KIBIYAR AJALI 17-18
_*17/18_*
*MASARAUTAR BASANNABAS*
Bashi da wata dama ko karsashi da zai kaiwa wani kukansa bare a ashere mishi. Kiri-kiri yana son bayyana abu a zahirance amman sai ya kasa, yaji tamkar ana shake masa wuya. Tsaye yake jikin taga
yana hangen duk wani motsin masu yawo a can harabar gidan, sannu a hankali ya hango mahaifiyarsa tana tafiya jikin ta sanye da mayafi, wanda alama suka nuna daga wani wajen ta dawo. Salman ya dauke fuskar sa daga kallon ta tare da takawa a hankali yaje ya zauna daga kan kujerar da ya taso.“Assalamu alaikum.”
Cikin ransa ya amsa be ce komai ba bare ya dago dan ganin
wace ce, muryar ta kawai ta shaida masa cewar jakadiya ce.
“Allah ya taimaki sarkin sarakuna, an buga an barka mazan
fama. Uwar gida kuma gimbiya tace a yi mata iso wajan ka.”
Kamar yace a'a saboda shi a yanzu yana da bukatar nazari
akan abin da yake shirin yi na auran da zai yi, yana so ya zurfafa tunaninsa ta
yadda zai yi ya ware inda zai sanya amaryar idan an daura aure an kawo ta
gidan, saboda yasan dole azo a nemi muhallin da zai ajiye ta. Da yake Jakadiya
tasan halinsa na shariya, hakan yasa ranta be baci ba har lokacin da ya ga dama
yace mata.
“Kice bacci nake ji.”
Ta kuma russunawa tare da sunkuyar da kai cike da girmamawa
tace.
“Gyaraaa kintse sarkin sarakuna, zanje na gaya mata kamar
yadda kace.”
Shi dai be kuma cewa komai ba har ta fita daga dakin, yana
zaune ya rasa wane irin tunani zai yi. Jakadiya ta kuma dawowa da alama ma dai
ita kanta uwar gidan nashi tana bakin kofa dan yaga Jakadiyar ba ta jima da
fita ba yaga ta dawo, yaja tsaki a cikin ransa, zuciyar shi tana zugi saboda
wasu mutum biyu da kwakwalwarshi take ta son tuna masa ko su waye a gurin shi
amman ya kasa tantance ainahin su.
“Allah ya ja da ran sarkin Basannabas, uwar gida tana neman
afuwa dai akan son ganin nan naka. Tace kanta bisa wuya, ka tausaya ka bata
damar shigowa ciki.”
Hannunsa kawai ya daga kuma Jakadiyar ta fahimta dan tashi
kawai ta yi taje ta sanar da ita sai gata ta shigo. Tana shiga Jakadiya ta yi
sauri ta nufi sashen Gimbiya Jaleela wato kishiyar mahaifiyar sarki Salman.
Hango ta tayi tana sakkowa daga bene cikin shiga ta alfarma, tana hango
Jakadiya ta kuma tsuke fuska dan dama bata sakar mata fuska duk kuwa da irin
yadda munafincin da take kawowa daga lungu da sakon cikin masarautar.
“Takawarki lafiya farin cikin marigayi sarki Aliyu, uwar
marayun masarautar Basannabas, farin ciki da walwalar bayin Basannabas. Allah
ya kara miki lafiya da nisan kwana uwar daki na mai share min kuka.”
Sai da tazo ta zauna ta gyara zama sannan ta kalli Jakadiya
cike da iko tace.
“Jakadiya meke tafe dake? Ina fatan dai kin zo min da
labarin da zai sanyaya min zuciya ta.”
“Ina neman afuwarki uwar daki na, sai dai wannan labarin da
nazo miki dashi ban san yadda zaki dauke shi ba.”
“Ina jin ki Jakadiya.”
“Dama yanzu Gimbiya Shaheedah tasa nayi mata iso wajan
maimartaba sarki, yanzu haka tana can gurin sa zasu yi ganawa ta musamman
tsakanin su.”
