Breaking News

YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 58-59


 *NUSAIBA*

        *'YAR AMANA*☘️☘️


Rubutawa Karimatu Abdulhamid

( *Mummyn Minal*)




*🌹 SUBBAHANALAHI WABI HAMDIHI SUBBAHANALAHIL AZIM*🌹


⚖️

*HAMDALA WRITIN'S ASSOCIATION💪*

        _*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL'UMMA📚}}*_

https://www.facebook.com/111403834371046

          *✨✨{{H.W.A}}✨✨*


         *PAGE 58-59*


*Ko kunsan cewa sauqe manhajar mujjalar adabi magazine awayoyinku na da muhinmanci matuqa domin ta nan ne zaku ringa sanin abunda ke faruwa a duniyar marubuta, sanan zaku ringa samun littafanmu masu dadi agurin harma da yanda ake girki za aringa koyarmuku, kude ku sauqe manhajar mujjalar adabi magazine awayoyinku, ga kuma muhawara da akeyi domin qaruwarmu, zaku iya sauqe manhajar mujjalar adabi magazine awayoyinku kushiga ta chrome kuyi download ko kuma kubi wanan link din domin sauqe manhajar*


https://www.mujallaradabi.com/p/manhajar-mujallar-adabi.html?m=1

Sai kunzo makaranta da marubuta dama mawaqa da manazarta karku bari abarku abaya nima na tafi domin kar ayi bani.


____ Tashi NUSAIBA tayi tana zun'bure-zun'bure tashige d'akin ta, shiko ABDULJABBAR da wani shu'umin kallo yabita ji yakeyi kamar yabita ya kwaci haqqinsa ta qarfi, amma kawai yayi qwafa ya ci gaba da tsayuwar jiranta.

Can sai gata ta fito da mayafi a hanunta, wani mugun kallo ABDULJABBAR yayi mata sanan yace " wazai fita dake da wanan mayafin? To ni agidana ba'asa gyale maza ki koma ki d'auko qaton hijjabi"


Itako NUSAIBA zun'buro baki tayi sanan ciki-ciki tace " kajini da mutum naga nan matarka da wani d'an iskan mayafi take fita da har zakace ba asa mayafi agidan ka"

Cikin zaro ido ABDULJABBAR yace " ke me kike cewa?"

"A'a nifa bance komai ba" da sauri ta shige dakinta.

Shiko ABDULJABBAR sarai yaji me take fad'a kawai ya qyaleta ne.

Fitowa tayi da qaton hijjabinta na sallah wanda har yana jan qasa.

Kallonta ABDULJABBAR yayi cikin tsokana yace " ko kefa amma da kind'auko wani qaramin mayafi sai kace wata budurwa"

Itako NUSAIBA murgud'a baki tayi tace " to da mecece in ba budurwa ba"

"Hhhhh kinde manta malama ai nariga nakar'be wanan budurcin naji dad'i abuna"

Ai da sauri NUSAIBA tafice tana hawaye.

Shiko bin bayanta yayi yana dariya yana qudura wani abu aransa, domin shikam yayi haquri iya haquri dan gaskiya ahannu yake, gashi tunda yad'and'ana zumarta kullum da begen ta yake kwana gashi yayi wa kansa alqawari bazai qara kar'bar haqqinsa taqarfiba agurinta har sai da son ranta.

Bin bayanta yayi a harabar filin gidan yasa meta, kai tsaye motar sa yanufa yabud'e yashige ya zuge glass d'in motar, ya leqo ta Window d'in motar NUSAIBA dake tsaye yayi wa magana yace " ki zo mutafi  kar mumakara musamu layi"

Ba ta kula shiba kawai takowa tayi ta bude  bayan motar zata shiga.

"Kidawo nan malama waye driver d'inki?!!!!!!!!!!!!

Yayi maganar a tsawa ce ai bashiri NUSAIBA tadawo  gaban motar tazauna tarufe qofar , ta da motar yayi megadi yabud'e musu qofa suka fice agidan.

