Breaking News

SAI A LAHIRA 39




 *🎀SAI A LAHIRA🎀*



              *NA*



*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




            *🅿️age 39*



*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






..........Ya shigo da sallama inda ya dubi baby da su humaira ya gaishe su.

"Sannunku baby ya gida?

"Ai fa Ni na San yanzu ne haukan ka zai tashi dan Allah Ni wuce daga kaina kar ka takani", Salim ya matsa don kar ya takata inda siyama ke wurgowa baby harara

Ya mikawa me shagon takalmin shi shi Kuma ya Miko mishi naira hamsin ya karba Yana godewa yasaka cikin aljihunshi inda ya maida hankalin shi ga siyama da take Jin ta muzanta akan abinda baby tayi mishi

"Ranki ya Dade kasuwa Kika shigo? 


"Wallahi kuwa munzo siyen ankon bikin anty baby ne  ya aiki? 

"Aiki mungode wa Allah

Ya dubi me shagon 

A

"Alhaji na nawane kudin kayanta? Me shagon ya ce dubu Sha takwas ne

Ya zura hannu aljifu ya fito da Yan dubu dubu ya kirgo dubu Sha takwas ya Mika mishi

"Gashi ka hada Mata kayan ya mikowa siyama sauran kudin dake   hannun shi "ga wannan kiyi kudin napep zuwa gida

Ya aje Mata agabanta ya fice abinshi inda ta kasa tankawa sai dai yabishi da ido. Baby taja tsaki "karyar banza Ni za a nunawa karyar arziki

Humaira tace "Anya kuwa siyama bakiyi kasuwa a wurin shoe maker din can ba?

Baby ta kyalkyale da dariya tace "Kuma Wallahi sun dace kawata shi fakiri ita Kuma zuhudu.

Siyama ta dauki kudin da ya aje Mata ta kirga inda taga dubu bakwai ga dubu Sha takwas ya biya Mata na anko duka dubu ashirin da biyar kenan

Zeenat tace "Kinga Allah ko kanwata Ashe rabo ne ya kiraki Allah yasa ayi damu  Siyama tayi murmushi ta Miko wa anty zeenat kudin gashi anty zeenat Ni Zan wuce sai kun taho..... 

Zeenat ta rikota "ai Baki Isa ba muzo tare ki ware tare zamu koma

Baby ta kirne fuka ta dubi siyama cikin takaici da bakin ciki


"idan har kikaci kudin wancan fakirin to ki kwana da Shirin biyan shi don ke da kanki kin San ba dai kudin shi bane  zakara me neman suna ya bada kwaya yaci tsakuwa.

Siyama ta dubeta tana murmushi don tasan haushi takeji akan kyautar da Salim yayi Mata.


"Haba dai anty baby Rahamar Allah ai tana da yawa Sana a sa a waccan Sana ar da kike Raina wa da kushewa zai iya samun abinda yafi gaban zatonki Kuma Koda zai zo yace min in biya shi Zan biya shi ke dai karkiji komai 


Humaira tace "haba ko da naji siyama dama nace shoe maker ya kyasa Allah yasa gidan ki ne ta fada da zolaya inda siyama ta amsa da ameen ya Rabbil alamin

Haka suka taho inda siyama ta raba kudin da Salim ya Bata ta bawa zeenat da humaira sai dai basu karba ba inda zeenat tace "kudin dinki ne fa ya Baki siyama rike abinki mun gode.

Ta mikawa baby inda ta wurgo Mata harara "nayi Miki Kama da me cin kudin shoe maker? Wannan sai dai ku wadan da suka koshi da zuhudu.


Da haka suka iso gida tana nunawa goggo kyautar Salim da kudin da ya Bata goggo tayi murna da saka albarka

Inda Kuma aka shigs hidimar biki Sai dai matsalar farko da aka soma samu shine bashir yace ba zai samu damar zuwa partyn da baby ta shirya ba saboda abokan shi ba zasu zo ba sai dai Suma zasu shirya mishi nasu party don haka amarya tana iya yin duk kalar party da take so Amma fa Babu ango abinda ya dugunzuma amarya baby

"Ban Gane abinda kake nufi ba bashir? Haka Zan Tara mutane ayi shagalin Babu ango? Wane irin gayan biki kake Shirin yi Mana? Gaskiya ba Zan yarda ba.....

Yayi saurin tareta

"Kinga baby Ina fa matukar girmama abokaina da ita Kanta abotar ba daga gareni bane daga garesu ne So kar wannan ya dameki Rashin zuwa na ba zai rage komai ba Kuma duk abinda kike so ki fada Zan yi Miki shi bana so dai Ranki ya baci.....

"Bacin Rai Kuma na nawa bashir? Wannan ai abun kunya ne in fita cikin taro Ni kadai Babu ango sai kace wata gantalalliya 


Ya fito da kudi rafofin dubu dubu ya Dora Mata Kan cinyar ta inda yake ta rarrashin ta Akan tayi hakuri idan ma tazo gidan shi zai hada Mata kowane irin party take so da haka sukayi sallama inda take Jin party Babu ango ai ba karamar fadowa bace sai taji duk hidimar tafita kanta 

Siyama ta Kira wayar Salim inda ya dauka Yana Mata fatan ta iso gida lafiya

"Me yasa kayi min haka Yaya salim ? "Me nayi ne siyama? Haba Yaya Salim dubu ashirin da biyar a wannan yanayin? Yayi murmushi"kina tausayi nane? Sosai ma kuwa .....

"To kiyi hakuri ba Zan sake ba 

To Babu komai nagode Ubangiji ya bude kofofin samu da arzki ....

"Allahumma ameen ameen ya Rabbil alamin wannan addua ma ai kamata yayi in biya...

Uhumm to ka biyata da salatin manzon Rahama... 

Ya amsa da S A W Ina godiya da haka  sukayi sallama


Ranar juma a Salim ya zo da maraice inda baby da siyama suka fito da niyar zuwa gidan me kunshi sukayi kicibus da Salim tsaye cikin SHIGA me burgewa inda baby ta wurgo mishi harara

"Kai wannan mutum yaci naci ya kora da ruwan Rashin zuciya to ko hada maita ka hada yau  sai na gaggura maka Mari ko zaka kiyayeni 

Ta daga hannu da Shirin  sharawa kyakkyawar fuskar Salim Mari inda siyama tayi caraf da hannunta  ta rike....

No comments