RAINA KAMA (BOOK 1) 7&8
*_♦RAINA
KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
👉🏻7⃣
.......Yau ake saka ran ganin wata, dan
haka kowane gida zaka iya jiyo kamshin miya
dana nama, harma da kayan snacks.
Muma agidanmu kusan hakanne ta kasance, dan
kowanne 6angare sunata hidimarsu, yau ko bud'a baki bakowa yasamu zaman yinsa
ba.
Muma muna namu 6angare muna taya innarmu
ayyukanta, dayake kowa yana miyarsane, da safe ahad'u ayi tuwo da masa da shinkafa,
haka muke had'a kalolin abinci iri-iri saboda yawan jama'a da gidanmu kan tara
a ranar salla, abokan yayunmu maza, abokan su abbanmu dawasu dangin iyayenmu
mata.
Har wajen 10 munata aiki, sai kuma a
lokacinne mukaji ana sanar da ganin wata.
Nannafa yara suka shiga murna gobe salla,
Muma kanmu manyan murnar mukeyi. badan mun kammala aikiba muka kwanta.
Washe gari tun kiran sallar farko aka
tadamu muka fara aiki, sai wajen 7am muka samu kanmu, a gurguje muka fara wanka
da shirin tafiya idi, duk shekara dama 'yan gidanmu a masallacin da sarki yake
salla muma mukeyi.
A gurguje duk mukaita fitowa saboda
horn da yayyenmu suketa mana, yara an d'urasu a school bos d'insu Na makaranta,
yayinda mukuma muka rarrabu a motar yayinmu datasu Abba dasuka bayar, tunda
bakowa keda motarna acikin yayyen namu.
Dagani har Munubiya cikin shigarmu muke
iri d'aya tamkar yanda muka saba a koda yaushe, dai-dai da kwalliyama iri
d'ayace a fuskarmu, komai namu mukayishi iri d'ayane, wannan yasaka ake gaza
banbancemu akoda yaushe.
Mun Isa filin idi, inda muka taddashi
dank'am da jama'a maza da mata, wasu harda iyalansu, kamar yanda muma muka taho
baki d'aya harsu innarmu, mu mata muna 6angaren mata, yayinda mazan sukayi nasu
6angare.
Khud'ubar da aka gabatar tazamo mana
mai ratsa jiki da 6argo, Malam yayita cikin tsantsar larabci, yayinda wani
malamin ya fassara acikin harshen Hausa, saboda marasa jin larabcin irinsu o e🙊.
Daga nan aka gudanar da sallar idi
kamar yanda addini ya koyar.
Had'a kan yaran muka shigayi gudin
karsuyi wani waje, sai dai hakan bata samuba, dan annemi Kamal da Haneep an
rasa, nannafa muka shiga bulayin nemansu, duk mun rikice, gashi baba k'arami da
Abbah sai fad'a suke wai sakacinmu ne.
Tamkar zan kifa haka nake tafiya da
sassarfa ina kalle-kalle. ban ankaraba naji naci karo da Abu, tunkan inkai
idona kansa k'amshin turarensa yabigi hancina. da sauri na ware manyan idanuna
bisa kamilalliyar fuskarsa dake d'aure babu alamar yasan miyema dariya, janye
idona nayi cikin fargaba da fad'awa kogin tunani, inban mantaba irin wannan
k'amshin naji a asibiti wajen Wanda aka kira galadima a wacan ranar da feena
batada lafiya.
Cikin yanayin tantama Na maida idona
nad'an saci kallonsa...
Tsaye yake kyam tamkar dutshin da aka dasa
waje d'aya, idonsa akan wayarsa dake k'asa a tarwatse, Wanda inada tabbacin
karon damukacine yasaka wayar fad'uwa.
A rikice nace “ya Salam” tareda
duk'usawa nafara harhad'a wayar.
A hankali ya durk'usa kamar yanda nima
nayi, ya d'ora hannunsa akan wayar dana ke k'ok'arin sakama battery ya zareta
daga cikin hannuna. bugun zuciyata yak'aru saboda tsoro gashi yak'i cewa
uffan, nasan nice da laifi, kafin Na
ankara ya sake d'oramin wayar bisa hannuna yamik'e yabar wajen.
Sororo nabisa da kallon mamaki da
al'ajabi, sanye yake cikin farar shadda k'al, wando da riga harda malun-malun,
ya murza hularnan da ake kira Minister bak'a a kansa, takalminsa da agogonsa
duk bak'ak'e, duk da bawani k'are masa kallo nayiba fuska da fuska nasan tabbas
yayi k'yau, kayan sun maidashi wani babban mutum. Ajiyar zuciya Na sauke saboda
ya 6acema ganina, nabi wayar daya barni da ita a hannu da kallo, tomi yake nufi
da hakan?.
