MIN QALB 42
MQ 42_*
Da lakabe anty zarah takai kanta cikin daki sbd dishi dishi
da idanuwanta ke 'dan gani hakama kaf kuzuri da qarfin qafafunta sun Gama
sarewa tun kafin ta Isa bakin gado ta zame ta zauna tareda sakin wani
wahalallen kukan dakeson fito Mata tun lokacinda MAHMOUD yabude baki yafara
Mata mgn.
Shikuma fridge ya biya ya dauko freshmilk me sanyi da ruwa
ya nufi bedroom dinsa yanajin wani irin walwala da nutsuwa na qadatuwarsa.
Har lokacin kwance take cikin lullubin data rufe jikinta da
Babu riga tayi zuciyarta na qoqarin zuqar numfashin dake neman gagararta,
Tasan tabbas anty zarah ce tadawo shiyasa ya, yafi kowa@'
try da kansa and xa
zuwa ga bude Mata qofa batareda yasamu ko damar ce Mata Yana
zuwa ba,
7 ya tube yashiga bai wani jima ba yafito ya sanya kayan
bacci kamar koyaushe farare tas dasu yazo ya zauna Yana duba saqonni ta laptop
da aketa kiransa akai yanashan freshmilk data rage sanyi yanayi Yana kallonta
cikin kulawa tunaninsa tayi bacci.
Rufe aikin yayi ya miqe tareda qarawa AC din dake aiki qarfi
sbd lullubin dazaiyi shima ya nufi gadon yahau tareda shigewa duvet din inda
fatar bayanta da Babu komai ta hadu da fatar qirjinsa dake bayyane sbd rufe botiran
rigar baccinsa da bayayi a qaida.
Rufe idanuwa da qarfi tayi zafin zuciyarta na tunzuro Mata
da fitar da yayi dazun ta yunqura zata matsa daga jikinsa saiga wayarsa na
qarar data sanyasu tsayawa su dukan musamman ita data gama sanyawa ranta Anty
zarah ce sbd idan ba ita matarsa ba waye zai kirasa cikin dare daidai wannan
lokacin.
Shi Sam baida niyar ko kallon wayar sbd Koda Rana ma daukar
wayarsa ganin dama ne bare yanzu da dare,
Katsewa Kiran yayi yakai hannu ya dauko wayar da niyar
kashewa saiga shigowar massage daga umman zarah ne ya tashi zaune Yana duba
Kiran daya katse yaga ita 'dince takira saiya koma ya bude massage dinta,
"_Mahmoud Dan Allah kaje kayi mgn da zarah ka fahimtar
da ita qarin aurenka ba Wai qarshen rayuwarta bane tanata kuka hankalina
yatashi nakasa samun nutsuwa nasake kira Bata dagaba morethan 8times. _"
Yana Gama karanta saqon ya 'dan dafe goshi Yana Jin tun
yanzu kamar kansa na neman qullewa,
Ta Yaya zarah zata damu kanta da kuka Bayan bawai yanxu ne
akai aurenba,
Auren da shekara uku yanxu Amma tanason saka Masa ciwon Kai
ga Amatun ma yaga alamar ita buga kansa zatayi ma da rigimarta.
Bai sake kallon Amatun dake kwanceba har lokacin taqi
motsawa ya sauko Kan gadon ya zura slippers tareda aje wayarsa ya fice dakin.
Yana fita ta rintse ido sai alokacin hawayen dasuka bushe
Mata suka Fara gangarowa ba qaqqautawa
Zuciyarta wani irin radadi da bugu takeyi kamar zata fasa
qirjinta,
Wannan wace irin qaddarace tahadata auren Dame Mata,
Wace irin masiface wannan takejin kanta ciki sbd tiririn
dake fita daga qirjinta Jin takeyi gwara ta mutu tabi Dr khalil dinta ba aure
da wannan masifa,
Uban me yasa zai ajiyeta Dan ya ringa barinta Yana tafiyarsa
saikace wata Mara sanin ciwon Kai.
