MIN QALB 46-47
MQ 46/47_*
_INA MASU SHA'AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA DAWWAMÀMMIYAR NISHADI TO GA DAMA TA SAMU KU NEMI LITTAFIN_ _*WASA DA ZUCIYA*_ _NA ZINNEE SMART WANDA TSARUWAR RUBUTUNSA DA TSAFTARSA TAREDA DADINSA SAIZA KU KAMU DA QAUNAR RUBUTUNTA A KARATUN LAYIN FARKO DAN SAMUN WANNAN QAYATACCEN LABARIN NATA ME SANYAYA ZUCIYAR ME KARATU
TA WANNAN NUMBERN_
👇👇👇
08080840567
*******
Yau kwananta uku da dawowa batareda ta sanarda kowa dalilin
dawowarta ba tadai ce musu hutu tasamu me Dan tsayi shiyasa tazo Dan haka Babu
Wanda yasa ko kawo tunanin komai cikin ransa gameda zuwan ko tsakaninta da
mijinta sai suka hau shaanin gabansu aka bude majalisar me zaman kanta gidan
kawu tasu maman junior Dan har wasu abubuwan gyare gyare suka Fara Shirin Fara
harhadawa Amatun na gyaran jiki Dana cikin jiki musamman ma iyami da dama batai
gyaran yarta ba lokacin da akai auren Dan haka yanzu zata gyara abarta.
MAHMOUD ZABEERA kuwa tunda yaji daga bakin kawu tana gida
taredasu sai hankalinsa yadan kwanta Amma duk da hakan a matse yake daya
dawo Nigeria din tun kafin kowa yasan halinda suke ciki Dan shi kunyama zaiji
ace matarsa ta tafiyarta Yana yawon neman komawarta ko Modibbo saiyace ba
MAHMOUD ZABEERA din dasuka sani bane gashi kamar zuwan nasa Kai tsaye bazai
samu ba sbd wani urgent work Kuma daya taso Masa Wanda dole saiyaje Dan haka
zarah kawai zata taho Nigeria shi zai wuce inda zaije daga Nan daga can zai
wuto Nigeria din.
Yau kwananta bakwai da zuwa zaune suke suna fira itada anty
salamatu da iyami Dan yau Yan firar tasu duk basanan sunfita anguwa Dan haka
yau gidan tsit ba hayaniya sai su kadai USI ma yadawo asibiti da wuri yau Yana
dakinsa baccin gajiya yakeyi sbd a asibitin ya kwana yau.
Sallamar umme sukaji Muhammad na bayanta tafe cikin gudu
hannunsa riqeda Ben10 soldier dinsa dayafi so cikin kayan wasansa Yana Kiran
sunan anty salamatu yana shigowa yaga mummynsa a zaune da gudu yayi kanta Yana
cewa''
Mumma mumma.
Rungumesa tayi tana cewa''
My Muhammad has become a superman ji wannan gudu fuiiiiii.
Dariya yayi Yana Jin dadin Superman data kirasa Yana sake
hayewa jikinta yace"
Mumma where is my Daddy?
Inason ganinsa i miss him""yafada Yana leqa
bayanta da kallon koina Yana son ganin baban nasa.
Murmushi tayi tana zaunar dashi gefenta tace"
Muhammad look"tafada tana nuna Masa su iyami tace"
Baka gaida grandma ba da antyty dinka"cewar anty
salamatu.
Gurin iyami ya nufa Yana miqa Mata biscuits din daya Ciro
aljihunsa wanda yakawo Mata yace"
Kaka iyami ga biscuits da umme ta siyomin ki ajewa kawu.
Dariya dmtayi tana jawosa jikinta suna sake gaisawa da umme
data zauna tana amsa gaisuwar Amatu data salamatu tana cewa''
Amatu wato muda muka matsu dason ganinki gamu munzo Muhammad
ya isheni Wai babansa yakeson akaisa gurinsa shine nace Bari muzo dai idan
yaganki qila ya rage fitinar neman uban.
