SARAN BOYE 28
No. 28
............Sake buɗe idanun yay ya saukesu bisa giza-gizai dake yawo cikin hasken sararin samaniya na yanayin asubahi. Karan farko a rayuwarsa da zuciyarsa ta tafi wajen tunanin da girmama UBANGIJI da ya halicci sammai, gata dai babu icce ko ɗaya daga kowacce kusurwa ta duniya da zakai zaton ta riƙeta. Sannan babu wata sarƙa ko ƙarfe da suma suke amsa sunan ginshiƙi a gareta. Da rana hasken *_Rana_
* ya mamayeta. Da dare hasken *_Wata_* ya ƙawata ta da adon taurari. da *_Damuna_* na _Giza-gizai_. Lokacin asubahi takan canja kala zuwa sky blue da wasu ado masu ban mamaki da al'ajabi. Hakama da yammaci lokacin faɗuwar rana takan ƙawatu da kalar sky blue da na yanayin faɗuwar rana. Duk wannan hikima da rahamar akan azurtamu da sune babu ko naira ɗaya. Babu kuɗin haraji babu na ƙarshen wata. To miyasa wanda ya azurtamu da ita bai taɓa jiran mu biyasa da ko taro ba? ‘saboda shi ɗin *_(SARKI NE GAGARA MISALI DA BAUTA KAWAI AKE KAƊAICE SA)’_* Wani yanki na zuciyarsa ya
bashi wannan amsar.
Samun kansa yay da sake lumshe
idanu ya sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya saboda wata kalma data faɗo cikin
kunnensa daga massallacin da aka kira salla dan sun saka tafsir ne.. (Kana son
sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?). Furicin ya fito daga bakin Sheikh
Sooraj Hashim jibiya (Baba malam) dan sun saka tafsir ɗin nasa ne.
‘Tabbas ina son sanin
ni'imar dake cikin addinin musulinci?’. Ya amsa tamkar shi ɗin akeyima tambayar
kai tsaye. yana mai cigaba da kallon yanda wata keyin ƙasa cikin giza-gizai
alamar lokacin faɗuwarsa yayi, zai bama rana guri itama tazo ta cika umarnin
ALLAH (S.W.A) akan aikinta.
Tabbas wannan tambaya ta tsayama
Yoohan a zuciya. Dan da ita ya ƙarasa sauran daren daya rage masa. Akan kunnensa
har aka kira assalatu akai salloli a massalatai. Sai da gari yay haske sosai
sannan ya iya barin jikin Window ɗin zuwa toilet.
Ji yake a ransa bazai taɓa samun nutsuwa
ba sai ya dangane da gidan baba malam a safiyar nan. Dan tabbas yana buƙatar sanin
(Hanyar fahimtar ni'imomin dake cikin addinin musulinci? A yau).
A gaggauce ya gudanar da komai.
Kamar ko yaushe yay shirinsa cikin ƙananun kaya. Blue jeans da farar shirt mai
gajeren hannu. Sai ya ɗora suit jacket fara tas itama. Yau dai bai saka necktie
ba, maɓallin shirt ɗinma ba duka aka rufe ba. Cikin ƙamshinsa ya baro cikin
hotel ɗin batare daya nema inda su Solomon suke ba.
Safiya ce sosai a garin,
hakan yasa da ƙyar ya samu keke napep, shima da mutum ɗaya a ciki. Bai damu ba,
duk da kuwa wannan shine karan farko a tarihin rayuwarsa da zai shiga napep ɗin.
Lokacin da mai napep ya tambayesa ina zasa? Da ƙyar ya iya haɗa hausan ya bashi
amsa da sunan baba malam kawai. Dan dama bawai ya iya hausan bane yana dai jin
abubuwa sosai saboda mu'amula da mutane marasa lafiya akan aikinsa. Sai dai bai
iya maidawa, bayan gaisuwa sai abubuwan da baza'a rasaba suma ɗai-ɗai ne.
Sai da aka fara ajiye wanda ya tarar a
ciki kafin shi a kaisa. Kusan dubu uku ya miƙama mai napep ɗin. Da mamaki shiko
yake kallonsa, yama rasa mizai ce masa dan ya fahimci hausa ba isarsa tayi ba.