Ta sauko daga gadon tabar dakin ma takasa sbd Sam ko
qafafuwanta bataji ajikinta sbd rufewar zuciya,
Hawayentane ke tsananta gudu suna jiqa pillon da kanta yake
kai.
Tashi zaune tayi ta kalla agogo idan tana qirgen mintuna
daidai to yafi mintuna talatin da barin dakin.
Tana Nan zaune idanuwanta na sake rinewa har tsawon awa daya
da mintuna ta miqe tsaye ta janyo towel ta daura ta nufi qofa ta fice bayan ta
share idanuwanta dasukai jajir ta nufi dakinta.
Tana Murda qofar dakinta Yana fitowa dakin anty zarah din ko
kallon inda yake bataiba ta shige kafin ta rufe saigashi a bayanta Yana kallon
idanuwanta dasuka bayyanar Masa da halinda take ciki ya riqo hannunta ta janye
batareda ta dago ta kallesaba ta nuna Masa qofa tace"
Bacci zanyi can you leave please.
Kallon fuskarta yasakeyi yanason ta kallosa su hada Ido Amma
taqi saima gado data nufa ta haye zata kwanta cikin qosawa da fitinarsu
yace"
Akan zarah ne??
Tsayawa tayi tareda dagowa tayi Masa wani irin kallo sai
alokacin shedan ya lurar da ita kamar rigarsa jikinsa tayi squeezing ta maido
kallonta Kan fuskarsa tace"
Meya kawo sunan anty zarah anan?
And akan wani dalili zaisa naji haushin kebantuwarka da
matarka bayan nafo kowa sanin kanada iko zuwa inda take aduk lokacin dakaga
dama Koda kuwa waye agabanka ko atare dakai.
Idan kinsan hakan then wats all this drama da kukan nan.???
Wani mugun takaici ne ya ciyota ta sauko Kan gadon tazo
gabansa ta tsaya tace"
Idan har kana tunanin nayi kuka kokuma kukan danayi akan
kaje gurin matarkane then u're dreaming sbd hakan baya gabana and idan kana
buqatan kebewa da ita meyasa ka zabi zuwa Nan da ita akwai guraren dazakuje da
basai ka tsaya yiwa wani bayanin Abinda yakaika dakin matarka,
Matark,Matarka,Matarka,Matarka please spare my life nagaji
da Jin wanna hayaniyar infact inaga I will have to give you guys a break ta
yanda zaka......
Will you just keep quiet" yafada a Dan hasale shima sbd
tashin hankali da fitinar daya samu kansa ciki kaf rayuwarsa wannna shine karo
na farko da wani ya tsaye yake fada Masa magana mace ma kuma bama namiji ba shi
baima taba sa'insa da wani ba.
Kukane ya balle Mata tace"
Nazamar muku lalura da zamana atsakaninku Nima kun Hana
zuciyata nutsuwa da shigowarku cikin rayuwata ta bangaren aure..
So yayi yai Magana Amma yafasa sbd juyawar da kansa keyi
tuni idanuwansa suka sauya ya juya yafice daga dakin.
Bakin gado ta koma ta kwanta tareda sakin wani sabon kuka
tana Kiran sunan Dr khalil daya tafi yabarta har haka ta sameta.
Washe gari gidan kaf cikinsu Babu Wanda yayi bacci musamman
shi da sautin kukan daya baro tanayi ya hanashi ko rintse idanuwansa Wanda ya
haifar Masa da ciwon Kai me tsanani Dan haka Koda gari ya waye ya yanke
shawarar zaiyi tafiya kozai samu samu nutsuwar zuciya data cikin kansa.
