BARIKI NA FITO (BOOK 2) 2
BOOK 2
PAGE 2
KIRA GA Y'AN
MATA MASU TURA MA MAZA HOTAN TSIRAICINSU TA SOCIAL MEDIA ZANYI DAN TSOKACI
KAD'AN AKAN WANNAN MATSALAN DAKE FARUWA....
WLH MATA MUJI TSORAN ALLAH MU DINGA TUNAWA ZAMU MUTU, DAKA KIN HAD'U DA
MUTUM A ONLINE BAKI SANSHI BA BAI SANKI BA, BAI TABA
GANINKI BA DAKA YACE MIKI
BANI ACCT NO YA TURA MIKI Y'AR 20K KO 50K KO KUMA YA TURA MIKI KATIN 1500,
SHIKENAN YA SIYE IMANINKI DAKA YACE TUROMIN HOTAN NONONKI KO HQ DINKI JIKI NA
BARI KIN TURA KAI WANNAN WACE IRIN RAYUWA CE BAMA A NAN MATSALAN TAKE BA NA
FARKO BAKI SAN KO WAYE BANE IN KINA TAKAMA YA TURO MIKI PIC DINSHI KIN TABBATA
SHI DINNE? WASU MAZAN BAYAN AN TURA MUSU DAI DAI KAN NONON KO HQ DIN, SAI SUBI
SUNA FAD'IN TUROMIN HARDA FUSKANKI, KE KUMA WAWIYA DANYA BAKI KUD'IN DA BAI KAI
YA KAWO BA JIKI NA BARI SAIKI D'AUKA KI TURA, BAYAN YACE MIKI INYA KALLA ZAI
GOGE KAI BAKI SAN KO WAYE BA, TOH WLH ZAN FAD'A MUKU DA BABBAN MURYA DUK WACCE
TAKE WANNAN ABUN TA DAINA DOMIN WLH NAGA CASE UKU DA IDONA WANDA AKAI BLACK
MAILING DINSU, D'AYAR MIJIN DA ZATA AURA AKA TURA MAWA BIKI BAIFI SATI BIYU BA
MIJIN FASA AURANTA YAYI GASHI KOWA YASAN LABARIN KUNGA SON ZUCIYA YAJA MATA
BARI IN BARKU HAKA NIDAI NA BAKU SHAWARA DUK MAIYI TA DAINA WLH
Tace haulat
zan kiraki mu had'u zuwa gobe ko jibi
Haulat tace
babu damuwa sai na jiki hjy amma fah kin San Nayi miki aiki Mai Kyau dan haka
ya kamata Ayi min kyauta Mai d'an tsoka
Hjy Umaima
tayi murmushi tare da fad'in turomin account dinki yanzu kam zan miki kyauta
dan Ina son bariki Sosai
Haulat tace
ina godiya hjy, yanzu zan turo miki acct no din
****
Yarima dai
har yanzu yana sume a inda yake
Ita kam
Gimbiya zinatu baccinta take domin bata ma San lokacin daya saceta ba gashi har
gari ya Waye hasken rana ya fara fitowa
Kwan kwasa
kofar bedroom din ake, karan bugun kofar yasa Gimbiya farkawa, bud'e ido ta
farayi ta hango yarima inda yake tun daren jiya, da sauri ta dira kasa tana
mamaki tare da tambayan kanta maiya sami Yarima? Ta gefe d'aya kuma gashi Anata
mata nocking, ganin bugun kofar yayi yawa yasa ta Fara kokarin ta rufe rigan
baccinta danta bud'e.......
Bud'e kofar
akayi jakadiya ce ta shigo ganin rigan gimbiya zinatu duk jini ga kuma Yarima
kwance Wanda a zatonta bacci yakeyi kuma kusa dashi ga jini nan duk da ya bushe
da sauri jakadiya ta fita Tana rangad'a bud'a gimbiya zinatu ta Kawo budurci
gidan mijinta bata zubar ma masarautarsu da kima ba, gidan sarauta in kayi abu
babu sirri nan labari ya fara bazuwa ai gimbiya ta kawo budurci, iyayenta sunji
dad'i Sosai koda labari ya iske mahaifiyar Yarima tace ai wannan ba abun shaila
bane sirrin Mata da miji ne, duk da itama taji dad'in hakan
Gimbiya gaba
d'aya hankalinta yayi kan Yarima domin dai taga yanda ta barshi haka yake,
cikin tashin hankali ta tashi da sauri ta nufi toilet cikin tashin hankali ruwa
ta fito dashi a cikin wani karamin roba, yayyafa Mai tayi a fuska, ganin ko
gezau baiyi ba yasa ta kuma yayyafa Mai ruwan lokaci d'aya ya fara numfashi da
sauri da sauri wanda da zata iya cewa bata ji, ganin haka yasa ta kara samai
ruwan.....
