KARUWAR GIDA 2
TSOKACI
wannan
labarin bai shafi wata ko wani ba,na rubuta shine domin ganin yadda rayuwar
mata ta sauya a wannan zamani duba da yadda kwadayi da son zuciya yayi yawa a
zukatan ku,ba nayi ne dan son yad'a bad'ala ba zanyi ne saboda na zak'ulo wasu
halaye da suka shiga gidan aure.Duk wanda yaga
abinda bai masa ba yana da kyau ya bude shafin zagina k'ofa a bude take
domin karbar hakan daka ko waye zagi d'an zagawa ne nasan baya tabo🤷♂azagi
kowa normal ne🤪
🅾2⃣
Amsawa
ZAINAB tayi da toh, ta sami d'aya daga cikin kujerun da suke gurin ta zauna
hadi da rungume ANAS," ita kuwa Hajiya Rukaiyya pharmacy dake cikin asibitin ta nufa kai tsaye domin
sayo magungunan da aka rubuta musu," tafiyarta kadan ZAINAB ta fada duniyar
tunanin baya yadda rayuwar ta kasance tsakaninta da mijinta uban 'ya'yanta
wanda take kallon a matsayi sanyin idon ta a wancan lkc ba yanxu ba,tunawa tayi
da irin soyayyar da ta nuna mishi had'i da bashi kulawa haka shima daga nashi
6angaren sam baya son abinda zai bata mata zuciya,rayuwa ce mai ban
sha'awa mai cike da kaunar juna tunda
ZAINAB ta auri RABI'U bata taba kai k'ararshi ba haka shima bai taba kai tata
k'arar ba sai lkc da ta sami cikin MARIYA ne aka fara samun matsala domin kuwa
cikin yazo mata da wani irin yanayin laulayi mai daga hankali komai taci sai ta
amayar dashi,aman yakan zo matane a ko wanne yanayi babu dare babu rana,wannan
ce tasa RABI'U ya fara tsanarta da hantarar ZAINAB a ko wanne lkc hakan ce tasa
duk abinda ZAINAB ta ta6a RABI'U baya iya amfani dashi ga k'yara da hantara a
duk lkc da ta fara amaye_amayenta haka zai tsallake ya barta babu tausayawa ya
fita , tun abin baya damunta, har ta fara tsangwamar kanta da cewar ko RABI'U
ya daina sonta ne? take ta k'aryata zuciyar ta akan abin da take zargi"
duk abinda ZAINAB tace tana marmari a matsayinta na mai ciki bazata samu daga
gareshi ba, tun tana iya tashi tayi komai da kanta har hakan ta gagara wannan
hujjar ce tasa ZAINAB ta nemi izinin RABI'U da ya barta ta tafi gida tayi jinya
acan" Katseta yayi da wani wawan mari hadi da daka mata tsawa na cewar ai
daman ba d'aureki nayi ba ko an gaya miki cewar zamanki anan yana da wani
muhimmanci a gareni ne?" Dafe kumatu ZAINAB tayi hadi da kallonshi cikin
mamaki duba da irin yadda ya rufe ido yake ta faman masifa kamar bai san da
wacce yakeyi ba ya fice ya barta anan
tsugunne kan gwaiwuyinta ,can kuma sai ta tuna ai dole zaiyi masifa duba
da yadda ta saba masa da mi'ka mishi
jikinta a koda yaushe, kamin cikin ya samu, tayi iya yinta itama wajan
taga tana iya jure masa a duk lkc da yaso hakan amman abin yak'i domin kuwa duk
lkc da RABI'U yazo kwanciya da ita ji take yana mata wani irin wari wannan ce
take k'ara sa ambaliyar amai da zarar ya nemata" shi kuwa sai yake ganin
ai ta raina shine hadi da wulak'anci shi yasa ko tausaya mata baya yi a duk lkc
da yaganta a irin wannan halin. tashi tayi da k'yar Ta mike ta goge hawaye da
yake fuskarta ko wanka batayi ba ta sake kaya ta dauki kudin mota ta nufi
gidansu,"tun daga sallamarta mahaifiyar ta tabbatar ba lfy ba, duba da
yadda taga ZAINAB cikin tashin hankali hakan ne yabata damar tambayar ZAINAB ko
lfy?" Asmwa ZAINAB tayi jiki a san yaye da cewar lfy qlu MAMA, ta tsuke
bakinta daga haka ta k'arasa dakinsu inda k'anneta suke, duk suka tashi da
murnar ganin yayar tasu"ta amsa fuska babu walwala ta nemi gefen gado ta
kwanta ba tare da ta kara cewa kowa komai ba a haka bacci yayi awan gaba da
ita." Sanin halin mahaifin ZAINAB da mahaifiyar tata tayi ne yasa ko bin
ta kanta bata k'arayi ba domin ba nisa yayi ba tasan da zarar yazo ya sameta
tare da ZAINAB din zaice tana kitsa mata wani abune na rashin arziki tunda tun
farko sai da ta nuna bata son ZAINAB ta auri RABI'U amman ZAINAB ta k'ek'ashe
idonta da cewar shine za6in zuciyar ta."