Banida mai bani amsa, dan haka nacigaba da
had'a wayar, sai alokacin Na lura da sim card d'insa dake kan wayar yacire
d'azun lokacin daya kar6a kenan.
Jujjuya wayar nashigayi cikin tafin
hannuna, wayace mai azabar k'yau ga k'amshin turarensa ya manne jikin wayar
tamkar itama ana fesa matane. 'Yar tsagewane tayi kad'an daga gefe, amma daga
hakan ni banga wata matsalaba, kenan yana nufin koyaya waya ta tsage a hannunsa
tatashi aiki a garesa?. Nanma babu mai bani amsata. Cikin mak'oshi Na furta to
wanene wannan d'in shikuma?”.
“Galadima!”. ‘naji wata murya tafad'a
abayana’.
Cikin
hanzari najuyon dan inga mai bani amsar tawa. wayam naga babu kowa, sai alamar
gittawar mutum mai jajayen kaya.
Goshina Na dafe inamai runtse idanuna,
cikeda mamaki nace, “kenan shine wanda yabama feena jini? Galadima!”.
Nafad'a cikin bud'e idanuna inabin inda
yabi da kallo tamkar zan sake ganinsa, a hankali nakuma furta _“Galadima!”_.
“galadima kuma?”.
Najiyo muryar Safara'u a bayana, da sauri
a cusa wayar cikin hijjabina Na mik'e, kallonta nayi cikin basarwa nace, “ya
angansu ne”.
Tace “eh mana an gansu tun d'azun, saikuma
aka koma nemanki, miya faru naji kina kiran sunan galadima?”.
d'an guntun tsaki naja “naji wasu 'yan
matane suna fad'in wai INA zasuga Galadima, tunda ance yazo sallar idi. shine
nikuma nake maimaita sunan Galadiman saboda takaicinsu”.
Dariya Safara'u tayi, ke 'Yar uwa
karkiga laifinsu wlhy, koni zan sameshi saina bar Sadeeq wlhy, yanzu fa Nima
ake nunaminshi, dama haka yahad'u? Wayyo ALLAH yau naga tsantsar gwanzartakar
sarauta ajikin bawan ALLAH nan, tafiyarsama kawai abin kalloce, inaga kuma yayi
magana?, kai ALLAH yakai damo ga harawa...... kedai kawai........
Baki kawai Na ta6e, batareda nagamajin
k'arshen zancen nataba nayi gaba abuna da mamakinta a raina, wai zata iya Barin
sadeeq?, saikace ba'akan sadeeq d'in bane akaso cin zarafina da innarmu, amma
yanzu saboda taga Wanda ya fishi bakinta yake furta haka.
Da gudu Safara'u tabiyoni. Kusan a tare
muka k'arasa Inda motarmu ta tsaya, yaa hameed yafara zagina akan INA kuma naje
Na tsaya?, hak'uri nabashi muka Shiga mota kawai, dan nasan shima d'in
masifafene kamar su abbanmu.
Amotar ana fira amma ni tunanina yanakan
had'uwarmu da Galadima ta yau, ga mamakin wayarsa daya bari yatafi a hannuna
batareda yace min uffanba, kai wannan Bawa yanaji da k'asaita da mulki.
Har muka Isa gida bakina bai iya furta
komaiba acikin hirar tasu. Mun tatar su innarmu ma harsun huta su, yara kan
summa fara cin abinci.
Ban zauna faloba kamar yanda munubiya
tayi, saina zarce bedroom d'inmu Na 6oye wayar sannan nacire hijjab d'ina
nashiga bathroom Na wanke hannuna gudun kar wani yaji k'amshin turaren saina
dawo falon.
Tuni gidanmu ya kacame da hayaniya,
munubiya tazubo mana masa da fankasu zamu faraci Ayusher da Feena suka shigo da
gudu, juna muka rungume muna murnar ganinsu, Yaa Fadeel & yaa Marwan suma
suka shigo, sai mama Rabi'a dake take musu baya tana rik'e da hannun Ahmad.
Nan muma muka kacame da farin cikin
ganin 'yan uwanmu wad'anda bamuda kamarsu, innarmu ta baje mana abinci da
kayayyaki da dama dansu duk ta tanadesu, sai makwafta dasuke gaisawar arzik'i
suma duk tabada ankakkai musu.
Bamusan hidimar da kowa keyi anasa
6angarenba, mudai namu muka sani.
Ayusher takawo bakinta saitin kunnena,
ahankali ta rad'amin sweet sis.... Wlhy k'amshin turaren Galadima kikeyi,
kinsan har abada bazan mance k'amshi nan ba”.
Cikin dakiya Na d'ago kai Na kalleta
tareda balla mata harara, “Ayusher wlhy ki kiyayeni, a'a k'amshin turaren sarki
kikaji bana Galadima ba k'arewa”.
dariya ta sanya harda rik'e ciki, nikuma
Na tashi Na canja waje ina mamakin Ayusher mai gani har hanji, duk dawanke hannuna danayi sosai amma ace wai
har yanzun anajin k'amshin turaren?, kai shikam wannan dawane mayen turare yake
aiki haka?”.