A fusace Gimbiya Jaleela ta kalli Jakadiya tana hararata
tace.
“Me nace miki game da cewa Salman sarki?”
“Ki gafarce ni Uwar daki na tuba nake Allah ya huci zuciyar
ki, sha'afa nayi wallahi ki yafe min.”
“Shikenan amman ki kiyaye gaba. Ina so kuma ki binciko min
abinda taje suka tattauna, bana kuma son kuskure kin sani dai.”
“Insha Allahu uwar daki na ba za a samu wani kuskure ba,
Allah ya ja zamanin ki.”
Daga haka ta mike ta fita tana rawar jiki. Bata wuce ko'ina
ba sai sashen Gimbiya Najwa wato kishiyar Gimbiya Jaleela, wace ita ce matar
marigayi sarki Aliyu Salman ta uku, yar Galadima ce. Ita kuwa tana kishingide a
tsakiyar katafaran parlorn ta, hadimanta suna ta faman yi mata fifita, wasu na
matsa mata kafafuwa yayin da wata ke gefe tana yanka mata kayan marmari d'aya
bayan d'aya tana sha. Gimbiya Najwa na ganin Jakadiya ta yi saurin sallamar
hadiman nata, dan tasan tabbas labari ne ta kawo mata game da Sarki Salman ko
Gimbiya Shaheedah ko kuma mahaifiyar sarki Salman d'in wato Gimbiya Sa'adatu.
Jakadiya daman tasan halayen ko wacce mata dake gidan,
saboda duk itace munafukar su, wajan kai gulmar ko wacce a gurin d'aya. Tasan
daman Gimbiya Najwa ba zata tambaye ta komai ba har sai idan ita ce ta fara yin
magana, wani lokacin Jakadiya takan jinjinawa irin girman kanta da takamarta
saboda kawai tana yar Galadima, da ace a yar gidan sarkin kacokam Allah ya yi
ta bata san me zata yi ba, duk da cewa a wannan lokacin su Waziri da shi
Galadiman sune suke jan ragamar sarautar Sarki Salman, sai abin da suka ce shi
za'a yi.
“Na gaisheki ta gaban goshin marigayi sarki Aliyu... Jinjina
da ban girma gareki shalelen Baba Galadima, uwa ga magajin sarki wato yarima
Ilyas(junior). Nazo miki da wani labari.”
Kamar ba zata amsa ba tsawon lokaci, sai da ta mulu ta
mulmule sannan ta kalli Jakadiya karo na biyu tace.
“Idan kin san maganar ba ingantacciya bace karki sanar dani,
ki bari idan kin tabbatar da ingancinta, sai kizo ki gaya min.”
“Na kuma gaisheki ta gaban goshi, tabbas bani da gamsashiyar
magana akan abin da nazo miki dashi. Kamar yadda kika ce, zan koma idan na gama
tabbatar da ko menene zan dawo. Na barki lafiya, farin cikin yarima kuma sarkin
gobe, shalele Ilyas.”
Tufa d'in dake hannunta taci gaba da ci ba tare da ta sake
bi ta kan Jakadiya ba, saboda ita Gimbiya Najwa tana da wasu munafukan bayan
Jakadiya, dan ita a cewar ta idan wata taga wani abun, wata be zama lalle ta
gani ba. Hakan yasa ta rarraba kafa ta baza masu gano mata sirrikan duk wata
mata dake cikin gidan. Shi yasa Galadima yafi waziri sanin duk wani abu da ya
shafi Gimbiya Shaheeda da kuma sirrin mahaifiyar sarki Salman.
Can kuma bangaran
Sarki Salman da uwar gidan sa wato Gimbiya Shaheeda, tana shiga ta zauna gefen
shi tana tsotsar alawar da take cikin bakin ta tace dashi.
“Wani lokacin kakan yi min abin da sam be dace ba a gaban
kaskantattun mutane, wato hadimai. Ya za'ai kamar ni nace ina son yin magana da
kai kace a ce min bacci kake yi? Karka manta ban da ni babu wacce zata iya zama
da kai bayan kowa yasan cewar ba da kwan haihuwa, ba zaka iya bawa Basannabas
magaji ba kamar yadda marigayi ya bar maka gadon mulkin sa wanda kake a kai
yanzu.”
