KARUWAR GIDA 1
AMENAT KABER
KIRU
SADAUKARWA:
WANNAN
LITTAFIN SADAUKARWA NE GA HJY ZALIHA YOLA(MMN AHMED)
GODIYA
Duk kan godiya
ta tabbata ga ubangiji talikai wanda bai haifa ba kuma ba'a haifeshi ba,salati
da daukaka da aminci ka qarasu ga dan Amenatu manzo tsira wanda babu
tamkarshi,alaye da sahhaban gidanshi tsarkaka.
TSOKACI
wanna
labarin bai shafi wata ko wani ba na rubuta
shine domin gani yadda rayuwar mata ta sauya a wannan zamanin duba da yadda
kwadayi da son zuciya yayi yawa a zu'katan mu, ba nayi ne dan yad'a bad'ala
ba,a'a zanyi ne saboda na zakulo wasu halaye da suka shiga gidajen aure. Duk
wanda yaga abinda bai masa ba yana da kyau ya bude dogon shafin zagina
kofa a bude take domin karbar hakan daga
ko waye,zagi danzagawa ne nasan baya tabo🤷♂Azagi kowa normal ne🤪
PAGE🅾1⃣
Da sauri
Mariya ta juya ta kalli mahaifiyar ta wacce ta ke 'kokarin fita daga 'karamin
dakin nasu ta kira sunanta a hankali tace UMMA dan Allah ki saurareni
mana" kallon yar tata tayi galala wacce bata wuce shekara goma sha d'aya a
duniya ba, tare da fad'in ina jinki, nisawa tayi da cewar UMMA ina zaki tafi a
wannan daren ki barmu bai kamata ki tafi ki barni nida ANAS a wannan halin ba.
daka mata tsawa tayi hadi da cewar ni zakayiwa nasiha?" Girgiza kai MARIYA
tayi hadi da cewar A'a UMMA kawai naga tunda kika dawo dazu ko magani baki
bashi umarnin ya tashi yasha ba gashi zaki 'kara komawa..... katse y'artata ta
'karayi da cewar naji ke din tunda har kinfini sanin abinda ya dace ki tasheshi
ki bash mana. tana fad'in haka ta kad'a kanta tayi waje ko sauraren MARIYA bata
'karayiba duk da tasan MARIYA gaskiya ta gaya mata amman ta kasa tsayawa ga
yaran nata, ita kuwa tunda mahaifiyar tata ta fita ta koma kusa da inda kaninta
yake kwance ta dagoshi da cewar ANAS tashi kaci abinci ka sha magani,da kyar
yaron ya dago daga kwanciyar da yayi yace toh yaya, amman ina UMMA?"
Kwallace ta fito daga idon MARIYA sannan ta amsa da cewar ta sake fita yanzu,
kad'a kai kawai ANAS yayi duk da 'kan'kantar shi a matsayinshi na karamin yaro
yace kai UMMA kai UMMA mai kikeson zamane adacan idan ance UMMA zata iya fita
nan da k'ofar daki ta barmu zanyi mamaki amman yau mune UMMA take gudu a
matsayinta na mahaifiyar mu. kafin ya karasa maganarshi tuni kuka yaci
karfinshi daga shi har yar uwarshi watau MARIYA hakuri ta shiga bashi da
rarrashin qanin nata. Sai da sukayi kuka mai isa,sannan ta mik'e ta dauko
abinci ta Zuba musu, ta fita waje ta dauko roba da ruwa ta umarci kaninta daya
tara hannunshi ya wanke a cikin robar, bayan ya gama ta dauki robar da ruwan ta
fita dasu itama ta wanke nata hannu sanna ta dawo sukaci abinci tare"bayan
sun kammala ne ta dauko magungunanshi ta bare ko wanne ta bashi ta qara gyara
mishi gurin kwanciyarshi sannan ta fita ta dauro alwala ta dawo daki,tayi