Wajen 12 muka fito domin zuwa kallon
sarki dazai wice yima governor barka da salla.
A wannan karan tafiyarmu daban data 'yan
gidanmu, dan mafi yawancinsu duk sun fice gidajen kakanninsu, tacan masu ra'ayin
zuwan suma zasuje.
Mukuwa mudasu yaa marwan muka tafi.
Acikin gari duk inda ka kalla jama'a ne
keta kai kawo, musamman yara da 'yanmata da samari, kowa yaci kwalliya ta kece
raini da garari (yo dama ai ance ba'a za6ar budurwa ran salla, saboda duk
k'azantar mutum ranar saika sameshi cikin tsafta da gayu😂).
Dukda akwai rana hakan bai hanamu
jeruwaba domin kallon wucewar mai martaba sarkinmu da jama'arsa.
Masu busa algaita da kid'an taushine
suka fara wucewa, sai kuma ga tawagar sarki Na biye.
tawagar saiki Na wucewa sai ta Galadima,
kamar yanda mukaji wasu gungun samari Na fad'ar cewa ga Galadima nan.
Kowa yasan dama tsarin haka yake, daga
sarki sai shi.
'Daga idanuna nayin donson sake ganinsa
a karo na biyu. yanzu kam ya canja shigarsa zuwa milk coulor d'in janfa da
wando Na lallausan yadi, Wanda aka k'awatashi da d'inkin surfani Na ainahin
gidan masu sarauta, ya d'ora Brown Na alk'yabba mai kwalliyar Milk Color,
hakama rawaninsa daya zagaye fuskarsa ya kasance milk ne, takalmansa heir cover
masu lankwasa daga gaba irinna sarauta, sukuma Brown. yanzun kam fuskarsa
d'auke take da k'asaitaccen murmushi mai kama da anmasa dole, hannunsa d'aya
dayake d'agama mutane yana d'aureda farin agogon azurfa, sai zabba biyu a
yatsunsa Na tsakkiya Wanda nake k'yautata zaton azurfane suma.
Nanfa su Ayusher suka fara d'aukarsa
hotonsa a wayoyinsu.
Tsaki naja ina hararsu, “mtsoww wahalallu
kawai, dama kanku kuka d'auka yafi Ku k'are wajen d'ura hotunan Wanda baisanma da
zamankuba a wayarku”.
Kafin cikin su Ayusher wata tabani amsa,
wasu 'yan mata dake kusadamu d'aya ta kar6e da fad'in “k 'yan mata kama kanki,
kodai kema son nasa ne yakaiki ga kishinsa?”.
Wata wawuyar harara Na buga mata,
“kekuma shasha waya sako bakinki?, kajimin ballagaza kawai, uwarmiye abin so a
jikinsa dahar ya isa ayi kishinsa? Ke dai dabakisan inda ke miki k'aik'ayiba
ita dakon wahala, dan nakula ke amatanma suffar mata maza ALLAH yayiki....”
Gaba d'aya suka taso min da masifa tamkar
zasu cinyeni d'anya itada k'awayenta..
Yaa marwan dake zaune saman mota a bayanmu
duk yana saurarenmu yad'ago kai ya kalleni, yasan tabas Munaya ce, baya
buk'atar k'arin bayani kuma ko tambayar wacece ita, tunda Na nuna halin nawa,
yace, “K munaya zoki shige mota”.
Nasan halinsa sarai baya wasa damu, cikin
tunzura baki gaba nazo nashige motar Na zauna, amma saina bar k'ofar abud'e
k'afafuna awaje, banida buk'atar cigaba da kallon kuma, dan haka nabud'e data
nashiga chart kawai ina cika ina batsewa masifa nacin raina, gashi kuma an
hanani amayar da'ita,. sai antayama yaa Marwan harara nakeyi ta gefen ido baima
San inayiba, gaba d'ayama sainaji dama banzo kallon hawanba.
Koda muka bar nan ba gida muka komaba, yawo
yaa Marwan yaytayi damu gidajen dangin babansu, bamune muka dawo gidaba sai
magriba, kowa yayi ti6is da gajiya.
Mun tarar innarmu da mama Rabi'a sunata
shan hirarsu ta zuminci.
Sai kusan 10 suka bar gidan.
★★★★
Washe gari muma agidansu mama Rabu'a muka
yini har innarmu, koda yakema fitarmu mukayi nida Munubiya, Feena, Ayusher,
mukabar su mama agida dasu Aryaan.
Yauma mun zaga gari sosai, dan Ayusher
takira mana wani saurayinta yazo ya kwashemu, yauma munje munga hawan sarki da
la'asar, saidai yau babu Galadima a tawagar, hakan bai dameniba, dan nama manta
da lamarinsa ni.