Jin kalamanta yasa ransa fara tafarfasa saboda zafin su da
yaji, bata da wani abu da take yawan yi masa gori irin rashin haihuwar sa.
Amman saboda tsabar shakkarta da yake yi sai bai ce mata komai ba har ta kuma
yin magana.
“Ni wallahi kasan ba da ban soyayyar da nake yi maka ba, da
tuni nasa ka sauwake min naje nayi wani auran na haihuwa. Amman saboda na san
babu matar da zata iya auran ka yasa nake daurewa ina lallashi zuciya ta akan
ta hakura ta zauna tare da kai.”
Ta yi shiru na dan wani lokaci, shi kuma wata irin tsanarta
ce take sake zama sabowa a zuciyar shi. Shi be ki ta ce ya sauwake mata ba
indai har tana da bukatar yin haka, baya jin komai a game da ita sai zallar
shakka da son bin duk wani abu da take so. Kansa a kasa dan ko da ta shigo be
dago ya kalleta ba sai ji ya yi tace.
“Honey dago ka kalle ni.”
Ta na rufa baki kuwa ya daga yana kallanta, ta yatsina fuska
tare da mika hannu ta zare bakin glasses d'in idan shi yadda zata ganshi sosai.
“Haba Honey, ba na hanaka kallo na da wannan glasses d'in
naka ba? Na yi na yi da kai ma ka dena saka baki amman ka kasa bari, idan ka
sashi kamar wani tsohon makaho wanda bashi da d'an jagora.”
Da yasan wannan maganar ce zata kawo ta da duk yadda zai yi
sai ya hana su hadu, sai dai ance rashin sani yafi dare duhu. Kuma idan da sabo
yaci ace ya saba da duk wasu abubuwa da ake yi masa a masarautar. Ita kuwa
kallon shi kawai take yi tana jin wata zazzafar kaunar shi, hakan ne yasa bata
son taji ana cewa ya kara aure shi yasa take kuma rike shi ta hanyar da
zuciyarta ta aminta.
“Sannan kullum nice nake nema ka kai babu wani abu da yake
damunka. Ina tunanin rashin haihuwar nan taka tana da nasaba da rashin sha'awa
da baka da ita. Ko kai kayi zaton sarakuna basa mu'amala da matan su?”
Salman ya yi shiru dan shi sam ba wani farin ciki yake ji ba
idan suna yi. Shi kawai yana yi ne ko Allah zai sanya ya samu rahama, ya kuma
fita a hakkin ta na aure. Ganin ba zai yi magana ba yasan yata tashi tana
murmushi ta wani jujjuya ya masa kugu ya kawar da kai, ba burgeshi take yi ba,
hasalima ji yake tamkar ya fashe da kuka dan haushi da takaicin abin da take
yi. Tana fita ya sauke ajiyar zuciya tare da rintsa ido kawai ya hangi Dije
tana ta yi masa murmushi a wajan fuskar shi. Sai ya samu kansa da kin bude idon
yana jin wani dadi a yadda yake ganin ta. Kiran sallar magariba shine ya tayar
dashi daga gurin, ya shiga toilet ya daura alwala daga nan ya shirya ya fito
zuwa masallaci dan kagabar da sallah.
°°°°°°°° °°°°°°°°° °°°°°°°°°°°
Tun da ta idar da sallah ta mayar da goshinta kasa bata sake
dagowa ba, addu'a kawai take yi tana zubar da hawaye. Cikin kaskantar da kai
take gayawa Allah muradanta duk kuwa da cewa tasan yasan tana cikin halin
bukatar taimakonsa. Sannu a hankali ta dago fuskarta sharkaf da hawaye, tasa
bayan hannunta tana sharewa. Gimbiya Sa'adatu kenan wato mahaifiyar sarki
Salman, mace mai tsantsar hakuri da juriya tare da kawar da kai.