ZAINAB bata fi minti talatin da kwanciyar ba mahaifinta ya shigo inda
mahaifiyarta ta sanar masa cewar ZAINAB tazo"da kanshi ya k'arasa har
kofar d'akin da take kwance yayi sallama yasa d'aya daga cikin k'anneta su taso
ta,a firgice ZAINAB ta tashi domin tasan mahifinta mutune mai a k'idar gaske
baya daukar raini, fitowa tayi da sauri wanda yayi dai2 da tashin zuciyarta nan
fa ta dinga amai babu k'auk'autawa ganin haka shine ya hana mahaifinta yin
fad'an daya saba. Ya koma dakinshi kai tsaye da cewar idan ta natsa yana
jiranta ta sameshi can" kai kawai ZAINAB ta daga alamar toh ta cigaba da
yin aman a inda ya barta. Mahaifiyarta yi tayi kamar bazata kawowa ZAINAB dauki
ba, sai da taga abin ya ta'azarra sanna ta baro inda take zaune take aiki ta zo
kanta domin tallafa mata" a hankali ta janyeta daga inda take ta samo ruwa
da tsumma ta gyara wajan sanna ta sake komawa ta hada ruwan wanka takai mata
band'aki, a sanyayye ZAINAB, ta mik'e tayi wanka,ita kuwa mahaifiyar tata dakin
yaran ta koma ta kara gyrawa sannan ta koma kan aikin da takeyi, ta fahinci
halin da ZAINAB take ciki watau na samun cikin nata ko daga yanayin sauyawar
walwalarta da kuma daukewar da jikinta yayi ga uwa uba amai da takeyi,"
wannan ne ya tabbatar mata cewar yar tata ciki gareta., Ba wani 6ata lkc ZAINAB
tayi ba wajan wanka ta fito ta koma dakin k'annen nata ta takure, kunun tsamiya
mahaifiyar ta damo mata ta shigo ta bata tace tasha"ba qaramin dadi kunun
yayiwa ZAINAB duba da yadda ta kasance cikin rashin jin dadin bakinta, a
hankali ta ringa shan kunun sai gashi ta shanye shi kamar wasa ga mamakinta kuma batayi amai ba, ganin ta
sami natsuwa ne yasa mahaifiyar ta, shigowa ta sanar mata da cewar taje
mahaifinta na jiranta" amsawa ZAINAB tayi da toh ta tashi ta nemi hijab
dinta ta saka ta bi bayan mahaifiyar tata
dakin mahaifinta ,tayi sallama suka amsa mata" zaune ta sameshi mahaifin nata yana duba littafin addini, ya
taso akan son yawan karatu k'ananun littafai na addini, sai da yakai k'arshen
karutunshi ya dago ya kalli ZAINAB da cewar na tamabayi mahaifiyarki ko lfy
kika zo gida? Tace min bata san dalili ba shine nace kizo naji daga
gareki" amsawa ZAINAB tayi cikin rawar baki da cewar daman banida lfy ne shine na taho"
kallonta ya k'arayi cikin ido da cewar uhumm?" Tai shiru a karo na
biyu" Ko RABI'U ne yace kizo gidan? Ta girgaza kai", ya k'ara da
cewar toh mekike nufi? Tayi shiru nan fa ya ringa yi mata fad'a kamar zai
doketa hadi da cewar shi gidanshi ba'a isa a ce anyo yaji har an zauna ba"
dan haka ta tashi ta shirya ta koma dakinta, ganin yadda mahaifin ZAINAB yake
ta fada babu sauki ko daga k'afa hakan ne yasa mahaifiyarta bata saka baki a
maganar ZAINAB ba." Hakan ce tasa ZAINAB dole ta sake kamo hanyar dawowa
gidan RABI'U gwaiwa babu kwari ta dawo,ko
data dawo haka rayuwa ta cigaba da tafiya a tsakaninta da mijinta yau da dadi
gobe babu, gashi tana tsoran taje gida ta Sanar a haka dai har cikin ZAINAB ya
isa haihuwa bata tsinke da al'amarin RABI'U ba sai a wannan daren da zata haihu
da ta rok'eshi da magiyar yaje ya sanar da mahaifanta halin da take ciki"
