QANIN MIJI 1
QANIN MIJI
Daga
alqalamin marubuciyar zamani✍🏼
MARYAM A.I
GITAL
@ Meerahgee pure moment
of life writers👌🏻
SADAUKARWA
GA JININANE REAL FANS, MUCH LUV GUYS😘
1
Fareedah
yarinyace matashiyar zamani, son kowa qin wanda ya rasa, mace ce iya mace domin
kuwa ta mallaki duk wani kayan yaqin da zata iya farauce zuciyar duk wani
lafiyayyen ɗa namijin da ya ɗora idanunsa a kanta, ta haɗu ta ko ina kuma sai
aka yi sa'a ta san me take yi, wato mai tsabtace ta qarshe da kuma son qyalli
da qamshi, ga uwa uba kamun kai, ta fuskar addini ma ba a barta a baya ba, duk
da dai ance mutum tara yake, bai cika goma ba
Kana ɗora
idanu akan fareedah zaka gane zallar hutu a kan fatarta da jin daɗi, alamun
babu wani abu da ta nema ta rasa a rayuwarta, saidai abin ba daga nan take ba
wai an danne bodari ta ka
Akwai wani
babban qalubale a cikin rayuwar fareedah da kullum yake addabar zuciyarta da
nutsuwarta, wanda yake hanata gamsuwa da fahimtar ainahin ni'imar da take ciki
a matsayin cikakkiyar ni'ima, bal ma wani lokacin takan tsawaita kuka da shiga
damuwa akan marqabun na rayuwar da take ciki
Toh fa masu
karatu sai mu bi fareedah domin gano matsalar, ni dai a tunanina ai an wuce
gurin tunda akwai kayan kwalyar da za a iya yin fiye da awa anayi, ko kuwa
readers😃
Cikin tsadaddiya mat ta ke mint green wacce
aka yi wa ɗinkin zamani, irin ɗinki ɗiban albarkan nan, amma ita a gareta na ɗeban
ladane tunda tayi ne dan mijinta, riga da sikirt ne da suka kamata tsamtsam,
rabin bayan rigar duk a waje yake, ya bayyana rabin fatar bayanta mai matuqar
sheqi yayin da gaban rigar ma ya bayyana saman nonuwanta da cika da batsewarsu
a waje, sikirt ɗin kuma duk wasu halittunta ta 'ya mace sun bayyana kansu zamzam tamkar an ɗinka ne da jikinta, ɗan
kwalin nan kuwa an masa ɗauri irin wanda
ake kira da dani zaka maigida?, shi ta baza, kai abin faɗi kawai mashaa Allah
tabarakallah indai akan fareedah ne, domin an wuce gurin, macece ta kece raini
Ta gama fesa
turarukanta kenan ta jiyo kamar qarar shigowar mota harabar gidan, hakan yasa
tayi saurin zuwa jikin window ta zuge labulen kaɗan ta leqa, kasancewar ta san
hafeez qaninsane zai je ɗaukoshi daga airport da motarshi yasa tana hango motar
hafeez ɗin taji wani irin daɗi da farinciki sun mamaye zuciyarta, dan Allah ya
sani tana matuqar qaunar mijinta, babu abinda ta fi so tamkar ganinta ga ta ga
shi, tana tsananin muradin zama da mijinta a koda yaushe cikin irin rayuwar da
zuciyarta take hararo mata kullum
Wani irin
sassanyar ajiyar zuciya ta sauke ta haske kyakkyawar fuskarta da murmushi mai
ratsa zuciya sannan ta sake labulen ta ɗage yatsun hannunta sama ta murza wani
haɗaɗɗen zobe mai masifar kyau da sheqi da yake yatsarta manuniya ta sumbata
sannan ta fara taku tamkar ɗawisu tayi hanyar fita daga ɗakin nata
Adana motar
hafeez yayi da kyau sannan ya fito ya je ya buɗe wa yayan nasa qofa wato
fa'eez, tare da masa bismillah fuskarsa ɗauke da murmushi
Da bismillah
a bakinsa ya fito cikin shiga ta alfarma, wata haɗaɗɗiyar dakakkiyar shadda ya sanya ruwan zuma a jikinsa wacce
aka baza mata zare coffee colour, hular kansa da takalmansa duk coffee colour
ne masu matuqar kuɗi, domin fa'eez ɗan gayene na nunawa a taron sallah, ga son
qamshi tamkar Ammar ɗin Elham😍