Kwanaki kusan biyar zuwa 7 munashan
shagalin salla, munsha yawo tamkar bamuda mafad'i mudasu Ayusher, sai Fauziyya
dakan bimu wani lokacin idan basu fitaba da mamarsu suma.
'Yan matan gidanmu kowa sabgar gabansa
yayi, rana d'ayane muka fita gaba d'aya domin gaida danginsu Abbanmu da Innaro
takafa ta tsare akan sai munje wai su Anty Ramla sunyo musu sallamar aure.
Kwanaki 10 cif dagama bikin salla muka
koma makaranta.
Haka rayuwa tacigaba da shud'ayawa,
yayinda 'yan gidanmu keta shirin bikin 'ya'yansu, shiri akeyi babu kama hannun
yaro, kowa burinsa ace 'ya'yan d'akinsa sune Star's, kuma sunfi kowa komai.
Sati uku kacal bikin yarage, an kawo lefe
daga gidan senator halliru, akwatina 24, siyama 12 Zarah 12.
Humm ai ranar munsha kallo Na al'ajabi
wajen mamansu yaa Hameed da momy Hadiza, habaici da gugar zana da burga, kowa
yashashi, har dai abin yak'ure mamansu haleematu da maman Safara'u suka tanka
musu, kafin kice mi gida yagama kacamewa da hayaniya, kowa yana ya6ama kowa
magana, saida suka gama cin zarafin junansu sannan sukayi shiru bisa
tsawatarwar baba k'arami, dayake yana gida a lokacin.
An bar maganarne kawai amma badan ta
k'areba, mudai a 6angarenmu ma innarmu hana kowa fitowa tayi, dayake weekend
ne.
Suma sauran duk an kawo nasu lefan, Aunty
Rahaima, Ramlah, Hauwa'u sai aunty khaleesa, suma dai Alhmdllh, komai sai dai
mak'iyi, duk da basukai nasu siyama ba gaskiya. a wannan karonma dai saida
akayi 'yan gulmace-gulmace a gidanmu, amma basu bari tafito sarariba.
Suma su yaa Hameed aka kai nasu lefan
gidajen matan dazasu aura shida Ya shafi'u da yaa Nasser. suma iyayenmu sunyi
k'ok'ari wajen had'a musu lefen girma, ankai kuma kowa Na sambarka.
Tun bayan gama kai lefe gidanmu yakuma
d'inkewa da k'us-k'us na gutsiri tsomar gidan yawa, kowa yana gulmar kowa akan
aga wace rawa zaka taka, su 5 masu aurar da 'ya'yan.
Mamansu yaa hameed zata aurar da 3, yaa
hameed, aunty khaleesa da Zarah.
Sai maman Haleematu zata aurar da aunty
Hauwa'u.
Sai Momy Hadiza zata aurar da Siyama da
aunty Raihan.
Mama Ruk'ayya kuma zata aurar da yaa
Shafi'u da yaa Naseer.
Maman Safara'u kuma Aunty Ramlah.
Innarmu da maman Fauziyya ne kawai bazasu aurar da kowa ba, dan haka suka
zama 'yan kallo, sai idan mazajensu sun saka su acikin shawarane.............✍🏼
*_Ya Rabbi
ka gafarta iyayenmu😭👏🏻_*
[4/16, 9:53
AM] +234 811 277 0720: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA
KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
_________________________
_Happy
marriage life *SANNA S MATAZU* ALLAH ya sanya alkairi da albarka a wannan aure,
yabaku zaman lafiya na har Abadan da zuria d'ayyiba, bad'i muzo cin rangam💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻😄👌🏻._
__________________________
👉🏻8⃣
.......Hidimar biki ta kankama
gadan-gadan, dan har bak'in nesa sun fara isowa, a ranar alhamis aka gudanar da
sister's and brother's day Wanda mune k'annensu muka shirya musu da yayinmu
maza. da farko a tsakar gidan innaro aka shirya, saboda su Abba bazasu barmu mu
saka kid'aba a gidanmu, gashi mun gayyato k'awayenmu ne, sai abokan su yaa
Nasser danasu Anas. daga baya kuma sai muka canja shawara saboda samun wani
fili damukayi can k'asan layinmu, filin a zagaye yake da katanga an saka gate.
Tunda safe suka fara shirye-shiryen gyara wajen, kasancewar sai 4pm za'a fara,
mudai makaranta muka tafi nida fauziyya da Munubiya, dan munada lectures, amma
sauran duk k'in zuwa sukayi, barema su Siyama amare.
Around 3pm muka dawo gida, yauma kam da
alama wasu bak'in sun iso, dan gidan Yakuma cika da yara da 'Yar hayaniya.
