BARIKI NA FITO (BOOK 2) 9
BOOK 2
Bariki bata
farka ba sai da asuba, jin kiraye kirayen sallah shine yasa ta farka, kuma bata
tashi da ciwon kai dinba, tashi tayi ta fad'a toilet, alwala tayi tazo tayi
sallah, tare da ro'kan Allah akan ya shiga lamarinta......
Koda ta idar kasa komawa bacci tayi sai
kayanta na sawa data fara sawa cikin karamin akwatinta domin zuwa wajan
iyayenta na bariki danta d'an Fara kwana a can, gashi yarima yace ta koma yau
dinma.
Bayan ta
d'iba kayanta na kwana biyar tasa cikin akwati ta rufe tare da ajiye akwatin a
gefe, kwanciya ta koma amma ta kasa bacci domin ba komai take ba sai tunani, a
duk lokacin da taso ta fad'ama Yarima gaskiya saita kasa, sai kuka yazo mata in
tayi kokarin ta daure ta fad'a mishi saiya kashe mata Giwa da fad'in bazai auri
mazinaciya ba... Wani hawaye ne ya zubo
mata Mai zafi, Tana son Yarima bata son rasa shi, lallai Indai tana son samun
Yarima a matsayin miji shine ta boye mishi labarinta har abada..... Da sauri ta girgiza kai tare da fad'in labari
na bazai taba boyuwa ba domin komin daran dad'ewa sai gaskiya ya fito, lallai
fad'ama Yarima gaskiya shine mafita amma sai bayan na aureshi, zanyi kokarin in
fad'a mishi gaskiya ranan daya aureni Nasan May be yayi min uzuri, tunda ba
haka nake ba, kaddara ce ta fad'amin wanda nida kaina bazan iya cewa ga abunda
ya faru ba, koda za'a samun wuka a wuya ban San yanda Abun ya faru ba......
***
Haulat ce
take jan akwatinta daka gani tafiya za tayi....
Hjy habiba
tana bayanta tana fad'in yanzu sai yaushe kuma?
Haulat tace
mum sai dai munyi waya, kawai
Farhan ne ya
fito tare da fad'in muje in kaiki train station.....
Hjy habiba
tace farhan ka Bari driver ya kaita mana,
Yace no mum
Bari in sauketa
Babu yanda
hjy habiba ta iya, dole farhan da haulat suka fita.
Haulat na
gaba farhan na mazaunin driver, ta kalli farhan tace plz mu biya ta gidan Hjy
Umaima zan amsa sa'ko.......
Farhan yace
ok, amma zaki missing train din 8, sai na 10 zaki hau,
Tace babu
damuwa
Juya motar
yayi sukai gidan Hjy Umaima, haulat ce kad'ai ta shiga..... Ta d'an jima Sosai ban San mai suka tattauna
ba sai gata ta fito ta shiga motar ta kalli farhan tana y'ar murmushi wanda
shima din ita yake kallo tace muje.....
Mai yakon
suje din saiya kama hannun Haulat yana fad'in haulat dagaske aure za kiyi????
Tace aure
kuma? A'a
D'an shuru
yayi yana nazari, toh tace a'a Bayan mum dinshi tace aure za'a Mata.....
Katse Mai
tunani haulat tayi da fad'in, farhan zanyi aure Indai na samu Mai sona kuma
wanda nake so, da an taba son had'ani da wani Wanda bana so..... Wanda shine silan fad'awa ta cikin
k...... Da sauri tayi shuru domin taso
tayi baran barama.
Farhan yace
inaji haulat
Tace andai
fasa auren nawa
Wani irin
ajiyan zuciya farhan ya sauke, tare da kallonta cikin ido yace haulat zaki aureni???
