SARAN BOYE 38
No. 38
.............Duk yanda su Abdallah sukaso a tuhumi Yoohan tun a asibiti game da zancen Nu'aymah baba malam ya hana, hakama su Abba basu bada goyon baya ba.
Zuwa yanzu dai Yoohan ya fahimci alaƙar
baba malam da patient ɗinsa. Ya kuma gane Nu'aymah. Sai dai taka maimai abinda
bai gama fahimta ba shine hotunan da Abdallah ya kawo masa da tsantsar ɓacin
ran da yake ganni tattare da samarin gidan su baba malam ɗin gaba ɗaya harsu
malam ƙarami da ya fara sabo da su.
Bayan samun damar shiga ɗakin da
Nu'aymah ke kwance da sukayi ɗai-ɗai suka dubata duk da bata farfaɗo ba baba
malam ya tattarasu su duka suka bar asibitin. Dan Yoohan ya tabbatar musu ba'a
buƙatar wani mai jiyya tattare da ita har sai ta farfaɗo.
Suna tafiya baifi da mintuna talatinba
shima ya amshi key ɗin motar Dr Mubarak Solo ya jashi zuwa gidansu baba malan ɗin.
Kamar yanda yay tsammani ya iske kowa a gida da alama ma zaman jiransa sukeyi.
Omar ne ya fito yay masa iso har sashen Hajjo. Hajjo ce kawai a sashen sai su
baba malam su duka. Omar ma yana shiga da shi fitowa yayi.
Duk da Hajjo najin haushin Yoohan sai
ta danne ta amshesa da fara'a kamar ranar salla dasu Ahmad suka shigo da shi
wajenta. Ta kuma kawo masa ruwa da lemo. Yaji daɗi kuwa sosai, tare da sake jin
ƙaunar ƴar tsohuwar har cikin ransa.
Bai iya sakin jiki ya sha ruwan yanda ya
kamata ba, ya ajiye kofin tare da sake nutsuwa yana jiran ji daga garesu.
Bayan shuɗewar shiru na wasu mintuna
Abba Musbahu yay gyaran murya idonsa akan Yoohan da kansa ke a rissine. Ba bu
wani kwalo-kwalo ya shiga zayyano masa duk abinda ke faruwa.
Sosai mamaki ya
kusa kashe Yoohan, ya sake tsuke fuska yana girgiza kansa. Idanunsa da suka kaɗa
sukai jajur ya ɗago ya duba baba malam, “Uncle ni a rayuwar turai da nayi ma ba
taɓa aikata haka da wata mace da yardarta ba ma balle anan ƙasata. Nasan anyi
hakane kawai don shiga tsakanin alaƙarmu, ko kuma kasancewata musulmi a yanzu.
Sai dai kuma ko wanene bai samu nasara ba, dan babu wani ɓatanci da za'aimin
koda yafi wannan da zai girgiza zuciyata daga barin bautama UBANGIJINA shi kaɗai.
Ban musulinta domin kowa ba, ba kuma zan fita domin wani ba. Nasan zaku yarda
da ni, Tunda har kuka yarda da dani alokacin da ba addininmu ɗaya ba ma, dan kuɗin
nagartattun mutanene masu ƙyawawan zukata. Zan faɗa muku ainahin gaskiyar
abinda ya faru”. Cikin nutsuwa da ɗacin rai ya bayyana musu tun daga haɗuwarsa
da Nu'aymah ta farko har zuwa ranar da ya musulinta. Bai iya ƙarya ba tun yana
kafirinsa, balle yanzun da ya ƙara sanin muhimmancin gaskiya a harshen ɗan
adam. dan haka ko kissing ɗin Nu'aymah da yayi bai ɓoye musu ba ya faɗa. Ya ɗora
da faɗin, “Zan koma asibiti yanzun insha ALLAH, na muku alƙawarin bincike akan
cikin da akace itama ya zuba a jikinta, dan sam ni dai banga wannan matsalar
tattare da itaba saboda ba akanta na fuskanci matsalarta ba. Amma zan kawo muku
hujja a yanzu da yardar ALLAH”.