Yarima ido
ya fara bud'ewa a hankali yana ganin dishi dishi, akan gimbiya zinatu idonshi
ya Sauka wanda yake ganin yayi mafarkinta yana kokarin sex da Zainab dinshi
saida ya shiga yaga ashe gimbiya ce..... Dan shuru yayi tare da sauke numfashi
da sauri da sauri ba komai ya tuna ba illar mafarkin da yayi ya sadu da gimbiya
zinatu yaji ba virgin bace...... Idonshi
ya kara kaiwa kanta inda ya ganta cikin rigan bacci duk jini ya bata rigan
gabanshi yaji ya fad'i tare da tambayar kanshi Mai ya faru tsakaninshi da
gimbiya????
Kodai ba
mafarki yayi ba? Kai she is not a virgin a mafarkin da nayi so how come?? Naga
jini a jikinta alaman jinin budurci ne?? Lokaci d'aya yaji kanshi ya fara mishi
ciwo domin tunanin da yaita yi ya akai yayi wani abuda gimbiya bai Sani ba anya
yana lafiya kuwa? Mai nasha Toh dahar na kasa tuna komai?? Ganin inya ci gaba
da wannan tunanin ciwon kan da yakeji k'aruwa yakeyi sai yasa ya basar da
tunanin, tare da tursasa ma zuciyarshi ta yarda da cewa yayi wani abu da
gimbiya kuma ya sameta a budurwa.......
Gimbiya
zinatu ganin irin kallon da yake mata yasa gabanta yaita dukan uku uku gashi
baice mata komai ba sai ido daya kura mata, wanda a duniya idon Yarima Aliyu
yana sata cikin wani yanayi Indai ta kallesu.....
Ganin ya
tashi ya fara tafiya yasa ta kura Mai ido har ya kusa kofar toilet yayi taga
taga kaman zai fad'i da sauri ta nufeshi tare da taro shi tana fad'in Yarima
lafiya kuwa???
Yarima Aliyu
wani irin jiri yake gani ga kanshi dake faman Sara mishi Wanda yake ji kaman
zai fita dan ciwo, dakyar ya iya fad'in help me with my phone.....
D'an
sakinshi tayi amma ganin ya kasa tsayuwa yasa tace muje in kaika toilet sai
kayi wanka May be kaji karfin jikinka
Yarima Aliyu
bai musa ba haka ta taimaka Mai sukai toilet tare da zamar dashi akan toilet,
kallonshi tayi tace zaka iya wankan da kanka? Oh should I help you??
Dakyar ya
d'aga kanshi ya kalleta, sannan ya girgiza mata kai alaman taje zaiyi da kanshi
Murmushi
tayi sannan ta fita, bayan ta fita ta rufo Mai kofar toilet din, ta buga wani
uban tsalle cikin jin dad'i domin abunda gimbiya Amina tayi Mata yasa Yarima
kasa gane komai akanta, ta tabbata Yarima yana kallonta a matsayin budurwa ya
sameta a hankali ta furta Kalman Alhmdlh in Allah ya rufa maka asiri babu wanda
ya isa ya tauna shi...... Toh gimbiya dai kiyi a hankali karki manta Allah yana
yafe laifi tsakanin bawa dashi, amma baya yafe laifin bawa da bawa har sai
wanda ka cuta yace ya yafe maka...... Kuma shi Allah ba azzalumin kowa bane sai
wanda ya cuci kanshi, da kaji kunyar lahira gwara kaji ta duniya...... Jin
karan wayanta alaman sa'ko ya shigo yasa
ta nufi wajan wayar da sauri,d'auka tayi taga gimbiya Amina ce da sauri ta
bud'e sa'kon kamar haka....