Sake miƙo masan da yayne ya saka mai napep ƙoƙarin haɗa ɗan turancinsa ya sanar
masa naira ɗari da hamsin ne kuɗinsa. Duk da dai turancin bai haɗu da ƙyau ba
Yoohan ɗin ya fahimci mi ya faɗa. Dan haka ya ajiye masa kuɗin a jiki yana faɗin,
“Na baka ne duka”. Yanda yay maganar da hausa abin dariya, harma mai napep ya
kasa haƙuri sai da ya dara.
Yoohan baibi takansa ba ya nufi
ƙofar gate ɗin su baba malam kansa tsaye, kai kace gidansa yazo.
Sau
uku yay Knocking sannan maigadi ya buɗe ƙaramar ƙofar ya leƙo yana tambayar
“Wai wanene haka da farar safiyar nan?” dan yasan su Baba malam ta ƙaramin gate
sukaje massallaci yau.
Bai gane Yoohan ba. Dan duk zuwan da yay
har sau biyu bashi kaɗai ya shiga ba sai da jagorancin masu gidan. Sai da ya
gama ƙare masa kallo sama da ƙasa kafin yace, “Samari lafiya kuwa? Mikake nema
ko buƙata anan?”.
Sam Yoohan bai fahimta ba, bayan
kalmar (lafiya da wasu ɗai-ɗai) babu abinda ya gane a zancen maigadi. Sai yay
shiru yana kallonsa cike da nazarin miya kamata ya ce da shi. Maigadi da haushi
ya kama ya sake maimaita masa tambayar?. Nan ɗinma dai ba fahimtar yayi ba. Sai
ma ya jefa masa tambaya da turanci shima.
“To bakajin hausa kenan?”. Maigadi ya
faɗa a hankali. Sai kuma ya kalli Yoohan yay masa alama da hannu (wai yana
zuwa). Kafin Yoohan ɗin yace wani abu maigadi ya koma ciki. Saurin yunƙurowa
Yoohan ɗin yayi zai tsaidashi sai dai tuni ya rufe ƙofar.
Cike da damuwa ya dafe kansa. Sai kuma
ya juya yana kallon titin anguwar. babu mutane sosai, sai tsilli-tsilli dake
fitowa cikin massallacin. Sai kuma sautin karatun yara da shima alama ta nuna
daga harabar massallacin ne.
Nufar gate ɗin massallacin yayi,
kasancewar shi a buɗe yake sai ya samu damar shiga kansa tsaye. Sai dai bai kai
tsakkiyaba wani cikin almajiran malam ya tsaidashi da sauri, dan kallo ɗaya zai
tabbatar maka Yoohan ɗin ba musulmi bane.
Anyi sa'a almajirin malam najin
turanci, sannan kuma duk zuwan da Yoohan yayi gidan sau biyu ya gansa. Ba
ƙaramin daɗine ya kama Yoohan ba jin cewar almajirin malam najin yaren da shima
yake ji. Cikin sauƙi suka gaisa ya sanarmasa wajen malam yazo. Kuma yana cike
da ƙaguwar san ganinsa domin dalilin babban uziri.
Duk da almajirin malam
yayi mamaki hakan bai hanashi yarda zaima Yoohan ɗin iso ba. Dan haka ya nuna
masa wani ɗan dakali alamar ya zauna ya jurasa. Shi kuma ya juya cikin
massallacin inda yasan malam na zaune yana karatu da azkar kafin ya fara karatu
ga magidantan anguwar dakan ɗauki karatun safe da baya wuce zaman awa guda.
Yoohan bai zauna ba. Sai ma faman bin
massallacin yake da kallo. A ransa yana sake jinjina ƙoƙarin da su baba malam
sukai wajen ginashi. Dan ƙaton gaske ne, kuma ya ginu da gini mai ƙyau. Gashi
an shafesa da farin fenti yanata ɗaukar ido tamkar ba'a shiga cikinsa, sai
shukoki da suka sake ƙawata shi suma. Ko ina kuma a tsaftace yake. Daga wajen
da yake tsaye yana shaƙo daddaɗan ƙamshin dake fitowa daga massallacin wanda
kullum safiya da maraice Nu'aymah ke zuwa ta sharesa ta saka turaren wuta da
kalolin Air Fresheners masu daɗin ƙamshi..........
