RAINA KAMA (BOOK 1) 5&6
👉🏻5⃣
...........Wajen 4pm muka fito daga cikin
makaranta, mu 6 ne yanzu, sa6anin d'azu damukazo mu hud'u, bayan tahowarmu
Safara'u da Haleematu suka taho suma, duk da mun rigasu gama
lectures sai muka
jirasu suka fito muka rankayo tare domin tafiya gida, bamu samu school bos ba,
dan haka muka da6o sayyadarmu har zuwa babban gate, muna tsaitsaye abakin titi,
tareda wasu daga cikin tsirarun d'alibai irinmu, tundaga nesa muka hango
tahowar motocin da uban gudu, saika d'auka sukad'aine akan titin saboda gudun
dasuke tsulawa tamkar zasu tashi sama. duk baya muka matsa, dan tabbas
wad'annan suka sameka babu abinda zai hanasu takeka su wuce batareda sun
damuba.
Tamkar wucewar iska haka suka dinga
gittamu, jikake shuuuu!! shuuu!! shuuu!!.
Furicin wani mayshin saurayi dake jingine
jikin motarsa yazo d'aukar wasu 'yan mata biyu dake gefenmu 'yan matan sunada jin kan masifa, ko'a
makarantar bakowa sukema maganaba, department d'inmu d'aya dasu amma ko kallo
basu isheniba, dan ko sallama bata ta6a had'ani dasuba..
Saurayin yabi motocin da kallo yana
fad'in “tab ashe *_GALADIMA!_* yashigo gari kenan?”.
“Da gaske yaa Usman?”. ‘d'aya acikin 'yan
Matan tafad'a cikin matuk'ar zumud'i’.
Yace, “da gaske mana baby, baga motocinsa
kuna ganin sun wuceba”.
Dan danan suka shiga murna, kai kace an
musu albishir da aljanna ne.
Baki na ta6e inajan k'aramin tsaki.
Fiddausi tace, “to waye shi galadima d'in?”.
“oho musu”, ‘cewar Munubiya’.
Budurwar dake tsaye d'ayan gefenmu itada
saurayinta suna jiran abin hawa suma tace, “Galadima d'an Sarki kenan, *Yarima
Sameer!”*.
“humm lallai kuce manyane, shiyyasa
suke gudun da kosunbi takan talaka babu abinda za'ayi”. ‘cikeda 6acin rai nake
maganar’.
Dariya su siyama sukayi suna fad'in
“toke ina ruwanki?, k'asarfa tasuce, sai yanda sukayi da ita, tsakaninmu dasu
saidai mu hangesu cikin mota ko ranar hawan salla”.
Dogon tsaki nakuma ja tareda kauda kaina
daga garesu na maida hankalina wajen tare wata taxi dake gabatomu.
A motama firar dasu Haleematu
sukaitayi kenan, ta Galadima ne ko
uwarmi ne ma Na manta. nidai uffan ban kuma tofawaba, hasalima haushi hirar
tasu takoma bani, dan mai taxi d'in yasaki baki sai wani basu labarin Galadima
d'in yakeyi dakuma kwarzan tashi, earphone na jayo a cikin lady's bag d'ina na
manna a kunne danma nabar jinsu gaba d'aya.
Saida muka iso gida sannan Fauziyya dake
kusa dani ta zungureni, d'agowa nayi Na kalleta sainaga duk sun fice, bance
komaiba nafito nima.
Mun iske innarmu bata nan, saisu Aiyaan
kawai zaune a falo suna kallo, shigowarmu yasasu tasowa da gudu suna mana
oyoyo, muma mun taryesu da murnarmu, Munubiya tace, “Aryaan miyasa baku cire
Uniform ba kukayi wanka?”.
“yo aunty mun dawo munga Innarmu bata
nanane”.
Nace “innarmu bata nan? to ina taje?”.
“muma bamu saniba aunty, munje kuma
kitchen bamuga abinci ba, kuma yunwa mukeji”.
Munubiya tace, “ya salam, kujira ina
zuwa”.
Fita tayi, babu dad'ewa sai gata tadawo
cikin damuwa, ina cirema su Aryaan Uniform, Na kalleta ina fad'in “mike faruwa
Munu...? Ina abincinne?”.
Kwallar idonta ta share, ta zauna bisa
kujera sannan tace, “naje mama tace wai innarmu ta d'auka abinci tatafi dashi
hospital, dan haka shine rabonmu”.
Raina a 6ace na mik'e zan fita, da sauri
munubiya ta ruk'oni, “please Munaya, kibarta kawai, yakamata mu kira innarmu
muji waye a hospital? Inaga wannan yafi komai muhimmanci nake gani akan abinda
mamar tamana”.
“Haba Munubiya, wannan wane irin rashin
mutunci ne, wai mi Matan gidannan suke tak'ama dashine? Idan suna tak'ama da
Ubanninsu muma ai nan gidan Ubanmune ko, yanzu ace yarannan kamar su Aryaan su
dawo school tun 3 amma ahanasu abinci, wannan wane irin zaluncine? Kisakeni
kawai naje naci kutumar uban matarnan munubiya, wlhy sai dai yau Abba yace
nabar masa gidansa”.
