SIRADIN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVEL
*Tushen Labarin*
Malam bilyaminu usman,haufaffen bafulatanin nijer a haihuwa da yare,ta wani fannin kuma d'an qasar *KAISA* kuma bahaushe magidanci mai halayya da dabi'u da al'adu irin na wasu daga bara gurbin hausawa,wadanda basu gama fahimtar abinda addini yayi magana akai ba kan iyali da haqqoqinsu dake bisa wuyan dukkan wani magidanci,walau saboda jahilci ko kuma sun take ne da gangan bisa son zuciyarsu da soye soyen rayuka.
Haifaffen agadez
iyayensa dukkaninsu suka kasance xallar fulanin niger,fatauci da neman kudi
yakawoshi qasar kaisa,wanda a yanzun ita tazame masa mazauni na dindin.
Yana da tarin
yara da suka kusa su ashirin da biyar,wanda dukkaninsu warin takalmi ne,mutum
biyu uku uwarsu daban,harda masu mutun d'ai d'ai da uwarsu ta haifesu su daya
tak cikin wannan gurguxu zuga da harqalla ta gidan,kamar yadda BILKISU take 'ya
daya tilo da mahaifiyarta tahaifa cikin gidan.
Saidai kash,dukka
wadan nan halayen nasa hakan bai hana a bashi aure ba,a duk sanda tabusa
mishi,ko ranshi ya raya masa,yayi katari da budurwa ko bazawarar da ranshi ya
kwanta mai da ita,tofa bazaiyi qasa a gwiwa ba wajen zage qwanjinsa da qarfin
aljihunsa koda qarfin aljihun wasunsa ta hanyar cin basussuka yakashe mata kudi
yakawota gidanshi.
Dukkan matar daya
aura takan fantama a lokuttan da take cikin amarci,takanyi yadda
takeso,takumayi yadda taga dama,saidai kuma da zarar wannan dama ta subuce daga
hannunta shikenan itama zata shiga sahun 'yan ci dakai da neman na wanki da
wanka,wanda hakan kan sanya wasu kasa jurewa,wasunsu sukan kai harsu
haihu,yayin da masu zuciya a kusa,masu qarancin haquri kan tafi da ciki su
haife a gida,bayan wani lokaci su dawo masa da yaro ko yarinyar da aka samu.
Cikin dukka matan
daya aura mutum biyu ne tak suka iya jumurin xama dashi,mace tafarko itace
kattume,wanda itace matarsa uku daya aura,tana da yara a gidan balaifi,hakanan
takama sana'a ka'in da na'in,tana daukan nauyin kanta dana yaranta,hakanan
cikin yaran takan yiwa wanda taga dama,hatta shi kansa malam bilyamun wani
lokaci yakanci cikin arziqinta,hakan yasanya babu ganin girma girmanawa ko
ganin mutunci tsakaninsa da kattume,idan ta hadosu babu wanda bazaiji kansu
ba,bata shakka ko shayin zazzaginsa,ko lafta mishi baqaqen maganganu,hakanan
yake zaune da ita shima saboda wataran yakan jingina da ita,sa'annan tazama
tamkar wata kujera a gidan,duk wani harqallarsa da auri sakinsa a gaban
idanunta yakeyi,hakanan za'ayi zaman a gama yasallami mace yasake jajibo wata.
Mace ta biyu
data juri zamanta a gidan kuwa itace maimunatu,maimunatu macen da bai taba
auren matar dayaji sonta cikin jiki da zuciyarsa ba irinta,macen dayaso har
zuwa randa tabar duniya,macen da haryau yake marmarinta duk da qasa tarufe idanunsa,macen
da bata taba daga kai ta kalleshi ba duk da mugunyar halayyarsa.
Yakance maimunatu tayi!,saboda ta soshi,ta qaunaceshi,takuma
zauna dashi,duk da banbancin ahalin,daraja,nasaba,kyau arziqi da dukiya dake
tsakaninsu,tazarace mai yawa tsakaninsa da maimunatu,amma duka bata duba wannan
ba,a zamanin tanunashi takuma zabeshi cikin dubban samari masu kyau dukiya da
aji da take dasu a zamanin.
Mahaifinta dan
kasuwane da yayi suna,hakanan ya shahara wajen arziqi,kamilin mutum mai
managartan halaye,nagartarsa tasanya bai duba matakin arqizin bilyaminu ba a
wancan lokacin yadauki maimunatu yabashi,duk da cewa su biyu tak Allah ya
azurtashi dasu a duniya.
Duk da tarin
wahala da fama da take a cikin gidan bata taba fasa halin da take ciki ba,tun
mahaifanta suna da rai har Allah yadauki abinsa,hakanan taci gaba da zama
dashi,sam babu jituwa tsakanin bilyaminu da qanwar maimunatu mai suna zuhriyya
saboda yadda take ganin yana gasa 'yaruwarta,ita kuma bata daga kai bare ta
nuba mishi bacin ranta,tsabar sanyin halin maimunatu yakawo hakan,tun zuhriyya
na budurwa idan tazo gidan bata kwana,iyakarta awa biyu uku tayi tafiyarta,don
tace ba zata iya ganin baqinciki da takaici ba,kusan har tafi maimunatu jin
zafin abun,don ko gaisuwa bata hadata da bilyaminu,hakan yasa ya shina yake
cike da haushinta,yakance
"Duk abinki dai baki isa ki raba qaunata da maimunatu
ba"
"Dana isa din ai da tuni na raba wallahi da baka kai
warhaka tare da ita ba".
Haihuwarta
tafari tasamu Bilkisu,yarinyar data fita daban cikin ahalin gidan da 'yanuwanta
gaba daya,hakan kuma baya rasa nasaba da dangin mahaifiyarta data dauko wadanda
suke jinin fulani,kakarta mahaifiyar maimunatu kuma shuwa ce.
No comments