Kukan wani yaro ne ya katse masa tunanin
nasa. Ya ɗan juya inda yake jiyo kukan. Hakan yayi dai-dai da fitowarta daga
cikin ajin da take koyarwa riƙe da bulalar dorina. Sanye take da dogon hijjabi
mai hannu fari tas dan har yana jan ƙasa. Hannunta na dama riƙe da Al-qur'ani,
na haggu kuma bulala. Yanda take jijjiga bulalan tana magana da nuna yaron ne
ya sakashi shagala da kallonta. A ransa ya raya, ‘Ashe kowa ma masifa take
masa?’. Jiba dai yanda takema yaro ƙarami duk da kuwa bayajin mi take faɗa.
Amma yanayinta ya nuna faɗa takeyi dan tama saka yaron kneeling ne a ƙofar
ajin.........
“Yahya! kai ne da safen nan?”.
Maganar baba malam ta katsesa daga kallon Nu'aymah daya
shagala yi. Numfashi ya sauke tare da juyowa ga baba malam ɗin. Baba malam daya
juya yana kallon abinda Yoohan ɗin ya shagala kallo shima ya ɗauke kansa ya
maido garesa. Sake mai-maita masa tambayar yayi a karo na biyu.
Yoohan da ya sunkuyar da
kai ƙasa yace, “Uncle, inason sanin minene ni'imomin dake a cikin addininku na
musulinci?!”.
Ba baba malam da yayma
tambayarba, hatta Abban su Abdallah dake fitowa daga massallacin sai da ya taka
wani uban birki.
Baba malam da jikinsa ya hau tsuma
yace, “Yoohan sake maimaitawa naji”.
Babu musu Yoohan ya kuma faɗin,
“Ina
son sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?!”.
الْحَمْدُ للهِ
الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat.
Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda
saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika.
اَلْحَمْدُ ِللهِ
عَلَى كُلِّ حَالٍ.
Alhamdu lillahi ala kulli halin
Godiya ta tabbata ga ALLAH a
cikin kowane hali.
Sai ya durƙusa a ƙasa yay sujida
hawaye na sauka masa a fuska.
Yoohan dake binsa da kallo yay saurin
duƙawa shima yana zaro manyan idanunsa a waje. durƙushewa yay gwiwa bibbiyu
yana kallon malam harya ɗago daga sujidar da yay.
Fuskarsa ɗauke da murmushi ya kama
Yoohan suka miƙe tare, sai kawai ya jawosa jikinsa ya rungume.
Duk da ba yaune karan farko da aka fara
yima Yoohan irin wannan rungumar ba sai yaji ta yau ɗin kamar daban ce a
rayuwarsa. Kamar ba irin wadda Papa da sauran mutane ke masa bace. Kamar girman
ta yau ɗin na musamman ne.
Baba malam ya ɗagosa da sauri tare da
riƙe hannunsa. Yace, “Lallai yau zaka fara sani da ga rahamar UBANGIJINA, domin
kuwa, *HASKE da RAHAMAR UBANGIJIN* al'arshi ta bayyana a zuciyarka da harshenka
Yahya!. Sai dai bazaka taɓa fahimtar tarin ni'imomin dake cikin musilinci ba
daga wajensa har sai ka shigo cikinsa”.
Yoohan da bai fahimcesa ba yay
shiru yana kallonsa ƙasa-ƙasa. Sai kusan seconds goma ya ɗago kaɗan ya kalli
baba malam ɗin da ƙyau, sai kuma ya sake maida kansa ƙasa. “Uncle ban gane
mikake nufi ba”.
Murmushi baba malam yayi, ya sake gyara
tsaiwarsa cikin harshen turancin da suke magana yace, “Ina nufin bazaka taɓa
fahimtar ni'imomin dake tattare da wannan addini mai daraja ba har sai ka
kasance musulmi Yoohan. Ta wannan hanyar ne kawai zaka ƙwanƙwaɗi madarar
ni'imar UBANGIJI fiye da zaton hasashen ka”.
Babu ko tantama Yoohan yace,
“Inhar zan sani ɗin ta wannan hanyar zan biya ko nawane na shiga addinin naku
dan na sani, dan na tabbatar idan ban sani ɗinba natsuwa zata cigaba da yin
nisa da ni har abada”.