Hey Wat up? Komai ya tafi dai dai kuwa ta
wajan Yarima? Gashi a nan ana ta fad'in kin Kai budurci
Murmushi
gimbiya zinatu tayi tare da bata amsa kaman haka.....
Eh komai ya tafi dai dai domin dai Yarima
bai gane komai ba, jinin da nayi amfani dashi yasa yake tunanin ni budurwa ce,
baki ga yanda yake ta kallona ba ko mamaki yake oho, amma fah tun jiya ashe a
sume yake, ina tunanin maganin dana bashi yayi mishi karfi, saida nasa mishi
ruwa ya Farfado, sannan har yanzu baya jin dad'in jikinshi, dan dakyar yake
tafiya saida na taimaka na kaishi toilet dan yayi wanka....
Gimbiya Amina tayi Mata reply da fad'in
Alhmdlh tunda shima ya yarda karki damu Idan ya sami bacci Sosai zai daina jin
jirin, ki barshi ya kwanta ya huta inda so samu nema ki kashe wayanashi yanda
zai samu yayi bacci Sosai Kar a dameshi, sannan kije ki tayashi wanka
din.......
Tana gama
karanta sa'kon Gimbiya Amina ta ajiye wayar tare da neman wayar Yarima danta
kashe a kan kujeran d'akin taga wayoyinshi har guda biyu d'auka tayi taga yana
da misscall da message bata tsaya duba waya mishi ba ta kashe wayoyin duka tare
da ajiyesu inda bazai gani ba, toilet din ta nufa tare da bud'ewa inda ta
barshi haka ta ganshi sai dai yanzu yasa hannunshi akanshi alaman yana mishi
ciwo Sosai, ganin haka yasa ta karasa da sauri tana fad'in Yarima maike
damunka? Bai kulata ba balle ya d'ago dakai ganin haka yasa tace Bari in maka
wankan
bai musa Mata ba dan yana son yayi sallah dan
baiyi ba,
Gimbiya ta
taimaka mishi yayi wanka tare da alwala, Bayan sun fito ta d'auko mai jallabiya
tasa Mai Yarima a zaune yayi sallah dan jiri yake gani bazai iya tsayuwan ba,
yana idarwa ya fara kokarin tashi.....
Nufanshi
tayi tare da kamo shi ta kwantar dashi akan gadon data canza zanin gado dan
wancan tasa jini akai,.
A hankali
yace give me my Phne
Tace ban San
inda ka ajiye ba ka kwanta ka huta, Kaga baka jin dad'i
Ido ya
lumshe tare da tunanin maike damunshi shidai tun jiya ya kasa gane komai, ga
zainab dinshi da yake son gani...... A
hankali yace yau Walima dinta and I promise to see her today, yun kurin tashi
yayi amma ya kasa dole ya hakura tare da cema gimbiya ta duba mishi Phne dinshi
ta kira Mai Dr ko kuma tama jakadiya magana a kira mishi Dr yanzu, yana maganan
ne hannunshi na kanshi tare da cije lebe
Gimbiya tace
ok bari inyi wanka insa kaya sai inje in fad'a a kirashi
Ido ya
lumshe sannan ya bud'e alaman OK
Toilet ta
nufa tana murmushi
Yarima kam
ido ya bita dashi, ya rasa mai yasa duk yanda yaso ya yarda da gimbiya zinatu
ya kasa, maiya sameshi jiya da daddare? Indai yayi sex da gimbiya zinatu tabbas
abunda yake ganin mafarki ne gaskiya ne gimbiya ba budurwa bace... Toh Inba budurwa bace taya naga jini a
jikinta sannan Nima gashi jinin ya
batamin riga??? Yarima kanshi yaji ya
kara Sara Mai da sauri ya kawar da wannan tunanin domin lafiyanshi yafi Mai
komai a halin da yake ciki gashi ya rasa mai yasa tunda ya farka yake jin
sha'awa gashi baya tunanin zai iya tabuka komai dan jikinshi babu kwari sannan
uwa uba yana son ya gane maiya faru tsakaninshi da gimbiya zinatu Kafin ya kara
kulata dan Indai bai gano komai ba baya tunanin zai iya yarda da ita harya saki
jikinshi da ita, yanzu burinshi Dr yazo ya dubashi yaga mai yake damunshi da
yasa jikinshi yayi weak yake ganin jiri daka nan yaje yaga zainab dinshi, ido
ya lumshe domin tunawa da yayi rabonsu da waya tun jiya da rana sanda yake
hotel, hakoranshi ya cije da lebenshi tare da fad'in nasan may be tana ta
expecting call dina, Allah yasa Kar tayi fushi.........