Mun tarrar innarmu tana d'akin abbanmu, dan
haka mukayi wanka muka fara shirin tafiya wajen taron, ko abinci bamu nemaba,
dagani har munubiya mun iya makeup, kasancewar mama Rabi'a tasakamu wajen koya
muda Ayusher lokacin damuka gama secondary, a d'an tsakanin kafin fitowar
results d'inmu, taga damuyi zaman banza gamma muje mukoya wata 'Yar sana'ar,
tunda bamusan inda rayuwa zata kaimuba. Ko gama shiryawa bamuyiba Rahma tashigo
kiranmu inji su Aunty Rahaima, dan mune zamu musu kwalliya.
Mun tarar dasu duk sunyi wanka dama mu suke
jira, zaman musu kwalliyar mukayi, ni nafarama Aunty Hauwa'u, yayinda Munubiya
takema aunty Ramlah.
Kiran Ayusher yashigo wayar munu...., ta
d'aga tana fad'in “kin isone?”.
Bansan mitace mataba daga can, naji tace,
“kizo muna 6angaren su Aunty Ramlah”.
Babu dad'ewa saiga Ayusher itama, ta gaggada
su Aunty's d'in, sannan muma tabamu hannu muka gaggaisa cikina musabaha.
“lah dear nifa harna fidda ran zakizo ALLAH”.
Ayusher tace “kibari kawai, wancan jarabbaben ne yasakani
aiki, tuwo mama tayi da rana, kinsan kuma bayaci shi, shinefa ya tsareni wai
saina masa sakwara, harfa nayi shirin tahowa”.
“uhm ai lamarin yaa marwan saishi,
matarsa dai taga banu wlhy, shi anya ma yata6a budurwa kuwa?”.
Dariya duk muka sanya a d'akin, aunty
Hauwa'u tace, “ai marwan akwai miskilanci wlhy shima, nifa zan iya cewa mun
ta6a magana dashi kuwa?”.
Ayusher tace, “yo aunty ai wannan kowama
haka yake masa, komu muka gaidashi sai yaso yake amsawa, kullum mama cikin masa
fad'a take amma abanza wlhy?”.
Nann dai hira Yakoma kan yaa Marwan da
mutane masu muskilanci irinsa, Munubiya ce mai kareshi, (dama ita suna d'an
d'asawa, nice dai kamar muna ganin hanjin juna dashi danma ina tsoronsa ).
Kasan cewar mu uku ne sai kwalliyar tai
sauri, dan danan muka kammala, nida munubiya mukayi tamu muma, simple makeup
mukayi, amma komai iri d'aya, dama haka mukeyi, komai namu kullmun iri d'ayane.
Munyi k'yau, 6angarenmu muka koma mukayi
shiri cikin blue d'in skirt da pink d'in Riga kamar yanda aka tsara sai veil
shima blue.
Na jujjuya ina kallon kaina a mirror, “kai
jama'a nikam bazan iya fita hakaba gaskiya”.
Ayusher dake kwance tana danna wata
tad'ago ta kalleni, “kai amma kuma wlhy kayan sun miki k'yau, kinganki kuwa?
dan ALLAH ki barsu, kiyi rolling veil naki kawai”.
“kai ba munaya kad'aibafa, nima bazan
iyaba, after dress zan d'ora wlhy”.
Dariya Ayusher tayi, ta tashi zaune tana
ajiye wayar, “waiku miyasa k'auyawane sister's, naga a ke6antaccen waje
za'ayi?”.
“amma kuma dai ai akwai maza kema kin
sani”.
“to alaranmiya, Ku saka, amma kafin Ku
saka d'in nidai kuzo miyi hotuna”.
Gaskiya koni nasan munyi k'yau,
kasancewar mud'in fararene, kalolin duk sai suka kar6i jikinmu blue & pink.
Wanda bai saniba saiya ce mu 'yan uku ne har Ayusher, dan muna matuk'ar kama da
juna, sai dai Ayusher tafimu haske da d'an jiki.
Sai da mukad'anyi hotuna sannan muka
fito. Innarmu tace kunyi k'yau, amma dan ALLAH kar inji wani yayi abinda za'ace
gashi-gashi, Ku kama kanku da mutuncinku kunga dai acikin anguwane, idon kowa
akanku yake”.
Mukace to innarmu insha ALLAH. mun fita
tana binmu da addu'a.
A k'afa muka taka har wajen taron, tunkan
mu k'arasa muke jiyo tashin kid'a. wajen dank'am yake da 'yanmata da samari,
k'awayen amare da namu muma, sai 'yan uwa kuma da abokan su yaa Nasser, dama
shi ya Hameed bai gayyaci kowaba, yace ya bar mana mu k'anne (shidama ba auren
farko bane).
Tunda muka shigo akai mana caa da idanu,
wasu tsantsar kamarmu ce tajawo hankalinsu kanmu, wasukuma burgesu mukayi, wasu
kuma gulmarmu sukeyi da zaginmu, to dama shi taro ya gaji hakan, ballemu da ake
ganinmu k'ask'antattu agidanmu, kamar kowama yafimu komai.
