MIN QALB 49
#*_MQ 49_*
*_THE FLAVORLAND BY ACEEY_*
Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors that complements each other, Yajin da ke daidaituwa da duk sinadaran abinci na al’adance da zamanance, Muna muka albishir da sanardaku cewa nesa tazo kusa domin @the_flavorland by Aceey yakawomuku duk nau’ukan yajinda kuke iya buqata Saboda yajin ya hada da:
Daddawa Yaji, Waton yajin daudawa
Garlic Yaji, waton yajin tafarnuwa da kuma
Beef Yaji, wato yajin Nama kuma me hade da nama
Domin ayukkanku da yau da kullum wanda ya hada da:
Dahuwar abinci/nau’uka na miyoyi DA
Gashe gashe da soye soye kamar su
Kaza
Kifi
Nama
Doya
Dankalin turawa/hausa
Awara
Danwake
Gurasa
Kwado da dai sauransu....
Ba Mu tsaya anan ba——
The_flavorland ya hada da kayan tande tande da lashe lashe
da suka hada da
Hoppers wato Fara
Milky candies wato alawar madara da kuma
Milky balls wato Gullisuwa da de sauran abunda rai ke
buqata...
Zaku iya tuntubar mu a kafofin sada zumunta kamar haka
IG: @the_flavorland
Whatsapp:08104673847
Sending Some treats your way.... l
Let us satisfy your cravings:
We Deliver anywhere and everywhere.
************
Ahankali ta bude idanuwanta dake cikeda nauyin baccin dabai
Gama isarta ba sbd sai Bayan sallar asuba ne tasamesa tana Gama budesu da
kyakkyawar fuskarsa tafara cin karo daf da tata numfashinsu na sarquwa cikin na
juna,ta kalli idanuwansa dake lumshe ta gangaro da idanuwanta Kan lips dinsa
wani gajeran murmushin samun nutsuwa ya subuto Mata ta motsa hannuwanta dake
sarqe cikin nasa taji yasake matsesu ta maida kallonta Kan fuskarsa da mamakin
da alama idanuwansa biyu kenan?
Hancinsa taji akan nata ya hade fuskarsu ya Dora mata ta Kai
idanuwanta Kan idonsa daidai Yana budesu cikin kasalar baccin dabai Gama
sakinsa ba ta dauke idanuwanta ahankali daga nasa zata sake zamewa yasake qin
Bata damar motsawa.
Ahankali ta bude bakinta dake daidai kunnensa cikin qaramin
sautin daya qarasa kashe jikinsa da saukar Masa da kasalar tace"
Yunwa.
Daqyar ya iya bude idanuwansa dasukai laushi da yanayin
yanda dumin numfashin bakinta ke shiga cikin kunnensa ta maganar datai Masa.
A kasalance ya saketa ta tashi zaune ta sauka daga Kan gadon
ta nufi toilet ta Shiga.
Wanka tayo tana fitowa daureda towel brown ta nufi closet
dinsa ta dauko wani sabon towel din qarami Tana sake goge kanta ta nufi gaban
mirror Yana duba dryer Amma Babu a dakin ta waiwaya ta kallesa taga idanuwansa
qyam akanta Yana binta dasu kamar wani mayen qarfe saita fasa tambayarsa sbd
ganin hadda miskilancinsa daya hanasa tashi bare Magana sai binta yake da
idanuwa ta nufi qofa ta fice zuwa bedroom dinta sbd akwai acan taganta jiya
gaban mirror.