Murmushi kawai tayi batareda tace komaiba saita kamo wani
zancen suka fada wani zancen Bayan anty salamatu takawowa ummen ruwa da
brabiskon dasukai Wanda ummen na sonsa sosai musamman yanda iyami keyinsa yayi
wani irin laushi.
Sai dare umme ta tafi tabar Muhammad dayace gurin mamansa
zai zauna.
Washe gari kwananta Tara kenan da zuwa suka shirya itada
anty salamatu suka fita da motar USI daya bar musu Wanda duk yanda taso taja
motar kasawa tayi sbd yanda ta koya tuqi a Greece daban da tuqin nan din Dan
haka Dole tabar anty salamatu da USI ya koyawa tuqi sbd fita da iyami ko
lalurar gida idan antashi Dan yakan bar musu mota ya tafi asibiti musamman idan
acan zai kwana.
Family house dinsu maman basiru sukaje barkar haihuwar da
qanwar maman basirun tayi shiyasama kwana biyu basa zaman fira sun Dan jima
acan kafin suka baro suka nufi kasuwa siyayyar takalman iyami data Basu saqon
anaso sun qare daga Nan gurin bada dinki suka Amatu tabada dinkuna sai yamma
sosai suka dawo gida Dan haka suna komawa sallah kawai sukai sukaci abinci
Amatu ta kwanta Dan matuqar gajiye take.
Washe gari tana buqatan gyara kanta daya Fara damunta suka
shirya zuwa blue fox itada anty salamatu Dan haka guraren 12 suke fice bayan
sunfara biyawa sun ajiye Muhammad a zabeera taje ta gaidasu Andi dasukai
mamakin Jin zato hutu Ashe Amma sanin ba ayi maganar tarewarta ba yasa suka
barta takomawarta gidansu inda ta sauka saidai Kam tunda har tazo Dole ayi
maganar tarewarta ta tare sbd daga yanzu idan tazo ta sauka a gidan mijinta
dama tuntuni anyi gyaran sashen marigayi Dr khalil an rushe komai ansauya
tsarin gurin gababaki daya Kuma sai akai qatuwar katanga aka zagayayesu cikin
qaramin gate me kyau tareda sashen zarah sai harabarsu ta zama daya me girman
sosai.
Daga zabeera blue fox din suka wuce suna Isa Allah ya hadata
da manager kuwa ai Nan ya tsaya kallonta cikin girmamawa da sauri ya qaraso
Yana cewa''
Ran Amaryar zabeera ya dade yau an tuna baya kenan.
Dariya taso Yi ta gimtse tana kallon gurin da aka sauyawa
tsari me kyau fiyeda da ga girma da fadada gurin da akayi ya sauya matuqar Dan
yanzu ma tun a gate Saida tickets ake shigowa ga uban securities tana jinjina
kai tace"
Manager komai na blue Fox yasamu sauyi Banda Kai kana Nan
yanda kake har halayen.
Dariya yayi Yana cewa''
Allah ya taimaki Amatun zabeera ai mu Babu wani sauyi daya
fiyemin blue fox musamman yanzu datake zaman mijinki Dan kuwa ya jima ya siyeta
gabaki dayanta Kuma nasan idan Allah ya yadda sbd ke ne tunda kowa yasan har
yanzu kina qaunar blue fox dinnan shine yayi Mana dukkanin wannan gyare gyaren
Takoma kamar turai yanzu hadda sashen geaming da sports munada aciki haka Kuma
komai namu anqara fadadashi daga restaurant din har spa din dasauransu.
Girgiza Kai tayi tana kallonsa tace"
Ga antyna dai ku gaisa sbd Naga ko ganinta bakayiba sbd
dadin labari.
Da sauri ya kalli anty salamatu dake sanye cikin riga da
skirt na red embellished atampa da gyalenta red shima sai tsawonta me tsari ya
fito cikin dinkin riga da skirt din ya washe dukkanin haqoransa da fara'a
yace"
Sannu da zuwa blue fox Ina Miki barka da zuwa sirikar me
gidanmu.
