuma ya ajiye ya mik'e yana cire jallabiyar
jikinsa.
Baki sake Munaya tabi wayar da kallo,
mike damun galadima haka? Muryarshi irin wadda tasan asalin galadima ce, hakan
na nufin akwai matsala kenan? to mine zaiyi da kayan da yara zasu saka?. batada
mai bata wad'an nan amsoshin dan haka ta mike tana ajiye Amaturrahman d'in,
aiko ta fashe da kuka an cireta bata k'oshiba, tsaki Munaya tayi tana fad'in
“ai saikiyi tayi, ku matsala ubanku matsala mutum yarasa wazai kama.
Ayusher da Aunty Salamah suka kalli juna
suna gumtse dariya.
Gyale taja ta lullu6a, dama tasaka doguwar
rigar matirial kafin dai time ya k'arasa. ganin zata wuce yarinya na kuka Auntu
Salamah tace, “dawo ki d'auketa mana, idan kinje can saiki bata nonon”.
Tamkar Munaya zata saka kuka haka ta dawo
ta kwashi Amaturrahman ta fice tana k'unk'uni.
A falo ta iske Sauban Na barci, wucewa
tayi cikin bedroom d'in kanta tsaye, amma saida tayi sallama ya bata izinin
shiga.
Tun da ta shigo taga yanayin da yake sai
gabanta ya dad'i, tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki ta mik'a masa ledar
data zubo kayan sannan ta zauna a kunyace saboda yanayin da yake babu kaya.
Ba tare da ya kalleta ba ya hau Fiddo
kayan, ya zubesu saman gado yana d'aukar hotonsu a waya, yay latse-latse nawasu
mintuna kafin yasaka wayar a kunne.
“Saleem ka dubamin kalar kayannan, koda
basu kaisu tsadaba, yanzunan kataho ka kawominsu”.
Bataji mi Saleem yafad'a daga canba.
Muryarta a raunane tace, “yalla6ai mike
faruwa wai?”.
Jajayen idanunsa ya d'ago ya kalleta,
k'ala baice mataba ya mik'e ya d'akko wani k'aramin box ya dawo ya zauna, ita
duk saima kunya takuma kamata, saboda dagashi sai boxer, amma taga ko a kwalar
rigarsa bai damuba, hidimar gabansa kawai yakeyi.
Kwantar da Amaturrahman tayi kusa dashi ta
tashi zuwa wardrobe d'insa, k'aramar t-shirt ta d'akko, tazo ta mik'a masa.
Ya d'ago ido yana zuba mata harara, dukda
ta tsorata saita daure tace, “please mana yalla6ai”. tayi maganar muryarta a
raunane.
Saida yayi k'aramin tsaki kafin ya amsa ya
saka, wani abu da batasan minene ba taga yana mak'alawa jikin kayan yaran,
saida yagama tsaf sannan ya maidasu a ledar, kallon Amaturrahman dake k'yalla
y'an idanu zata fara k'aramin kuka yayi, ya shafa kumatunta batare da ya
d'auketa ba.
Laptop d'in sa ya jawo ya saka eye
glasses d'insa, ya kalli Munaya yamata alama da ido akan tazo.
Babu musu ta taso zuwa kusa dashi ta
zauna.
Laptop d'in ya d'ora mata akan cinya yace,
“wanene SD a cikin su?”.
Nutsuwa Munaya tayi tana kallon hotunan,
cikin waro ido tace, “kai ga Fu'ad ai”.
Da mamaki Galadima yace, “Fu'ad!?”.
“eh wlhy yalla6ai, Wanda ya kaimu birnin
gayu plaza ranar da abunnan ya faru”.
Kar6a laptop d'in Galadima yayi yakuma
kallon hoton da k'yau yana taunar lips, kuma mik'a mata yayi batare da yace
komaiba. itama batace dashiba tacigaba da bin hotunan da kallo sannu a hankali. Harta kai k'arshensu babu SD. ta
kalleshi cikin damuwa, “yalla6ai babushi fa anan gaskiya”.