sallah tare da kara gyara nata makwancin hadi da yin addu'a ta shafejikinta ta
kwanta amman ta kasa bacci sakamakon tunanin ina mahaifiyar tasu take zuwa babu
dare babu rana?" Juye juye tai tayi tana tunanin sauyin halayyar da suke
gani a tare da mahaifiyar su, A dan tsakanin nan. Sabida karancin shekarun
MARIYA bata iya gano amsar komai ba a haka dai taita juyi har mahaifinta ya shigo
jin shigowar tashine yasa ta mike tsaye zumbur daga kwanciyar da tayi hadi da
cewa sannu da dawowa ABBA" a ciki ya amsa hadi da cewar ina ZAINAB ta tafi ne?"bata damu da rashin nuna ko
in kula da mahifin nata yayi ba tace yanxu ta fita babu dadewa,kwafa yayi da
cewar toh,kawai ya nufa inda abinci yake
a ajjiye ya dauko ya ajje shi daga gefe hadi da umartar MARIYA data dauko mishi
abin zubawa"mikewa tayi ko tsoro bataji domin idan da sabo ta saba da
halin mahaifin nata,na rashin tausayi ko jin k'ai a garesu ita da qanninta fita
tayi ta hado komai tazo ta ajje masa komai sannan ta koma gefe ta zauna tana ta
kallonshi yana muzurai haka ya zuba abincin ya fara ci ko wanke hannu bai fita
yayi ba,ya fara ci kenan MARIYA tayi farat da cewar au ABBA na manta ban gaya
ma jikin ANAS ya kara tashi ba. Wurga mata ido yayi hadi da kai lomar hannunshi
baki yace toh sai akayi yaya? ZAINAB ce ta ce ki gayamin haka da zarar na fara cin abinci ko? dan ku hana zuciyata sukuni toh bari kiji
sabida ku wallahi bazan kashe kaina ba'" girgiza kai MARIYA tayi hadi da
cewar A'a ABBA, tare da matse kwallar da ta rufe idonta,tsawa yayi mata hadi da
nuna mata makwancita da ta tafi ta kwanta, tashi tayi a hankali ta nufi
shinfidar ta ta kwanta cikin kunar zuciya,da mamakin anya kuwa ABBA shine ya
haifesu ita da qaninta?AMMA ce mai tausaya musu tai musu komai amman yanxu
itama ta sauya a yan tsakanin nan bata san menene yake faruwa a tsakanin iyayen
nasu ba, a haka bacci yayi awan gaba da ita, Ita kuwa ZAINAB tun fitar ta bata
zame ko ina ba sai gidan kawarta Hajiya Rukaiyya tayi sallama tayi aka amsa
mata daga ciki ta karasa tayi sa'a Hajiya ta dawo ba kamar dazu da tazo tai ta
faman jiranta bata dawo ba,da fara'a Hajiya Rkaiyya ta karbi ZAINAB da cewar
kawata kece a yanzu haka?"amsawa ZAINAB tayi hadi da zama kan daya daga
cikin kujerun falon, kawata da cewar ai
nazo daxu bakya gida UMAR bai gaya miki ba?" Har yace bakiyi nisa
ba"nan nayi ta zaman jiranki da naga rana tayi sosai shine na koma gida na
daurawa yara abinci na danyi aikace_aikacen gida, yanzu ma harsashe nayi da
cewar duk inda kika tafi kin dawo gida tunda yace ance min ba dadewa zakiyi
ba,dariya Hajiya Rukaiyya tayi da cewar hakane qawata kuma da na dawo nayi
kamar nima na bi ta gidan naki sai kuma dai naji nagaji na bari da safe kamin
na fita na shigo ta gidan na duba ANAS da jiki, murmushi ZAINAB tayi da cewar
ai yanxu ma matsalar jinkin nashice ta tasoni shine nazo na sanar miki hadi da