Daidaituwar
qafafunsa akan qasa ba daɗewa ya ɗago hanunsa mai ɗaure da agogon rolex ya duba
time yayin da hafeez yake qoqarin rufe qofar motar bayan ya ɗauko masa mr boss ɗinsa
a bayan motar (briefcase)
"na
kusa makara hafeez, ni ban ga saurin jirgin nan ba" cewar fa'eez cikin haɗe
fuska da rashin walwala
Hafeez yana
murmushi yace "an gode Allah dai tunda gashi ka iso gida lafiya
yayah"
Wani kallo
ya bi hafeez da shi sannan ya ɗauke kai yana cewa
"a
sallah kawai kullum sau biyar nake gode ma Allah"
Dariya
hafeez yayi ya sosa qeya yace "afuwa yayana"
Sannan ya
dafe wa yayan nasa baya ganin ya fara tafiya cikin tafiyarsa ta qasaita duk da
sauri yake yi
Da sallama
ya shigo falon yayin da fareedah ta haɗa amsa sallamar da oyoyo, da gudu ta je
ta rungume kayanta tsamtsam tana cewa
"oyoyo
my handsome" cikin wata iriyar murya mai cike da kirsa da kisisina
Maimakon ya
appreciating ɗinta ya tayata su enjoying moment ɗin, sai ma ya ɗagota daga
rungumar da ta masa ya ɗan sake fuskarsa kaɗan ya cire hular kansa ya miqa mata
tare da juyawa ya kalli hafeez da yake tsaye yana kallonsu cikin wani irin
yanayi ɓoyayye yace
"ka ban
15m zan shirya in fito ka kaini office, ka kira maxwell kace ya haɗa min zama
da su cikin gaggawa, ina zuwa yanzu"
Yana gama faɗin
haka ya raɓa gefen fareedah ya wuceta ya shige cikin gidan
Daga
fareedah har hafeez bin bayansa suka yi da kallo yayin da idanuwan fareedan
suka ciko da qwallah, muryar hafeez ne ya dawo da ita daga duniyar da take
yayin da ta ji yana cewa
"matar
kin haɗu wallahi, gaskiya ke wankakkiyace ta qarshe, samun irinki ribace da ba
za a iya qirgawa ba, kullum ina taya yayana murnar samunki, ina ma nima in
dace, maganar gaskiya kin yi kyau, kuma daman ke kyakkyawace, tsaya in miki
hoto pls"
Mai da
qwallar idanunta tayi ta watsa masa haɗaɗɗun idanunta farare yayin da shima ya
kafeta da idanu yana murmushi
Yaqe tayi
tace "hafeez ba ka gajiya da tsokana, ka gama dube dubenka ba zaka samu
kamata ba sai qasa dani, mummuna ma"
Hmmm yace
tare da yin murmushi yace "Allah ko"?
"sosai"
sannan ta ɗora da cewa "ban briefcase ɗin ka gani in yi sauri in tafi
gurin mijina kar yayi fushi"
Taɓe baki
yayi yace "wato ma mijinki,? hmmm, zo muyi selfie ki wuce ki turo minshi
ko inyi tafiyata"
Dariya tayi
tace "toh ai ba ni zaka yi wa burga da bulanci ba"
Bai amsa
maganar ba sai ma ciro wayarsa da yayi daga aljihunsa ya matso jikinta tare da
haɗa kansu ya fara ɗaukarsu a hoto yana
yi yana canza style ɗin tsayuwarsu, sun haɗa kai suna murmushi zasu ɗauki na
qarshen dan har ta nemi damuwarta ta rasa sai ga fa'eez ya fito cikin suit
jajaye yayin da ta cikin ta kasance baqa siɗik ya kallesu ya ɗauke kai sannan
yace
"ku ba
kwa rabo da shiriritar banza, ina ta jiranki ke kuma kin tsaya a nan kuna ta
shirme, ko me za ku yi da hoto ohonku, mts ku dai baku san muhimmancin lokaci
ba"
Sai da
hafeez ya ɗauki hoton kafin ya kalli yayansa yana murmushi yace
"ina
yin hakan ne in na yaba da kwalyar matar, kai ma yaya ya kamata ka yaba, ka
tsaya in ɗaukeku ko guda ɗaya"
Yatsina
fuska faeez yayi kamar ya ga abin qyama yace "wa?, ni?, caɓ, kai ma ba ka
da aikin yine, ka zo mu wuce in kana da time" yana gama faɗin hakan ya
wucesu ya fice abinsa
No comments