Kansa ya jinjina mata yana kar6ar laptop
d'in, cigaba yay da danne danne, itadai Munaya tana kallonsa.
Kuma d'agowa yay ya kalli Munaya,
“duba annan kuma fa”.
Kallon hotunan ta shigayi, canko saiga
hoton SD, tace, “Alhmdllh gashi anan”.
Kallon hoton Galadima yayi, da mamaki yace,
“kinsan wanene wannan kuwa?”.
“Ah! yalla6ai SD ne mana”.
“Munaya kin tabbata wannan ne kika gani
a wajen Abba?”.
“Wlhy shine yalla6ai, bazan ta6a manta
fuskarsa ba ai komai dad'ewa. balle acikin abinda bai rufa 2years ba, amma kasanshi
ne?”.
Bai iya cemata komaiba, sai zuciyarsa
dake wani irin bugawa da sauri-sauri kamar zata fad'o, mamaki ya hanashi motsin
kirkirma, Alhaji Shehu Darma shine SD kenan, babban Amini kuma d'an uwa ga
Mahaifin su Samha, innalillahi, ya abubuwa keneman koma masa rikid'ar hawainiya
haka?, wannan fa Fu'ad d'in d'ane ga yayar Uwargidan Sarki mahaifiyarsu
Matawalle, cikin cije lips ya buga hannunsa akan gadon yana fad'in “Kai!!!!
miyasa hakane? miyasa duk Wanda Na yarda dashi shike fara bayyana a maicin
dunduniyata?!! miyasa rayuwa tazomin da irin wannan rikicin ne?, oh God!!”. ‘ya
k'are maganar cikin matsanancin k'araji, tareda runtse hannayensa waje d'aya.
Tsoro ya kama Munaya, ganin yanda duk ya
rikice kamanninsa suka canja, idonsa yayi matuk'a jajur, jijiyoyinsa da gashin
jikinsa duk sun mimmmik'e, ga Amaturrahman data tsorata lokacin daya buga
gadon, d'aukarta tayi tahau jijjigawa.
Sauban ma a firgice ya tashi, ya hau
waige-waige, ganin babu kowa a falon saiya nufo hanyar bedroom d'in Galadima,
tabbas muryarsa yaji a yanayin da ba'aso. harzai murd'a k'ofar saiya fasa
saboda jin kamar muryar Munaya tana magana.
Tunda tasamu Amaturrahman tayi shiru sai
ta d'auki towel d'insa ta goyata, ta matsa kusadashi a tsorace, hannunta ta
d'ora akan nasa daya dafe mirror, ko motsi baiyiba balle ya kalleta.
Murya a d'arare kuma a sanyaye tace,
“please yalla6ai, fushi baisa a samu sauk'i saidai ya k'ara zafi, kaine kasha
gayamin wani karatun baya buk'atar fassara ko dogon nazari, akan barsane kawai
a yanda yazo, dukda bansan tushen matsalarba zan iya bada gudunmawa wajen kama
bakin zarenta, kayi hak'uri ka kwantar da hankalinka, ita fahimta fuskace, ba
fushinka ko tsantsar damuwa ne abin buk'atarba yanzu, d'ana tarkon dazai fara
kamo maka hannun mak'iya shine jarumta, ka danne kuma ka daure, ni dama Dan
banida ikon hana walimar nanne kawai, amma inaji a jikina akwai lauje cikin
nad'i, saidai wad'anda suka nad'a d'inne bamuda ilimin saninsu sai ALLAH yaso
Samar damu, amma ai duniya makarantace, idan su a can suka yini kaikuma saika
nuna musu kwana kayi, lokuta da dama fushinka ke lalata maka aiki, dan inhar
kana cikin fushi dukkan aikinka tafiyar hawainiya yake, wannan lagon naka suka
samu suke wasa da hankalinka, koda ace wani ya salwanta cikin yarannan karka
d'aga hankalinka, ALLAH n daya baka yafika sanin hikimar k'addara hakan, duk lokacinda kaga Matsaloli
sun raunana, buk'atu kan kuma kan yalwata ne,
kasa a ranka wannan wata damace tazo gareka, ai duk lokacin da aka rasa
kwallo a cikin wasa, ba wasan ake dainawa ba, wata kwallon ake jehowa a cikin
fili”.