Amare suma duk sunyi k'yau cikin tasu
shigar ta Riga da wando pink gaba d'aya, sai suka d'aure k'ugunsu da blue d'in
belt, suka d'aura jacket blue.
Snacks ne kawai akad'anci a wajen da
drinks, sai pictures da'aka d'auka da video, 'yan mata sunata casar rawarsu da
samari, mudai muna daga gefe zaune muna shan kallo. mun rarraba gifts d'in
damuka tanada, bawani Abu bane masu tsada. silifas d'in wankane sai brush,
MacLean, soson wanka da sabulu d'ad'd'aya aciki, gifts d'in nan mun shiryashine
kawai dan tsokana dama. gabda magriba taro yatashi lfy, kowa ya kama gabansa.
muma gida muka koma.
★★★★★
Washe garima saida mukaje makaranta, sai
dai 11:30 muka fito lecture, ALLAH ya taimakemu muka samu taxi da wuri.
Sanda muka dawo har 'yan jere sun dawo,
kowa dangin mamarsa sukaje jerensa, shiyyasa mukaji tsitt babu gutsiri tsoma.
Muna dawowa ko wanka bamu tsaya yiba
mukaci abinci muka tafi shagon auntynmu data koyar damu makeup domin yin
k'unshi da saloons.
Cikin farin ciki ta tarbemu, dan mun rabu
da ita cikin mutunci bayan mun iya aiki, Aunty salamah batada damuwa, inkaga
tana maka fad'a to baka fahimtar abinda take koyar dakai ne, kwazon damuka nuna
alokacin yasa takeji damu over. Tana kiranmu 'yan ukun ta.
K'unshi aka mana mai k'yau da gyaran
kai, (dan d'aurema k'arya gindi irinnan aunty salamah harda mana gyaran jiki😊, wai tanaso muma musamo mazajen aure🙈).
Kowa ya gammu yasan munyi k'yau sosai.
Amakare mukaje gida, dan mun tarar amare
nata jiranmu mu musu kwalliya, 'yan gidanmu harsun fara k'ananun magana, wai
wulak'ancine yasa muka fita ai, kuma muna kallon lokaci yana k'urewa mukak'i
dawowa. hakan da innarmu taji yasata kiranmu tana mana fad'a, hak'uri muka bata
dacewa gamunan a hanya.
Masifa mukaitayi nida Ayusher, munubiya na
bamu hak'uri, wlhy badan innarmu ba da bazanyi kwalliyar nanba yau.
Babu zancen mu huta muka hau musu
kwalliyar. aikam ranar k'in fita wajen kamun nayi da akayi a tsakar gidanmu,
kwanciyata nayi, innarmu taitamin fad'a kuwa.😕
Washe garin asabar d'aurin aure, dakam
gidanmu yacika tab, 6angarenmu dai da sauk'in mutane, sai mama Rabi'a kawai da
matan abokan Abbanmu.
K'arfe goma aka d'auro auren yaa Hameed da
amaryarsa, sai yaa Nasser shima da yaa Shafi'u.
Na 'yan matan kuwa sai k'arfe 1:30pm.
K'ofar gidanmu yacika dank'am da jama'a ta ko'ina, 'yan siyasa tawagar senator
halliru da abokan su Sa'eed, hakama mijin aunty Rahaima d'an siyasane, dan haka
harda governor a mahalarta taron d'aurin auren.
Har aka gama d'aura aurarrakin ina
d'akinmu kwance, ko wanka banyiba, garama munubiya da Feena da Ayusher su duk
sunyi, amma suna d'akin basu fitaba, sai balkisu k'awarmu da itama tazo mana.
Hira suketayi, nikam dai ina kwance kaina
namin ciwo.
Gidanmu babu masaka tsinke, tako ina
jama'ane, amare ansha k'yau, su siyama baki har k'anne an auri 'ya'yan sanata,
hakama iyayensu sai burga sukeyi, ranar munga gasar dressing wajen iyayenmu
mata kam, kowacce so take ace itace uwar amarya datafi kowa fita.
Innarmu kam babu ruwanta, shiga d'aya tayi
ta atanfar da Abbanmu yamusu Na fitar biki, sai da yamma ta canja da less.
Aranar kowaccensu tayi yini. Baza'a
kai amareba sai washe gari, saboda anason agudanar da dinner waje d'aya, amma
an kawo nasu yaa Shafi'u sudai.
Yau d'inma dai mune muka musu kwalliyar
su dukansu, kafin k'arfe 8pm afara kwasar mutane zuwa wajen daza'a gudanar da
dinner d'in.
Gurin yayi k'yau sosai, yayinda aka
shirya ma amare da anguna hi table.