qarin neman taimakonki akan dan Allah qawata ki tallafi rayuwata ki qara
taimakamin da aron kudi zan kaishi asibiti, murmushi Rukaiyya tayi da cewar ai
kawata tunda na ganki a wannan lkc nasan damuwa ce ta kawo ki gareni Amman dan
Allah ina RABI'U yake ne da yabarki kike ta fakan2 din neman kudin kai yaro
asibiti? "Murmushi ZAINAB tayi da cewar ai tunda ya fita sallah asuba bai
kara dawowa gidan ba har na fito din na" nisawa Hajiya Rukaiyya tayi da
cewar gaskiya ZAINAB baza rufeki ba kin sakarwa mijin ki fuska da yawa har ya
samu damar wulakantaki haka, amman babu komai sai ki cigaba da hakuri da shi
haka nan tunda da yara a tsakanin ku, mikewa tayi daga falon ta shiga dakinta,
ta dauko naira dubu biyu ta mikawa ZAINAB tace mata gashi ba ranta miki nayi
ba, zanzo muje asibitin tare da safe sai muga yadda Allah zaiyi ko kawata"
toh ZAINABA tacewa Hajiya Rukaiyya" ta amsa da babu komai amman yana da
kyau kije ki sanarwa da iyayen ku halin da kike ciki keda mijinki,shawara na
baki bawai dan na gajiya da baki wani abu nawa ba,toh ZAINAB taqara cewa
qawarta hadi da yi mata godiya sukayi
sallama ta kamo hanya tayo gida.Koda tazo kofar
gidanta sai ta tarar har mijinta ya rufe kofar gida nan ta hau bugun
kofa, takai kimamin mitin talatin tana bugun kofar kamin yazo ya bude mata a
fusace ya bude yana faman hucin da cewar daga ina kike,?" Shiru ZAINAB tayi
kamar bata ji ba ta wuce ta barshi a tsaye
ta shige ciki abinta" mayar da kofar yayi shima ya rufe ya bi
bayanta hadi da kara tambayar ta daga ina take?" Amman shiru jin bata da
niyyar amsawa yasa shi ya kara bude murya ya shiga zazzaga masifa a wannan dare ko kallonshi batayi ba bare ta tanka
mishi haka dai yai ta zagi da gori da jifanta da bakaken maganganu amman tayi
shiru, ta shiga daki ta cire hijab dinta sai kuwa ya hango k'yalin kudi nan fa
ya kara gyara sai ya shiga rarrashita da cewar ai baki gaya min zaki fita bane
shine dalilina, na yi miki fada amman kiyi hakuri ZAINABUWATA ai nasan bazaki
wuce gidan Hajiya Rukaiyya ba toh ya kika barta?" Shiru ZAINAB tayi kamar
bataji abinda yace ba hadi da waye kudin ta dauresu a ha6ar zaninta sanna ta
nufi gado ta kwanta, biyo bayanta yayi shima ya kwanta gefe, yana jiran yaji
abinda zata ce masa amman shiru, tashi yayi ya cire kayanshi ya dauko wata
dukunku_nanniyar jallabiya ya saka kana ya qara hayowa gadon ya kwanta yana
faman huci," haushine ya kara kama ZAINAB ta kara juya mishi baya ta kama
bacci, bata farka ba sai ji tayi zakara na chara, sauri tayi ta mike tsaye tayi
waje ta dauro alwala tayi sallah shi kuwa gogan naka ai bata farka ta ganshi a
d'akin ba tuni ya fice, tashin MARIYA tayi dacewar taje tayo alwala, da sauri
MARIYA ta mike ta bi umarnin mahaifiyar tata da cewar to" tayi waje ta
d'auro alwala tazo tayi sallah.