D'an ta ne, amman ba ta da wani iko akan shi, daga nesa
kawai suke hango junan su amman basa haduwa face to face saboda an riga an
janye mata shi daga gareta.
°°°°°°°
°°°°°°°° °°°°°°°
Kishingid’e gimbiya shaheeda take a doguwar kujera dake
tafkeken parlorn ta na alfarma. Wanda komai na cikin parlorn kirar samfarin
kayan sarauta ne wanda turawa kewa laqabi da ‘Royal design’. Kai hatta salular
da ke saqale ajikin da bango itama ta Royal ce.
Bayinta biyu ne a zaune kowanne yana mata tausa a kafa d’aya
d’aya. Sai lumshe idanu take ahankali tana mai cigaba da taunar tufar dake hannunta,
Wanda take gutsira ahankali cikin k’asaita.
Wayar tace dake kusa da ita tayi haske alamar saqo ya shigo,
Sai data mula tasha iska tukun sannan ta daga wayar ta duba. Ta jima kafin ta
daga musu hannu alamar su dakata, Sannan ta mike ta gyara zaman wani hadadden
mayafin jikin ta mai beza. Bayin guda biyu suka bi bayanta kowacce kanta a
kasa.
Sashen su ta nufa, Dake dare ne, Tarwar masarautar take da
hasken lantar ki. Tsuntsaye nata kuka. Shiga tayi cikin wani babban parlor. Duk
sun hallara aciki, Kowacce tana hakimce a kujera tana jin kanta. Kallo d’aya
zakai musu kasan manyan mata ne masu aji, Wanda ke watayawa a duniyar masu
kudi.
Gaishe su tayi. Ta samu waje ta hakimce itama. Bayin dake
wajen duk suka basu wuri. Babbar matar ta tsakiya dake hakimce ta mike kafafun
ta akan center table itace tafara magana,
“Shin ya sanar muku
da halin da ake ciki kuwa....?”
“Hmm! Ki bari kawai.. Mun fara sanya fa. Yacemin kwana biyu
ya kasa gane kansa.”
Cewar Haj Huwaila ta bawa Haj Jaleelah amsa tana tana jijjiga
kafafu.
“Shin Gimbiya Shaheeda kin fara ganin alamun canji kuwa?”
Haj Najwa ta tambayi Gimbiya Shaheeda dake kallon su baki
d’aya. Gimbiya Shaheeda taja majina tana jujjuya zobunan daham din hannun ta.
“Toh.. Gashi nan dai.... Ba wani matsala gaskia. Yanzu ma
wanka nakeso nayi ayimin iso wajen sa.”
“Karki sakaci da maganin nan Gimbiya. Wallahi Malam ya
rantse da abinda zai kashe shi wannan maganin babu na biyun sa..”
Haj Jaleela tace da Gimbiya Shaheeda data mike lokaci guda
tana Yatsina fuska,
“Duk yadda ake ciki...”
Sallama ta musu ta dauki hanyar sashen ta. Kallo d’aya tayi
wa sashen mai babban daki tayi gaba tana sake daure fuskar ta.
Su kuwa ko bayan fitar ta sa zancen ta suka yi a gaba.
Sunata shewa suna tafawa. Tamkar ba kishiyoyi ba ada. Aminan juna ne na qut da
qut.
Gimbiya Jaleela ce ta gyara zama tana faman jujjuya ido
tace.
“Ni wallahi so nake a fara bawa mata sarauta a kasar nan.
Ina ji a jiki na zan iya duk wani abu da ake yi a cikin sarauta. Kuma nayi
mafarki nan gaba kadan mata zasu dawo sune suke jan ragamar mulkin masarautar
Basannabas.”
Ta gama maganar tana dora kafa daya kan daya tare da juyawa
ta kalli sauran one by one. Cike da tsantsar dariya irin ta rainin hankalin nan
Gimbiya Najwa ta mike tsaye tare da yin taku daya biyu zuwa uku ta tsaya a
tsakiyar su tana gyara kafadun rigar jikinta tace.