Sai dai kuma wata sabuwa, ba duk angunan
bane suka halarci wajen dinner d'in, nan fa aka fara 'yan gulmace-gulmace
tsakanin dangin iyayenmu mata, tuni labari harya kai kunnuwan iyayenmu mata
dasuke zaune a gida.
Amaren da babu angunansu sunsha kuka,
wad'anda kuma dama sukasan angunan nasu ustazaine bazasu zoba basu damuba.
Haka dai aka gudanar da dinner d'in
zukatan wasu babu dad'i, tunkan agama ma wasu sukaita tafiya gida abinsu.
K'arfe 11 aka tashi.
A wajen dinner kam nayo saurayi mai suna
Fu'aad, hakama munubiya da Ayusher dun sunyi, Fu'aad k'yak'yk'yawa dashi masha
ALLAH, duk da dai bawani sake masa nayiba ya burgeni.
Su Ayusher sunata tsokanata, nidai ban
kula suba.
Washe gari da safe kuwa saida abin yazama
fad'a, wai ankama wasu suna gulma akan rashin zuwan sauran anguna, kuma dangin
momy Hadiza ne, aikam sosai aka zuba rikici, har saida abbanmu ya tsawatar.
Aranar aka shirya kai amare, dole sai dai
a rarrabu, tun la'asar aka fara kawo motoci, baba k'aramine yabada shawarar
ahad'a tafiyar kawai gaba d'aya, su aunty Hauwa'u suma su siyama rakiya, sannan
suma haka.
Haka kuwa yayima wasu iyayenmu mata dad'i,
dan kobabu komai saji yanda gidan kowacce ya kasance.
mun fara kai su Siyama da Zarah, wad'anda
babu alamun kuka a idanunsu, gidajensu jere da juna, sunyi k'yau masha ALLAH,
kayan gado dai duksu Abba sukayi, kuma kud'insu d'aya, saidai kowa da za6insa,
kayan kitchen ne kowa uwarsa tayi da sauran tarkace, ananne kowa ya ware ido
dan aga kwazon uwar mutum, nidai agareni babu makusa, gidansu Zarah duk yayi.
Mun ajiyesu tareda k'awayensu, mukuma muka
tafi kai sauran.
Daga Nan sai gidan aunty Rahaima, itama
masha ALLAHU wlhy, saidai mak'iyi, gidanta yayi k'yau, sai dai tanada kishiya.
Saikuma gidan aunty khaleesa, itama dai d'in
zamm zamm wlhy, daga nan sai aunty Ramlah, wlhy itama yayi d'as, itama tanada
kishiya. Aunty Hauwa'u ce k'arshe dan itace babba, itama gidanta yayi k'yau
sosai.
Nidai aganina babu wadda mahaifiyarta
batayi k'ok'ari ba wlhy, amma hakan bai hana sauran gumtso gulmarmakiba aka
taho da ita.
Kasancewar duk babu Inda muka zauna aka
taho gida da wuri, harzamu wuce Fu'aad daya d'akkomu yace bari yashiga Birnin
gayu plaza damu.
Nace a'a muwuce gida kawai, kar aga kowa
yadawo mu bandamu, gashi lokacin har 8:30pm ya wuce.
Ayusher ce tace indai bazamu dad'eba
ashiga, saimuce muna gidajen su siyama mu, mun zauna jiran anguna.
Kamar dai nace a'a amma nayi shiru,
saboda naji munubiya da feena suma sun bada goyon bayan mu Shiga, sannan Fu'aad
yace bazamu dad'eba.
Ya kalleni murya k'asa-k'asa yace, “ginbiya
bakice komaiba?”.
Murya a sanyaye nace, “indai bazamu wuce
1hour ba muje”.
“insha ALLAHU my luv bazama mu kaiba”.
A kasalance Na d'aga masa kai saboda
agajiye make ti6is.
Haka yashiga wajen nidai zuciyata Na dukan
uku-uku daban San Na miyeba.
Munshiga cikin plaza d'in, bansan
takamaimai miyasa Fu'aad yace mushigo wajenba, tunda dai bawani abin ci ake
saidawa a wajenba.
Mun shiga 6angaren kayan kwalliya, yace
kowa yaza6i abinda yakeso.
Nidai nace masa a'a mun Gode.
6ata fuska yayi yana hararata, ya maida
kallonsa gasu munubiya dake tsaye “please dan ALLAH karku biye mata, kuje Ku
d'auka”.
Badan suma sunasoba suka amsa da to.
Ya kalleni yana fad'in “mujeto ni na
d'ebar miki”. bance masa komaiba nabi bayansa ganin kamar yayi fushi, wayarsa
aka kira, ya zaro daga aljihu, saida yad'an saci kallona yaga hankalina baya
kansa sannan ya d'aga, murya k'asa-k'asa tamkar mai gulma yace, “nagama
aikina”.