Duk maganar da takeyi ko motsawa
baiyiba, baikuma juyo ya kalleta ba, saidai alamu sun nuna yana saurarenta, ta
janye hannunta ta juya zata fita tana hawaye.
Cak ta tsaya saboda rik'o hannunta da
yayi, kusan minti 1 suna a haka, ta waigo ta kallesa, har yanzu yana a yanda
yake, kallon hannunsa daya ruk'o nata tayi.
Bai kalletan ba kuma bai saki hannunba
yace, “Lallai ina shaidama dukkan Wanda ya maida rayuwata data ahalina magijin
kallonsa, zan tsiyayar masa da idanun, sannan zan kacaccala rayuwarsa Na
binnesa da ransa”. ya mik'e tsaye sosai tareda juyowa ya jawo hannunta ta fad'o
jikinsa, saurin dafe Amaturrahman dake bayanta tayi da d'ayan hannun. Ya saka
idonsa dasuka firgitata cikin nata, fuskarsa dab da tata yace, “kedai kibama
yaranki kariya kawai, dan sune fitilar zuciyar mijinki”.. sakin hannunta yay ya zagayeta yabar wajen.
Tamkar sokuwa haka ta bisa da kallo,
yayinda zuciyarta keta kuma maimaita maganar tasa, _yaranta, kuma mijinta?_ mi
yake nufi to?, amsar itace bata saniba.
Jitai kawai ya saka mata ledar kayansu
Abdurraheem a cikin hannu, baice k'alaba yabar wajen zuwa gaban wardrobe d'insa
yafara fiddo had'add'iyar Shadda gizna ash colour, sai maik'o take da d'aukar
idonu.
Ganin ya shareta yana cigaba da hidimarsa
itama saita juya ta fice.
Tunda Sauban yaji motsin kama handle d'in
k'ofar yabar wajen da sauri.
Fitarta babu dad'ewa Saleem ya kawo
kayanda Galadima ya umarcesa.
__________________________
Munaya Na komawa Aunty Salamah tahau
shiryata, dukda taga a yanayin data dawo bata tambayeta daliliba, saida tagama
gyara mata fuska tana gyara mata gashi Munaya tafara fad'a mata iya abinda taga
ya dace kawai Aunty Salamahr ta iya Sani, sauran kuma sirrinta ne ita da
mijinta.
Murmushi Aunty Salamah tayi, tace,
“dukda banida tabbacin faruwar wani Abu dagani har Munubiya dama mun shirya
hanyoyin d'aukar matakai saboda tsaro, kowa baisan dalilin Munubiya na dagewa
akan ki dawo gida ki haihuba, amma ita tasan dalilinta, ba son zuciya ya sakata
yin hakanba, Ubangiji Na kallon kowa kuma zaiyi maganin komai, tun a shekaran
jiya Saleem yazo mungama tsara komai dama, kuma ya tabbatar min Muftahu yasan
komai dan yaga alamar shima tsaye yake da k'afafunsa, inaga yau dai shine
yabama Galadima satar amsa, kuma hakan da yayi shine dai-dai, saboda duk abinda
zai faru a yau d'innan shi Galadima zai fara zargi”.
Munaya tace, “hakane Aunty Salamah,
shiyyasa wlhy Muftahu yafara bani tausayi, ALLAH ya kawo ranarda zai wankesa
ayi walk'iya aga kowa dai”.