Tana Isa dakin ta zauna gaban madubin ta jonata ta kunna ta
hau busarda gashin tana kallon fuskarta dake wani irin blushing da qyalli ta
cikin madubi,
Tana gamawa ta gyara Kan ta daure ta shafa Neutrogena oil
sai bodymist dasu spray ta qara da humra me sanyin qamshi ta miqe takoma jikin
wardrobe ta bude Bata wani tsaya zabe ba ta dauko wani plain drylace peach ta
saka riga da skirt ne saita fito Palo tana qoqarin nufar kicin akai Knocking ta
nufi qofar ta bude,
Cikin sa'a kuwa abinci ne anty zarah ta aiko musu Dan haka
saita fasa aikin ta ajiye a dining ta Kama hanyar zuwa tadoshi aka Kuma
knocking taje ta bude wani abincin ne daga umme itama ta karba duk ta hada ta
ajiye a dining tana juyowa da nufin zuwa tadosa saigashi yafito shirye tsaf
cikin wani milk yadi me tsananin taushin daya bayyanarda tsadarsa fili ya
nufota Yana kallon kwalliyarta tareda nuna yabawarsa a fili Yana Mata kallon
qasa qasa daya sanyata Jin kunya me tsanani sbd kallon ya qunshi yagama da
saninta cikinta da wajenta ga sauke Kai daga kallonsa tana juyawa ya riqota ya
dawo da ita gefensa suka nufi dining din Yana kallonta qasa qasa da wani irin
murmushi harsai data gaji cikin muryar shagwaba tace"
Dady Allah zantashi na tafi.
Qaramar Daria Mara sauti ko kadan yadan saki Yana sauya
kallonsa daga kanta yace"
Ok sorry sorry na daina Zo Nan lemme feed you.
Akan cinyarsa taci abincin tana bashi Yana Bata sai sake
kashe Masa jiki takeyi da rashin zamanta guri daya ajikinsa daqyar dai aka gama
cin abincin ya dauketa suka koma daki tana wani zille zillen daya qarasa juyar
dashi daga MD ZABEERA.
Qarfe goma sha daya harda kusan rabi suka fito tana riqeda
hannunsa ta sauya wasu kayan sbd wani wankan datayi tayi simple makeup da wani
irin hot red lipstick daya zauna daram Kan lips dinta dayaketa saukar hankalinsa
Amma Dole ya dauke Kai suna shiga palon zarah ya saki hannunta ya nufi sama
inda hafsatu tace musu tana can yatafi yabarta tana kallon hannunta daya saki
domin zuwa ga wata wani rashin Jin Dadi ya taso ya rufe zuciyarta ta zauna Kan
kujerun dake palon Ahankali tana Kiran sunayen Allah tareda kore shedan daga
cikin Kai da tunaninta taji motsin saukowarsu ta daga Kai tana kallonsu
hannuwansa duka biyun riqeda zarah din suna saukowa yanajin kamar ya daukota
gaba dayanta ya sauko da ita sbd ganin yanda take tafiyar sbd tace Masa da
ciwon qafafu ta kwana.
Har Kan kujerar yakaita ta zauna Rana kallonsa cikin farin
cikin kulawarsa gareta tace"
Thank you MD.
Murmushi me sanyi ya sakar Mata Yana zama kusada ita
yace"
Akwai godiya tsakanin miji da Mata ne?
Dariya tayi tana kallon Amatu dake qaqalo murmushi
tace"
Amatu Yana tambaya tayani bashi amsa sbd zaifi ganewama idan
Kika fada Masa Dan Naga yafi gane yarenki.
Maganar ta daki zuciyarsu daga Amatun har shi Musamman shi
ya tsura Mata idanuwansa yanajin wani irin yanayi me nauyi na rashin Jin Dadi
wato tariga da ta amincewa kanta yafi son Amatu kokuwa yafi daukar Amatun da
mahimmanci akanta ko me?
Amatu ma Jin tayi nauyi da rashin Jin Dadi ya dabaibayeta
take sbd maganar antyn Magana ce data fito dauke da raunin da zuciyarta ke ciki
batareda tasani saitakejin sabon mutuncin antyn na sake shigarta koba komai
haryanxu anty mutum ce me tsananin mutunci da ganin qimar Dan Adam duk wannan
auren na bazata da akaiwa mijinta da qanwar data ke yiwa kallon uwa daya uba
daya bai canzata zuwa wata daban hakama vai sauya kyawawan halayenta ba.
Kallonta tayi taga cikin Yar dariya tai maganar bakin
gskiyarta batasan tayi mgnar da wata manufa Abinda yake gskia ta fada Dan haka
sai itama ta qirqiro murmushi cikin batar da zancen tace"
Anty baya buqatan amsa yasan akwai godiya tsakani ma'aurata
musamam ma keda kikeji da Rabin ranki godiya bakomai bace.
Dariya anty zarah tayi tareda kallon Amatun tana jinjina
sunan Wanda rabonta dataji tun zamansu asibiti jinyar Muhammad.