Dawowa yayi wajena bayan ya katse
wayar, da kansa yake za6ar mini duk abinda yadace.
Su munubiya ma sunacan suna d'auka, kamar
ance munubiya ta bar wajen saita zagaya tabaya, a dai-dai wannan lokacinne
shikuma yake tunkarowa shida wasu matasan samari guda biyu, da alama yana
zagayene kowani abun daban. tafiya yake cikeda nutsuwa da sarauta, sai sautin
takunsa dakakeji, tunkan su iso gareta k'amshin turarensa ya iso.
Waige-waige munubiya tafara, tanason tuno
mai wannan k'amshin. bata ankaraba saijinta tayi tatafi suuuu santsi ya
kwasheta.
Shi mutumne mai yawan tausayi da taimako,
da sauri yayo kanta kafin taje k'asan, Dan yasan fad'uwarta a wajen babban
had'arine, yakai hannu zai rik'eta itakuma ALLAH yabata ikon dafe wasu tarin
baskets dake wajen. Cikin runtse ido da sauke ajiyar zuciya ta furta
“Alhmdllh”.
Janyewa yayi daga rankwatowar dayay kanta
tamkar zai rungumeta, batareda yace uffanba yafar wajen.
Muduka akan idonmu komai ya faru, wad'anda
suke tare dashine sukaima munubiya sannu, mukuma muka k'araso da sauri gareta
muna tanbayarta babudai wata damuwa ko?.
“babu komai Alhmdllh”. ‘tafad'a tana
gyara tsayuwarta’.
Nace, “kunga kuzo mu tafi hakanan, wlhy
inajin tsoron agane bama gidansu siyama”.
Duk
suka amsa da gsky mu tafi, da k'yar muka yarda mukaje wajen biyan kud'in.
yabiya sannan muka tafi.
ALLAH ya taimakemu ba'a mana fad'aba.
Duk cikinmu babu Wanda yakuma maida hankali
akan abinda yafaru a birnin gayu plaza, saidai abin yakasa barin raina, kamar
zuciyata tana cikin fargaba, amma bansan ta miyeba, ita kanta Munubiya wani
sukuku nake ganinta, bandai tanbayeta ba Na share.
Washe gari Monday, muka tashi da shirin
makaranta, saida muka gama gyara gidan tsaf sannan muka tafi harsu Ayusher,
dayake lectures d'inmu Na yau sai 1:30pm ne. yauma sauran 'yan uwanmu bakowa
yaje school d'inba ma har fauziyya.
Tun muna tsaye abakin titi muna jiran taxi
naga wasu tsirarun mutane nabinmu da kallo. ban kawo komai arainaba muka samu
taxi.
Driver ma yana tuk'i yana kallonmu ta madubi, sainaga kuma ya kalli
takardar dake saman cinyarsa. d'an fara tsarguwa nayi, amma saina dake ina
zaton irin dirobobin nanne masu shegen kallon tsiya.
Da muka sauka cikin makaranta ma bata
sauya zaniba, kallonmu akeyi har ana nunamu, wasu da jaridu a hannu wasu kuma
waya.
Munubiya tace, “Manaya bakiga abinda ke
faruwaba tundaga fitowarmu gida zuwa nan ne?”.
“nagani wlhy Munubiya, bansan miyakawo
wannan kallon k'urilla d'inba, dama bakiga kallon da direban can yake manaba ni
da ke harya saukemu, ko sanda muke sallama dasu Ayusher idonsa Na kanmu kyam
kuma yana kallon wata jarida dake cinyarsa”.
Muduka kallon jikin junanmu mukeyi,
babu wanda shigarsa tazama aibu acikinmu, sannan bama tareda wani abin kallo,
Hannun juna muka kama muka cigaba da tafiya
cikin tsantseni da nazartar kallonda 'yan uwanmu d'alibai suke mana.
Tunda muka shigo cikin class sai duk aka
zubo mana idanu, kuma anata k'us-k'us. yanzu kam hankalinmu yatashi sosai, wai
mike faruwane? saikace yau mutane suka fara ganinmu? shin yaune muka fara
shigowa makaranta?.
Bamu da mai bamu amsar tanbayarmu, muka
nufi Bilkisu dake zaune itama tazubo mana idanu, ga jarida agabanta, kamar
yanda muka gani wajen sauran 'yan department d'inmu, wasu narik'e da jaridu
wasu wayoyi, sunyi group group kuma suna k'us-k'us.
Da sauri Na k'arasa zan d'auki jaridar
gaban Bilkisu amma saitayi saurin d'aukewa............✍🏼
Babbar
magana, shin mike faruwane? kallonmi jama'a kema su Munubiya? Sannan mi ake
kallo a jikin jaridar da wayoyin kuma?🤦🏻♀.
Nasan masu
karatu ma wannan amsar suke son sani🤔
*_ALLAH ka
gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
No comments