Amin ya rabbi gimbiyar Galadima Sameer,
ku kwantar da hankalinku, komai kam ya taho gangarar zuwa k'arshe, dan alamomi
suna nuna haka”.
“nima inajin haka a jikina Aunty Salamah”.
Da wannan hirar aka gama gyaran kan tahau
shiri cikin less d'inta Ash colour irin kamar kayan da Galadima zai saka kenan.
Hummm masha ALLAH, maganar k'yawun da
Munaya tayima 6ata lokacine, amma tayi k'yau.
Yaranma tsaf aka gama shiryasu, abin kamar
ka sacesu ka gudu, sunyi fes.
Kowa yagama hada-hadar shiri, ana
fitowa daga sallar La'asar za'a fara kwasar mutane zuwa hall d'in da aka
tanada.
*_4:00pm_*
Dukkan mai ruwa da tsaki akan wannan taro ya
hallara a gaban motocin da za'a kwashi jama'a, ana fitowa daga salla kuwa aka
fara tafiya.
Munaya dai tana d'aki bata fitoba, hakama
Galadima saida ya dawo salla sannan yafara shiri ma shi.
Saida kusan kowa ya tafi sannan iyayen
gayya suka fito.
Munaya ce tafara fitowa, kuyangi Uku Na
d'auke da yaran a bayanta, yayinda wasu kuma ke take mata baya, a babban falon
sashensu suka tsaya jiran fitowar Galadima.
Tunkan ya fito daddad'an k'amshinsa ya
fara isowa, saikuma sautin takun takalminsa wanda tarihi yaso maimaita kansa ga
munaya, dan takun nasa Na daidaituwa ne da bugun zuciyarta.
Yana gaba Sauban na binsa a baya, Tunda
ya fito Kuyangin duk sukai k'asa da Kansu, yayinda ya k'araso sai suka zube
k'asa suna kwasar gaisuwa, hannu kawai ya d'aga musu, idonsa akan Munaya wadda
itama ta risinar da idonta tana masa kallon k'asan ido.
Ba k'arya yayi matuk'ar k'yau, komai
nasa Ash colour ne, kuma kayan sarauta y'an asali, harda rawanin daya kuma
fiddi ainahinsa Na jinin sarauta, rawanin ya sakaya sajensa hancinsa zuwa
bakinsa kawai ake iya gani, idanunsa na cikin eyeglasses dabaka isa kaga
kwayarsu ba, dan ya toshe su 6am.
Juyawa yay ya kalli Sauban dake gefensa,
Sauban ya fiddo Alk'yabbar dake cikin bag d'in hannunsa ya mik'a masa, kar6a
galadima yayi yana mik'ama Sauban had'ad'd'iyar sandar hannunsa da zaka iya
d'auka ta gold ce, ya warware alkyabbar ya matsa gaban Munaya dake tsaye har
yanzu, yayinda kuyanginta ke a dur kushe har yanzu suma.
Matsawa yay jikinta tamkar zai rungumeta,
k'amshin turarensa ya cika hancinta ta lumshe idanu, ya sako alk'yabbar ta
bayanta, Sauban na gefe yanata zuba murmushi da d'aukarsu hoto.
Tamkar sokuwa haka Munaya ta tsaya har
Galadima ya gama saka mata alk'yabbar a jiki, ya juya Sauban yakuma bashi
turaren dake cikin jakkar, feshi ya shiga yimata da turaren, zuciyarta sai
kaikawo take yi na d'umbin mamaki da al'ajabin wannan salo,
Bayan ya gama ya maidawa Sauban turaren
yanama Munaya nuni da suje da hannu.
Haka suka fito a jere Kuyangi na take musu
baya, yayinda Sauban yake gefe yanata zuba musu hotuna a Camera.
Motar da Sarki ya bada ita aka bud'e
musu suka shiga, Sauban ya kar6i yaran d'ai-d'ai ya mik'a musu, sannan ya shiga
gaba kusada sarkin mota da Amaturrahman shima.
