QANIN MIJI 2
Yanzu ma
bayansa suka bi da kallo sannan suka juyo suka haɗa idanu, kowa da irin kallo
da yake yi wa ɗan uwansa, cike da damuwa fareedah ta sunkuyar da kanta qasa
yayin da hafeez ya matso kusa da ita cikin muryar rarrashi da tausasa lafazi
yace
"kullum
irin wannan damuwar takan bayyana akan fuskarki, in tambayeki, idan tana
maganin wani abu, ya kamata a sake ganin wata damuwar a fuskarki"?
Idanunta ta
watsa masa ba tare da tace komai ba, hakan bai hana shi fahimtar amsarta ta
cikin idanunta ba, murmushi ya mata ya lumshe idanunsa ya buɗe yace
"then
smile"
Ba ta iya
riqe kanta ba, dole ta murmusa kaɗan, dan hafeez yana da muhimmanci a gurinta,
duk da ta daɗe tana yakiceshi daga jikinta saboda qyamatar wasu abubuwan da
yake mata amma yanzu ya fara yin galaba a kanta domin mafi yawancin
farincikinta da walwalarta daga hafeez ne
Duk da dai
murmushin mai kama da yaqene amma ya ji daɗin ganinshi kan fuskarta, saɓanin
damuwar da ta shiga da farko
"sai
mun dawo matar, ki shirya mana haɗaɗɗiyar supper, dan ni dai bayan hajiyarmu
duk duniya babu matar da ta kai ki iya abinci"
Sai da ta ɗan
dara cikin muryar dariyar tace
"um um
dai hafeez, bana son ganin ido"
Yana qoqarin
ficewa ya ɗan juyo yana dariya yace
"Allah
kuwa matar, shiyasa nake sonki sosai, ba ke ba kishiya, i realy love you, ki ji
daɗin rayuwarki kawai kiyi yadda kike so"
Bai saurari
amsarta ba ya fice da gudu-gudu sauri-sauri
Dam dam
fareedah ta ji zuciyarta ta mata lugude, sai da ta nemi guri ta zauna kan ɗaya
cikin kujerun falon saboda yadda maganar ta shigeta, kalmar i realy love you ta
fi komai dukan zuciyarta
Wannan
kalmar ba a bakin hafeez ya kamata ta ji shi ba, a bakin mijinta ya dace ta ji,
amma idan ba mantuwa ba, ko a first night ɗinta ba ta ji wannan kalmar ba balle
a sauran zamansu na tsawo shekaru uku
da watanni, rabonta da wannan kalmar tun a filin nema, wato dandalin soyayya,
nan kam ta ji su har ba iyaka, amma tunda ta shigo gidan, ba za ta iya tuna
rana ɗaya da ta ji wannan kalmar daga bakin fa'eez ba, ko ita ta faɗa masa
hakan ma sai ya ga dama yake nuna jindaɗinsa ko yayi murmushi kawai, ranar da
'yan rahar suke kusa kuma ya ja hancinta, shikenan an gama, babu wani abu da
yake biyo bayan nan,
Tun tana ɗaukar
lamarin wasa wasa, kamar za ta iya canzashi, sai gashi sun kwashi shekaru ba
canji, ita kuma ta kasa sabawa da hakan sam sam, dan ba haka ta tsara ba ko a
cikin mafarkanta, rayuwar soyayya ta so shimfiɗawa filla fillah
Hawayene
suka fara gangaro mata a fuskarta suna bin haɓarta, daga qarshe ma dai ta fashe
da kuka ta tashi ta bar falon ta haura ɗakinta
Ta daɗe tana
kuka ta ji wayarta da take kan side na gado tana neman agaji, tsayar da kukan
tayi ta je toilet ta wanke fuskarta ta fito daidai da shigowar wani kiran, hafeez
ta gani, hakan yasa ba ɓata lokaci ta
clearing throat ɗinta ta picking call ɗin
Dawo da
sallamar da ta masa yayi cikin raha yace
"ina
kuma kika shiga matar"?
Qirqirar
walwala tayi cikin muryarta tace
"ka
ganni nan wai baccine yaso ɗaukana"
"kash
amma ban ji daɗin katse miki barcin da nayi ba matar, ki gafarceni"
Ya qarashe
cikin marairaice murya
Qyalqyalewa
tayi da dariya tace "ni daɗi ma naji da ka tasheni, aiki zan yi
yanzu"
Daga
muryarshi ta gane ya ɗaure fuska sannan yace "ba kin qi mai aiki ba, sai
kiyi ta tiqar aikinki ke kaɗai ai"
Dariya tayi
cikin sigar lallashi tace
"sorry
mijin, tun a gida ina da qyanqyamin girkin mai aiki, ni ko wanke wanke aka yi
mana sai na sake wanke waɗanda nake amfani da su"
"ok,
toh ki bi a hankali dai, kar ki dinga gajiyar da kanki"
"na
gode hafeez"
Shiru suka
yi sannan ya ɗora da faɗin
"kiranki
nayi in faɗa miki na kai miki mijinki office lafiya, yanzu haka ya shiga
meeting da ma'aikatansa"
Murmushi
tayi tace "ka kyauta"
"toh
sai mun dawo ko?"