Bayan ta idar ta gaishe da mahaifiyar tata
" amsawa ZAINAB tayi cikin kulawa tace mata lfy qlu" mamaki ne ya
kama MARIYA duba da yadda taga mahifiyar tata kwana biyu bata sakar musu fuska
sai tayi tsammanin ko wani abu tayi mata," murmushi ZAINAB tayi ganin
yadda yar tata har ta saki jikinta a wannan lkc, ta qara muskutawa gefe ta
kwanto zanninta da zata bawa MARIYA kudin da tasamu jiya ta sayo musu gasarar
koko a ciki ta shafa babu su,ta juya ta koma kan gadon bata ji su ba, shiru ta
yi hadi da zubar hawaye da sauri ta goge kar MARIYA tagani,duk da haka yarinyar
ta fuskancin chanji da tagani daga mahaifiyar tata, sai tace mata UMMA tunda
bakiga kudin ba ai ABBA ya rage abinci jiya ki barshi kawai maci haka. Toh
kawai ZAINAB tace ta koma gun da ANAS yake kwance ta daga shi tayi waje dashi
ta sashi yayi fitsari kana ta wanke masa bakinshi ta dawo dashi daki ta fita ta
hada wuta ta dumama musu abincin sanna ta daura musu ruwan wanka. Bayan sun
gama cin abin tayiwa ANAS wanka ta hadawa MARIYA nata ruwan wanka ta
kaimata" sanna ta dawo ta gyara ko ina sanna ta debi nata ruwan
wanka" tana fitowa sai ga kawarta Hajiya Rukaiyya ta karaso gidan kamar
yadda ta al'qarta mata, tana shiga MARIYA
ta gaisheta,Sai ta tashi ta fita
tsakar gida, tabar mahaifiyar tata suna
gaisawa da kawarta,bayan sun gaisa ta
tambayeta jikin ANAS ta amsa da yaji sauki,can tace toh ki shirya muje asibitin
ko, shiru ZAINAB tayiwa Hajiya Rukaiyya hadi da zubda kwallah tace ai babu
damar zuwa" amsawa Hajiya Rukaiyy Tayi da cewar kamar yaya, RABI'U ne ya
hanaki zuwa kai yaron asibiti?" Girgiza kai ZAINAB tayi da cewar
A'a,mamaki ne ya kama Hajiya Raukaiyya tace toh menene?" Amsawa ZAINAB
tayi da cewar ai ya sace kudin da kika bani jiya" ta6e baki Hajiya
Rukaiyya tayi tana mamakin wanne irin sauyin yanayin ne yazowa ZAINAB
haka?" Ace mijinta shine yake neman tagaiyyarata ci gaba tayi da tafe
hannu tayi ta kara tambayar ZAINAB sata fa?" Daga mata kai ZAINAB kawai
tayi, ta cigaba da kukan da takeyi duk maganar da sukeyi MARIYA na tsakar gida
tana jinsu,a sanyaye itama Hajiya Rukaiyya tacewa ZAINAB toh kiyi hakuri ki
barshi kizo mu tafi kawai mu kaishi ai baza'abar yaro hakaba" toh ZAINAB tace ta dauko hijjab hadi da
rungumo ANAS ta rufo kofar dakin nata"suka rankayo har MARIYA sai da ta
sakashi cikin motar kawar tata, sannan ta juya tace mata bari nayiwa
makofciyata sallama" toh Hajiya Rukaiiya tace mata kawai ta bude mota ta
shiga tana jiranta" , juyawa tayi da saurinta ta cewa MARIYA muje gidan su Haiidar ko nayi musu
sallama,ta shiga ta bayar da ajjiyar MARIYA hadi da yi musu sallama,ta dawo ta
bude motar kawar tata ta shiga,ita kuma taja mota suka dauki hanyar asibiti, sai
da sukayi nisa sannan Hajiya Rukaiyya ta dan nisa ta kalli ZAINAB da cewar wai
yaran nan duk sun daina zuwa Makaranta ne?"murmushi ZAINAB tayi da cewar
yace bazai iya biya musu kudin makarantar ba, ta gwamnati ya mayar dasu,ita
madin ya daina biyan komai nasu nice nake biya toh nima yanxu ta ritso banida
kudin shine dalilin da yasa basa Makaranta,wallahi kawata banida jari jarina
duk ya kare banida yadda zanyi,shine dalili, ko jiya da kikayimin maganar na
saka manya cikin maganata da babansu nayi nayi,abin yakiyi Ke kisan yadda nake
da shi a dacan ban taba tsamanin zai min
abinda yake min a yanzu ba, daga ni har yarana,amman babu yadda zanyi da
halayyar da ya sauya min, naje na sami iyayenshi akan suyi masa fada,wallahi