Motar ta d'auki shiru tamkar babu wani
mahaluki mai numfashi, Galadima ya zubama Abdurahman dake hannunsa ido kawai
yana kallo, yayinda ya sak'ala hannunsa d'aya cikin Na Munaya yana murzayatsuna
a hankali.
Itama dai tayi shiru sassan jikinta Na kar6ar
sak'on ninsa.
A haka suka Isa har cikin harabar hotel
d'in, Wanda ya cika dank'am da motoci, duk Wanda yagani yasan yau taron Na
manyane, kodan tsaro Na musamman da wajen ya samu tundaga farkon Layin da hotel
d'in yake.
Sauban da Sarkin mota suka fito, ba'a
bud'e su Munaya ba, kalonta Galadima yayi fuskarnan dai babu walwala har yanzu,
batareda yayi maganar ba ya kamo kwalliyar zaren gaban alk'yabbarta ya matso da
fuskarta kusa da tashi, ta bud'e baki zatai magana ya d'ora nashi.
Saida ya shanye jambakin lips d'inta tas
sannan ya saketa yana zuba mata harara.
Idonta harsun tara kwalla, cikin lumshe
idanu da k'asaitacciyar muryarnan tasa mai had'e da izza yace, “Sau d'aya nake
gargad'i, karki bari nasake miki na uku akan fita da lipstick a baki”. ya k'are
maganar da kad'a mata yatsansa.
Wani yawu Munaya ta had'iye kawai tana
jinjina masa kai, wannan ikon ikoko yana bata mamaki, shiyyasa fa tace Aunty
salamah ta saka mata janbakin kad'an, gashi yamata k'yau amma tsabar mugunta ya
shanye, lips d'insa sai zafi yakeyi, ta harari Abdurraheem dake cinyarta,
saikace shine yayi laifin🤭😂.
Bud'e musu akayi suka fita, Samha da
Ayusher suka kar6i yaran.
Munaya taji matuk'ar dad'i da ganin ashe
harda y'ar uwarta a walimar, itama sunsha k'yau cikin Brown d'in kaya itada yaa
Marwan, tana cikin less irinna Munaya, kalarce kawai ta banbanta, shikuma Yaa
Marwan harda babar riga, maganar k'yawun dasukaima 6ata lokacine, suma Yaa
Fadeel da Feena suna d'auke da yaransu.
Sun shiga cikin hall d'in da tawagar rakkiyar
Kuyangi da dogarai, masha ALLAH Munaya tafad'a dan ganin d'unbin jama'a da aka
Tara a wannan k'aton hall, manyan mutane da iyalansu sun halarci wannan waje,
hakama ahalinsu Munaya kwai da kwarkwata sunzo, harda y'an anguwarsu, duk yawan
mutanen nan bai hana a saka mata kan tsaro masu tauriba a wajen.
Kowa saida su Galadima suka birgesa,
abin akwai tsantsar birgewa da sha'a a cikinsa,
A cikin fans harda masu k'yasa Galadima🙆🏽.
