YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 62-63
*NUSAIBA*
*'YAR AMANA*☘️☘️
Rubutawa Karimatu Abdulhamid
( *MUMMYN MINAL*)
*🌹SUBBAHANALAHI WABI HAMDIHI SUBBAHANALAHIL AZIM*🌹
⚖️
*HAMDALA WRITIN'S ASSOCIATION💪*
_*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL'UMMA📚}}*_
https://www.facebook.com/111403834371046
*✨✨{{H.W.A}}✨✨*
*PAGE 62-63*
____ Haka gidan Mum yakasance kullum cike da danginsu da dangin Alhaji Halliru wato mijin Karima qanwar Mum, inda ABDULJABBAR kullum shima sai yaje gidan yasha hira da Antinsa.
Kishiyar Karima qanwar Mum kuwa tana jin Labarin karima tadawo, ta haukace tabi duniya, dukiyar mijinsu kuwa antatara an ajiye akan sai anga jariryar karima abasu, domin karima tasanar dasu komai game da 'batanta da jaririyarta kuma tace tabawa wani mutum amma batasan waye bane, kuma tin daga nan bata sake sanin wani abu ba gashi yau tsayon shekaru 18 kenan tadad'e tana cikin hauka.
Dan haka daddy yasa ake ta addu'a domin yarinyar intana raye ta baiyana.
*BAYAN WATA DAYA*
'YAR AMANA kuwa da IKIRAM sosai suka mayar da hankali akaratunsu dan ma exam sukeyi nagamawa, inda in sunkamalla zasu jona poly, amma ABDULJABBAR yace NUSAIBA ita sai ta haihu zata fara, dan kuwa cikin ta yanzu yafito sosai yakai kusan wata shidda wanda awoma daqar take yarda yakaita, sosai ABDULJABBAR yake kula da ita akan cin ta shanta da karatunta maganar haqqinsa kuwa babu shi domin sam NUSAIBA taqi yarda, sai ma rigima da take masa akan yakaita gurin baffanta dan haka yamata alqawarin inta haihu zasuje kuma anan zai saketa yakar'bi babynsa da qar yasamu NUSAIBA ta yarda.
Yau ABDULJABBAR koda zetafi gurin aiki sai da yabiya gidan su inda ya zauna sukai ta hira da Antinsa Karima har IKIRAM itama tazo gidan ita da Mus'af, nan Anti Karima take tambayar waye Ikiram nan Mum tasanar da ita itace jaririyar da sukahaihu lokaci d'aya, rungume Ikiram Anti Karima tayi tana kuka azuciyarta tana jin yanzu itama duk inda jaririyar ta take muddin tana raye takai girman Ikiram.
Daqar Su Mum suka rarasheta tayi shiru nan Anti Karima tace " ABDULJABBAR yaishe zaka kawomin surikartawa inganta ne"?
Kallon Mum yayi, wata uwar harara mum tadafka mar, sanan tace " ina sai matar qwarai ya aura zai kawota ku gaisa"
"Bangane ba Yaya Murjanatu mekike nufi"?
Anti Karima tatambaya.
"Hhmm kede kibari Karima yaronan naga yarinyar arziqi na had'ashi aure da ita, amma yaronan yamata wulaqanci ya koreta hakan ma bai isheshiba qarshe de wai sai da yagano dukiyar mahaifinta bata halal bace yasa aka kama mahaifin yanzu haka yana can hanun hukuma atsare, qarshe ya 'bige da auran wata yarinya 'yar matsiyata wanda ni har yau banga wani nata ba"
"Ikon Allah to yaya Murjanatu tayaya auren nasu yakasance tinda baku san kowa nata ba"?
"Oho masa shida magulmacin uban sa ashema andad'e dayin auren acan qauyensu ni bansani ba sai rana daya Allah yatonu asirinsu"
"To yaya Murjanatu ai yanzu shikenan komai yawuce"
"A'a Karima ba abunda yawuce mudin yanaso yaga farin ciki na to yaje ya auri Safna"
"Wacece Kuma Safna?" Karima tatambaya.
Safna 'yace ga Alhaji Usman dala ina fatan kintinashi"?
Ikiram ce tace " haba Mum sbd me kikeyin haka gaskiya ni bangoyi bayan yaya ABDULJABBAR ya auri Safna ba duk da tana qanwar Mijina gwanda itama tasamu nata rabon agaba"
Wani mugun kallo Mum tayiwa Ikiram tace " to Sannu uwata tinda yana auren qanwar uwarki ai bakyaso amata kishiya ba"
Kallon ABDULJABBAR MUM tayi tace "kai kana jina?"