Gimbiya
zinatu ta d'auki lokaci a toilet Sosai koda ta fito cikin shiri tasa wata
doguwar riga yayi mata kyau, gani tayi Yarima yana bacci, daka gani baccin
saceshi yayi bawai yana son yi bane, dan yanda ya kwanta ya nuna mata alaman
haka, dan haka saita Fara komai a hankali dan karya farka daka karshe ma d'akin
ta Bari tayi falo inda taga an jera kayan abinci a dinning.....
***
Kaman yanda
habib da bariki suka tsara hakan ko akayi habib ya kawo mata duk sunsha hijab
da nikaf, kaman dagaske gidan su bariki sukayi da suka kama haya a u/kanawa
harda iyayen bariki din anyi ma kofar gidan fenti yayi kyau Sosai kaman bashi
ba.
Barika kam
gaba d'aya ta shiga damuwa na rashin samun Yarima a waya, toh maiya faru dashi
Anya yana lafiya kuwa? Na tabbata akwai wani abu haka kawai Yarima bazaiki
kirana ba sannan bazai kashe waya haka ba......
Habib ne ya
Katse Mata tunani da fad'in bariki kizo Ayi hotunan mana dansu samu su wuce
Tashi tayi
jiki babu kwari habib yaita d'aukansu hoto da aka gama bariki ta sallamesu suka
wuce ya rage daka habib sai iyayen bariki na karya
Habib kallon
bariki yayi tare da fad'in wai lafiya naga yau duk kinyi wani sororo kina
tunani kin kasa sakin jikinki?
Bariki tace
uhm Yarima rabona da muyi waya tun jiya da rana gashi wayanshi tun dazu nake
kira a kashe
Habib tabe
baki yayi tare da fad'in toh yana can wajan amarya ana soyewa yaushe zai tuna
dake.....
Bariki
kirjinta taji ya fara mata zafi tare da bugawa da karfi, lokaci d'aya taji wani
irin kishi na taso Mata, lallai Yarima tabbas saboda hakan ya kashe waya Inba
haka ba ai baya kashe waya wani hawaye ne ya siraro mata Mai zafi........
Hmmmm rayuwa
kenan, wai Mai yasa komai mutum yaga yana samu a sama ba tare da kwabon sisin
shiba sai kuga yana wulakanta abun, inda mutum kud'i yasa ya siya novel dinnan
a kasuwa na tabbata babu Mai zagi na, saboda mutum yasa kudinsa ya siya, haka
zalika a online akwai wanda novel dinsu ba free bane saika biya ake saka a
group, Suma bana ji ana zaginsu saboda ka biya kud'i ne ka shiga yau a media
abunda na Lura dashi muda mukeyin novel a free mu ake zagi kowa yake samun
daman fad'a mana magana Hmmm inaga nan gaba zan daina posting sai mutum ya biya
May be zan huta da zagi da kuma cewa ban San abunda nakeyi ba, ikon Allah Wai
mutum yana karanta Littafin wacce bata san abunda takeyi ba🤣🤣🤣 Indai mutum zai karanta Littafin
wacce bata san abunda takeyi ba Toh shi miye🤔🤔 inaga May be Idan mutum ya fara biyan kud'i zai gane
nasan abunda nakeyi wai ni maryam nice zan lalata wasu oh ni mairo kunji sharri
Toh ku Masu fad'amin hakan ku a shirye kuke kenan Mai yasa ban lalata kuba??
Ikon Allah Wlh wasu suna bani mamaki daka dawo wana daka hutu yau na fara
posting har an fara sai kace jirana akeyi ai kwayi hakuri inyi kwana biyu Ina
posting Kafin a fara zunduma min ashar din ance Ina saka batsa kunga kenan,
maryam na rubuta batsa kuna tsine Mata kuna rage mata zunubi 🤣🤣 maryam Obam da rubuta batsa ku kuma
da kwasan zunubi 😎 .......
MARYAM OBAM
No comments