ya amsa, fita yayi ya nemi mai mashin ya
daukeshi yaje gidan su ZAINAB yayi sallama a lokacin yayi sa'ar
mahaifinta ya dawo daga masllaci ya sanar masa da cewar ZAINAB tana gida tana
nak'uda aje kanta, da sauri malam AUDU watau mahaifin ZAINAB ya koma ya sanarwa
da mahaifiyarta halin da ZAINAB take ciki hadi da yi mata umarnin ta shirya
taje gareta," toh kawai tace a hanxarce ta koma dakinta, ta dauki hijab,
" bai tsaya jin ta bakin matarshi ba yasake dawowa kofar gida domin neman
shawarar sirikin nashi kan yadda za'ayi da ZAINAB ga mamaki yana fitowa baiga dan mashin da
yakawo RABI'U gidansu ba bare RABI'UN
mamaki ne ya rufeshi amman sai ya kawo
ko firgicine hakan tasa ya koma cikin gidan domin kara SA mahaifiyar ZAINAB
tayo hanzari su tafi tare, A soron gidan yayi kaci6us da mahaifiyar ZAINAB din yace mata yawwa kin
taho?" Ta amsa da cewar eh" yace hanzarta muje na rakaki mamakine ya
kama mahaifiyar ZAINAB ganin yadda MALAM AUDU ya keta rawar jiki, batayi
tsammanin hakan daga gareshi ba tunda tasan mutum ne mai tsatsauran
ra'ayi" tafiya suka cigaba da yi har suka k' arasa titi motar ta ratsa ta
tsakiyar unguwar tasu, suka yi sa'ar samu mai texi din da zai kaisu unguwar da
ZAINAB take, a hanya ne MALAM AUDU ya roki mai motar ya taimaka ya kaisu har
kofar gida yar tasu da sanar mishi halin
da suke cikin ya tausaya musu matuk'a driver, sanna ya karfafa musu gwaiwar zai
taimakesu zuwa gidan yar tasu."
ita kuwa mahaifiyar ZAINAB jinsu
kawai takeyi amman bata fashintar maganar da malam yakeyi da driver sabida
hankalinta baya tare da ita, har suka k'araso kofar gidan yar tasu," koda
sukazo a bude suka sami kofar gidan ZAINAB kamar yadda sukayi tsammani,
kaitsaye mahaifiyar ta kutsakai cikin gidan bata tsaya jiran umarnin mai gidan
na taba, sallama tayi tun daga tsayar gidan amman shiru har ta kusa k'arasawa
d'akin Sai taji ZAINAB ta amsa da k'yar hakan ne yasa ta k'arasawa cikin dakin
da saurin inda ta sami ZAINAB kwance cikin jini kware_kaware a gigice ta dagota
tana yi mata sannu,kai kawai ZAINAB ta d'agawa mahaifiyarta, da sauri ta
jinginar da ita jikin gado takoma waje wajan MALAM AUDU domin ta sanar mishi
halin da ZAINAB take ciki" tana fita ta sanar mishi, tambayarta ya farayi
da ina sirikinshi?"amsawa mahaifiyar ZAINAB tayi da cewar ai babu kowa a
gidan sai ita kad'e mamaki ne ya kama
MALAM AUDU amman sai kuma yayi tunanin
RABI'U ko yaje kiran likitane" duk abinda akeyi driver taxi din nan yana
tsaye bai tafi ba, yana jiransu ya ji idan asibitin zai kai su toh ya jirasu" nuni MALAM AUDU yayiwa
matarshi da cewar ta koma ciki gashi nan zuwa"komawa mahafiyar ZAINAB tayi
ba tare da tacewa mijin nata komai ba'
tana shiga sai ga mai gidan nata ya shigo shima ya shigo har tsakiyar
d'akin ZAINAB din bai jira wata_wata ba ya kalli matar tashi da cewar HALIMA
mai zamu jira garinyi?" Ai kawai kamomin ita muje asibiti tunda naga
alamar tana jin jiki"toh kawai mahaifiyar ZAINAB tace domin ta dade bataji
mai gidan nata ya ambaci sunana ta, sabida tsabar kawaici" daukanta sukayi
chas har mota suka sakata,sanna mahaifiyar tata ta dawo ta gidan nata ta dauki zannuwa ZAINAB ta janyo d'akin nata ta
