BARIKI NA FITO (BOOK 2) 8
BOOK 2
Bariki
dariya tayi, tana mamakin irin kishin Yarima Aliyu, gashi baya iya boye kishin
shi, dole saiya fito dashi......
Katse mata
tunani yayi da fad'in dariya koh??
Tace a'a
Yarima kawai naga kana tunanin daba haka bane....
.
Yace miye ba
haka bane? Tell me, tunda kika fito zaki cemin maza basu kalleki ba??
Tace Yarima
yanzu fah dare ne Waye zai kalleni? Inba Kai ba.
Murmushi
yayi tare da girgiza kai yace my princess you r too much kin iya Kare
kanki..... Anyway yaushe kike son Ayi bikin mu?? Domin Idan Mai martaba ya turo
lokaci kad'an za'a sa.
Bariki rufe
fuskanta tayi cikin jin kunya tace Yarima BANDA ZABI sai abunda su Abba
sukace.....
Yarima Aliyu
yace hakane but Nasan Kema kina da lokacin da kike so ayi in muka shirya basai
mu fad'a ba!?
Tace hakane
Yarima yace
ni ko yanzu aka bani zan tafi dake.....
Ido ta zaro
lokaci d'aya kuma ta saki dariya Sosai, tace Yarima ni nafi son yakai Nanda
shekara d'aya.....
Da sauri
Yarima yace what?? Amma dai you are joking koh? Ni bamma tunanin yakai nan da
wata d'aya....
Bariki tace
Yarima watsa d'aya yayi wuri, ni Ina tunanin nan da wata uku....
Yarima yace
hakan yayi miki???
Kai ta d'aga
alaman eh, domin Kafin nan ta Gama istabra'i sannan zata samu lokacin gyara
kanta Sosai duk da tasan komai tayi bazata dawo budurwa ba, amma zata gwada duk
wani kayan gyaran jiki danta d'an gyara kanta.....
Katse mata
tunani yayi da fad'in gobe ki koma Gida Zanzo in ganki a can da rana insha
Allah,
Tace Yarima
gobe kuma?
Yace yes ko
you don't want to see me ne?
Da sauri
tace a'a kawai naga kullum sai kazo, baka zama ga amarya a gida, inaga ya
kamata ka zauna ka bata hakkinta, da lokacinka
Yarima yace
ok hakane, zan zauna bazan zoba har sai kin nemeni, sannan ita amarya Ai tare
muke kwana da ita.....
Ganin yanda
ta canza fuska yasa yayi murmushi danya Lura taji haushin magananshi ne.....
Kamo
hannunta yayi tare da matse su duka biyun, yace my princess I love you so much,
plz ki dinga kulan min da kanki Sosai...
Kallonshi
tayi ganin shima ita yake kallo yasa tayi k'asa da kanta, cikin sanyin murya
tace Yarima....... Shuru kuma tayi tana jin nauyin abunda zata fad'a.....
Yarima Aliyu
yace ina jinki my princess.....
Hawaye ne ya
zubo mata Mai zafi da sauri tayi k'asa da kanta dan karya gane tunda hannunta
na nashi hannun..... Cikin rawan murya
tace Yarima Idan ka aureni kaji ba yanda kake expecting ba zaka iya saki na????
Yace ban
fahimta ba?? Mai kike nufi?
Tace Yarima
Ina nufin Bayan auren mu kaji ba yanda nake ba I mean..... Shuru kuma tayi lokaci d'aya tasa kuka mai
sauti........
Yarima ido
ya kura mata cikin rud'ani...... Tare da tunanin mai take son fad'a mishi
haka???? Ganin kukan nata na k'aruwa yasa ya fara share mata hawaye cikin
tausayinta....... Ya fara magana kamar
haka Zainab Ina son ki fad'amin abunda yake damunki ko miye I will accept you a
yanda kike, ina miki so dani kaina ban taba tunanin zanyi ma d'iya mace irin
wannan son ba, tell me maike damunki????
Kasa magana
tayi sai kuka da take ta faman saki cikin tashin hankali da damuwa,....
Yarima kam
ido ya kura mata ganin taki magana sai kuka,... Yace Zainab kodai kina pretending ne bakya
so na.......
Da sauri
tace a'ah Yarima Ina Sonka, kaine rayuwa na, Ina maka son da baki bazai iya
fad'anshi ba, sonda nake maka sai yasa nake tsoran fad'a maka abunda nake son
fad'ama a halin yanzu saboda ban San yanda zaka d'auki abun ba......
Katseta yayi
tare da fad'in Zainab tell me?? Fad'amin Mai yake faruwa?? ......plz Zainab
tell me abunda yake damunki kin sani cikin damuwa......