Gaba ɗaya sun gamsu da bayaninsa har
Hajjo da Abba Musbahu ke fassarama maganar Yoohan ɗin dan da turanci yay
bayaninsa.
Baba malam ya ɗanji nauyin
zuciyarsa ya ragu sosai da bayanin Yoohan, a yanzu kuma hankalinsa ma yafi
kwanciya da binciken Yoohan ɗin fiye da na likitocin farko. Sannan tunaninsa ya
fara karkata akan wani abu da ban kuma.
Ko mintuna goma Yoohan bai ƙara a gidanba ya
fice ya koma asibiti. Sam baiji zafin su baba malam ba akan wannan maganar. Sun
ƙarama mutunci a idanunsa ne, haka yake son iyaye su kasance akan ƴaƴansu. Ya
sake fahimtar addinin musulinci addinine abin koyi, domin yana ƙyamatar abinda
wasu addinan su a wajensu ado ne, Wayewace. Hasalima zuciyarsa wani hasashe
take masa daban akan wannan ƙullin da akai musu. Duk da bai tabbatar ba amma
zuciyarsa na kinsa masa papa.
Tare suka koma
asibiti da su Abdallah da har yanzu su dai basu wani gamsu da Yoohan ɗinba.
Shi da Doctor Aysha suka gudanar da duk
wani bincike akan Nu'aymah da har yanzun tana cikin halin sumar allurar da
sukai mata. Dr Aysha ta tattara komai zuwa lab ta danƙama wanda ta aminta da
shi. Daga haka ta dawo ta sanarma Yoohan.
Kansa kawai ya iya ɗaga mata, dan yana
lafe jikin kujerarsa ne idanunsa a lumshe. Fuskar nan tasa kuwa a tsuke take
matuƙa. yana cigaba da nazarin komai dalla-dalla. Babu abinda ya iya taɓukawa a
wannan yinin sai zuwa salla idan lokaci yayi da leƙa Nu'aymah da suke tsumayen
farfaɗo warta a kowane irin lokaci.
Misalin ƙarfe biyar saura na
yamma Dr Aysha ta kawo masa duk results ɗin bincikensu. Ko buɗewa baiyi anan ba
ya miƙe da shi ya fito, su Abdallah da suka zame masa bodyguard shi da Nasir da
Ahmad biye da shi.
Har zuwa yanzun su baba malam duk suna
gida suna jiransu. Yanzun dai saɓanin ɗazun, duk mazan gidan ne suka taru banda
ƴammatan da yaran da su Umm, dan hajjo ce kaɗai mace ma a cikinsu. A maimakon
Yoohan ya buɗe yanzun ma sai ya bama Abdallah damar buɗewa dan ya tabbatar musu
zai gane.
Tun a result ɗin
farko Yoohan yaji saɓanin abinda yay tsammani. Hakama sauran ƴan gidan, aka
tafi na biyu dana uku, Abdallah baima ƙarasa na ukun ba Yoohan ya miƙa hannu a
hankali ya zare file ɗin da takardun results ɗin ke a ciki yana binsu ɗai-ɗai
da kallo. Tabbas babu ƙarya dai-dai Abdallah ke faɗa. Dan kuwa duk Results ɗin
sun nuna Nu'aymah tasan ɗa namiji, ta kuma ɗauki cikin sati shida da wasu
kwanaki, cikin kuma tayi ɓarinsa kwana biyu kenan.
Dimmm kan Yoohan yayi na ɗan wani
lokaci, sai kuma ya sake duba duka takardun sannu a hankali. Su baba malam dai
babu wanda yay magana sunata binsa da kallo. Sai Abdallah ne da Naseer ke
jifansa da wani mummunan kallo tamkar zasu hau kansa da duka.
A harzuƙe Abdallah yace, “Yanzu
kuma wace ƙarya zakai mana dan ka kare kanka?”. Yay maganar yana riƙo rigar
Yoohan.