fito ta fad'a mota,shigar su mota ke da wuya sai ga RABI'U ya dawo da sauri
MALAM AUDU ya fito ya tareshi da cewar munzo gidan ne tunda nazo bamu ganka
ba,gashi ZAINAB tana buqatar taimakon gaggawa shine zamu kaita asibiti"
yak'e RABI'U yayiwa MALAM AUDU hadi da juya yar bak'ar ledar hannushi da cewar
babu damuwa, kuje kawai zan biyo bayanku, bari na shiga na ajje ledar hannuna
daman magani naje sayo mata"toh kawai MALAM AUDU yace ya koma mota a
tunaninshi abinda RABI'U ya fada gaskiya ne,suka ja mota suka tafi amman ko
lek'awa baiyi yace wa ZAINAB y jiki ba" haka suka nufi asibiti suka kai
yar tasu babu RABI'U babu dalilinshi bare bare wani nashi duk da dare ne"
a haka har Allah yasa ZAINAB ta haihu lfy ta sami santaleliyar budurwa duk da
tsammaninsu ko RABI'U bai sami abin hawan da zai hayo ba tunda dare ya shura,
MALAM AUDU ya buga wayar RABI'U arufe
daga baya ya yanke shawarar bari ya jira gari ya k'arasa wayewa ya kira
ta mahifin RABI'U ya sanar mishi, haka Kuwa akayi domin MALAM AUDU yana fitowa
daga masallacin asibitin ya latsa lambar mahaifin Yayi sa'ar mahaifin na RABI'U
wayarshi na bude yayi sallama a ka amsa daga can 6angaren ,bayan sun gama
gaisawa ne cikin girmamawa sannan ya sanarwa da mahifin sirikin nashi cewar
ZAINAB ta haihu tun daren jiya ta sami mace amman suna asibiti tare da ita,yayi
murnar matuk'a shima mahaifin RABI'U sanna ya k'ara da cewar basuda labarin
rashin lfy tata, domin kuwa d'an nasu bai sanar musu ba,koda mahaifin RABI'U
yazo kan wannan maganar sai MALAM AUDU ya nuna mishi babu komai hadi da sanar
mishi da sunan asibitin da suke watau SAUDAT clinic wanda yake bayan katangar
B.U.K a nan unguwar kabuga Jan bulo daman nan ZAINAB ta sanar musu tana zuwa
awon ciki, anan k'awarta RuKAIYYA SHITU
ta sami aiki shine har ta bude mata file anan," basu wani bata lkc ba suma
iyayen RABI'U suka hallaci asibitin da kayan baby kaca_kaca nan fa dangin suka
shiga yiwa juna murnar haihuwar da ZAINAB tayi, amman har a wannan lkc gogan
naku baizo asbitin ba bare yazo yaji
halin da ake ciki, duk gwaje_gwajen da za'ayiwa ZAINAB da baby anyi sanna aka
sallamesu daga asibitin kai tsaye ZAINAB gidatan aka mayar da ita ta bakin
mahaifin nata, wai bayason wata bid'ar tafiya gida wanka hakan baiwa mahaifiyar
ZAINAB dadi ba,amman su iyayen RABI'U sai sukaji dadi kalmar MALAM AUDU domin
kuwa suna ganin baya kyau tuwa ayi sunan surukar tasu a gidan iyayaenta, tunda
daga asibiti MALAM AUDU yayi ma su mahifin RABI'U sallama yace zai koma gida ya
shirya yaje kauye domin sanar da danginshi ya dauko wacce zata kula da ZAINAB
wajan yi mata wankan jego godiya, suka k'ara yi masa da yabawa bisa hallacin da
yayi musu sannan ya tafi,. Ita kuwa
mahaifiyar ZAINAB kafarta kafar yarta har gidan ta,inda suka rankawa tare da
iyayen mijin ZAINAB din ,suka tarar da RABI'U yana gidan yanata sharbar bacci
abinshi har wannan lkc,mahaifiyar ZAINAB batayi mamakin abinda yayi musu ba tun
daga daren jiya har kawo safiyar yau din" shi kanshi RABI'U tashi yayi a
kunya ce bisa ga abinda yayiwa iyayen matar tashi, koda ya fuskanci basu