Kuka take
Sosai lokaci d'aya ta fad'a jikinshi ba komai take son fad'a mishi ba sai
rayuwarta wanda tsoro da fargaban abunda zai biyo baya yasa ta kasa fad'a mishi
sai kuka tare da nadama
Yarima tunda
ta fad'a jikinshi ya kasa furta koda kalma d'aya ne sai Shafa mata baya da
yakeyi tare da tunani Kala Kala akan Mai take son fad'a mishi?? Lallai akwai
wani abu mai muhimmanci daya danganci rayuwarta da take fargaban fad'a mishi,
to miye abun??? I need to knw, tunanin
baya ya farayi tasha son fad'a mishi magana amma saita kasa, lallai akwai wani
abu a tare da ita toh miye wannan abun?? I have to find out........
D'agota yayi
tare da fad'in Zainab kukan ya isa haka, what I want you to knw is dat Ina
sonki I cnt live without you......
Zainab tun a mafarki Allah ya had'ani dake har na had'u dake a zahiri,
ina son ki sani had'uwa na dake had'in Allah ne, na Fara sonki tun Kafin inga
Fuskanki, ina son ki sani bawai saboda kyanki ko wani abu nake sonki ba a'a
kamalanki da mutunci da yanda kike suturta jikinki yasa na kara sonki koda na
had'u dake...... So Zainab dnt be afraid
to tell me what in ur mind..... Zainab
Abu d'aya zaki aikata in barki duk irin sonda nake miki domin bazan iya juraba
dan Indai zan ganki Abun zan dinga tunawa shine ZINA duk da Nasan rasaki a
rayuwa ta kaman baraza na ne a tare da rayuwa na, bana tunanin koda a mafarki
Zaki iya aikata hakan, ina matukar kishinki Sosai harta habib da kike mu'amala
dashi hakuri nakeyi badan ina so ba, tunda kince kaman dan uwanku ne, ban son
inga wani abu yazo inda kike Inba niba........
Ido ya kura mata tare da fad'in tell me wht on ur mind I need to
knw......
Bariki
jikinta yayi matukar sanyi Sosai lallai Yarima in yasan wacece ita ya barta har
abada..... Tsayawa tayi da kukan amma hawaye na zuban Mata a ido Sosai amma
yata iya tata kaddaran kenan dole ta fad'a mishi gaskiya domin hakan shine zai
sa ta sami salama duk da itama ba zata iya juran rashin Yarima Aliyu a rayuwarta
ba, domin so ya mata shigar sauri sonshi ya shigeta Sosai wanda bata san
lokacin da hakan ya faru ba.......
Katse mata
tunani yayi tare da fad'in Zainab tell me plz....
Shuru tayi
tana kokarin yin magana amma ta kasa domin muryanta ya dashe......
Ganin haka
yasa Yarima fad'in kiyi shuru kibar wannan kukan plz Kinji my princess?
Kaita d'aga
mishi alaman toh
Yarima Aliyu
idonshi na kanta ya tabbata akwai abunda take boye Mai, but koma miye zai
sani..... Ganin tasa hannu a kanta alaman yana mata ciwo yasa yace my princess
ciwo Kai din yake miki?
Kaita kara
d'aga Mai alaman eh , bud'e kofar motar yayi ya shiga wajan driver ya kunna
motar,
Da sauri ta
d'ago ta kalleshi ganin yaja motar yasa ta kura mishi ido, taga Ina zashi da
ita...... Karan wayanshi ne yasa ta dawo
daka duniyar tunanin data fad'a
D'auka yayi
tare da fad'in USMAN sorry yanzu zamu dawo, zan kaita pharmacy ne a bata magani
she has a headache..... Yana fad'in haka
ya kashe tare da fad'in Ameen
Yarima cikin
gari suka shiga inda aka bama Zainab magani, tare da sai mata kayan fruit
sannan suka kamo hanya, bayan sun karaso
Bariki suka gaisa da USMAN sannan Yarima yayi mata sallama akan taje tasha
magani, ta kwanta ta huta sai sunyi waya......
Bariki
gidanta take ta koma ta shiga d'akinta ta kwanta bayan tasha magani bata dad'e
ba bacci yayi awon gaba da ita
Usman tun a
mota yake tsokanan Yarima Aliyu, akan dole ya mutu akanta yarinyar tana da kyau
sai dai karama ce ba wata babba bace......
Yarima dai
banza da USMAN yayi domin haushin yanda yake ta fad'in Tana da kyau yakeyi,
d'an tsaki yayi cikin ranshi yace bazan kara zuwa dashi ba, tunda Kalle min
Mata yake tayi...