“Abdallah!!!!” Abbansa ya daka
masa tsawa yana miƙewa. Ransa a ƙololuwar ɓace yace, “Sake sa”.
Kamar Yah Ab ya kashe Yoohan
haka yakeji, amma kasancewar an musu tarbiyyar jin maganar magabatansu sai ya
saki Yoohan ɗin da shi sam hankalinsa ma bawai yana tare da su baneba. Dan gaba
ɗaya zuciyarsa ta shige a wani sabon nazari ne. Ɗan hankaɗashin da Abdallah
yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa. Ɗagowar da zaiyi sai idanunsa suka sauka
jikin Windown falon hajjo. Inuwar mutum ya gani, yay ma wajen kallon kusan
seconds goma kafin wanda ke a tsaye ya farga ana kallonsa yay saurin barin
wajen. A take kan Yoohan ya kawo masa wuta kasancewarsa mutum mai kaifin
tunani da basira.
Kallon sashen da baba malam yake yayi,
ya ɗanyi luuuu da idanunsa da haskensu ya ɗan sirka yana wani bahagon murmushi,
kamar zai lumshe su sai kuma ya ɓuɗesu a hankali. Cikin muryarnan tasa mai
kauri da amo data hadu da ɓacin rai a yanzun yace, “Uncle wannan tatsuniyar
akwai marubucinta kusa da mu daf. Amma mizai hana ka bani damar yankar ticket ɗin
fara game da shi? Dan ni bana wasa a saman ruwa tunda ba masinci bane. Nafi
yarda da shiga ƙarƙashin ruwan kasancewata mai yawan bincike akan ma'adanai.
Kasan masu iya magana kance idan ka hango biri bisa tsumagiyar reshe ba
gangancine ya kaisa ba, tsabar ƙwarewa ce a iya hawan bisa. Ko zaka amince ka bani
aurenta idan ta girma?”.
Kowa a falon sai da ya
zaro idanu waje, harma da masu zabura. Nasir da Ya Ab kam ai dingangan suka
tsaya akan ƙafafunsu tare da hassalowa lokaci guda kamar zasu haɗiye Yoohan da
ko kallo basu ishesaba. Sai dai kafin su ƙarasa Abban Adawiya ya daka musu
tsawa. Tilas suka ja burki badan rayukansu sunso hakanba.
A karon farko baba malam
yay tattausan Murmushin da har haƙwaransa sai da suka bayyana. idanunsa ƙyam
akan Yoohan. zamansa ya gyara da ƙyau yabi duk jama'ar falon da kallo, su Abban
Adawiya ma duk murmushin sukeyi, hadda hajjo da malam ƙarami ke fassarama
maganar yoohan ɗin.
Murmushi baba malam ya
sakeyi a karo na biyu, kafin yace, “Yoohan maganar aure ba abin wasa bace a
musulinci, dan haka bazan iya baka amsar bukatarka a yanzun kai tsaye ba. Amma
kaje zanyi magana da ƴan uwana, duk hukuncin da muka yanke zamu sanar maka
insha ALLAHU”.
Duk da Yoohan yaso samun
amsar baba malam take a wajen sai kawai ya jinjina masa kai alamar ya amince da
hakan. dan haka ya miƙe yay musu sallama ya fice abinsa yana jifan Naser da
Abdallah da wani irin kallon na ban ƙyaleku ba kuma, kamar yanda suma suke
binsa da kallon kishi da tsana.
A yanzun kam zamu iya cewa
komai ya harmutse musamman a gidan su Nu'aymah. Dan tun bayan barin Yoohan
gidan baba malam ya kasa zaune ya kasa tsaye da fashin baƙi akan kalaman yaron
mai hikima. Kai kawo kawai yake a bedroom ɗinsa tamkar mai safa da marwa.
Hakama Abdallah da Naser hankalinsu a matuƙar tashe yake, dan su dukansu suna
tsananin son Nu'aymah har cikin ransu. Umm kam da hajjo bama a maganar halin da
suka tsinci kansu a ciki. Umm ba maganar wa Nu'aymah ya kamata ta aura bane
damuwarta. Abinda likitocin keta tabbatarwa ga ɗiyarta shine tashin hankalinta.