You'll never change manager" Amatu tafada tana yin gaba
Yana biye dasu Yana musu bayanin yanda tsare tsaren gurin yake ayanzu da kansa
yaje jiki na mazari ya karbo musu tickets na komai da zasuyi yakawo musu a
kebantaccen gurin da sai oga zabeera din yazo da kansa shikadai ke zama acan
suka Fara cin snacks kafin suka nufi spa Dan komaima yimata zaayi.
Da gyaran Kai aka Fara musu kafin da aka gama aka koma
gyaran qafafuwa daganan aka koma gyaran jiki.
Basu baro blue fox ba sai magrib suna isowa gida itace tafara
fitowa tana juyowa sai Jin Muhammad tayi a jikinta ya Fado Yana mata
"oyoyo mummah"
Da mamaki take kallonsa suka nufo cikin gida tana cewa''
Waye ya dawo da Kai?bakace Kuma gurin umme kakeso ba sbd ka
ringa wahalarda mutane zaka ringa saka masu kaika da dawo dakai yawo.
Daddy yazo Dani...
Kallonsa tayi da sauri tana kallon bakinsa daya furta dadyn
tace"
Dadynka Kuma?
Eh dady ne yadawo yau yazo Dani yace muzo mutafi da mummah.
Kallon inda yake kalla tayi numfashinta nason sauya fita ta
hanyar qara sauri tana dannewa ta kalli gurin tagansa zaune Kan kujerun harabar
gidan tareda kawu
Kawu sai zuba yake Masa Amma shi idanuwansa na kanta ya zuba
Mata su cikin yanayi da kasalar da ganinta ya sakar Masa idanuwansa na
bayyanarwa sbd wani lumshewa dasukeson Yi Amma Basu lumshe din ba.
Bugawa ZUCIYARTA ke Naman Yi sbd wani irin kyau da sheqi
tareda qwarjinin da Allah ya horewa wannan bawa nasa MAHMOUD DAHEER ZABEERA ta
dauke idonta ahankali tareda juyawa ta shige ciki batareda tabari kawu ya gansu
ba Dan yanzu zai Fara kawo Mata zantukan tazo ga mijinta.
Suna shiga daki tashige ta tube saidatai wanka kafin tayi
sallar magrib da yanzu aka gama ta sanya doguwar riga mara nauyi me kamar
boubou ta fito tana tambayar abinci ta nufi kicin ta dauko zobon da iyami keyi
tana sawa a fridge sbd baqi dakuma kawu dakeson ruwa me kala ta fito tana Shan
zobon saiga USI yashigo yace taje palon kawu yana namanta.
Can ya wuce Kai tsaye sbd ta daina Jin hayaniyar Muhammad
tasan sun tafi ne tunda dare yafara Yi takumasan babansa bai Bari ana fitar
dare dashi.
Tana shiga da Muhammad din tafara cin karo kwance yayi bacci
jikin kawu tana ganin hakan saita daure fuskarta taqi kallon dayan gefen
Dan taji ajikinta MD ne agurin.
Kallon kawu tayi muryarta na daidaituwa cikin nutsuwa
tace"
Kawu likita yace kana kirana.
Eh mijinki ne gashinan zaune yazo tun dazu bakwanan yanata
zaman jira.
Miqewa kawun yayi daukeda Muhammad ya fice yakaiwa iyami
dakinta ya fita zuwa gurin abokanan hirarsu ta dare a qofar masallaci.
Kawun na fita ta nufi qofar fita itama batareda ta kalli
inda yake ba ko qofar Bata qarasa isaba taji yariqo hannunta tareda dawo da ita
baya har bayanta na gugar qirjinsa ya bude baki da muryarsa me taushi
yace"
Why?
Meyasa Zaki taho a irin yanayin da kike ciki Kuma ki dauki
fushi Bayan nine yakamata na dauki fushin tunda kin baro batareda sanina ba.
Juyowa tayi ta kallesa ahankali kafin ta zame hannuwansa
cikin nata daya riqe ta wuce tabarshi tsaye Yana kallonta.
Qofar data fice yabi da kallo Yana Dan rintse idonsa ya
sauke numfashi Yana komawa zaune dama yasan Amatu bazata sauko acikin sauqi ba.