Da sauri ta
kura Mai ido, tare dajin bugun zuciya, lallai farhan ya had'u ba tun yau take
sonshi ba, tunda ta Fara ganinshi, domin yanda yake nuna mata kulawa, wanda ko
wace mace tana son taga ana nuna mata caring..... Sau da yawa rashin nuna halin ko in kula da
maza suke nuna ma matansu suke sa su Fara neman mata y'an uwansu, misali namiji
ya fita office, ko kasuwa, kodai wajan da yake Sana'a, bazai kiraki ba, may be
in kin kirashi bazai d'auka ba, namiji inya auri mace babu kalaman love duk sai
ya daina, in baki da lafiya babu sannu koya jiki, inya biya kud'in magani
shikenan, maza kuma kuna da laifi Sosai wajan fadawan wasu matan halaka, mace
tana son Mai kula da ita Sosai, yau koda auren dole akama mace bata son
miji..... Indai yana kyautata mata wlh
sai kuga ta Fara sonshi..... Amma kai
miji babu kyautatawa daga tayi abu sai hantara...... Idan tana da k'awa taga tana kyautata mata in
bata da lafiya, bini bini ta kirata tana ya jiki kaza da kaza, in kawar Tana
bin mata haka zatai ta janta a jiki in aka samu Mai raunin imani ganin yanda
kawar tata take mata inta fito mata da kudirinta saita yarda ta amince
Mata...... Wlh maza kuma kuna da laifi
Sosai, damme bazaka dunga nuna ma matarka soyayya da kulawa ba,bayan aure
shikenan daka anyi aure sai a fara d'aure fuska haba haba maza ya kuke haka,
sannan saika gama d'aure fuska in dare yayi ka lallabo kana Kai hannu ko kunya
babu😏........
Farhan ne ya Katse ma haulat tunani da
fad'in.... Haulat why r you silent and stare at me lyk this????
Murmushi
tayi tare da fad'in nothing, kawai Ina mamakin abunda kace ne......
Farhan yace
mamaki kuma? Kodai bazan samu karbuwa bane? Haulat tun ranan dana ganki Allah
yasa min sonki, Wlh haulat so nake na aureki inhar kin amince Kece mace ta
farko dana Fara ji ina burin in aura.......
Haulat wani
irin murmushi ta saki tare da fad'in farhan zanyi tunani akai, yanzu dai muje
train station Kar in makara.....
Tada motar
yayi suka wuce kabuwa station, koda suka je saida suka zauna bayan yasai mata
ticket, zama sukayi suna jiran lokaci,
Haulat ba
komai take tunani ba, sai abunda suke aikatawa da hjy habiba, Uwar farhan gashi
d'anta yau yace yana Sonta, in kuma tace bata son farhan tayi karya, tashin
hankali uwa da d'a....... Ido ta lumshe
tare da fad'in Anya wannan abun zaiyi kuwa? Maganan farhan bai kamata in
daukeshi da muhimmanci ba, domin ba Abu bane mai yihuwa naga tsiraicin mum
dinshi na cita..... Yanzu kuma sai kawai inzo in auri d'anta Kai no way.......
Farhan ne ya
Katseta tare da fad'in when zaki dawo? Koni inzo kaduna?
Dariya tayi
tare da fad'in mudai yi waya kawai..... Dai dai lokacin aka fara fad'in su
tashi train yazo.....
Tashi haulat
tayi tana kallon farhan tare da fad'in sai munyi waya
Kai ya d'aga
alaman ok tare da bata Wani karamin Leda daya ciro cikin aljihun shi,
Amsa tayi
tana fad'in ngd tare da tafiya..... Koda haulat ta shiga jirgi tunanin farhan
tai tayi wanda ta rasa dalili........ Bud'e ledan daya bata tayi taga wani
kwali karami anyi raping dinshi bud'ewa tayi taga wani zoban zinari Mai shegen
kyau, bata san lokacin data saki murmushi ba........
***
Yarima Aliyu
ne zaune gaban iyayenshi yana mi'ka musu gaisuwa, mai martaba yace yaushe zaka
Fara aiki a asibitin ka?
Yarima Aliyu
yace Abba duk sanda ka bani umarni Niko yau zan iya Fara aiki....