"Eh Mum ina jinki"
"To inaso idan na isa dakai kaje ka auri Safna domin kasan duk irin sonda yarinyar take maka basai nafada maka ba, dama dan ganin ka auri FINAH ne shi yasa ta janye amma nasan har yanzu tana sonka dan haka yazama dole ka aureta"
Cikin fushi Ikiram tace " haba Mum sbd yaya ABDULJABBAR bashi da damuwa shine zaki ringa aura masa matan da ranki yakeso akan me yana zaune da matarsa lafiya sai ansa yaqara aure dole to ni inajin NUSAIBA tamkar jinin jikina sbd haka bazan bari amata kishiya ba Kishiyar ma tsohuwar guzuma irin Safna"
Wani wawan bugu Mum takaiwa bakin Ikiram, ai kuwa bakin yafashe sai jini cikin masifa Mum tace " ke har kin isa ina fada kina fad'a mutumiyar banza kawai"
Ikiram kuwa d'aukar mayafinta tayi takalli Anti Karima, tace " gaskiya Anti kiyiwa Mum fad'a akan abunda takeyi yanzu idan nice akace anayiwa haka agidan aure na zataji dadi"?
Bata jira abunda zasu ce ba tafice tana kuka, Itako Anti Karima kallon Mum tayi tace " gaskiya ne yarinyar nan take fada me zehana ki haqura kibar maganar qarin auren"
Cikin masifa Mum tace " ai qarya kenan ni saina nuna musu nima na isa, bani suka hadewa kaiba" sanan takalli ABDULJABBAR tace " inaso kafara zuwa zance gunta kafin manya su shigo lamarin kuma kar ka qara zuwa gidan nan har sai kaje gurin Safna, kuma banyarda kanuna ni na turo kaba kaji nafada maka"
ABDULJABBAR kuwa cewa yayi "shikenan Mum zanyi yanda kika ce" sanan yatashi yafice adakin.
Ikiram kuwa tana fita agidan su gidan yayanta tawuce a taxi, NUSAIBA nazaune a parlour tana kallo kamar daga sama taji Sallamar Ikiram ai kuwa tana dago kai taga itace da sauri NUSAIBA tatashi suka rungume juna, Ikiram kuwa cewa " tayi yi ahankali kar kimin asarar baby na"
Nan fa suka shiga hirar yaushe gamo, Ikiram ce tace " NUSAIBA baki san qanwar Mum da ta'bata shekaru dadama ba yanzu anganta shin meyasa bakije kinyiwa Mum barka ba?"
Shiru NUSAIBA tayi sanan tace " Ikiram tsoro nakeji bana so injene Mum ta wulaqantani domin ina tsoron fadan Mum shiyasa naqi zuwa dan kullum sai yayanki yace inje amma naqi"
Ikiram tace " ai kuwa kincika wawiya to bara kiji gwanda kisan mekikeyi muddin kinason zama da yaya na, ki san irin siyasar da zakiyi ki shawo kan Mum domin kuwa aure takeso yaqara kuma kinsan wa Mum takeso ya aura?"
"A'a" NUSAIBA tace.
"To Safna qanwar mijina MUM takeso ya aura kinde santa kinsan wayewarta muddin kika bari ya aureta tofa sai kinbar gidan nan ko bakyaso, kuma kifadamin inkinbar nan ina zaki, kinsande sbd auren yaya ABDULJABBAR daddy yariqeki, shi kuma wanda kikeso din ya yaudareki yagudu to wlh kisan abunyi idan Kuma rigar ku kikeso ki komawa azabar Gwaggo kamar yanda kika ba da Labari to za'bi yarage naki.
Domin inaso kisani yayana mutumin kirkine nagartacce wanda ko wacce mace zataso ganin tasamu miji irinsa sbd haka NUSAIBA ina sonki ne shi yasa nake fada miki haka muddin kika bari yaya ABDULJABBAR ya kubce miki lalle kinyi asarar miji har abada.
IKIRAM tana kaiwa nan azancenta tatashi tafice a gidan NUSAIBA tana qiran ta amma taqi juyowa........
Hhmm muje zuwa de my pants
Dan Allah inkinkaranta ki tura asauran groups
*ko kinsan Mummyn Minal tana nan tafe muku da wani qayataccen Novel mai suna MIJINKI MIJINA NE !, hmmm kede nemi naki 'yar uwa kisha karatu dagaji kinsan zaiyi suger, domin samun littafin kituntubi Number nan 09065120158*
*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAKA*🤲

No comments