Hakanan ya fito ya wuce batareda kowama yasaniba Yana Isa
gida ko abincin dare daqyar yaci sbd kada Zarah daya lura kamar itama tafara
iya Magana akan Abu tayi Magana bazai iya daukar wani stress Bayan Wanda yake
daukaba yanzu aikin dayayi a Sudan duk tsawon kwanakin baiwani bada hankali
yayi Abinda yakaisa ba sbd har lokacin komai Kiran dazaiyiwa Amatu baya
samunta,
Wanka yayi ya kwanta kawai dama akwai gajiya a taredashi sbd
yau din ya dawo.
Washe gari ma taso fita Amma iyami ta hanata sbd cewar
mijinta na gari ba Maganar yawo yanzu Dan haka Dole ta zauna gida tana kallo su
Anty salamatu hadda iyamin suka tafi gurin sunan qanwar maman basiru suka
barta.
Tana zaune Palo tana kallo sama sama bayan la'asar har bacci
ya Dan Fara daukarta taji qamshin imperial majesty na shiga hancinta kobata
juyoba tasan shine zai shigo palon ta tashi zata shige daki tun bai qarasa
shigowaba tana kaiwa tsakiyar palon Yana shigowa da sallamar cikin sauti me
taushi ya tsaya gabanta Yana kallon fuskarta dake daure tam sai yaji jikinsa
yayi sanyi ya rasa kalmar furtawa ya riqo hannunta cikin nasa idanuwansa na
kanta a gajiye da wannan fitinar yace"
Wannan shirun naki is killing me
Kiyi mgn Koda zakiyi fada ne I'm ready Zan dauka infact I
won't say a word indai har Zaki sauko.
Bata kallesaba ta kwace hannunta a hankali kafin tace"
Zan kwanta Kuma bakowa a gidan nikadai ce.
Tunda yadawo gida zarah ta rasa gane kansa abun duniya ya
isheta ga cikinta nada damuwa an hanata sakawa Rai damuwa Amma wlh bazata iya
rashin damuwarba sbd Abinda take gani shi ake Kira da asalin damuwar,
Yau satinsa guda cif da dawowa Amma yarasa gane Kan Amatun
tun abin na iya tsakaninsu har gidansu Amatun dai kowa yasan Abinda yake faruwa
kawu dayaji hadda 6arin ciki tayi sai baiji dadin yanda MAHMOUD din yabari
tadawo ba ita kadai cikin yanayi irin wannan Amma zamansa uba saiya ringa bin
Amatun da rarrashi har gwara iyami na Dan Mata zafi wani lokacin Amma duk da
hakan shidai MAHMOUD baiga sauqi ba saima yakoma ya hurawa su Andi wutar batun
tarewar Amatun Wanda yabar Andi cikin mamakinsa dakuma tunanin shima wato
lokacin gyaransa yayi a hannun Amatu sai suka aikawa kawu yace zai Basu ranar
tarewa idan yayi mgn da Amatu.
Jin hakan sai tension dinsa yafara bayyana ga aikinsa Dan
duk wasu ayyukansa da meetings dinsa na watan kusan duka yayi postponing dinsu
sbd kwanakin Yana samun matasalar saurare a bangaren aikin shiyasa ya tsayar.
Batareda tsayawa neman bayanin kowaba yasa aka Zo aka zubawa
sashen sabbin royal furnitures masu kyau da tsari saidai har lokacin Amatu
takasa tsayawa dashi ko Magana suyi tun Yana daukar Muhammad Yana zuwa dashi
harya Bari kada ya kwashi sanyi da yawa
Zaune yake Yana duba wayarsa hankalinsa gabaki daya baya Kan
wayar Yana wani gurin..
Fitowa tayi daga dakinta cikin Dan adonta na riga da skirt
na atampar data Dan fitar da qaramin cikinta daya Fara Dan turowa ta kallesa
tana nazarinsa tsawon lokaci kafin ta sauke numfashi ta nufi kicin ta bude
fridge ta dauko Masa lemondrink da cup ta Dora Kan tray ta dawo takawo gabansa
ta ajiye tareda zama gefensa ahankali tana budewa ta zuba Masa ta miqa Masa
ahankali tareda Kiran sunansa cikin sanyin murya.