“A'a munaya, duk hakama bata tasoba,
idan hankali ya6ata hankali ke nemosa, bai kamata mutaru muzama d'ayaba mu da
su. bara kawai naje kicin d'in Na dafa mana wani abun mai sauk'i, kiyi hak'uri
dan ALLAH, kinga innarmu bazataji dad'iba idan tatarar da faruwar hakan”.
Badan raina yaso ba Na hak'ura, saman
kujera nakoma Na zauna ina huci, nikad'ai nasan minakeji a zuciyata.
Munubiya tafita dan nema mana abinda zamuci,
nikuma Na d'auki waya domin Kiran innarmu naji abinda tajeyi asibiti.
Harta katse bata d'agaba, nakuma kira
akaro Na biyu sannan ta d'auka, gaisheta nayi da tambayar mitajeyi asibiti?.
Daga can tace min Nafisar mama Rabi'a Ce
jikinta ya motsa yanzu hakama jini ake buk'ata amma an Gaza samu, gashi yaa
marwan dayakan bata jinin baya nan yayi tafiya shida Abbansu.
Hankalina a tashe nace “innarmu ganinan
zuwa yanzunnan insha ALLAH, kuna general hospital ne?”.
“eh muna nan”.
“ok insha ALLAHU ganina zuwa”.
'Dakinmu nashiga da Sauri nad'an watsa
ruwa a tsaitsaye saboda naji dad'in jikina, komai ban tsaya shafawaba Na zira
doguwar Riga jallabiya Na fice da
hanzari. A k'ofar fita falo naci karo da munubiya d'auke da babban faranti
tazubo spaghetti tanata turiri.
namatsa baya da Sauri INA fad'in sorry,
munubiya bara naje asibitin wajensu innarmu, wai jikin feena ne ya motsa kuma
ana buk'atar jini, gashi yaa marwan sunyi tafiya da abba”. Munubiya tace, “toko Na juye mana
abincin a kula mu tafi gaba d'aya?”.
Nace, “a'a munu... Ki zauna dasu Aiyaan
bara naje ni kad'ai, baikamata mubar wajen ba kowaba”.
“to shikenan, yanda akayi ki ta6oni
awaya, amma in kunkai dare zakuganmu muma, abincinfa?”.
“humm munu bar abincinnan, banida wata
nutsuwar cinsa, saina dawo”.
Ban jira amsarta ba nafice. ALLAH ya
taimakeni INA fita nasamu napep. Mintuna kad'an muka isa hospital d'in,
kud'insa na biyashi nashige da hanzari ina k'ok'arin kiran innarmu.
Babu dad'ewa kuwa ta d'aga, nace mata gani
acikin asibitin. Kwatance tamin na inda aka kwantar dasu 6angaren masu sikila.
A rikice na iske innarmu da mama Rabi'a,
saboda jikin feena ya motsa mata sosai a wannan karon.
Nace, “mama yanzu mi ake cikine?”.
“Rashin jininne matsala yanzu Munaya,
sunce kuma anemoshi da gaggawa, to dama can jinin Fadeel baya yimata shiyyasama
ko gwadasa ba ayiba, Marwan dake bata kuma sunyi tafiya da abbansu”.
“mama ina zuwa, bani takardar da suka
baku”.
Mik'omin tayi nafita da saurina. dukna
rikice inata kai kawo dan ganin ansami jinin, amma har magriba ta rufa ba a
samuba, saboda jinin feena yanada wuyar samu, ana cikin kiraye-kirayen sallar
isha'i saiga Ayusher ta iso itama, dama an barta a gidane saboda babu kowa, to
takasa hak'uri tabiyo sahu, da ita muka cigaba da shiga da fita, saida aka fito
sallar isha'i ALLAH yasa aka dace da samun leda 1, saura 1, dama biyu suke
buk'ata. ana cikin d'aura mata saiga Munubiya ita dasu Aryaan da kulolin
abinci.
Koda aka gama sakawa sai muka koma Neman
d'ayar ledar data rage, yanzu harda munubiya muke tare.
Muna a lab d'inne muna shawarar ko a
d'iba namu jinin idan zaiyi babu damuwa. Takun takalman damuka jiyo yasamu
juyawa harda likitan da maganarsa takatse bisa k'ok'arin bamu amsa dayakeyi.
wani ni'imtaccen k'amshine ya iso hancinanmu tunkan mamallakin turarenma yakai
ga isowa inda muke. d'auke kaina nayi na maida ga mai d'ibar jinin.
Likitan naga yafara gyara kujera yana
fad'in “dama yalla6ai ya shigo gari yau? Ni nama manta yaune ranar dayake bada
jini”.
Bai samu mai bashi amsaba a cikinmu har
tawagar Wanda yakira yalla6ai suka iso wajen.
Munubiya da Ayusher suka matsa gefe
saboda wata uwar tsawa da masu take masa baya suka daka mana, nikam koma
motsawa banyiba bare nasan ALLAH yayi ruwansu awajen, saima baki dana ta6e na
d'auke kaina daga saitin dasuke.