“Kwarai kuwa Hajjaju, ina jin kuma ni aka bawa damar karasa
yin wannan daddadan mafarkin naki da kika fara. Domin kuwa ni na hango kai na
akan wannan kujerar ta sarauniyar Basannabas. Kuma a cikin d'in bin halacci na
har na baki mukamin Baba na, wato waziriya ta. Ke kuma..”
Ta Nuna Gimbiya Huwaila wato yar ciroma tare da cewa.
“Ke kuma na yi miki mukamin Baban Hajjaju Najwa, wato
Galadima. Na san dai wan.....”
Bata karasa ba Gimbiya Najwa tayi saurin da katar da ita ta
hanyar cewa.
“Ya isa dan Allah, wannan ai shirme ne. Idan zaku dawo cikin
serious d'in ku toh ku dawo, amman ta ya zaku zauna kuna ta yi mana wasu
zantuka na shirme. Yanzu mu maida hankali wajan ganin yarinyar nan ta yi aikin
da muka bata, Salman d'an girman kai ne, ko uban shi be yi wannan jiji da kan
ba wallahi.”
“Haka ne kam, dan naga kwanan nan itama ya fara yi mata
gardama, juya dashi amman sai shigen fadin rai.”
Duk suka yi dariya tare da yin tafi da hannayensu. Gimbiya
Huwaila ta ce.
“Sa'adatu ce ma ni take bani mamaki, matar nan Sam taki
yadda da cewa yaran nan baya son ganin ta, amman kullum cikin wahalar da kanta
take wajan koke koke da wasu addu'o'in ta na shirme. Ai gara ka yiwa kanka
maganin matsalar ka, amman kace zaka jira ai sai ka dade, koma ka mutu baka
cimma burin ka ba.”
“Ai Baba (Madaki) yace abu d'aya ne yasa shi barin matar
nan. Shine baya daukar ta a matsayin mutun mai rai, amman da tuni yasa anyi
shekara lahira.”
“Gaba d'aya manta ta nake a cikin tsarin rayuwa ta.”
Jaleela ta fada cikin yatsina fuska. Haka suka zauna suna ta
shirya makircin su kamar yadda suka saba. Ita kuwa Sa'adatu tana sashen ta tana
kukan zuci da na idaniya. Kuncin da take shiga wani lokacin har mutuwa take
roko tazo ta dauketa saboda wahalar da ranta yake yi. Amman tasa a ranta komai
daga Allah yake zuwa, yasan kuma lokacin da zai warware mata wannan masifar da
take ciki.
Tsab ya yi shirin bacci, yaje ya kwanta akan gado sai gata
itama ta shigo cikin shigar kayan bacci masu santsi gasu shara-shara. Gadon
itama ta hau tare da rungume shi ya kawar da kai, tunda tasa hannunta ta shafi
kirjinsa shikenan ya nemi nutsuwa ya rasa. Kansa ya yi girma yaji kamar an dora
masa duniya da abinda ke cikin ta. Wani barin na zuciyar shi kuma yana kusanto
masa ita akan ya yi mu'amala da shi.
Kafin kace menene ya firgice sun zama abu d'aya, koda suka
dawo cikin hayyacin su wani gigitaccen bacci ne ya dauke shi. Ta tsaya tana
kare masa kallo mai cike da fassarori kala-kala. Kanta ta dora saman kirjinsa
take itama bacci ya dauke ta a jikinsa.
Garin ya yi shar
gwanin dadi, sarki Salman ya fito akan farin doki da aka kawata shi da ado mai
daukar hankali. A hankali yake tafiya har ya isa wajan wani ruwa inda wata
tsohowar mata tana durkushe sai kuka take yi. Ya tsaya tare da sakkowa yaje
kusa da ita cikin sassanyar murya yake mata magana.
“Baiwar Allah lafiya? Me yasa ki kuka a cikin mulki na?”
Ba tare da ta wai go ba ta gyara yagaggen mayafin da ke
jikin ta tana share hawaye tace.
“Yara na duk sun guje ni, ba su san gani na bare ganin
fuskata.”