Waiwayo yayi ya kalleta tareda kallon kwalliyar jikinta datai
Masa ya karbi drink din Yana qaqalo sahirtaccen murmushi ahankali yace"
Thank you and you look great.
Kurbawa yayi ya ajiye Yana kashe wayarsa gabaki daya ya
ajiye ya qara daukar drink din yanasha harya shanye ya ajiye cup din yasake Dan
juyowa ya kalleta Yakuma cewa''
Thank you"Yana maida kallonsa kan TV Yana kallon news.
Jinjina Masa Kai tayi tareda fuskantarsa gabaki tana jinjina
qarfin Rai irin na MAHMOUD din dayake dannewa da boyewar abindake ransa kamar
yanda ya Saba boye al'amura saidai yanxu wannan damuwar ta dabance Dan itadake
taredashi tana iya hango damuwa ataredashi.
Numfashi takuma saukewa akaro na biyu kafin ta Kai hannunta
ta Dora Kan nasa ya juyo ya kalleta da idanuwansa dasukai laushi sbd rashin
isashen bacci ta bude baki ahankali tace"
I'm really sorry MD sbd tun farko daban Bari ta tahoba da
duk haka bai faruba,
Laifina ne na yarda Kuma Inshallah idan munhadu Zan fahimtar
da ita hakan but for now idan akwai ta inda Zan taimakawa alamarin let me know
please..
Shiru yayi idanuwansa a rufe na mintuna kafin ya budesu
ahankali ya juyo ya kalleta na mintuna Yana NAZARIN yanayinta ya bude baki
yace"
She respects you fiyeda komai sbd tanajin nauyinki fiyeda
komai because of the old relationship that you two shared Wanda deep down haryanxu
tana Miki kallon yayarta.
Kallonsa take da dukkanin girman idanuwanta bugun zuciyarta
na sauyawa sbd Fara tammahar inda zancensa keson dosa muryarta na rawa
tace"
To ta Yaya hakan zai.....
Ki tayani fahimtar da ita Abinda nakeson tagane please.
Saura qiris zuciyarta ta buga daga cikin qirjinta ta da
Abinda ya fada din,
Wani dishi dishi take neman Fara gani sbd bugawar da
zuciyarta keyi da sauri,
Wani irin zafi yafara taso Mata tun daga cikin qasan
zuciyarta Yana mamaye zuciyar Tata take taji tsanarsa nason darsuwa a zuciyarta
akaro na farko a rayuwarta Amma ta yakice hakan tareda kallonsa cikin Ido ta
bude baki Kai tsaye tace"
For the first time yau MAHMOUD ZABEERA ka farkar Dani daga
wani babban kuskuren danake ciki,
Miqewa tsaye tayi ta kallesa cikin muryar dake bayyanarda
jarumtarta tace"
Zuciya ce a kirqina ba dutse ba dan haka inaga ko dan Abinda
yake cikina na cancanci wata karramawar Amma duk da hakan tunda ka buqata Zanyi
mgn da ita Amma bisaga sharadin idan Bata dawoba Nima nagama zaman gadin gangar
jikinka sbd inason ayau kasan sonka zuciyata ya Kama bawai zuciyar ya cinye ba.
Zaiyi mgn tabar gurin batareda ta tsaya sauraronsa ba ta
nufi dakinta ta shige tareda rufowa ta Isa bakin gado ta zauna tana son fashewa
da kuka Amma Abinda takeji yafi qarfin kukan sai kawai ta miqe ta zari
doguwar hijab da keys din motarta ta fice tanajin idan Bata bar gidanba komai
zai iya faruwa.
Tana Isa gidansu Kai tsaye dakin ummanta ta wuce ta zube Kan
gado sai alokacin wani gigitaccen kuka ya 6arke Mata me ciwo.