Bulala d'aya daga masu jajayen rigunan
ya d'aga da nufin zubamun.
“Wanda suke kira Yalla6ai dake zaune a
kujerar da doctor ya ajiye masa ya d'agamasa hannu da Sauri, alamar karya
dakeni”.
Cikeda girmamawa yace, “angama zaki
s.........”.
Hannu Yakuma d'aga masa alamar baya
buk'atar kirarin.
Baki nakuma ta6ewa sannan na ra6a ta gefensu
nafice, banga fuskar Yalla6ai d'in nasuba, saboda ya juyamin bayane ni, sananan
shima tunda yashigo bai kalli kowaba a lab d'in, yanata aikin danna wayarsa,
kuma baiyi magana ba, ko doctor da Norse's d'in da suka gaidashi hannu kawai ya
d'aga musu, kuma ko d'agowa baiyiba yanata aikin danna waya kai kace zai danno
hanyar zuwa aljannane aciki.
Waje na dawo nayi zamana ina cigaba da
game a waya, su Munubuya dai suna cikin, bansan uwarmi suka tsaya yiba awajen.
Kusan mintuna 40 saigasu sunfito, takun
takalmansu kawai naji, amma ban d'agoba, sai k'amshin turarensa daya cika
illahirin wajen, saikuma gaisuwar da mutane keta faman zubewa sunayi masa, ko
sau d'aya banji ya amsaba.
Tsaki naja inamaijin haushin wannan
mutumin, to wayema shine? dayakema mutane wannan jinkan., motsooww aikin banza
kawai.
Tabbas yaji tsakin da akayi, hakanne
yasakashi d'ago k'yawawan idanunsa yakai duba saitin Inda yajiyo tsakin, akan
*munaya* dake zaune bisa kujerun dake Jere awajen ya sauke su, sai dai baya
ganin fuskanta sosai, saboda ta duk'ar da kai tana danna waya, kuma gyalen
jallabiyarta yarufe mata Rabin fuska,
ita kad'aice zatayi wani motsi awajen suji, dan tafi kusanci da Inda
suke tsaye.
Janye idanunsa yayi kawai daga gareta,
yay saurin d'agama bayin dake k'ok'arin tafowa gareni hannu. Cikin Wata tattausar murya mai aji dake cike da
k'asaitar masu isa najiyo yana fad'in “Bayta kawai”.
Cikeda girmamawa bawan yace, “ya shugaba
tsaki tayi fa”.
Shiru yay kamar bazai tankaba, saikuma
najiyo yace, “kasan dawa take?”.
Bawan girgiza kai yayi alamar a'a.
Bai sake cewa komaiba yay gaba suka bishi a
baya.
'Dago ido nai nabi bayansu da kallo,
sainaga sun nufi 6angaren mata masu haihuwa.
janye idona nayi ina fad'in “kadaiji dashi
Malam, kana fama da Girman kai kamar wani Sarki? Abinma dariya ko (R) bai
iyaba, wai bayta”.
Dai dai nan su Ayusher suka iso cikeda
farinci, hannunsu d'auke da ledar jinin
Cikeda jin
haushi nace, “wai uwarmi kuka tsaya yi acikin lab d'inne?”.
“Uwarmu ta gode”. ‘ cewar Ayusher’.
Munubiya kuma tace, “zaman namu aiko yayi
amfani, tunda gashi mun samo sauran jinin ko”.
Na kallesu da mamaki, “ina kuka samo jinin
kuma to?”.
“Galadima ya bayar”.
Cikin ta6e baki nace, “miye kuma Galadima?
A inama kukaga wani Galadima kome ma kukace?”.
“wanda yashigo muna cikifa, ai Galadima
ne (Yareema Sameer d'an sarki)”.
Ido na waro waje, “wai kuna nufin wannan
mai shegen girman kai d'in dama shine Galadiman? kenan munu.... shine yawucemu
d'azu munfito makaranta?”.
“kwarai kuwa sweetheart shine, kuma wlhy
bashida Girman kai kamar yanda kike zato ko Sis.. Ayusher? ”.
“Wlhy kuwa hakane Munu..., ashe duk
k'arshen ko wane wata saiyazo asibitinan yabada jininsa gamasu buk'ata, gashi
jinin nasa mai irin wahalar samu d'inanne irinna feena, kai mutuminnan yayi
wlhy, Sarauta ba karya baceba, danyau naga tsantsar sarauta da mulki da
k'asaita ajikin Galadima, yanzu haka zai zagayane yaduba marasa lafiya”.
Harara na ballama Ayusher daketa zabga
surutu uwa aku, na warce jinin daga hannun munubiya ina fad'in “idan kun gama
shirmen kwa taho”.
Kallo suka bini dashi, Ayusher tace,
“Anya yarinyarnan batada aljanu?, ke kowama bai mikiba?, yanzu nan duk had'uwar
Galadima Munaya tana nufin bai burgeta ba kenan?”.