goya masa baya ma sukayi da cewar ai bashida sarari wanda ni nasan ba haka bane
son zuciya ne irin na wasu iyayen mijin, da na dawo na sake yanke sahwarar naje
na sanarwa da nawa iyayyen domin su shigo cikin lamarina amman abin duk yaci
tura sun kirashi dan jin abinda nake masa yace babu komai, anyi mana fada gaba
daya kamar zai gyara amman ya sake komawa kan halinshi wallahi kawata yanxu
tsakanina da BABAN ANAS babu abinda ya sani nawa sai bukatarshi zuwa
gareni,kinga kuwa dole zan fita hayyaci na,duk lokacin da naje gida hakuri ake
bani, ace na dawo kan yarana ,nima duk lkc da so mu rabu idon yaran nake kallah
sai naji na kasa tabuka komai a kanshi Amman yanxu tausayin yaran ya fara
gushewa daga zuciyata domin bansan me zanyi ba, matukar hakan ba hakuri ne
ba,kawata" nisawa hajiya Rukaiyya tayi da cewar kawata babu komai kedai ki
cigaba da hakurin da ake cewa kiyi ai baya karewa, shiru ZAINAB tayi hadi da
goge kwallar da ta cika mata ido ta amsa da cewa insha Allah kawata zanyi komai
kike cemin,a haka dai suka cigaba da tafiya har suka zo dai_dai inda danja ta
tsayar dasu suka tsaya nan fa ZAINAB ta dan bude glass din gefenta sakamakon
dan zafin da aka fara na dagawar hantsi tana budewa taji ana kiran Sunanta daga
motar da take gefenta takara lek'o da kanta tayi domin ta tabbatar ita din ake kira
ko wa? Tana dubawa sai ta hango mai kiran nata hakan yayi dai2 da basu hannu da
danger tayi domin su wuce, da sauri ta cewa Hajiya Rukaiyya kisan mai kirana
kuwa?"A'a tace mata hadi da cigaba da tukin motarta tana kallon
gabanta,"ZAINAB tace ai HAFSAT AL'AMEN ce a motar, kaminta karasa maganar
tuni ta zo saitunsu ta yi ma Hajiya Rukaiyya nuni da su sami guri suyi parking
nan fa suka dan tsaya a gefen hanya suka gaisa hadi da tambayar su ina
zasu?"ZAINAB ce ta amsa mata da cewar zamuje kai yaron wajena asibiti
ne"da sauri HAFSTA ta leqa sit din dake baya motar ta gano ANAS da yake a
kwance yana ta faman bacci, kallo daya HAFSAT tayiwa ZAINAB ta tabbatar ko
ba'ace mata komai kanta ba tasan tana cikin wani hali komawa tayi cikin tata
motar ta dauko jakar hannuta ta bude ta debo kudi masu yawa ta mikawa ZAINAB
hadi da kara jajanta mata rashin tafiyar ANAS din godiya tayi mata, a lokacin
Hajiya Rukaiyya itama ta kara saka baki a maganar tasu tayiwa HAFSAT godiya,
har sun juya zasu koma mota ta kira sunan ZAINAB hadi da tambayar ta number
wayarta tace ko dan sanin halin da kike ciki Sosa k'eya ZAINAB tayi da cewar ai
banida waya a hannu na yanxu,mamakine ya kara kama HAFSAT da cewar toh bari na
baki card dina duk duk lkc da kika sami dama sai ki kirani ta miqa mata, ZAINAB
ta karba ta rike hadi da kara yi mata godiya, sukayi sallama ta shiga motar ta
suma suka koma tasu suka dauki hanyarsu ta zuwa asibiti. Basu wani kara bata
lkc ba suka karasa wani karamin clinic wanda suka shiga suka karbi kati a inda
suka wuce sunga likita ya duba ANAS da kyau inda ya sanar musu cewar ba wani
ciwo ne mai tsanani ba, garkuwar
jikinshi ce tayi laushi sakamakon rashin samun wadatacan abinci mai gina jiki,
hakan shine yasa yake yawan zazzabi mai zafi, cikin kwarewa Dr ya rubuta musu
magunguna karin jini da na cin abinci da basu shawara akan su ringa bashi
abinci mai gina jiki,suka amsa hadi da yiwa Dr godiya suka fito gurin zama
Hajiya Rukaiya ta nuna ma ZAINAB da cewar ta zauna ta jirata taje ta sayo
magungunan da Dr yayi umarnin su saya......
Comments
dinku shi zai sa insan kuna son Inci gaba da rubuta muku wannan labarin
No comments