“UBANGIJI kai ne gagara misali a
tunanin hankali ko hasashen zuciya. Tabbas kai mai ikone ga wanda kaso, a kuma
lokacin da kaso. Yahya shiga addinin musilinci ba'a biyan ko sisi. *_ALLAH maɗaukakin
sarki ya halicci halitta ne domin su bauta masa, kuma ya sawwake musu abinda
zai taimaka
musu na arzikinsa, ALLAH maɗaukakin sarki yana cewa:_*
_“Kuma ban halicci aljan da mutum
ba sai domin kawai su bauta mini. Bana neman wani arziki daga gare su kuma bana
bukatar da su ciyar da ni. Lalle ALLAH shi ne kaɗai mai azurtawa kuma ma’abocin
karfi sosai”._ Suratuz Zariyat, aya ta:56-58.
*_Mutum a halittar da ALLAH ya
yi masa zai bautawa ALLAH ne shi kaɗai inda za’a bar shi, ya zama mai son ALLAH
ya na bauta masa ba ya yi ma sa shirka, sadai abinda ya
ɓata wannan (dabi’ar) kuma yake karkatar da ita shi ne abin
sheɗanun aljanu da na mutane su ke ƙawata mata na abinda sashin su yake yi wa
sashi wahayi na ƙawatacciyar Magana kawai don ruɗi, shirka wata aba ce da ta zo
daga baya kuma ta kutsa kai ga halittar da ALLAH
ya yi wa mutum, ALLAH maɗaukakin sarki yana cewa:_*
_“To, ka tsayar da fuskarka ga wannan
addini kana mai kaucewa shirka, halittar ALLAH wacce ya halicci mutane a kan
ta, babu mai canza halittar ALLAH”._ Suratur Rum, aya ta: 30.
*Kuma Ma’aikin ALLAH (S.W.A) ya ce: “Dukkan
abin haihuwa ana haihuwarsa ne akan musulunci, to iyayan shi ne su ke yahudantar
da shi, ko su Nasarantar da shi (kiristan da shi) ko su majusantar da shi”.
Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito.*
Dan haka Yahya UBANGIJI baya
buƙatar ko sisi da ga gareka face amsa kalmar *_La'ilaha illallah......._*”.
Sosai abin ya bama Yoohan mamaki
da wannan bayani na baba malam. dan haka ya gyaɗa kansa yana mai gyara
tsaywarsa da faɗin, “Na shirya amsar wannan kalma Uncle”.
Murmushi sosai ya sake faɗaɗa a
fuskar baba malam, batare da ya sake cewa komai ba ya kama hannun Yoohan sukabi
ta ƙaramar ƙofa zuwa cikin gida. Abban su Abdallah na biye da su zuciyarsa fal
tunanin inda ya taɓa sanin mai kama da Yoohan ɗin a wasu shekarun baya..
Sashen mahaifinsu kai tsaye suka
nufa, ko ina fes yake dan ana gyarawa saboda sukan zauna a ciki musamman randa
sukaso nishaɗi. Duk hidimar bikin salla ma jiya a ciki sukayita su huɗun. Sai
da duk suka zauna, Yoohan da Abban Abdallah kowa nama ɗan uwansa kallon sani
baba malam ya katsesu da faɗin.
*_“Shaidawa Babu Abin Bautawa Da Gaskiya
Sai ALLAH, Kuma Muhammadu MANZON ALLAH ne”_*.
_“Waannan kalmomin shahada guda
biyu, sune ƙofar shiga musulunci, sune kuma rukuninsa mafi girma, kuma ba a yin
hukunci da musulusncin mutum, sai da furuci da su, da kuma aiki da abin da suka
ƙunsa, da wannan ne kuma kafiri yake zama musulmi._
1-Ma’anar kalmar shahada: Ma’anar
shaidawa da cewa babu abin bauta da gaskiya sai ALLAH, shi ne yin furuci da ita
tare da sanin ma’anarta, da kuma yin aiki da abin da ta ƙunsa, zahiri da baɗini,
malamai sun haɗu akan cewa furuci da kalmar shahada, ba tare da sanin ma’anarta
ko yin aiki da abin da ta ƙunsa ba, ba shi da amfani, kai sai dai ma ta zama
hujja a kansa, kuma ma’anar (La Ilaha Illallah) shi ne babu abin bautawa da
gaskiya sai ALLAH shi kaɗai matsarkaki maɗaukaki.