Dariya Munubiya tayi, sis... Ayusher har
yanzu baki gama fahimtar Munaya ba na lura, kyagama abinda yafi haka indai daga
wajentane. Yanzu hakama tunda kikaji tace haka ko sau d'aya bata kalleshiba
wlhy bare tasanma kalarsa. kinga muje kinji.
“humm aiko wlhy inabata kalleshiba anyi
babu ita kuwa, ruwa ta shata kuma, yo kobabu komai aina bada koda labarine nace
nata6a ganinsa ido da ido ko”. ‘cewar Ayusher’.
Dariya kawai Munubiya tayi, taja hannunta
suka tafi.
Sanda suka iso harma an fara k'ok'arin
sakama feena jinin, dama wancan yak'are.
Duk muna zaune a k'ofar d'akin bisa
kujerun wajen, Aryaan da Aiyaan duk suna jikin mama Rabi'a barci ya d'aukesu,
fadeel na kusada innarmu yanacin abincin dasu Munubiya suka kawo, zama nayi
kusada fadeel d'in na saka hannu nad'au cokalin dayake cin abincin ina fad'in
bro... nimafa yunwarnan nakeji, rabona da abinci tun kusan 1 danaci a kafteriya
na makaranta”.
Kallona yayi yana cewa “sannu da k'ok'ari
sis...., shiyyasa gakinan tsula guda bak'ya gaba bakya baya keda munu....”.
Cokalin nakai zan kwala masa a kai ya
kauce yana dariya, nima dariyar nayi na d'auki kular abincin na k'ara mana.
Muna cikin ci Ayusher ma tamatso tace
zataci, munci mun k'oshi sannan muka gyara wajen, mama da innarmu ma sukaci,
dan zuwa yanzu duk mun sami 'Yar nutsuwa.
Kusan 10pm saiga Abbanmu shida baba
k'arami, duk muka gaidasu suka tambayi mai jiki, innarmu da mama Rabi'a suka
amasa musu da sauk'i.
Har
d'akin suka shiga, suka duba feena daketa barcinta, sannan sukace muzo mu tafi
gida, za'a bar innarmu da mama Rabi'a su kwana.
Saida safe mukai musu muka fito, Fadeel ya
d'akko Aryaan, baba k'arami ya d'akko Aiyaan.
Saida muka fara sauke Ayusher da Fadeel
gida sannan mukuma muka wuce.
Mun tarar gidan tsitt alamun duk anyi
barci, saidai masu wayar dare da samari irinsu aunty Ramla, saikuma masu
charts.
Abbanmu da baba k'arami suka d'auki su
Aiyaan, har d'akinsu suka kaisu sannan suka fita.
Muma shirin barci mukayi muka kwanta cikeda
kewar Innarmu, muna kwanciya muka kirasu da k'arajin mai jikin sannan muka tafi
duniyar barci muma, dagani har Munubiya babu mai wani saurayin da zamu 6ata
lokaci wajen yin hirar dare...............✍🏼
Kumuje zuwa
my guys🤩👎🏻
Gobe idan
ALLAH ya kaimu baza kujiniba, inada wani d'an uziri, sai Monday idan ALLAH ya
kaimu kuma.
https://chat.whatsapp.com/K1qwmMusX7ILDLATGSvfHJ
*_RAINA
KAMA........ FANS CLUB_*
_Duk Wanda
yasan yana karanta wannan buk d'in ya garzaya yanemi link Na RAINA KAMA FANS
CLUB, a wannan gidan kawai zan dinga posting a halin yanzun, awannan karon
bazan turama kowa buk ta PC ba, narigada nayi rantsuwa. Amma annan zaka iya
samu da faro, sannan inhar ba'a tattaunawa akan novel d'in zanyi waje da mutum
babu ruwana, kuma kar a turomin kowanne novels acikinsa Dan ALLAH, inba hakaba
zan fidda mutum ko Yaya nake dashi🙅🏻,
nabud'e gidanne saboda anan kawai zan dinga posting yanzu, sai wasu groups
dabasu wuce 3 ba._
Ina fata zaku bani had'in kai please, inba
hakaba ALLAH zai koma Na kud'ine saboda tsaro ba tsoroba😎🤣
https://2gnblog.blogspot.com/
One luv🥰🥰
*_ALLAH ka
gafartama iyayenmu👏🏻😭_*
[4/16, 9:53
AM] +234 811 277 0720: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA
KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
_____________
*_ASSALAMU
ALAIKUM_*
_Jiya da daddare akaita kirana mutane Na
tanbayata Yaya jiki, tun ban fahimci maganarba hardai nafara tsarguwa nayi
tambaya. Dan sai kira kan kira ake jeramin, wata take sanar dani taga wani
posting ne yana yawo wai za'amin CS. babu shiri nabud'e data naga mike faruwa,
group d'in farko dana bud'e sainaci karo da wannan posting d'in mutane nata
comments, nabud'e nabiyu ma hakan dai._
*_Assalamualaikum Alaikum,Dan Allah kuyiwa
billyn Abdul(ma rubuciyan RAINA KAMA. Adua'baby ya mutu a cikin ta zaa cire
Mata Shi yanzu_*
_sai daga
baya nakejin Bily galadanci ce batada lfyar, amma wata ta maida zancen haka
saboda sunan namu yazo d'aya, to ALLAH yabata lfy itama._
_sannan ina shawartar jama'a Dan ALLAH
kuringa nutsuwa wajen tantance Abu kafin Ku yad'ashi, domin wadda tayi wancan
write up d'in ta zaunane ta tsara nata son zuciyar, wadda tayi posting d'in
farko akan ciwon Bily galadanci sunan Bily tasaka ba nawaba, itakuma ta canja
nata tsarin tashiga ya d'awa, ALLAH ya shiryar damu, yakuma bama marasa lfyarmu
lafiya._
*banyi niyar posting ba yau, amma ganin
wancan write up d'in yana cigaba da yad'uwa yasani dole yi Dan na warware muku
zancen.*
______________________________
👉🏻6⃣
.......Bamusan abinda yafaruba, mukaji
'yan gidanmu suna k'ananun magana da safe, wai girkin jiya na dare da mamansu
yaa hameed tayi sai asararsa akayi, girkin yay d'anye yak'i dahuwa, kuma a gas
tayi girkin bare ace iccen yabata matsala, gashi kuma normal gas d'in yake
aiki.