Umman data fito toilet taganta tana kukan sai kawai ta barta
tayi me isarta kafin tabar gefenta Takoma Kan kujerar dakin ta zauna tana
kallonta tace"
Wannan kukan dakikeyi ki Dena zarah sbd Abinda yake taredake
Wanda baya buqatan irin wannan tashin hankalin tunda kinfi kowa sanin yanda
cikin baida qwari.
Tashi zaune tayi tana share hawayenta ta zare hijabin
jikinta ta dago ta kalli umman dake Mata kallon jiran jin dalilin wannan kukan.
Bude baki tayi ta korowa umman bayanin komai zata Dora da
wata maganar umman ta daga Mata hannu cikin takaicin ZARAn da cewa''
Zarah kinada matsala babba idan har Baki dawo hayyacinki ba,
Shi so da zaman aure duk ba hauka bane,
Ta Yaya Zaki maida kanki doluwar qarshe akan gudun zuciyar
namiji,
Shin meye amfanin rayuwar aurenda babu fahimtar tunani ko
Babu so ana zaman aure me Dadi idan kowa yasan mutunci da darajar kansa data
abokin zamansa,
Matsalarki zarah itace kin kasa bawa kanki darajarda shima
abokin zaman naki zai baki,
MAHMOUD ya zaune dake cikin girmamawa da mutuntawa tsawon
shekaru masu tsayi batareda ya taba complain ko nuna muzantawa garekiba duk da
kece Kika kasa kawo sauyi da shaquwa acikin auren naku sbd kece mace kinada
hanyoyi da damarmaki da Zaki sauya MAHMOUD tun kafin wata tashigo
rayuwarku Amma Kika kasa yanzu abin yazo a biyu na farko koki yarda ko karki
yarda MAHMOUD son mararsa AMATULLAH yake so me tsanani musamman tunda yanzu
gatanan tana bude Masa hanyoyin sanin zamantakewar aure sannan akwai fadanda ko
sunyi abunsu na tsakanin ma'aurata ba huruminkineba Shiga gashinan yanzu kin
qare zuwa bikon kishiya Wanda idan dai baki koyi sanin darajar kankiba data
Kama kanki akan Abinda Babu ruwanki har ruwan wanka kina Kan hanyar daukarwa
kishiya Dan haka kada kiga laifin mijinki laifinkine
Da Zaki farka ki nuna Masa kinsan darajar kanki data aurenki
da zamanki matarsa tsaf zakiga yazo yazauna daku anbawa kowacce haqqinta
anzauna lafiya.
Bance kinyi baya ba sbd wannan halindakike ciki Allah na
gani Kuma Yana sane wlh zakiga irin tanadin sakamon da Kika samu agaba Amma
gskia zarah ki farka Babu Wanda zai qwaceki a cikin wannan yanayin sai kanki da
kanki Zaki qwaci kanki ki tashi kije bikon naki dakika daure kanki da zakiyi
Danni bana cikin wannan mutuwar zuciyar.
Mutuwa jikinta yayi ta miqe ta wanko fuskarta tadawo ta
dauki keys ta fice batace qala ba ta shiga mota ta nufi gidansu Amatu.
Tana Isa tayi parking ta fito tana daidaita kanta da
nutsuwarta ta nufi ciki ta Isa qofar Palo tashiga da sallama
Su iyami dake zaune palon duk suka juyo suna kallonta
Saiga Amatu ta fito daga kicin daukeda indomie data dafo
tana ganinta itama ta tsaya cak tana kallonta.
Anty salamatu ce tayi saurin miqewa tana cewa''
Zarah kece da yamman Nan sannu da zuwa.
Iyami ma cewa take"
Qaraso ki zauna zarah kinji sannu da zuwa fitar yamma.
Murmushin qarfin hali tasaki tana qarasowa ta zauna tana
kallon Amatu dake kallonta tana Mata sannu da zuwa itama.
Murmushi tasaki tana cewa''
Amatu idonki kenan.
Indomin ta ajiye tana murmushi tace"
Anty zarah kedai karkice komai nakira wayarki Allah harso
biyu bana samu.