“Suna raye kuma?”
Tace,
“Ban sani ba ni, sai dai ina ji a jikina tabbas suna raye.
Me ye amfanin yaran da zaka haifa da cikin ka amman su guje ka? Me ye amfanin
wahalalliyar nakudar da zaka haifi yara amman su gaza sanya ka farin cikin
rayuwa? Kaico da irin wannan duniyar mai cike da tsantsar hasara....”
Ta wai go a fuska sai kawai yaga fuskar mahaifiyarsa, ta
riko kafafunsa ta riƙe gam tana cewa.
“Zan tafi, zan kuma yin nisa da yara na da suka kasa gane
matsayina a gurin su. Ka tausaya min ka dawo min da yara na, gwara mu zauna
cikin talauci tare da su akan su yi arzikin da za'a raba mu. Karka tafi ka bar
ni ya shugaba, ka tuna yadda ake ji idan aka rasa wani bangare na jiki. Ka
tausaya min ya......”
Sarki Salman dake kwance kan katafaran gadon shi, ga matarsa
kwance a jikin sa, kawai sai ji ya yi ya tashi a gigice yana sakin wata
firgitaacciyar kara. Jikin shi kuwa sharkaf kamar an tsamo tsumma daga cikin
mai....
*KHADIJA*
____Wajen Aisha kawata naje, Wadda muka yi British da ita,
yanzu ta kai matakin lecturer a jami’a. Mun sha hira sosai kafin na dau hanyar
dawowa gida. Ta babbani shawarwari sosai akan rayuwa, Da yadda zan cigaba da
gudanar da ita. Kasancewar garin damina ne tuni hadari ya hadu aka shiga
kwarara ruwa tamkar da bakin kwarya.
Gashi na sallami TK driver tun dazu nace yaje ba komai zan
dawo idan na kammala. Adaidaita sahun da nake ciki sai tangadi take a titi
tamkar zata kifar damu saboda yadda iskar damina ke kad’a ta. Ganin gamu ga
gidan rediyon mu hakan yasa na tsaida shi na falfala da gudu na tsaya a rumfar
motoci, Waya na lalubo na kira Mas’oud nasan shi kullum yana nan, Baya da day
off Saboda kasancewar sa babban ma’aikaci awajen, Na sheda masa ina waje ruwa
ya tsare ni. Cikin barin jiki kuwa sai gashi
Da lema a hannun sa ya karo yai saurin rufamin ita akai,
“Sannu Habibaty.. Ya
akai haka, Ina kika je?”
“Hmm bari dai Habiby.. Wai zuwa nayi na gayda Aisha da naje
wankin kai, Kasan kusa da jami’ar sune shine na biya.”
“Ayyah sannu, Muje ciki ki huta, Dama wannan damina da ake
marka marka..”
“Allah yasa mu wuce Lapia..”
Nace dashi, Muka shiga ciki, Kowa yagan mu sai ya tsokane
mu, musanman ni. Wai na biyoshi wajen aiki na kasa hak’uri. Office dinsa muka
shiga. Sai rawar sanyi nake.Rigar sanyi ya dakkomin acikin kayan custume da ake
ajiyewa. Muka shiga hirar soyayya hankalin mu kwance,
“Kyanta ace Ruwan nan
da ake ni da ke muna matsayin mata da miji. Mezesa mu wani fito aiki.. Ai sai
dai ragargazar soyayyah da..”
Katshe shi nayi. Domin sai ina taka masa birki, Kunya ce ke
lullube ni duk sanda yai wadannan kalaman,
“Wai love sai Yaushe
zaka zo ka gayda Kawu daddy ne?”
“Zanzo Insha Allahu! Banason zuwa ne batare da komai ya
kammala ba. Kinga akwai gini da kawo kudi da sauran su. “
“Gini kuma love?”
“Oum waleeda gwara ace son samu komai na rayuwar da zamuyi
ya zama na is ready . Banason muyi wahalalliyar rayuwa.”