sanarwa mahaifanshi ba sai ya marzaye idon shi kamar bashi yayi wannan rashin
mutuncin ba. Da mahaifiyar ZAINAB da tashi, haka da sauran dangin haka suka hadu
suka gyara ZAINAB da babynta kana suka gyara komai wanda ya lalace tun farkon
fara nak'udar ZAINAB ta fara a
gida" daga k'arshe mahaifiyar ZAINAB tayi musu sallama itama ta koma gida
domin ta sanarwa nata dangin da mak'ofta cewar ZAINAB ta sauka lfy, "Tana
isa gida ta fara aikawa makwaftanta cewar ZAINAB ta sauka lfy" nan fa
gida ya cika da jama'a duk da ba ta sami
natsuwar da zata aikawa da sauran
danginta da suke nesa ba,amman anyi mata kara iya mutuk'a" shi kuwa
MALAM tun bayan dawowarshi daga asibitin shima gida ya dawo ya shirya ya tafi
kauye su watau GULU domin sanar da yan uwanshi cewar ZAINAB ta haihu lfy, ko da
ya isa ya sanar musu da hakan sunyi matuk'ar farin ciki da jin yar tasu ta
sauka lfy,haka dai sukai ta aikawa 'yan uwansu
na kusa ana sanar dasu cewar ZAINAB ta haihu" MALAM AUDU bai baro
kauyesu ba sai da yayi duk wata shawara da yan uwanshi kan cewar INNA TALATU
ce zata zaunawa ZAINAB tai mata zaman da6aro" sakamakon ita
kade ce mace a gurin mahaifan su MALAM
AUDU" tana zaman gida ne sakamakon
rasuwar mijinta wannan hujjar ce tasa koda suka sanar mata da kudirin yayan
nata,batayi musu ba, batada miji bare ta
buk'aci jiran umarni" a yammacin ranar suka taho da yayan nata hadi da
kayan sha tara ta arziki wanda yan uwa da dangin suka hado aka fara yo gaba
dasu kamin su biyo bayan su kashe gari Domin ganin lfy maijego"
bayan saukar MALAM AUDU gida da shi da y'ar
uwanshi, gaisawa kawai tayi da matar yayan nata, tayi musu sallama da cewar ta tafi kula da
tafiyar yarta watau ZAINAB" zo kaga rawar kai gurin angon karni watau
RABI'U domin shima kayayayaki ya sayowa jaririyar da ZAINAB masu kyau da tsada,
sai shiga yake yana fita shima kamar bashine yake nuna halin ko in kula da
ZAINAB din ba"Ita kanta tayi mamakin yadda taga cikin k'ank'anin lkc mijin
nata ya sauya kamar bashi ba".
"Dangin mahaifinta dana mahaifiyarta duk
sunzo ganin lafiyarta kashe garin da ta haihu kamin yan suna su zo suna".
Haka
dai RABI'U yayi ta hidima shida
iyayenshi da sauran dangin da abokanan arziki" Suma a nasu 6angaren dangin
mijin na ZAINAB sunyi duk abinda ya dace sannan domin kuwa tunda suka dawo daga
asibiti lbr ya ishe sauran danginsu haka sukaita zuwa ganin jaririya da
kayayayyakin su na barka"Abufa yakai Abu domin kowa yasan mahaifan RABI'U
mutane ne masu kara da zuminci shi yasa duk wanda yaji matar d'ansu ta haihu
baya k'asa a gwuiwa sai yazo yaga lfy ZAINAB da 'yart haka dai 'yan uwa da
abokanan arziki sukai ta zuwa da abin
arzik'insu".
Acan ma
gidan su ZAINAB haka iyayenta da danginta suka kawo nasu kayan sha tara ta
arzik'in suka kawowa ZAINAB,"
"har
akai suna yarinyar taci suna MARIYATU sunan kakar RABI'U ce ta wajan uwa gidan
baya yankewa da jama'a wannan ce tasa RAB'IU ya mayar da hankalinshi sosai kan
ZAINAB da 'yarsu gudun kar aga wani bak'on yanayi daga gareshi lbr ya sami
iyayenshi wannan ce tasa ya mantar da ZAINAB duk wata cusgunawar da yayi mata a
baya"..............
No comments