Sai da motar su tahau kan titi sanan ABDULJABBAR yadubi fuskar NUSAIBA ganinta yayi ta had'e rai, shi abunma dariya yaso yabashi, amma  yadake, yaci gaba da tuqinsa can de yace " ataimakawa yaronan abashi haqqinsa ko bayawa kar ya lalace yabi wasu matan awaje" yafad'a yana kallon NUSAIBA.

Itako NUSAIBA tasan sarai ina ya dosa dan haka cikin tsiwa tace " yadad'e baibi wasu matanba idan yanaso yabi mata dari ma wa yadamu, tinda ba'ason mutum ba'a qaunarsa ko ana dolene mmmmmttttsssssss" tayi tsaki abunta.


Wata mahaukaciya ce tahawo kan titin zata tsalaka, gashi ABDULJABBAR yataho aguje babu yanda baiyi ba dan ya kaucewa Mahaukaciyar amma ina tini yakwasheta.

Salati NUSAIBA tasa tare da kuka, shima ABDULJABBAR arud'e yaci wani wawan burki yafita amotar aguje yayi kan Mahaukaciyar itama NUSAIBA aguje tafita tabi bayansa, gashi kan titin yahanga amma bakowa, NUSAIBA ce cikin kuka tace " please kamata mukaita asibiti"

Haka kuwa akayi suka kamata sukasa amota suka shiga ABDULJABBAR yaja motar, tun kafin suqarasa asibitin yaqira abokinsa dr Musa yasanar dashi komai, ai kuwa suna isa horses suka taresu suka d'auki wanan Mahaukaciyar suka nufi emergency da ita.


Shiko ABDULJABBAR da NUSAIBA kai tsaye suka wuce office d'in dr Musa inda bayan sungama gaisawa ABDULJABBAR yayiwa dr Musa bayani kamar yanda NUSAIBA tace. Akan abu namata motsi aciki.


Nan dr Musa yaqira wata Norse yasa tatafi da NUSAIBA dan tamata duk abunda yadace, ai kuwa nan sukaje suka mata gwaje-gwaje harda scanning, sanan aka kawo wa dr Musa sakamakon nan dr Musa yabud'e yagani, murmushi yayi sanan ya kalli ABDULJABBAR yace " congratulations sauran kadan kazama daddy.


Tashi ABDULJABBAR yayi yace " bangane ba mekake nufi dr Musa?"

"Abunda nake nufi shine matarka na d'auke da ciki har natsawon wata4

"Allahu Akbar" ABDULJABBAR yace.

Sanan yayi sujadar shukur, kamar yanda manzon Allah salallahu ailaihi wassalam, yace idan abun farin ciki yasamu dayanku to kuyi sujjada domin nuna godiyarku ga Allah.

Itako NUSAIBA aguje tafice ad'akin tana kuka, ai da sauri ABDULJABBAR yakar'bi saqon yabiyo bayanta.

Yana qiran ta amma taqi kulashi har ta fita a asibitin mai keke nafef tatare tashige, sai da sukayi tafiya mai nisa mai nafef din yatambayeta ina zekaita da zata ce gidan daddy, amma tafasa, tasa yakawota gidan ta dake unguwar Ahmadu bello way.

Shiko ABDULJABBAR yana ganin tashiga nafef sai yayi tunanin gurin Anti Amarya zata, dan haka da sauri ya shige motar sa yanufi gidan su kai tasaye 'bangaren Mum yanufa cikin murna dan har yamanta gabar da Mum takeyi dashi,  Mum nazaune akan kujera yafad'o mata d'aki yana sallama, cikin farin ciki yace " albishirinki Mum!  Yanzu daga asibiti muke......... " ABDULJABBAR kafita min a parlour tun raina bai 'baci ba domin kuwa banso ganinka kajeka can ka qarata"

"Dan Allah Mum kitsaya kiji NUSAIBA ce akace tana da............ Baiqarasa ba sai ji kakeyi Tas !Tas !!Tas!!! Mum tasauqe masa maruka uku kyawawa, sanan tace " fitamin mutumin banza kawai, ai bazan ta'ba sauraranka ba koda kuwa uwata ce tadawo tinda kabijiremin"


Shiko ABDULJABBAR cikin qunar zuciya yafice a shashin Mum yanufi na Anti  Amarya da isarsa Anti Amarya tafara tambayarsa ina Ikiram, dan haka sai yagane batazo nan ba, agurguje suka gaisa yafice yashiga motar sa a d'ari yabar gidan yanufi nashi domin yana tunanin NUSAIBA nacan.