_Rukunan wannan kalmar (shahada)
sune: (korewa da tabbatarwa), wato kore haƙƙin bauta daga wanin ALLAH, kuma
tabbatar da shi ga ALLAH shi kaɗai ba shi da abokin tarayya. Haka kuma wannan
kalmar ta ƙunshi kafircewa ɗagutu (shi ne dukkannin abin da ake bauta masa
wanda ba ALLAH Maɗaukaki ba, ko da kuwa ya kasance mutum ne (tare da yardarsa
da bautar da ake masa), ko dutse, ko bishiya, ko son zuciya, ko sha’awa), da
nuna masa ƙiyayya da yin kuɓuta daga gare shi._
*_Wanda ya faɗi wannan kalmar
(shahada da bakinsa) amma bai kafircewa abubuwan da ake bauta
musu wanin ALLAH ba (a aikace), to tamkar bai faɗeta ba.
ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Kuma abin bautarku abin bauta ne guda ɗaya.
Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Mai rahama Mai
jin ƙai”.(Baƙara: 163)._*
*_Kuma Maɗaukaki ya ce: “Babu
tilastawa game da (shiga) addinin
(musulunci), haƙiƙa shiriya ta bayyana daga ɓata, saboda
haka wanda ya kafirce wa ɗagutu kuma ya yi imani da ALLAH, to haƙiƙa ya riƙi
igiya amintacciya, (wadda) ba ta yankewa. ALLAH kuwa Mai ji ne, Masanine”._*
(Baƙara: 256)
_Kuma kalmar (Ilah)
tana nufin abin bautawa da gaskiya, duk wanda ya ƙudurci cewa abin da ake nufi
da kalmar (Ilah) shi ne: Mai halitta, Mai arzutawa, ko wanda
yake da ikon ƙirƙira, kuma ya ƙudurci cewa yin
imani da wannan kawai zai wadatar, ba tare da kaɗaita ALLAH
da ibada ba, to haƙika faɗin kalmar (La Ilaha
Illallahu) ba za ta amfane shi ba, a nan duniya wajen shiga
Musulunci, kuma a Lahira ba zata kubutar da shi ba daga azaba madawwamiya._
ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Ka
ce (da su): “Wane ne yake arzuta ku daga sama da ƙasa? ko kuma wane ne yake
mallakar ji da gani?, kuma wane ne yake fitar da mai rai daga matacce, ya kuma
fitar da matacce daga mai rai? Wanene kuma yake tsara al’amura?” To za su ce:
“ALLAH ne”. To ka ce (da su): yanzu ba za ku ji tsoronsa ba?”
(Yunus: 31).
*_ALLAH Maɗaukaki ya ce:
“Ko wane ne ya halicci sammai da ƙassai, ya kuma saukar muku da ruwa daga sama,
sannan (da wannan ruwan) muka tsirar da (shukokin) gonaki
masu ƙayatarwa, ba kuwa za ku iya tsirar da bishiyoyinsu
ba?, shin akwai wani abin bautawa tare da ALLAH, A’a, su dai mutane ne da suke
kauce wa (gaskiya)”. (Naml: 60)._*
Kuma ALLAH Maɗaukaki ya
ce: “Kuma lallai idan ka tambayesu, “Wanene ya halicce su?, Lallai za su ce:
“ALLAH ne” To, yaya ake juyar da su (daga bauta wa ALLAH)?” (Zukhruf: 87).