Tun kafin su tashi Amatu tariga kowa tashi ta wucewarta
makaranta bayan ta barwa anty zarah note din ta tafi school bakin qofar dakinta
Dan batai niyar Shiga dakinba sbd kada antyn ta fahimci halinda take ciki,
Itama zarah din daga ciki ta rufe qofar yau batada niyar
budewa Amatun sbd kada ta fahimci halinda take ciki sbd nemawa kanta sauqi ma
cikin Daren tayiwa kanta booking ganin likita a _Santorini_ ta Dan samu tabar
gidan na kwana biyu ko zata samu nutsuwa Dan haka tanajin ficewar Amatu itama
ta tashi ta shiga wanka tana fitowa ta shirya ta dauki duk abin buqata ta dauki
waya takira numbern MD cikin sa'a kira 'daya tana daf da katsewa ya dauka
tafara gaidashi cikin sanyi da nutsuwa
Ya amsa Mata kamar ko yaushe kafin tayi Masa bayanin
tafiyarta ganin likita yayi shiru da farko saikuma yadan gyara murya kadan yace
ta fito idan tashirya su tafi tare sbd shima Dana Santorini din yayi niyar
zuwa.
Jin hakan ta fito cikin farin ciki harta hada musu tea
saidai itakadai Tasha yace shi Yana azumi.
Wayar Amatu yakira so daya Bata dauka ba sai kawai yayi
texting dinta kafin suka wuce
itadai Anty zarah mamaki da ikon Allah kawai take kallo
MAHMOUD dinda wani lokacin saiya Isa inda zaije yake fada Mata yayi tafiya wani
lokacinma sai idan taga baidawoba takira yace Mata sorry ya aiki yadauki
hankalinsa bai fada Mata yayi tafiya ba bayanan Amma gashi agabanta yake Kiran
Amatu zai sanar da ita zaiyi tafiya 'yar ikon Kuma taqi dauka qarshe ya qare da
rubuta text.
Jin tayi tafiyar tafita ranta Amma Kuma sbd lafiyartane Dole
zataje kodan Allah yabata haihuwar Nan dai itama ko ALLAH zaisa hankalin MD din
ya tsaya akanta itadake son abinta.
Lokacinda Text din ya shigo wayarta tana zaune cikin wani
restaurant tareda annah sunacin abincinda Sam batamada appetite cin kawai
takeyi tana karanta massage din tagama tabbatarda MAHMOUD ZABEERA qarshenta
yakeson gani wato ta mutu ya huta,
To baza'a yi hakaba zaisan dawa yakeyi.
Gida Takoma ko makarantar Bata komaba tana zuwa tahau hada
kayanta tana qoqarin danne hawayenta daga saukowa.
Saidata hada kayanta acikin akwati biyu kafin takira annah
tace ta tayata ayi Mata arranging room a hostel zata dawo Nan.
Ba musu suka shigarda application din accommodation akace
sai Nanda 7 to 8 days zata samu.
Dole ta hakura har zuwa lokaci tanata fatar asamu kafin
dawowarsu din.
Daina fitama tayi Sam tana tsumayin jiran akairata akan
angama Mata arranging komai na zaman hostel din wani gefen Kuma har yanzu
zuciyarta batada nutsuwa bare sukuni gashi tun Yana Kira Bata dauka harya
tattarata ya share dama baiwani Saba da duk irin wainnan abubuwan ba.
Kwanansu biyar suka dawo da anty zarah kawai ta gaisa ta
shigewarta Bata sake fitowaba sai dare data fito cin abinci tagansu a dining ta
wucewarta kicin ta dafa noodles taci tafito ta wuce daki
Anty zarah data fahimci da akwai matsala wato a tsakaninsu
taso yin Magana saikuma tafasa tana cewa''
Kama kanki zara'u kafin abin ya juyo kanki Dan abin juyi
juyi ne kowa da ranar baqin cikinsa indai zaman kishi ne.