Yanason fita Amma sbd yakira Dr Fatima yasa ya jira harsaida
tazo ta duba zarah din ta tabbar Masa da bakomai bane duk cikin laulayin cikine
sai nauyi da cikin zai Fara shiyasa Dan haka bayan fitar Dr Fatima fita yayi
shima ita Kuma Amatun ta Dan jima kafin ta tafi sbd qafafun anty zarah din ciwo
sukai Mata sosai Sai data Dan tattausa Mata su tasamu tayi bacci kafin ta fito
Takoma tayi sallah ta kwanta tanajin bacci.
Da daddare Takoma tasake dubo anty zarah din duk da ba wani
Abu dake Mata ciwo kawai qafafun ne acan tabarosa tadawo Saida antyn tayi bacci
yadawo sukai wanka suka kwanta.
Washe gari zai bar sashenta yakoma na anty zarah Dan haka
tun safen bai fita ko Ina ba suna Palo suna shiririta ita ala Dole saiya
lallasheta yasata bacci kafin yatafi haka dai suka shiririce har sallar magriba
tayi ya tafi.
Zarah duk yanda tayi tunani da Shirin dauriyar abubuwan
dazataita gani tareda daukarwa kanta alqawarin dangana tayi Shirin zaman hkr
sai abin yazo Mata a baibai yabarta da mamaki sbd MD sauya Mata yayi daga MD
ZABEERA zuwa asalin miji,
Ya sauya ta bangarori dabam dabam,
Babban mamakinta ayanxu shine zaman gida daya koya sosai
yake zama agida wani lokacin Yana yini guda cikin zabeera bai fita ba Yana
tareda iyalinsa ga yawan fara'a daya samu kansa aciki Abu daya datake
maimaitawa shine Bata taba Tunanin ummanta datace Mata wata kishiryar kamar
alheri ce sbd tana gyara maka mijin daka jima Yana wahalarda rayuwar aurenku
hakama wasu yancin naki wata kishiyar itake kwato muku keda yayanki gurin miji
ta hanyar sauyasa,
Tabbas ta yadda da hakan,
Akwai Abinda bazaka iyaba arayuwar zamantakewarka da mijinka
sbd ka kashe zuciyarka Dan haka kodai duk wadda za'a auro kingama cutarta sbd
kin sabawa mijin da yin shiru akan haqqinki Dan haka itama bawani dadinsa
zataji ba kokuma kisamu wadda zata sauya mijin kisamu rayuwar dabaki samuba
abaya,
Kishiya ko wace iri kasamu ta gari ko akasinta tasan da
akwai ciwo Amma dai duk da hakan tana jinjinawa Amatu sbd ta taimaketa tanan
Dan ita dai daza'a barta saidai suyi rayuwarsu sugama ayadda suka Fara bazata
iya yiwa MD hayaniya ko yunqurin sauyashiba sbd yafison rayuwar kadaicinsa
kamar tafi Masa nutsuwa takega shiyasa batason shige Masa sosai.
Abu dayane data lura
dashi shine wen ever Amatu is around idanuwansa akanta suke sbd bazai iya Hana
zuciyarsa Abinda takeso ba saidai Bata damuba sbd itama aduk lokacinda take
kusa to hannuwansa bazasu iya zamaba sai acikin nata Koda Amatun na kusa Wanda
hakan ya tabbatar Mata da tanada nata bangaren me mahimmanci a rayuwarsa.
Anasa bangaren kuwa yasamu kwanciyar hankalinda baitaba
samuba a rayuwarsa tun bayan rasuwar mahaifiyarsa tabarsa,
Yasamu nutsuwar zuciya da rayuwa,
Yasamu kwanciyar hankali data ruhi,
Rayuwa cikin iyalin dakake matuqar so suke sonka tareda baka
nutsuwa shine asalin Abinda baisaniba sai yanzu,
Amatu ce takawo sauyi arayuwarsa da zuciyarsa Amma Kuma
zarah ce abar jinjinawa kwanciyar hankali da nutsuwar rayuwar dasuke sbd itace
ta dauki komai da salama da dangana
tareda sawa kanta nutsuwa batareda damuwa ko tashin hankali ba azaman Wanda
yasa ake zaune kalau,
Da Bata bada wannan gudunmawarba da duk yanda suka Kai ga
tsananin son juna shida Amatu bazasu samu wannan kwanciyar hankalinba da
nutsuwar zaman lafiya.