"Alah
ya tsare ku dawo lafiya"
"ameen
matar"
Ajiye
wayoyin suka yi, sannan fareedah ta wuce kitchen bayan ta kalli agogo, a ranta
tana raya cewa dole ta sake wa fa'eez ɗinta abinci duk da bai ko kalli wanda ta
shirya masa ba, toh yaushe ma ya zauna?
***
Zaune suke su ukun suna taking supper ɗinsu,
sai qarar spoons kawai yake tashi, ba magana, yayin da fa'eez yake haɗa cin
abincin da danne danne a waya kamar wani admin😁, hhh gaskiya matan admins kuna da hakuri, admin mai zuga kenan amma
na......😍, gaskiya kana shan 143 admin, Allah ya sawwaqa dai😂😂😂, dan Allah mata aji mana plss
Hafeez kuwa
sai kallon fareedah yake yi yana mata murmushi, yayin da ita kuma hankalinta ke
kan nurulhayat ɗinta, gaskiyar magana fareedah tana qaunar fa'eez qarshe, kullum
zuciyarta ruruwa take da wutar qaunarsa, ta rasa wacce irin kamo mijin nata ya
mata haka, kuma fa fa'eez ɗin ya kai a soshi, dan ubangijinsa ya qerashi
maqurar qira, kamar jinin annabi yusuf dan haɗuwa da zallar madarar kyau,
muninsa kawai halayensa
Gyaran murya
hafeez yayi ya calling attention ɗinsu kansa sannan ya kalli fareedah ya mai da
kallonsa kan yayan nasa yace
"kai
gaskiya mu kam mun yi sa'a"
Da kallon
tambaya duka suka bishi yayin da yayi murmushi yace
"anya
yaya kana ganin bayan girkin aljanna ba sai wannan ba kuwa a daɗi"?
Kallon juna
fa'eez da fareedah suka yi sannan faeez ɗin ya kalli hafeez da 'yar harara a
fuskarsa ya ɗauke kai ya cigaba da cin
abincinsa
Murmushi hafeez yayi ya sake cewa
"mu dai
muna godiya wa Allah, yayanmu ya iya zaɓe, gangariya, kai abincinma sun kai ayi
hotonsu, bari in ɗauka"
Buga cokalin
hanunsa yayi akan plate ɗin abincin yace
"kai....
Hafeez, wallahi ka cika surutu, ku qarata ni sai da safe, zaka hanani aiki,
idan kana da buqatar wani abu ka tambayi fareedah dan za ka iya wucewa school
ban fito ba"
"goognyt
yaya, bana da buqatar komai"
Ko amsawa
bai yi ba ya wuce samansa abinsa bayan ya ɗauki laptop ɗinsa da yake kan kujera
kusa da inda suka ci abincin
Harara
fareedah ta banka wa hafeez tace
"ka ga ka kora min miji, haba!!!" tana gama faɗin haka ta
tashi ta bi bayan fa'eez tana cigaba
da surutu wa hafeez
"ni dai
ban kora miki miji ba malama" cewar hafeez cikin dariyar tsokana, ko
kulashi ba ta yi ba ta haura ɗakin mijinta
Ta sameshi
har ya cigaba da aikin da yake yi ta waya, zama tayi kusa da shi ta kwanto a
jikinsa ta marairaice murya kamar za ta yi kuka tace "my man kamar kayi fushi"?
Kallonta
yayi ya ɗan murmusa kaɗan da gefen bakinsa, in ba ita da ta san halinshi ba ma
babu wanda zai ɗauka murmushi yayi sannan yace
"wa ya
faɗi hakan"?
"toh ba
gashi ka taso ka bar mana gurin ba"
Janyeta yayi
daga jikinsa yana cewa "je ki kuyi hiranku dan Allah ki barni in yi
aikina, bana son hayaniya"
Marairaicewa
tayi tace "nice hayaniyar"?
Yana janyo
laptop ɗinsa yace "idan haka kika ɗauka
ba"
Wani baqincikine ya tokareta, sai ga hawaye ɗaya
na korar ɗaya
Galala ya
tsaya yana kallonta sannan cikin muryar mamaki yace "me aka yi"?
Maimakon
amsa sai ta fashe da kuka ta kife a gurin tana rerawa abinta
"ok.....,
na fahimceki, kina da buqatar mijinki ko"?
Ba ta yi
magana ba sai ma cigaba da tayi da kukanta
Agogo ya
kalla sannan ya taɓe baki yace
"ban da
abin fareedah kwata kwata kwana nawane ba a haɗu ba, na ga ba a wuce two weeks
to three ba, kina son wahalar da kanki, ina so ki sani, nima fa ba wai
buqatarce bani da ita ba, kawai na cire wa rainane saboda bani da lokaci,
ayyuka sun min yawa, kema da kin cire wa ranki zai fi miki, mtss bari in gani
ko zan iya baki 30m, je ki shirya ki zo,
ban minti biyar" ya qarashe yana mai duba agogo again
Readers in
kece me zaki ce?, yi maganar kamar kece fareedah
More
comments, in ba comments daman ayyukan suna da yawa, na tsani tanx
ISLAM IS MY
IDENTITY
No comments