barama namuku gulma, can Na hango muku
tawan Miss xoxo fa idonta kamar zai fad'o, hakama zee bawa da Aysha dansabo da
kdeey🤥, dukda harar da Maman Khady da
takwara billy galadanci ke musu sunk'i rusunar da idanu, lamari ya girmama
Slimzy harda k'ok'arin mik'ewa fa wai zata iya barin sadeeq d'inta, da sauri
saffiya Huguma ta maidata mazaunin tana hararta, Ummi Ai'sha tace, “kai dan
ALLAH Ku nutsu kar'ace 'yan Haske muncika ruwan ido”, Faxy Fation da party
zarah da Feedohm sukace ai Galadima
d'inne fa yaji gishiri da magi, Hafsat Rano ta toshe baki tana dariya, hajja
kam yitai kamar bata wajen, sai loda nama take a baki, Ayusher da khaleesat
dake kallonta sukace wai hajja bazaki rage filiba a cikinki?, Mamu gee tace,
“kukuma ga sa ido” “kema k'ya fad'a dai” cewar zee yabour, Asmy b Aliyu datun
d'an tai shiru itada Ummu Basheer suka yamutsa fuska suna fad'in “please kuja
aji mana 'yan haske, kunafa ganin yanda aka karrama mu fiye da kowa, karku jafa
a maidamu kujerar baya wlhy”. Ni bilyn Abdull da lamarinsu ya girmeni nace,
“kubarsu kudai kawai, sosuke susa a hanamu ganin sarakuna, kokuma mama Fulani
ta rainamu, kuna dai ganin innaro ma kanta yanda taja aji ta kwamushe a gefe
tana mazurai.
Miss xoxo dake gefena tayi k'asa da murya
tana dai-daita kanta, tace, “gaskiya kika fad'a tawan, nidai kinsan dama dai
Galadima ya dad'e a k'ok'on raina, ko sau d'ayane kisan yanda kikayi aka mana
hoto tare”. Nace, “karki damu tawan, Salfe ma zakuyi, amma fa ki kula, dan
Munaya babu sauk'i”. “gulmar mi kukeyi?” cewar Ayusher tana jeho mana
handkerchief d'in hannunta. zamanmu muka gyara nuna wani basarwa🥺, kunsan fa muma mun fara koya a
wajen Galadima😜.
Lallai, fans sannunkufa, lallai kunma
munubiya da Munaya kara, ko Galadima nasan kun gama birgesa aradu, irin wannan
anko da kukasha, ko a UK albarka y'ay'an baba buhari😝.
____________________
Isowar Sarki Jalaluddeen da Sarki
Abdul-fatah da tawagar wasu amintattun sarakunan abokan Abie ya saka kowa ya
mik'e cikin girmamawa, saida suka zauna sannan kowa ya koma ya zauna, an fara
bud'e taro da addu'oi ga jarirai da kuma kakansu sannan aka fara gudanar da
abinda ya Tara jama'a cikin nutsuwa.
Kusan dai lamari Na manya, mudai Fans d'in
raina kama sai zuba salfe muke, karkaje kabada labari ace k'arya ka zula
bakajeba😆, shiyyasa muka kafa hujja koya kukace my sweet fans🤷🏻♀😂?.
Masu 6oyayyen shiri a zuciyaa fa
sunata k'iyasata yanda abubuwan da suka shirya zasu gudana, saidai kuma idan
sunsan wata basusan wataba, dan eyeglasses d'in idon Galadima Google ne😏, (wato camera ne) tundaga Inda yake yanayo zooming
d'in wad'anda suka k'arshen hall d'in ma, duk Wanda zuciyarsa ta saka masa
alamar tambaya akansa yana tantancesu ne d'aya bayan d'aya.
Nidai Galadima ka kula banda fans d'in
raina kama😨🙆🏽.
Anyi nisa da taro harma Anfara zubama
cikin maik'o da mask'i, ga mai zak'i da sanyi muna korawa, Galadima ya kalli
agogon azurfa dake hannunsa sannan ya d'ago ya kalli Muftahu suka had'a ido,
lips ya ciza, Muftahu daya fahimci yaren ya gyad'a masa kai, ya kuma kallon
Saleem da Nuren da Aunty mimi Mom and Sauban Samha Ayusher, kowannensu Kansa ya
gyad'a alamar fahimta.................✍🏻
Turk'ashi, tofa masu karatu, shin mike
shirin faruwane haka? Wannan amsa tana page 26 da zaizo ranar Monday insha
ALLAH. musha weekend lafiya sisters and brothers.🙋🏻🙋🏻🙋🏻
Barkanku da juma'at😁🤝🏻
*_ALLAH ka
gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
No comments