Mai martaba
yayi murmushi domin duk cikin yaranshi babu wanda yake so kaman Aliyu bawai dan
yana d'a namiji ba kawai, a'ah harda irin biyayyan da yake mishi... Mai martaba
yace saika shirya cikin satin nan ka Fara
sannan akwai wani fili da nake dashi a u/sarki saika Fara ginawa tunda a
can zaka Fara aiki, Nasan wata rana iyalanka zasu bika can din in aiki yayi
yawa .......
Mum din
Yarima tace Kai Masha Allah, ina taya Yarima godiya
Mai martaba
murmushi yayi tare da fad'in kin ara bakinshi kenan kinci Mai Albasa
Yarima yace
Abba na gode Sosai Allah ya kara girma, Allah ya biya dan gidan Aljanna
Mai martaba
ya amsa da Ameen tare da fad'in waziri zai baka takardun filin sannan zai nuna
maka filin,
Mum dinshi
tace sai ka Fara ginin mata biyu koh?
Yarima kasa
magana yayi, sai mai martaba da yace ginin mata biyu kuma? Aure yace miki zai
K'ara?.....
Mum tace eh
gashi nan ya fad'a maka da bakinshi....
Mai martaba
ya kalli Yarima Aliyu tare da fad'in ina jinka??
Yarima ya
fara magana da fad'in Abba dama dama akwai dama....
Murmushi mai
martaba yayi tare da fad'in dama me?
Gaba d'aya ka kasa magana, mai martaba yaci gaba da fad'in Aliyu inaso
ka sani bazan hanaka k'arin aure ba, amma sai dai Ina Mai baka shawara kayi
hakuri nan gaba domin baka dad'e dayin aure ba ko sati d'aya bakayi dayin aure
ba, inaso kayi hakuri nan gaba kad'an sai a taso da maganan auren da kake son
yi, amma fah shawara ce ba umarni ba.....
Yarima Aliyu
yace Abba umarni ko shawara duk abunda kace min a matsayin umarni yake a
wajena.... Abba kayi hakuri a kullum nafi son kaban umarni domin Ina Mai
biyayya ga duk wani abunda kacemin
Mai martaba
yace Allah yayi maka albarka, kaima Allah ya baka masu yi maka biyayya
Yarima ya
amsa da Ameen Abba,
Mai martaba
yace yarinyar y'ar inace????
Yace Abba a
cikin kaduna suke, a u/kanawa ,sannan Abba mahaifinta bamai karfi bane....
Mai martaba
yace babu damuwa, ya tarbiyan gidan yake??
Yace Abba
Alhmdlh gidan akwai tarbiya domin yarinyar yau kwana hud'u data sauke
AL'QUR'ANI Mai girma kuma hadda....
Mai martaba
yace Alhmdlh, lallai gidan akwai tarbiya, Allah yasa na tsoran Allah ne sannan
duk Wanda yake da ilimin addini yaji dad'in duniya da lahira zai iya zama da
kowa, dukiya ko mukami bashi bane Abun dubawa tarbiya itace Abun dubawa, kaje
zansa Ayi bincike akan gidansu......
Yarima tashi
yayi yana mai yima mahaifin nashi godiya sannan ya fita cikin murna yana K'ara
godema Allah da har mahaifinshi ya yarda yanzu tunda Mai martaba ya amince toh
ya Gama samun Zainab insha Allah, lallai Allah Abun godiya bai taba tunanin zai
samu amincewan mahaifin nashi cikin sauri haka ba...... Gefenshi ya nufa na da, koda ya shiga rufewa
yayi tare da nufa bedroom dinshi ya fara kallon hotunan Zainab din, Wanda ya
zana, tunani ya farayi Mai Zainab take son fad'a mishi wanda take tsoron
fad'a??? Kodai in tambayi habib?? Nop
bai kamata ba ita ya kamata ta fad'amin koma miye, and d way yanda take kuka
yana nunamin abunda take son fad'a Kaman ya shafi rayuwanta? Toh mai take son
fad'amin ido ya lumshe yana tunani.....