*_“Ma’anar Shaidawa
Lallai MUHAMMADU MANZON ALLAH ne:_*
_Ma’anar shaidawa lallai
(Annabi) Muhammadu
MANZON ALLAH ne shi ne a yi masa biyayya cikin abin da ya
umarta, da gaskatashi a kan abin da ya ba da
labari, da nisantar abin da ya hana kuma ya yi tsawa a
kansa, kuma ba za a bautawa ALLAH ba sai da abin da ya
shar’anta._
*_Tabbatar Da Shaidawa Lallai
MUHAMMADU MANZON ALLAH ne:_*
_ MANZON ALLAH ne: Shaidawa lallai
(Annabi) Muhammdu Manzon
ALLAH ne tana tabbata ne da yin imani da cikakken yaƙinin
cewa lallai (Annabi) Muhammdu tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi
bawan ALLAH ne, kuma Manzonsa ne ya aiko shi zuwa ga Aljanu da mutane gaba ɗayansu,
kuma lallai shi ne cikamakin Annabawa da Manzonni, kuma shi Annabi tsira da
amincin ALLAH su tabbata a gare shi bawa ne makusanci a gurin ALLAH ba shi da
komai daga siffofin ALLAH, kuma (wannan shaidar tana tabbata ne) da yi masa
biyayya da girmama umarninsa da haninsa, da lazimtar
sunnarsa a baki, a aikace, kuma a ƙudurce._
*_ALLAH ya ce: “Ka ce: ya ku
mutane lallai ni MANZON ALLAH ne
zuwa gare ku gaba ɗaya” (A’araf: 158). _*
_Kuma ya ce: “Ba mu kuma aiko ka ba face
zuwa ga mutane baki ɗaya, kana mai gargaɗi da bushara” (Saba’a: 28)._
_Kuma ya ce: “(Annabi) Muhammadu
bai kasance uban ɗaya
daga mazajenku ba, sai dai (shi) Manzon ALLAH ne kuma
cikamakin Annabawa” (Ahzab: 40)._
_Kuma ya ce: “Ka ce tsarki
ya tabbata ga Ua
UBANGIJINA, ni ba
kowa ba ne face mutum kuma Manzo” (Isra’i : 93)._
Wannan (tabbatar da shaidawa Annabi
Muhammadu Manzon ALLAH) ya ƙunshi al’amura kamar
haka:
Na farko: yarda da Manzoncinsa da
ƙudurceshi a ɓoye cikin zuci.
Na biyu: yin furuci da haka da harshe a
bayyane.
Na uku: koyi da shi da yin aiki da abin
da ya zo da shi na gaskiya, da barin abin da ya hana na ƙarya.
*_ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Sai ku
yi imani da ALLAH da Manzonsa, Annabi Ummiyyi¹, wanda yake imani da ALLAH da
kalmominsa, kuma ku bi shi don ku shiriya” (A’araf:
158)._*
Na huɗu: gaskatashi a kan dukkan abin
da ya ba da labarinsa.
Na biyar: Mutum ya so shi sama da son kansa da
dukiyarsa da ɗansa da mahaifinsa da mutane baki ɗaya; domin shi MANZON ALLAH
ne, kuma haƙiƙa sonsa yana daga cikin son ALLAH, da so saboda ALLAH Haƙiƙanin
son MANZON ALLAH shi ne yi masa biyayya wajen bin umarninsa da nisantar haninsa
da
taimakonsa da jibintarsa.
*_ALLAH ya ce: “Ka ce:
idan kun kasance kuna son ALLAH, to ku bi
ni, sai ALLAH ya so ku, ya kuma gafarta muku” (Ali Imran:
31)._*
Kuma ANNABI tsira
da amincin ALLAH su tabbata a gare shi ya ce: “Ɗayanku ba ya zama mumini har
sai ya soni fiye da mahaifinsa da ɗansa da mutane gaba ɗaya” Bukhari da Muslim
ne suka ruwaito shi daga hadisin Anas ALLAH ya yarda da shi.
*Kuma Allah Maɗaukaki ya ce:
“Saboda haka waɗanda suka yi imani da shi, suka kuma girmama shi, suka kuma
taimake shi, suka kuma
bi hasken da aka saukar a tare da shi, to waɗannan su ne
marabauta” (A’araf: 157).*
Na shida: Ƙudurce cewa sunnarsa
asali ce ga shari’ar musulunci, kuma ita sunnar kamar Alƙur’ni mai girma take
(wajen dogoro da aiki da ita), saboda haka ba a saɓa mata domin hankali ya ci
karo da ita.
Na bakwai: yin aiki da sunnarsa
da gabatar da maganarsa a kan maganar kowa, da miƙa wuya zuwa
gare shi, da yin hukunci da shari’arsa da yarda da ita.
*_ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Na
rantse da girman UBANGIJINKA ba za su yi imani ba, har sai sun sanyaka mai
hukunci game da abin da ya faru a tsakaninsu, sannan kuma ba su sami
wata ƙunci ba a zukatansu game da abin da ka hukunta, su
kuma miƙa wuya gaba ɗaya” (Nisa’: 65)._*...............✍

No comments