Data lurada shima ko kallon inda Amatun tabi baiyiba saita
sake Kama kanta da shishigin shiga tsakani karta jawowa kanta fitinar da gwara
tasu musamman da yanzu magungunan da likita ya dorata akai yace ba'a son tana
saka damuwa ko kadan shine zasufi aiki da yardar Allah zata samu ciki Dan haka
saurin dauke kanta tayi akansu ta maida himma taci abincinta ta qoshi Tasha
ruwa Tasha magani tana satar kallonsa sbd kobai Bari angani ba a fuskarsa tana
iya hango tension ataredashi.
Kwana biyu gidan ana zabga rayuwar ba ruwan wani da wani
tsakaninta dasu anty zarah ce kawai take zuwa har daki ta gaidata musamman
dataga tana Shan magunguna ta tambayeta batada lafiyane ta sanarda ita na neman
haihuwar tane take ta Kama kanta saima taji son komawa hostel dinta yaqara
qarfi.
Duk wata hanyar haduwarta dashi ta toshe duk da dai yanzu
futowarta take Palo tayi abindake gabanta sai hakan yaso ya daga hankalin anty
zarah Kuma yanayin shegun kayanda Amatun ke sawa kamar wata baby ko ita dake
mace idan taganta dasu dauke Ido takeyi bare ace namijine yaganta ahaka.
Ranar daya dawo
idanuwansa suka sauka akanta da wata riga guntuwa Mara hannu tana kicin
tana dafa taliya saura kadan yafadawa anty dake Masa sannu da zuwa ta kallesa
tana mamakin irin yanda idanuwansa suka kasa daukewa daga Kan Amatun sai kawai
ta juyawarta tabarshi tsaye Yana nufar hanyar kicin din
Amatu hangosa tafe ta sauke abincin ta fitowarta tana dauke
kanta daga kallon inda yake harta gotashi taji yadawo da ita gaba dayanta ya
matse cikin jikinsa Yana kallon idanuwanta datake dojewa kallon cikin
idanuwansa tana qoqarin janye jikinta ya matseta dakyau cikin jikinsa gudun
zarah ta fito tagansu wani aikin yasamesa yasashi dagata gabaki daya ya nufi
dakinsa da ita bai sauketa ko inaba sai Kan gadonsa yaqi sauketa daga Kan
jikinsa Kai tsaye yace"
Ankirani daga hostel na makarantarku cewan ur accommodation
is ready,
Abinda banganeba anan waye zaikoma hostel din?
Sai alokacin ta dago da idanuwanta ta kalli cikin idanuwansa
tace"
Nice zankoma hostel.
Wani wadataccen murmushin da Bata taba ganin yayiba yasaki
Yana sake tungumarta yace"
Keep dreaming.
Daure fuska tayi tana qoqarin qwacewa daga jikinsa
tace"
Nagaji da zama anan zantafi I need a break.
Serious yayi da fuskarsa Yana sakinta yace"
You are not going anywhere ki cire ran zama koina.
Masifa takeson suyi Dan haka Kai tsaye tace"
Bazan zauna anan ba nafi son zama can din.
Kallon fuskarta ya Dan Yi zuwa lokacin ransa ya Dan Fara
baci ya sauko Kan gadon Yana cire agogon dake hannunsa tareda links din rigarsa
yacire takalmin qafarsa ya nufi toilet Yana cewa''
Zangani idan kina zaman kanki ne coz I can see hankali bai
isheki ba ita wadda kike kishin tafiki iya son mijin sbd tana kiyaye bacin
ransa.
Kadan ya rage ta Dora hannu akai ta kurma ihun Abinda yafada
idanuwanta sukai jajir ta sauko gadon ta nufi qofa ko gani batayi sosai sbd
masifa ta fice tana cewa''
Yau wallahi bazan kwana a gidan Nan ba tunda dai kafito fili
kafada Banda amfani.