Zobo anty salamatu takawo Mata suna qara gaisawa zarah
tace"
Iyami wannan 'yar Taki zaneta zamu farayi sbd tashin jinta
yanzu kiduba kiga yanda takasa aje fushin datakeyi damu shiyasa nazo da kaina
nabata hkr tunda taqi sauraron mijinta to gani nazo Dan yau bazan fita gidan
nanba saida ita.
Kallonta Amatu tayi cikeda mamaki tace"
Anty zarah.
Tsit antyn tayi sbd tsawon lokaci sai yau takirata anty
zarah complete.
Juyowa tayi ta kalleta zuciyarta na rauni da damuwar datake
ciki Amma tana daurewa kada ta gasa ta bude baki zatayi mgn sukaji sallamarsa
dukkaninsu suka juya.
Iyami na ganinsa gaisawa kawai sukayi ta miqe ta bar gurin
hakama anty salamatu.
Kallonsa zarah tayi harya qaraso gabanta baice komaiba ya
kamata hannunta ya miqar da ita yace"
Let's go.
Kallonsa tayi da idanuwanta dake son cikowa ya sakar Mata
murmushin dake nuna banhaqurinsa Yana girgiza Mata Kai yace"
Ita tariga ta taho gidansu ke dakike taredani bazan Bari ki
barni ba,
Bazaki bawa kowa hkr ba sbd selfishness ba.
Wani irin sanyin Dadine yake kwaranya cikin zuciyarta
haryana bayyanuwa Kan fuskarta tasaki wani yalwataccen murmushi tana girgiza
Kai tace tunda nazo zankoma da ita idan har da akwai mutunci da ganin girma a
tsakaninmu.
Gyaran muryar kawu sukaji daga bayansu suka juya Banda Amatu
da abun duniya ke neman shawa Kai.
Palonsa suka nufa aka zazzauna Nan ya rufe Ido duk su dukan
yayi musu fada tareda sanarwa da kowa laifinsa Kuma ya buga rantsuwar yau
Amatun a gidanta zata kwana da daddare iyami da salamatu zasu kawota.
Godiyar da MAHMOUD din yaringa yiwa kawun yasa su iyami Jin
wani iri sbd zarah din.
Bayan tafiyarsu Amatu Tasha kuka harta gaji iyami ta kalleta
tana cewa''
Amatu kiji tsoron Allah kobaki zauna da mijinki lfy Dan
Allah ba Kya zauna dashi lafiya kodan baiwar Allan Nan tasamu nutsuwa gidan
aurenta,
Karki manta shifa aure hkr ne cikinsa kusan gabaki daya,
Bakiyi rayuwar zaman aureba da Khalil ya rasu sai yanxune
zakiyi rayuwa Kuma wlh duk Kika dagawa MAHMOUD hankali har hakan yasa aka Shiga
haqqin zarah Allah bazai barki ba,
Matar Nan koba komai wlh duk Wanda yasameta abokiyar zama ya
huta a rayuwa sbd matardake danne kishin Mijinta Dan kawai a zauna lfy ai itace
abarso da tattali Banda shi so yake wani dabam,
Dan haka Amatu Dan Allah ki dauke Ido ki koyi hakuri Kuma ki
zauna da Matarnan tsakani da Allah kamar yanda kuke ada ni wlh tausayi take
bani Kuma Ina tsananin ganin girmanta.
Itadai Amatun Banda hawaye Babu Abinda takeyi sbd hukuncin
da kawu ya yanke akanta ta wani bangaren Kuma yanzunema zasu Fara tsara zaman
auren dakuma kishin tunda yanxune za'a hadesu araba musu kwanan aure da
komaima.
Daki Takoma anty salamatu na hada Mata sauran kayan Sha da
iyamin ke hada Mata kullum tun ranarda aka Fara maganar tarewarta.
Har dare Basu Gama Shiri ba sai Bayan ishai tayi wanka ta
shirya cikin wata farar lafaya da wani lace me taushi aka bita da turaruka masu
sanyin qamshi suka fito bayan kawu yaqara tashi nasihar.
Andi ne dakansa ya aiko drivern dayazo daukarsu suka nufo
zabeera inda ake jiran isowarsu.

No comments