Muna cikin yima su Aiyaan shirin school
muka fara jiyo hayaniya, sai da muka gama musu shirin sannan muka fito,
cirko-cirko muka iske 'yan gidanmu, yayinda mamansu yaa hameed keta zabga
masifa. tana fad'ama abbanmu wai mune muka mata kwari shiyyasa jiya abinci yay mata
d'anye danta hanamu abinci, kuma gashi yanzuma tasaka doya amai tak'i soyuwa.
Ni dariyama taso bani wlhy, wai mune
muka mata kwari, to miye kwarinne ma datake magana a kai? danni bamma
sanshiba.....
Maganar Abbanmu ta katsemin tunanina.
“
'Yan biyuna kuzo nan naji kunji”.
K'arasowa mukayi kusada abbanmu harsu
Aiyaan, ya kallemu cikeda kulawa, “haba 'yan albarka mike faruwa haka?”.
Cikeda rashin fahimta nace, “Abba a
ina?”.
“haba twins d'in Abba, bakuji mi mamanku
take fad'aba? abinci yamata d'anye jiya da yau”.
“amma Abba Dan abinci yayi d'anye kuma sai
ace mune? Kagafa jiya munama asibiti bamuci abincin dareba agida, darana ma
mama hanamu tayi tace innarmu tatafi da kasonmu asibiti, haka muka dawo muka
iske su Aryaan sunajin yunwa, sai Munubiya Ce tamana girki, kuma tayi takai
mana wani asibitin, ni wlhy Abba bammasan wani kwari dasuke maganaba akai,
wannan ai canfine, tunkuma zamanin da aka barsa”.
“canfin uwarki, kujimin munafukar
yarinya, inbakune kukayi muguntarba uwarwaye yayi, to wlhy ahir d'inku, ba 'yan
biyu ba ko 'yan gomane ni ubanku zanci a gidannan.......”
Afusace Abba yace, “to ai gani, saikizo
kici ko, ai gaskiyama yarinyarnan tafad'a, wannan canfine kawai, dan abinci
yayi d'anye saikuma a fassarashi dawani Abu daban, haba Dan ALLAH, saikace wata
mara ilimin addini? Karna sake jin wannan maganar, inba hakaba rankowa zai
6acine a gidannan”.
Yana gama fad'a yabar wajen. muma ganin
haka muka tasa su Aiyaan gaba muka koma 6angarenmu. duk da nakasa fassara mi
mama ke fad'i hakan yamun dad'i, koba komai dai ai ALLAH yamana sakayya da
hanamu abinci datayi muda wad'anan k'ananun yaran da basu da alhakin kowa.
Yanzuma munubiya Ce ta dafo mana
indomi mukaci, sanan ta zubama su Aiyaan a kulolinsu Na makaranta, suna tafiya
muma mukayi shirin tafiya School.
Bamu tsaya jiran sauranba mukayi gaba
saboda zamu biya ta asibiti, kuma munsan acikinsu babu mai binmu, harmun fita
saiga Fauziyya tabiyomu, itama zataje taduba feena d'in.
Alhmdllh munma tarar an sallamesu sunata
shirin tafiya gida, mukaima feena sannu, ta amsa tana fara'a da tambayarmu ya
makaranta?. mukace gatanan zamu tafi.
Bamufi mintuna 30 ba muka fito, Fadeel ya
d'aukesu, mukuma muka wuce school.
A mota Munubiya take bama Fauziyya
labarin ganin Galadima damukayi jiya a asibiti, ko sau d'aya ban saka musu
bakiba har muka sauka.
★★★★★
A wannan karon har mamansu yaa hameed tagama
girkinta Na kwana biyu asarar abinci akaitayi, Dan kullum d'anye yake mata.
hakan yasa taita sakin habaici agidan itada muk'arrabanta irinsu momy hadiza,.