Tana shiga dakinta ta janyo jallabiya baqa ta sanya tareda
janyo akwatinta dasuke dama a shirye ta adauki Jakarta tafara Jan akwatin tana
fitowa dasu ta nufi qofa idanuwanta na zubo cikowa da hawaye taji anriqe
anruqota ta baya tareda zagayowa gabanta Yana mamakin fitinarta da yanda rigima
Bata isarta ya rasa ma yazaiyi Mata azauna lafiya gabaki daya neman zaitashi
take ya karbe akwatin hannunta cikin sarewa yace"
For God sake AMATULLAH meke damunki?
Qin Magana tayi tana qwace hannunta yasake riqewa Yana
rintse ido cikin rashin sanin mafita yace"
Kince kin gaji da Nan ko
To Zan canza Miki gida Zaki zauna ke kadai Babu Wanda zaizo
ya zauna shikenan..
Kallonsa tayi zatayi Magana cikin wani irin sanyin murya
dake nuna galabaitarsa da rigumar yace"
Please"
Yanayin yanda yayi maganar yasa jkinta neman mutuwa ta dauke
Kai tana cewa''
Bance haka ba nidai bazan kwana agidan Nan ba kawai ka...
Daukarta yayi gaba daya har handbag dinta ya nufi dakinsa da
ita Yana cewa''
Wannan kishin naki Mara dalili ne Bari na nuna Miki wani Abu
tukuna saikiyi me dalilin.
Tanajin haka tayi saurin kallonsa daidai lokacin dayake
shimfideta Kan gadon Yana sakar Mata wani sahirtaccen murmushin daya kashe
jikinta Nan take ya hanata motsi saima lumshe ido datayi tana lafewa cikin
jikinsa ya shafa kanta ahankali ya furta"
My stubborn wife kina mantawane ke uwa ce kokuma duk zafin
kishine zaisa ki zauce ki zauta MAHMOUD ZABEERA,
Rufe idonta tayi qasa qasa tace"
Waye zai jawo to?
Wani murmushin me sanyi Yakuma saki Yana shafo gashinta da
Rolling dinta ya zame yakawo bakinsa daf da kunnenta ahankali yace"
Tell me meyasa?
Bude Ido tayi ahankali ta zuba Masa ta kalli bakinsa dake
daf da nata tasan ko budewa tayi zatai magana sai lebanta ya hadu da nasa ta
sake maida idanuwanta cikin nasa saitaji kunyarsa na shigarta ta juyar dakai
ahankali tana kallon ta rufe Ido taji saukar hannunsa Kan cikinta taja numfashi
daqyar tana rufe Ido ya Kai bakinsa ahankali yayi kissing din idanuwanta
dasukadaine suka Isa su kalla cikin nasa idanuwan ya gangaro ya Dora bakinsa
Kan nata Yana qarasa janye doguwar rigarta daya jima da zarewa zip din gaba ya
jeho rigar qasa Yana shafa hooks din white lace push-up bra dinta dazai balle
ya balle ya jehota qasa itama tayi saurin qanqamesa tana sake rintse Ido wani
numfashi me wahalar fita na fito Mata shikuwa haduwar qirjinta da nasa Babu
Kaya yasa numfashinsa daukewa na daqiqu kafin ya zura hannuwansa bayanta zuwa
wuyanta.
Qarfe Tara da mintuna hudu tasamu damar fitowa daga dakinsa
tana tahowa ahankali sbd gajiya da Kuma uban tsamin da jikinta keyi da
akwatunanta na jiyan tafaracin karo a Palo kafin anty zarah dake zaune tana
Shan maganinda daqyar yake samun hanyar wucewa a maqoshinta sbd Abinda ya tare
Mata maqoshi sukai turus sunayiwa juna kallon kallo
Amatu wata irin masifaffiyar kunya da girman anty zarah data
iya zama gidan datake kallon mijinta da wata hartana iya bacci tabbas tana qara
jinjinawa antynta babu kamar anan kusa itakuma anty zarah wani irin kallone
takewa Amatun zuciyarta ma takasa daukar tunani daya acikin tunani fiyeda dari
data keyi akanta.

No comments