Ai kuwa da shigarsa parlour ya ganta zaune akan kujera tana kuka,  zama yayi akusa da  ita, yakamo hanunta ya riqe yace " haba My  sweet wife yanzu dan ance kina da ciki shine kike kuka  maimakon kiyi murna?"

Kwace hanunta tayi sanan cikin masifa tace " ni karabu dani tayaya bazanyi kuka ba ni gaskiya banason cikin nan dole acireshi domin bazan ta'ba sonsa ba"


"You are very very stupid NUSAIBA!

Yanzu dan bakyasona shine jinina ma baza kisoba please NUSAIBA karkimin haka dan Allah kibarmin jinina wlh ina sonsa wai me nayi mukune da bakwason haihuwa dani please?"

ABDULJABBAR yafad'a yana hawaye yana kallon 'YAR AMANA.


Itako 'YAR AMANA kallon sa tayi cikin masifa tace "bana sonka ne ABDULJABBAR ni bana sonka sbd haka tayaya kake tinanin zan haihu da wanda bana so?"

"Shikenan NUSAIBA naji yanzu kifad'amin wakike so?"

Shiru NUSAIBA tayi tana kuka.

Shiko ABDULJABBAR cigaba yayi dacewa "to ya baki da amsane kawai kice min har yanzu wanan mayaudarin saurayinaki kikeso wanda na tabata bake yake soba jikinki yakeso, inda yasamu kuma da yanzu bakwa tare"


"Nidai koma me zakace kace amma bana sonka kuma cikin nan bazan haifeshi ba"

"Please NUSAIBA kifad'amini mekikeso nabaki domin kibarmin jinina, idan dukka abunda na mallaka kikeso ashirye nake nabaki dan de karki salwantar min da d'ana".


"Taya kake tinanin abun duniya nakeso, ni banason komai sonka ne kawai banayi"

"To shikenan naji NUSAIBA badan niba dan Allah karki salwantar min da d'ana inaso kitina ko nata'ba miki wani abu na Alkairi arayuwar nan, to nima inaso kisakamin tahanyar luramin da abunda yake cikin ki"

Yana kaiwa nan yashige d'akinsa yabarta a gurin.



Itako NUSAIBA tsayawa tayi a parlour d'in tana jujuya maganar sa, tabbas tasan ya ta'ba mata abun Alheri arayuwarta domin yaceci rayuwarta daka fad'awa halaka.

Nan tafara tinanin ratuwarta tabaya, kuka sosai takeyi cikin kuka take cewa " shikenan ABDULJABBAR zan kula ma da abunda ke cikina duk da banasonku amma zanyi hakan ne dan kar nazamo mai rama Alkairi da sharri domin ni bana sonka, amma kataka rawa arayuwata kome nazama agaba kaine sila domin kacireni daga rayuwar jahilci kakawoni birni ta dalilinka ratuwata ta inganta, sai de ABDULJABBAR bazan ta'ba addu'ar insoka ba domin kuwa hakan qalu balene atayuwaya taga ba dan kuwa mahaifiyarka zata iya sawa akawar dani, shi yasa banaso in haifi d'a ko 'ya dakai dan kar yazo yayi irin rayuwar da nayi abaya. Kuka sosai NUSAIBA takeyi kamar zata shid'e k'arshe barci yayi gaba da ita a gurin..........



Hmm muje zuwa my pants

Shin ko NUSAIBA zatabar cikin jikinta oho?



*MIJINKI MIJINA NE*

Labari daya acikin millions kede 'YAR Uwa kinemi naki kisha karatu, domin kuwa dagajin sunan littafin kinsan akwai gwarama.



Dan Allah idan kin jaranta kitura asauran groups




*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAKA*

No comments