Maman Fauziyya ta sanar ma innarmu komai
tun randa taje duba feena agidan mama Rabi'a, Dan haka Innarmu tayi kunnen uwar
shegu dasu, tamkarma batasan da ita sukeba balle ta nuna tama fahimci zancen
nasu.
Innaro ma tazo tayi tata tsiyar San rai,
tabi duk ta zagemu dacin mutuncin innarmu, koma fitowa innarmu hanamu yi tayi,
har Innaro tagama tafice. Matan gida najin dad'i.
★★★★★★
Haka rayuwar
tacigaba da tafiya, yau da gobe kayan ALLAH har gashi azumi ya rage saura
kwanaki uku kacal a fara, Dan haka musulmai NATA shirin tarbar wannan wata mai
tarin albarka da falala.
Kasuwanni sun cushe saboda yawan hada-hada,
duk da 'yan kasuwa sunyi taiyar tasu ta k'arama abinci kud'i, maimakon su
sassauto bayin ALLAH su sami sauk'i (ALLAH ka shirya 'yan kasuwarmu subar
wannan hali dai).
A 6angaren gidanmu ma iyayenmu maza duk
sunyi shirin, Dan dukkan wani abun buk'ata an tanadeshi, sai abinda ba'a rasaba
dazai iya lalacewa idan an ajiye, wannan anbarsa yayunmu maza su ringayo
cefanensa kullum kamar yanda aka saba.
Itama Innaro an ajiye mata dukkan abinda
zata buk'ata, dukda kullum daga gidanmu ake kaimata abinci, safe yamma da dare,
kuma dolene kowane 6angare sai sunkai nasu.
Muma a 6angarnmu munyi dukkan namu
shirin, dukda abin zai had'e mana da zuwa makaranta, hakan yasa nake tausaya
mana, gashi ana tsula rana mai zafi kuma.
Alhmdllh yau ta kasance Alhamis, kuma
yaune ake saka ran ganin wata atashi da azumi washe garin juma'a.
Har zuwa 9pm kunnen kowa naga redio da
talabijin, jira kawai Muke muji sanarwa daga sarkin musulmai. sai wajen 9:30pm
sanan aka Sanar da ganin wata, duk wani Muslim yana cikeda d'okin fara azumin
watan Ramadan da zamu Shiga goma ta marmari (inji hausawa😂).
Tun alokacin duk muka d'auki niyya,
kasancewar girkin innarmu ne tayi shirin tafiya d'akin Abbanmu, muma tace mu
kashe TV muje mu kwanta kar atadamu da asuba kuma muzo muna k'unk'uni.
Badan mun soba muka kashe mukaje mukai
shirin barci muka kwanta da addu'ar abakunanmu.
Aiko da asuba dak'yar innarmu ta iya
tashinmu mukai sahur, tea kawai muka shama, dama mu bama sahur da abinci nida
munubiya, garama ita wani lokacin takan had'a da kunu ko fura.
Bamu kwantaba saida akayi sallar asubahi,
still kwanciya muka kumayi, sai 8 innarmu ta tadamu, kasancewar yau saima 10
mukeda lecture, kuma zamu fito 12 ne.
Tunkan aje da nisa azumin yafara garani,
dak'yar Na daure aka kammala lecture muka fito, amma badan Na fahimci komaiba
nidai yau.
Su Munubiya sai dariya suke mini wai
Raguwa, nidai ban kulasuba, Burina kawai naga mun Isa gida Na kwanta.
Tunda muka dawo school nazube a falo
k'asan carpet, ban sake Sanin duniyar danake cikiba saida munubiya ta tadani
nayi salla, Ashe harsu Aryaan sun sako masallacima inata barci, sallarma
dak'yar nayita atsaye, INA kammalawa nakuma kwanciya.
“oh ni Aisha, wai Munaya mikikeson maida
kankine? yanzu azumin kikema langa6e haka?
saikace yau kika fara azumi a rayuwarki?”.
“ALLAH innarmu bazaki ganeba, nidai
ALLAH yasa akira salla da wuri”.
Munubiya dasu Aiyaan suka sakamin dariya.
“Aunty yanzufa k'arfe 2 ma, sauran kusan awa 5 dawani Abu asha ruwa”. ‘Aryaan
yafad'a yana dariya’.
Harara Na Dalla masa INA fad'in “ALLAH
inbaka rife wannan bakin naka mai gajerarrun hak'oraba zaka dakune, Dan
k'aniyarka kaiba yanzu kagama lodama cikinka abinciba?”.
Aunty nimafa Dan innarmu bata tadamu
baneba kawai, amma insha ALLAHU gobe zamuyi ko Aiyaan?”.
cikin zumud'i Aiyaan yace, “eh mana,
muma zamuyi bro”.
“kuma wlhy yaro bai Isa karyashiba,
garama karku d'auka”.
Munubiya tamik'e tana dariya, “imm
innarmu bara kiga naje nafara rage aikin, miza'ayi?”.
“ki fere doya kafin Na fito, Munaya tashi
maza kuje, kekuma ki gyara kayan miya”.
“wayyo innarmu ki tausaya min mana”.