Yarima bayan
sun koma direct gefenshi ya nufa inda yayi bedroom dinshi yayi wanka, yana
cikin sa jallabiya danya kwanta
Gimbiya zinatu ta shigo d'akin tare da fad'in
Yarima .....
Yace ya
akayi....
Tace ina son
magana dakai
Baice mata
komai ba sai zama da yayi akan gadon d'akin tare da d'aukan wayarshi yana
dannawa.....
Kollonshi
tayi cikin jin haushin rashin kulata din da baiyi ba, tace haba Yarima wai mai
yasa kake haka, yau kwana na uku a gidan nan a matsayin matarka, amma baka da
lokaci na, kullum inka fita sai dare, karka manta wannan baya d'aya daka cikin
abunda miji ya kamata yayi ma amaryanshi, duk wani ango zama yakeyi a gida in
yayi aure ya dinga kula da matarshi, yau koda bazawara ka aura ai kayi d'auki
balle ni budurwa....
Yarima Aliyu
kallonta yayi tare da d'an sakin murmushi yace d'auki?? Akan me? Bayan har yanzu ban San maina aura
ba......
Cikin
faduwan gaba tace kaman ya Yarima ban gane ba ...
Idonshi na
kanta domin yana son yaga yanda zatai reaction amma ga mamakinshi sai yaga
batai yanda yake zato ba, kenan gimbiya budurwa ya sameta dagaske, inko hakane
ya kamata ya dinga bata hakkinta duk da bawai yana jin Sonta bane a ranshi,
amma tunda ta kawo budurcinta sai yaji tayi girma a idonshi, duk da Abun ya
bashi mamaki, dan baiyi zaton haka dinba......
Jin kukan
gimbiya zinatu shiya sa yarima ya dawo daka duniyar tunanin da yake...... Ganin
yanda take kuka yasa zuciyar Yarima tayi karaya tare da tausayinta , tashi yayi
ya ka mota ya kwantar da ita akan jikinshi yana fad'in plz ki daina wannan
kukan.....
Cikin kuka
take fad'in haba Yarima dole inyi kuka, yanzu Yarima ace Ina amarya amma kullum
saika fita, kuma inka fita sai dare, har an fara magana akai na, ana fad'in
baka d'auki na , kasan gidan sarauta akwai ya'da magana haba Yarima mai yasa
baka sona? Maina rasa......
Hannunshi
yasa akan bakinta yace ya isa haka,
Ganin kaman
Yarima ya tausaya mata yasa taita Mai juye juye a jiki,
Nan sha'awa
ta motso ma Yarima Kafin ace Mai har an fara harka.......
***
Alh madu ne
shida hjy babba kallon hjy babba alh madu yayi yace abunda yasa na kiraka
dagaske ne bariki zatai aure ko wasa takeyi??
Hjy babba
yace haka tace kuma ina ganin kaman dagaske take, dan naga gskya yanzu bata bin
maza, inma tanayi Toh a boye takeyi....
Murmushi Alh
madu yayi tare da fad'in ok, ina son kayi min bincike akan wa zata aura sannan
a ina yake, ina nufin Ina dai son sanin Waye shi da kuma sanin daka inda ya
fito.....
Hjy babba
yace an gama ranka ya dad'e
Kud'i alh
madu yaba hjy babba, sannan ya tafi
Alh madu
yace bariki Nasan bana gamsar dake, amma ni kina gamsar dani, inko dai bani
zaki aura ba, shima wanda yake son canza ki dole ya rasa ki,inko na bari kinyi
aure toh sai dai in zaki amince ko kinyi aure kici gaba da bina murmushi ya
saki tare da fad'in zan nuna miki ni Alh madu ba'amin wargi.........
AYSHA
BAGUDO..... na amsa sa'ko Ina matukar godiya Allah yabar k'auna da zumunci,
Allah yasa zumuncin mu har abada Allah ya tsole idon makiya, Wlh naji dad'in
sa'kon da kikayi min Sosai ngd ngd, ina matukar kaunarki kaman yanda kike
kaunata Allah ya biya miki bukatunki na alkhairi, makwabciyata ta gidan Aljanna
insha Allah
MARYAM OBAM
[8/22, 4:13
PM] 🅰 "🅰 " D'🅱⭕Y🔛🔝: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100 📚📚_
[5:36 PM,
8/22/2019] M. I Abubakar: [8/22, 4:18 PM] 🅰 "🅰 " D'🅱⭕Y🔛🔝: BARIKI NA FITO
BY
MARYAM
ALHASSAN DAN'IYA
No comments