Itace ta haifi Nu'aymah, itace tai mata tarbiyya, sannan a gabanta ta tashi har
zuwa yanzu da ake akan rikicin. Tunda take da yarinyarta bata taɓa kamata da
kuskuren sauka akan turbar tarbiyyar data ɗorata ba. To tayaya za'ace hakan ta
faru? Kanta ya kulle gaba ɗaya, tama rasa wazata gaskta tsakanin likitoci
da Nu'aymah. Dan zuciyarta taƙi aminta ƴarta zata aikata haka, to sukuma
likitocin mizaisa su musu ƙarya? Ta yama zasu musu ƙarya bayan sun kasance
daban-daban?.
A ɓangaren Yoohan kam yana fita
yaci karo da Solomon. Bai wani zaman tunanin yanda akai ya biyisaba ko inda ya
samo motar da yazo ɗaukarsa kawai ya shiga kusa da mazaunin driver.
A tsorace Solomon ya dubesa,
kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru. saurin zagayawa yay mazaunin driver ya
tada motar suka bar anguwar. Har suka isa hotel babu wanda yace uffan a
tsakaninsu. Solo yay masa rakkiya har ɗakin da ya kama masa. Yana ganin ya
shiga shi kuma ya koma da baya. Wayarsa ya zaro yay kiran papa. Bugu biyu kuwa
Papa ya ɗaga saboda muhimmancin da Solo yake da shi a wajensa. Cikin girmamawa
ya gaishe da shi, kafin suyi magana mai tsajo wadda bilyn ku bataji saboda da
yare Solo ke magana. Sun kusa mintuna talatin sannan Solomon ya yanke wayar
yana wani cizon lips da yin ƙwafa.
Ƙarar waya ce ta saka
Yoohan dake zube saman gado idanu a lumshe ko takalmi bai cire ba buɗe
idanunsa. Kasancewar ring ɗin daya sakama iyayensa da banne yasa ya fahimci
papa ne. Sai da wayar ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. Ya saka a kunne batare da
yayi maganaba.
Daga can Papa yace, “Yoohan kana
lafiya?”. “Uhhm!” Yoohan ya amsa a taƙaice. Papa da keta ƙoƙarin danne fushinsa
yace, “Ni bansan lokaci daka fara zama maƙaryaci ba. Ni nasan dagajin muryarka
akwai matsala ai, dan an kirani daga asibitinku an sanarmin duk abinda ke
faruwa”. Kamar Yoohan zaiyi magana sai kuma yay shiru abinsa yana sake tsuke
fuska. Takaici ya kuma kume papa, yace, “John kana jina kuwa?”. Yanzunma kamar
bazai amsa ba, sai kuma ya nisa muryarsa a harɗe yace, “Papa inason nayi aure!
Kuma ɗiyar Sheikh Sooraj Hashim jibiya zan aura, sai dai yarinyar ta cika
ƙankanta”.
Wani irin bugawa ƙirjin Papa yayi a
lokaci guda. Tamkar wanda aka ƙwaɗama guduma a saman kai ya miƙe zumbur da faɗin,
“What?!. John! Are you Mad?!!”. Yanda papan yay maganar da tsananin tsawa ne ya
saka Yoohan janye wayar daga jikin kunnensa yana matse idanu tam-tam. Sai kuma
kawai ya yanke wayar yay wurgi da ita ta tarwatse ƙasa kamar wani zararre.
Harya ɗan zabura zai miƙe sai kuma ya koma baya ya sake zubewa a gadon yana
ambaton addu'ar da Manager Hamza Ibrahim da a yanzu suka sake zama abokai sosai
ya koya masa. Ita ya shiga maimaitawa a cikin ransa. Cikin amincin UBANGIJI a
hankali yaji ƙirjinsa ya fara rage nauyi, sai kuma wani irin barci ya fara
fisgarsa a hankali.