“mukuma mu kashe kanmu tunda bama
azumin ko?”. ‘cikeda gatse tayi maganar’.
“a'a innarmu, bara naje kodaga zaune
sainayi”.
“kimayi daga kwance, raguwar banza
kawai, ai mijinki yashiga uku, wataran sai yadawo aiki baki gama abinciba”.
Baki Na tura gaba sannan nafita.
Mun rage aiki sosai kafin la'asar, sai
bayan sallar la'asar d'in 'yan Matan gidanmu suka shishshigo kitchen d'in kamar
yanda aka saba, dama duk shekara gaba d'aya muke had'uwa a kitchen d'in
6angarenmu ayi abincin bud'a Baki, saidai saboda munada yawa akanyi time table
saboda a rarrabu kowa da ranar da Zai taya mai aikin ranar.
Da yake
aikin yawane dandanan muka kammala kafin 6, a can tsakar gida aka shinfid'a
manyan tabarmi bayan an tsaftace wajen, duk azumi gaba d'aya muke had'uwa asha
ruwa dama anan, kafin matar ya hameed ta rasu har itama anan suke zuwa suyi
bud'a Baki.
Bayan mun had'u mun gama shirya komai kowa
yanufi 6angarensu ya watsa ruwa kafin akira salla, dolene kaga jama'ar gidanmu
aranar mu burgeka, babu fad'a babu hantarar juna, (yo kowa azumi yagama cin
k'aniyarsa🤣🤪).
Kasan cewar babu wuta ya kamal yazuba
fetur a Gen... Ya tada, kowa yayi wanka saiyayi shirinsa da alwala yadawo
tsakar gida ana jiran kiran salla, yara dabasuyi azumi baneba suketa
shargallensu a tsakar gidan.
Yanda na zube a tabarman tamkar mara
kashi yasaka yaa Shafi'u fad'in “kai kekam anyi raguwar yarinya wlhy, nasan dai
Munaya Ce, Dan Munubiya tafiki jarumta”.
Dariya wad'anda ke wajen sukayi, yaa
Naseer yace, “gaskiya mijinki yaga banu, yo idan yayi wasa dai bazai dinga cin
abincin bud'a bakiba a gidansa”.
Cikin dariya Aunty Hauwa'u ke fad'in “sai
ya d'auka mata 'Yar aiki ai”.
Caraf maman Safara'u ta amshe zance...
“yo basai idan mai halin d'aukar 'Yar aikin bane, ana fama da masarar tuwo da
shinkafa a jajibo mai aiki?”.
Gurin tsit yayi kamar ruwa ya cinyemu, da
alama kowa baiji dad'in furucin Na maman safara'u ba, sai mamansu yaa hameed ce
tayi dariya itada momy Hadiza.
Ganin abin zai koma cin zarafin juna sai
maman fauziyya ta d'ako wani zance, daga nan aka koma hirar d'inkin salla. babu
dad'ewa ma aka kira sallar magriba, cikeda d'oki kowa yafara k'ok'arin cin
dabino. tab aini kam bandani, tuni Na d'ebi ruwa mai sanyi nafara sha, Dan
shine babban burina. a gida mukayi jam'i, baba k'arami yajamana limanci. da
ganan kuma kowa ya maida hankalinsa wajen bud'a baki, harda su hajiya innaro😕, tayi kane-kane ita masu gidan 'ya'ya😏, koda wasa dagamu har innarmu babu Wanda yashiga
sabgarta gudun gwalasa, har aka gama lafiya muka gabatar da sallar isha'i da
asham. daga nan aka d'an ta6a hira kowa yahad'a kan 'ya'yansa zuwa 6angarensa.
haka muka cigaba da gudanar da ibadar
azumin watan ramadan, tun ina ragwan taka harna fara daurewa, an gama goman
farko aka shiga ta biyu (goma ta wuya🙊 ).
Gaskiya nad'an wahaltu a tsakanin, ga
makaranta ga aikin gidanmu dabaya k'arewa, ko wanke-wankema ya isheka, dukda
had'uwa akeyi anayi kuwa.
Azumi yana 13 aka kawo kayan sallarmu, an
bajesu tsakar gida kowa ya za6a, kala uku-uku ne dama duk shekara, atanfa,
shadda, les, saikuma iyayenmu mata su k'ara mana gwargwadon abinda ALLAH ya
hore musu.
Munada telolinnmu masu mana d'inki iya
'yan gidanmu kawai, shiyyasa bamuda matsala. Washe gari kuwa sukazo suka
gwadamu, kowa aka saka sunansa ajikin kayansa da style d'in data za6a.
Innarmu ma sun saya mana itada mama
Rabi'a, dan tunma kan azumi an kammala mana d'unkunanmu mudasu feena, (innarmu
tana business itada mama Rabi'a) shiyyasa duk wani abun kwalliya Na 'yan mata
bama rasashi, duk da dai 'yan gidanmu suna mana d'agawar sun fimu komai, saboda
danginsu masu kud'ine, suna ganin kayansu sunfi namu tsada. hakan baita6a
damunmu ba, dan aganina duk sutura sunanta sutura, yawan kud'in nawani bai
d'ad'ani da k'asaba, to barema Munubiya da babu ruwanta.