Nuratu tazama tamkar aminiyarta yanzu sbd kusan kullum gurinta
ma take yini hardai ranarda anty salamatu tazo gidan yini sukeyi fira USI ma da
tintini yarinyar ta fice Masa arai sbd kusan itace silar komai tun Yana shareta
har suka Fara sabawa sbd Amatu dakuma yaganta Dr salman dayake babban abokin
shawarar USI dabaida amintaccen Dan uwa irinsa da hakan dai suka Fara sabo da
ita sosai.
Satinta hudu da tarewa tafara Shirin komawa sbd school
karatunsu yadauki zafi Dole zata koma Dan haka duk sukabi suka wani sukukuce
musamman ita dazata Koma ita kadai ko Muhammad gurin umme zaiyi zamansa daqyar
ma dadynsa yabari Dan acan yaso sanyashi school Amma ummen ta toqa hakama shima
Muhammad din yafison gurin ummen yanzu sbd tana sakaltashi da yawa gashi Kuma
yaga Yana ganin dadynsa anan.
Ita kanta anty zarah zatai kewar Amatun sbd sunyi sabon sabo
duk da har abada zasu taba komawa yanda suke Ada ba Amma ko yanzu sunyi sabon
shaquwarsu suna tsananin mutunta juna da gujewa Shiga haqqin juna.
A gidansu ta yini Daren ranarda zata koma canma Saida tayiwa
su iyami kukan barin gida kafin yazo da daddare ya dauketa suka koma gida.
Washe gari Saida tayiwa kusan kowa dake cikin zabeera
bankwana kafin suka wuce USI ne dakansa yakaisu airport suka wuce yadawo.
Sbd son cire Mata damuwar data sanyawa ranta yasa Basu koma
Greece ba direct suka nufa US.
Wata irin rayuwar Jin Dadi da sakewa sukai a US tamkar
turawan qasar Dan sai alokacin tasake sanin asalin waye MAHMOUD ZABEERA sbd
wani bangarensa data gani na dabam wato Dan rayuwa.
Duk yanda zatai rayuwa bazata manta wainnan kwanakin dasukai
a US ba sbd ya shayar da ita soyayyarda har abada bazata barta ba,
Ya sanyawa zuciyarta wani sabon maganadisun sonsa da
qaunarsa.
Kwanansu takwas suka tattara suka nufi gida saidai Kuma
kamar karsu dawo tunda suka dawo tafara zuwa school kwana biyu shikenan ciwon
zazzabin dare ya sanyota gaba sunyi yawon asibitin hardai aka tabbatar musu da
ciki ne Dan haka ba wani magani haka suketa fama duk wani aikinsa ya ajiyesu
jinyar matarsa yake cikeda kulawa da tsananin qauna.
Ganin harya share kusan wata daya da rabi yasa ta daure ta
bawa kanta qwarin ta nuna Masa ta warke sarai kafin yafara maganar komawa sbd
tarin ayyuka da Kiran dayaketa faman Sha dazai tafi ita dakanta takaisa airport
suka fito motar ya kamo hannunta ya matso da ita cikinsa Yana kallonta da
fararen idanuwansa dake bayyana newarta tun kafin ya tafi ya bude baki ahankali
Yana shafo cikinta cikin laushin murya yace"
I will miss you wife.
Dan dago qafarta tayi sbd yafita tsayi takai bakinta Kan
nasa ta Dora ahankali ta zura Harshenta tabashi wani irin kiss tana kallon
cikin idanuwansa tace"
I will miss you More.
Rungumeta yayi tareda sauke ajiyar zuciya Yana shafa Bayanta
yace"
I love you.
Qanqamesa tayi kalmarsa na sake kashe jikinta.
Sun jima ahakan kafin lokacin tafiyarsu yayi yabata kiss a
goshi ya wuce tana kallonsa harya shige ta juya jiki amace ta shiga mota tabar
airport din tana Jin kewarsa kamar tabisa.

No comments