Gaba ɗaya papa ya haukace a
gaban abokansa da ƙanninsa. Dan suna a tare lokacin wajen wani meeting ɗinsu na
manyan ƙauyensu, dan dama yaje ƙauyensu ɗinne tun jiya da daddare saboda
meeting ɗin mai muhimmanci ne suka shirya yi.
Uncle Godwin ne ya kama hannunsa ya
zaunar da shi yana faɗin, “Hah Friend. Please calm dawn ”.
Papa ya furzar da
wani zazzafan huci jikinsa na wani irin tsuma, ya doka sandar hannunsa a ƙasa
yana cizar lip ɗinsa na ƙasa da masifar ƙarfi. Da turanci yace, “Tayaya kake
tunanin hankalina zai kwanta Godwin? Ko nauyin faɗamin Yoohan baijiba wai zai
auri ƴar arewa, ɗiyar hausawa masu sallah?”.
Da sauri Uncle Mike yace,
“Ah!Goshpower wani lokacin kana abu kamar ƙwaƙwalwarka baya aiki da kyau. kai
nefa ka sanar min yaron nan ya sanar maka yana da manufa akan duk abinda ya
keyi. Mizai hana ka amince masa ya aureta ɗin. Muma wata damace tazo hannunmu
akan mahaifinta.....”
A fusace papa yace, “Sai kuma akace muku
da ɗana kawai zamu iya samun wannan damar? Salon suje su maidashi mai salla, to
ni......”
Saurin ɗaga masa hannu wani da suke kira
Chief yayi da sauri. Ya juya maganarsa zuwa yarensu da ayanzuma bilynku bataji
ba😪. Magana ya farayi kamar zai haɗiye harshenshi cikin maida gaba ɗaya
hankalinsa ga papa. A mamakina kuwa sai naga gaba ɗaya papa ya nutsu yana
saurarensa tamkar ƴan uwansa. A hankali na ga fushin papa ya fara sauka daga
fuskarsa. Saima ya koma sakin wani mugun murmushi yana gyaɗa kai. Kafin ya miƙe
cike da wani irin farin ciki ya rungume Chief ɗin. Suma sauran duk tsantsar
farin cikinne ya bayyana a fuskokinsu. Da alama dai shawarar Chief ta zauna da
ƙyau a zukatansu.
Tashi papa yay ya shiga neman Number
Yoohan. Sai dai kusan kira goma bata shigaba. Canja akalar kiran yay ga
Solomon.
Yoohan na kwance har yanzu a
gadon Solomon yay knocking. Bai motsaba balle ya amsa masa. Shikuma Solo jin
yayi har kusan sau huɗu babu amsa sai kawai ya tura ƙofar ya shigo. Ƙarasawa
yay inda Yoohan ɗin ke kwance cike da tsoro da girmamawa yace, “Am sorry sir.
Boss ne yace na baka waya”. Kamar Yoohan bazai tankaba ya watsar da shi. sai
kuma zuwa can ya miƙa masa hannu alamar ya basa wayar. Yana bashi ya fice
abinsa. Yoohan ya ɗora wayar a kunne batare da yayi magana ba.
Cikin sanyin murya papa daga can yace,
“I am so sorry my son. Raina ne kawai ya ɓaci dan ina tsoron su canja min kai
su cuceni. Amma kuma sai nayi tunani da sake tuna bayanin da kaimin kwanaki sai
na fahimci kaima ba ƙaramin abune mai muhimmanci zai saka yin hakan ba. yanzu
yaya kaso ayi to?”.
A karon farko Yoohan yayi wani
munafukin murmushi ya kai hannu ya shafi sumar kansa har zuwa sajensa. Idanunsa
ya buɗe a hankali ya sauke bisa frame ɗin da akai adon ɗakin hotel ɗin da shi.
Magana ya farama papan nasa da yare cikin taushin murya.
To su dinɗin dinkum balkisu saina koma gehe kawai ina zare
idanu dan anzo dai-dai wajen. Turancinma da yaya nake haɗosa nake masa fassara🙄😜🚶🏻.