Ana cikin haka muka shiga goman k'arshe
Na azumi (goma ta d'okin sallah🤪😂).
Ranar wata weekend yayyanmu maza suka
kwashemu domin za6o takalma da sauran tarkace Na kwalliya, dama duk ankai yaran
suma kowa ya za6o, mu matasan 'yan matan muka rage dakuma yayyenmu su Aunty
khaleesa.
Plaza ce babba mai k'yau da burgewa,
kayansu Na manyane, amma yayyenmu dayake sunaso mufito suka kaimu can, sa6anin
da da ake kaimu kasuwa kamar sauran yaran, su aunty khaleesa ne kawai ake
kawowa nan saboda sune manyan 'yan mata, to yanzu muma mun shigo layi💃🏻.
Sosai muka rikice da tsarin wajen,
takalmane 'yan waje wad'anda duk inda kayi taku sai an kalleka ansan kagama
Isa. Harda bags, kayan makeup, turarurruka da dogayen ruguna irinsu Arabia's
gowns, gyalilla da kayan 'yan kunne, kananun Maya Na garari Na mata da maza,
kai inaga babu abinda zakazo Baja sameshi awannan PLAZA d'inba kam”.
Lallai an narka dukiya a wannan waje, ko
plazan wanene? oho. munga dai sunan plaza d'in *BIRNIN GAYU!!*
“Lallai kuwa taci sunanta birnin
gayu”. ‘ cewar Anty Ramlah’.
Haleematu tace, “wlhy wannan ace plaza
d'in mijinace to bazan maimaita kaya sau uku ba, hakama waya duk wata za a
dinga canjamin”.
Dariya tabamu, dan haka muka shiga darawa
kuwa. kowa yad'auki abunda yakeso gwargwadon iko, yayyanmu suka biya da kud'in
dasu Abba suka basu, sannan suka cika mana danasu kud'in, kowa yafito cikin
farin ciki muna jera musu godiya, mun d'auki picture's sosai awajen kuwa. muna
tafiya a mota nake cewa yaa Anas dan ALLAH wai Plaza d'in waye wannan?”.
“ai plaza d'in ta babban kwaroce k'anwata,
plaza d'in *GALADIMA* ce”.
shiru nai kamar banjishiba, danjin
sunan wanda ya ambata, inada tabbacin kuma wannan mai girman kan tsiyar yake
nufi kenan, yayinda 'yan uwana suka rud'e da firar galadiman.
d'an tsaki naja nace, “ashema Na mai
shegen girman kai d'innan ne”.
Kusan atare sukace ke a ina kika sanshi?
dahar kikasan yanada girman kai”.
Shiru namusu, sai Munubiya ce tashiga
basu labarinsa da had'uwar damukayi a asibiti da shi, aikam duk sai sukabi suka
rikice, harda masu fatan yazame musu mijin aure.
bansan miyasa duk hirar tasu ta
k'untataniba, tabani haushi, saina maida hankalina ga kallace-kallacen jama'ar
daketa kai kawo akan titi.
Har mukaje gida suna hirar Galadima sudasu
yaa hameed dake basu labarin halayen kirki Na Galadima d'in, wai kuma bashida
girman kai kamar yanda Na fad'a, kawai dai dan ban fahimcesa bane nima.
Nidai jinsu kawai nakeyi, amma badan Na
yarda baida girman kai ba, tunda da idona Nagani ba labari aka baniba.😏ehe
Innarmu tayi mamakin wad'annan kanya, dan
haka takasa hak'uri, har 6angaren samarin gidanmu taje tamusu godiya da fad'an
d'awainiyar tayi yawa ai, ga hidimar biki Na tunkarosu.
Sunji dad'i sosai akan hakan da innarmu
tayi, koba dad'i kowa yayi aikairi yanaso anuna jindad'i kuma amasa godiya.
Sukace tayi hak'uri, ai k'annensu ne, idan
basu mana ba wazai mana, da samari suzo suna mana hidima su lalata mana rayuwa
ai garasu sumana su kare mutuncinmu.
Sosai innarmu ma taji dad'in furicinsu, dan
hakan ya nuna cewa su basu d'auki halayen iyayensu mataba Na raba d'aya biyu.
Salla nata gabatomu, yayinda aka fara
'yan kimtse-kimtse Na shirin bikin sallar, masallatai nata rufe tafseer, hakama
gidajen redio dana talabijin..............✍🏼
*Kusaka
yayan mahaifiyata a addu'arku, ALLAH yamasa rasuwa ranar alhamis😭👏🏻, ALLAH ya gafarta masa, ya raya
abinda yabari.*
_Bansan
makaranta Raina kama.... kunada yawa hakaba wlhy, nazata ki rabin group bazaku
kaiba🙆🏻, gashi yacika wasu basu sami wajeba kuma._
https://2gnblog.blogspot.com/
Na gaisheku
k'yauta, ina fatan duk kuna cikin k'oshin lafiya kuda iyalanku🤝🏻😊?.
No comments