Kullum dai zancen kenan. Na ka’da kai kawai ina mai mamakin
kalaman sa. Ni fa wallahi Saboda rin k’aunar da nake masa ko lefe zan iya yafe
masa .
“Shikenan Mine! Amman da ba sai ka wani wahalar da kanka ba,
Ko da irin haya sai mu fara ko..?”
“Shi kenan Oum Waleed zan samu alhajin mu da maganar, Kinsan
suna ganin Ya Haysam bai aure ba gani zasu yi nayi kankanta.”
Cuno baki nayi gaba na masa gatsine,
“Ai. Ai.. Ni dai nai
dai nima ba canai nima ayi auren ba. Kawai dai saboda Kawu daddy yasan da kai
ne.”
“Haba tawaje na.. Ai
ke tawa ce. Nine mallakin gangar jikin ki da soyayyar ki Insha Allah. In Shaa
Allahu zaki ji..”
Banbashi amsa ba saboda nasan yanzun sai ya kauce hanya.
Mikewa nayi na saqale jakata. Ganin ruwan ya tsagaita.
“Zan tafi gida...”
“Okay muje na sauke
ki..”
Gaba nayi yana biye dani abaya muka shiga mota ya tayar.
Tunda ya fara tuki na juya masa baya ina kallon waje. Yanayi na damina gari
yayi shar-shar dashi.
“Oum Waleeda fushi
ake dani..?”
“Haba ni na isa?
Kawai Ina kallon sarautar Allah ne.”
“Ina son ki.. Ina miki son so tawan..”
Rufe fuska ta nayi da tafin hannaye na da suka sha kunshi na
sudan, Sunyi maroon gwanin sha’awa.
“Lallen ki Yayi
kyau...”
“Godia nake Habiby..”
Har k’ofar gida ya kai ni, Dai dai lokacin da Kawu Daddy ya
dawo Shima. Ganin na fito yasa Mas’oud fitowa Shima ya rissina ya gayshe da
Kawu daddy daya futo da sauri da alama mantuwa yayi,
“Kawu daddy sannu da
zuwa..”
“Yauwa Sannun mu
Khadija..! “
“Yallabai Barka da rana...”
“Barka kadai... Ya
aiki?”
“Alhamdulillah!”
Mas’oud ya bashi amsa yana sosa kai, Kawu daddy ya kalle ni
ya kalle shi,
“Kamar na san shi
ko?”
“Abokin aikinta ne ni
yallabai..”
Cewar Mas’oud, Na juya na galla masa harara,
“Abokin aiki kuma?”
Na tambaye shi ina hade girar sama data Kasa,
“Oganta ne ni.. Naga
garin da lema shine na sauke ta..”
Mas’oud ya bani amsa yana kallon Kawu daddy. Nayi k’wafa
kawai ina galla masa harara,
“Ah Allah sarki, ai na gane ka yanzu. Kai ne mai jinyarta a
asibiti. Angode sosai. Tukur driver baya nanne?”
“Eh nace ya dawo gida
dazun.”
Musabaha sukai da Kawu daddy ni kuma na shige cikin gida da
sauri, Kawu na biye dani. Ya dauki brief case dina a parlor da alamun shi ya
manta, Har ya kai kofa, Ya juyo,
“Khadija..”
“Na’am Kawu daddy..!”
“Idan kin samu Lokaci
zuwa gobe haka zamuyi magana Insha Allah.”
“Toh.. Kawu...daddy..”
Na bashi amsa a rarrabe saboda yadda cikina ya soma
hautsinewa, Kodai ban kyauta bane yadda Mas’oud ke kawo ni gida? Wata zuciar
tabani amsa da ‘Kwarai baki halacci ba Khadija. Driver sukutum guda da mota fa
aka baki..
“Kawu kayi hak’uri ..”
“Kin cika Shirme! Wayace lefi ki kai? Magana kawai zamuyi ta
hankali. Alkhairi ne In Shaa Allahu.”
Yana gama magana ya fice da sauri, Ni kuma na haye sama ina
hada hanya. To maganar me zamuyi? Oho.....

No comments