Papa da Yoohan sun ɗauki lokaci
mai tsaho suna waya. Dan har sai da na ƙosa kafin su kammala. Yanda naga Yoohan
ɗin ya ɗan rage buyagin nasa ne ya sakani fahimtar maybe har sun gama tsara
wani abune.
★★★★★
Kusan ƙarfe tara na dare
Nu'aymah ta farfaɗo. Dr Sa'ad dake tare da ita dan duty ɗin dare ne da shi yay
azamar kiran Dr Yoohan da har yanzu yana a hotel ɗin bai kuma waiwayar asibitin
ba.
Cikin kuwa mintuna ƙalilan ya shigo
asibitin. Tsabar yanda ransa ke a jagule sai ya toshe idanu da baƙin Glasses da
yay masifar sake fiddo masa ƙyawun fuskarsa da kwarjinin hasken musilinci dake
mamaye da shi. Tunda ya shigo asibitin baiyi magana da kowa ba. Ko gaidashi da
Nurses suke da sauran ma'aikatan hannu kawai ya dinga ɗaga musu kansa a
ƙasa ya rufe rabin fuskar da p-cap bayan glasess ɗin. Shi dai Solomon na biye
da shi kamar jela.
Ɗakin da Nu'aymah ke a kwance ya
tura a hankali ya shiga da sallama ƙasa-ƙasa. Dr Sa'ad da Nurses guda biyu dake
a tare da shi suka amsa suna ɗagowa. Da girmamawa Nurses ɗin suka risina suna
gaishesa. Batare da ya amsa musu ba suma ɗin ya ɗaga musu hannu kawai. Kafin ya
miƙama Dr Sa'ad hannun sukayi musabaha shi kuma.
A hankali ya juya kansa
zuwa ga sashen da kan Nu'aymah ya ke. Ya ɗan ranƙwafa kanta ƙaɗan ya janye wani
igiyan na'uran dake a gefen kanta gab da kunne.
Yanda ƙamshin turarensa ya buga mata
hancine ya saka ƙirjinta harbawa. Buɗe idanun nata tayi da ƙyar saboda bala'in
nauyin ciwo da sukai mata. Dai-dai Dr Yoohan ya dubeta shima yana ƙoƙarin zare
glasess ɗin idonsa. Kallon ido cikin ido sukaima juna, duk da ita ɗin
dishi-dishi take ganinsa hakan baisa ta gagara ganesa ba.
Wani irin juyawa
kanta ke mata, daga ciki tanaji kamar ana karta mata ƙarfe, zabura tayi, ta
yunƙura zata tashi Sai kuma tai saurin dafe kan nata tace, ‘Aushhh kaina!’.
Yoohan da shima zuciyar
tasa ke wani irin harbawa, da sauri ya wani ɗauke idanunsa daga kanta cike da
basarwa, tamkar bai fahimci halin da take a ciki ba.
Yanda jikinta ke wani irin ɗan karkarwa
ga kanta data riƙe da duka hannayenta tana jujjuyawa ya saka Nurses ɗin nufarta
da sauri tare da Dr Sa'ad. Yoohan dai na tsaye baiko motsaba. Sai dai yana
kallonsu ne ta ƙasan ido. Yanda duk sukaso Nu'aymah ta nutsu hakan ya gagara,
dan ganin Yoohan ɗin ya sake dawo mata da komai cikin memory ɗinta, wanda hakan
ke mata barazana cikin kanta tamjar ƙwanyarta zata tarwatse.
“Ku barta” ya faɗa a hankali
tamkar ba shine yay maganar ba. Baya Nurses ɗin suka ja domin cika umarninsa,
amma tausayin Nu'aymah fal ransu. Dr Sa'ad kam sai ƙoƙarin son riƙo hannun
Nu'aymah data riƙe kanta da shi gam ya keyi. A bazata yaji an riƙe masa hannun
lokacin da yake gab da ɗorasa saman nata..............✍

No comments