Na farko dai bata da wani aibu balle yace ga abunda take kokarin
fad'amai, to Mai Zainab take boyemai??.......
Kai ban tunanin abun serious ne inda serious ne data fad'amin.... Wata zuciyar tace mishi kaika sani ko nauyin
Abunne yasa ta kasa fad'ama? And kuma Inba serious bane mai yasa take kuka haka
in tayi kokarin fad'a Mai? Ganin duk iya tunanin da yayi ya kasa gano komai
yasa ya cire abun a ranshi tare da fad'in koma miye Indai Mai muhimmanci ne zai
sani, yanzu dai ya kamata in mata surprise inje in ganta....
Bariki na
kwance taji ana mata nocking, tashi tayi ta bud'e kofar da sauri ta saki kara
tare da rungume haulat Tana fad'in mutanan abuja sai yau, ko waya babu.....
Dariya
haulat tayi tare da fad'in kiyi hakuri bariki Wlh wayata ce ta fad'i bani da
number d'inki yanzu, sai yasa ina dira kaduna Wajanki na fara zuwa Kinga ko
d'akina banje na ajiye akwati ba nazo Wajanki.....
Bariki tace
shigo mana
Haulat shiga
tayi tare da zama tana fad'in Kai nasha abuja
Bariki tace
gashi kin kara kyau da k'iba kaman bake ba, kai zama waje d'aya yayi
Murmushi
Haulat tayi tare da fad'in dan bani wayarki in tura hotuna na tare da number
d'inki, banda pic dina dake ko d'aya a phone dina
Bariki mi'ka
mata wayar tayi tare da fad'in yunwa nake ji wlh Bari in duba habib
Haulat tace
ok, haulat ta d'auki abunda take so cikin wayar bariki, sannan tayi murna da
abunda ta samu a game da bariki din......
Bariki bata
dad'e Sosai ba ta dawo, cikin d'akin tare da fad'in habib ya cika yawo kaman
yaci kafan Kare.... D'aukan iPhone dinta
tayi ta Fara kiran habib harya tsinke bai d'auka ba......
Haulat tace
ashe kinyi iPhone ga Samsung ga iPhone gskiya bariki kina jin dad'i.... Tashi
haulat tayi tare da mi'ka ma bariki wayarta Tana fad'in Bari inje inyi wanka in
huta anjima nazo
Bariki tace
ok but nima zanyi tafiya sai dai munyi waya
Haulat tace
ok tana murmushi ta fita
Bariki ganin
data dinta a bud'e yasa ta shiga whatsapp da message keta faman shigowa ganin
Alh madu ya mata message yasa ta bud'e nashi ganin hotunan daya d'aukesu
tayi, tsaki taja tare da shiga gallery
ta goge dan in an turo Mata hoto shida kanshi yake bud'ewa bata rufe ba, harda
na Hon salis duk ta goge su Wanda ya tura mata kwanaki, duk wani hoto data
d'auka wanda bai dace ba ta goge a cikin wayarta...... Kiran Alh madu ne ya
shigo cikin wayarta kaman Karta d'auka saita tuna da hotunan daya turo Mata Wanda
hakan ya tabbatar mata yana son Mata wani tuggu sai yasa ta d'auka tare da
fad'in lafiya?
Dariya yayi
tare da fad'in hotunan sun d'auku da kyau koh?
Tace tir da
hali irin naka
Yace na baki
awa biyu kizo inda nake ko yanzu ki ganki a internet ansa hotunan da mukayi
kuma da fuskan wani ba nawa ba danna biya kud'i anyi min aikin , babu wanda zai
gane an canza fuskan domin kwararru sukamin aikin kuma ba y'an kasar nan
bane.....
Bariki k'asa
tayi tana hawaye wayar ta sulale a hannunta......
MARYAM OBAM
No comments