Breaking News

SAI A LAHIRA 33


 *🎀SAI A LAHIRA🎀*


              *NA*



*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




            *🅿️age 33*



*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






........ Hakika so dafi ne kuma me yin so makaho ne bayaji baya gani shiyasa in kaga Wanda ya fada komar so to ka tausaya mishi  kamar dai yadda Salim ya fada tarkon son baby Amma sai yagane Ashe haka duniya ta zamo inda baka da kudi to Babu wulakantacce irin ka duk nagartar ka kuwa

Gashi dai Ubangiji ya jarrabeshi da son baby tamkar yayi hauka Amma saboda tana ganin shi din fakiri ne take ta wulakanta shi har yayi nufin fito Mata a matsayin shi na Dan gidan minister kudi sai Kuma yaga Bari kawai ya barta ta kalleshi a matsayin kaskantacce Amma fa ya mutu asonta don haka sai ya fito da wani sabon salo Wai shikar dare inji kaza inda ya fada Mata saboda ita kawai zai koyo yadda ake gyaran takalma idan nata ya tsinke sai ya gyara Mata ai kuwa sai gashi da kayan shoe maker Yana zaga gari inda suka hade  a wata Rana sun dawo daga makaranta baby da humaira da Kuma siyama


"Lah baby ga mutumin ki Ashe shoe maker ne? Inji humaira wadda ke maganar tana dariya

Baby taja tsaki

"Ke mahaukaci ne fa humaira Kila dai Kama nayi mishi da mahaukaciyar budurwar shi.


Yayi murmushi baby don Allah ki tsaya akwai maganar da nake so muyi dake...


"Kai ko Kai maye ne tam zaka barni Wai bakaji abinda na fada maka ba? Idan ka Kuma cewa ka sanni Allah sai na yaga ka irin yadda ake yage takardun bogi.

"Dubeka da Allah a cikin shoe maker zaka aure Ni har ka cida Ni? Fakiri da Kai Ni sai babbar harka Babu ruwana da kyau tunda ba a wuya Zan daura ka ba .......

"Haba anty baby don Allah me yasa kike haka? "Ina laifin Wanda yace Yana sonka? Ubangiji ma ya karrama Dan Adam bareke ki wulakanta shi

In Baki son shi ba haka ya kamata kiyi mishi ba......

Kwab ta buge bakin siyama 

"Wa ya sakoki acikin maganar? Ban son shi sai Yaya? Idan Zaki burgeni don Allah ki aure shi uwar imani.

Ta Kama hannun humaira suka wuce suka barta.

Salim ya dubi siyama wadda ya tabbatar Yar uwar baby ce sai yaga me yasa ma baiga siyama ba sai baby? Shi da kanshi ya tabbatar da siyama tafi baby nesa ba kusa ba

Yana cikin fasalto kyawun siyamar yaji ta katse shi


"Don Allah kayi hakuri da abinda tayi maka haka take da kin talaka Bata San Allah shine masani akan yadda bawa ke tako arziki ba 

Yayi murmushi "na gode Yar uwa Amma ke sister ta ce ko? Ta amsa mishi da eh

Ya Sanya hannu cikin aljihunshi ya fito da kudi ya zari dubu biyu ya miko Mata 

"Karbi sister mu sai dai Babu yawa....

Tayi saurin katse shi ta hanyar girgiza Kai

"A a wallahi na gode Allah yasaka da ALHERI don tana ganin karfin halin shi me wankin takalmin da kyautar dubu biyu? 

Shima ya katseta

"In dai ba Raina wa kikayi ba karbi don Allah Baki ma fada min sunanki ba sister",

"Sunana siyama ta fada tana karbar kudin

Inda sukayi sallama tana godiya 

Ta nunawa baby kyautar dubu biyun da yayi Mata inda babyn taji takaici don ko ba komai inda ita ya bawa tana da tarin bukatun kudin Amma sai ta gwasale

"Karyar banza karyar wofi ni za a nunawa karyar arziko"?

Dama hikima yayiwa kanshi ya dawo wurinki yadda Kika koshi da zuhudu shine daidai ke tunda gashi Nan Yana Miki kyautar dubu biyu......

"Ai Ni wallahi idan Ubangiji zai bani irin shi wallahi Zan gode don me zuciya ake fadawa biki ba me dukiya ba.

"Da zakiji shawarata anty baby sai ince ki cire son abin duniya aranki ki roki Allah abu mafi ALHERI a Rayuwar ki  idan fa Ubangiji ya barki da kanki wallahi Baki da mafita.

Bance lallai sai kin so Wanda yace Yana sonki ba Amma gaskiya ki daina wulakanta Wanda yace Yana son ki don Baki San inda Rana ke faduwa ba......


"Wata Kila dai kece Baki San inda take faduwa ba Ni na San inda take faduwa yamma take faduwa. Kuma daga yau kar ki Kuma shiga Rayuwa ta haka Nike Jin zanyi Kuma ke Baki Isa ki sauya min Ra ayi ba 

Kuma in son shi kike ai na ce na bar Miki shi tunda kufi Marcin dashi ma akan ni

"To shikenan tunda haka kikace Ni Kam Banda zabi akan mijin Aure Ubangiji nake nufa da bukata duk Wanda yake shine ALHERI agareni to Ubangiji ya zaba minshi  koma waye. Haka Kuma in Sha Allahu Zan Daina SHIGA Rayuwar ki kiyi hakuri tunda fada Miki gaskiya ya Zama laifi.

"Mtsss ta katseta da Jan tsaki ta bar wurin inda siyama tayi murmushi

"Allah ka shirye mu ka Dora mu bisa hanya ta gaskiya",


Kwana biyu da yin haka Salim ya sake zuwa kofar gidan su baby ya tura yaro yayi mishi kiranta ba tayi zaton zai dawo ba saboda cin mutuncin da tayi mishi

Aiko tana fitowa taga shine 

"Wayyo Allah na", "Kai Kam ko acikin Mayu Kaine karshe nace ban sonka ban kaunar ka ana so Dole ne?

To kurwata kur namana da daci sai dai kaci kanka Kasha bakin ruwa


Bata Bari yace komai ba ta juya gida inda ta fito da bokiti me dauke da ruwan wanke wanke ta antayo mishi ajiki 

Yayi tsamo tsamo Yana diga

"Idan har na Kuma ganin keyarka anan kofar gidan Wallahi sai na saka yara sunyi maka ature da duwatsu

Siyama da taji tijarar da baby keyi ta leko inda taga aikin da baby tayi mishi sai ta fito tana salati

"Subhanallah don Allah kayi hakuri

Yayi murmushi

"Babu komai siyama so ne yaja min

Baby taja tsaki ta barsu anan ta shige gida

Salim yayiwa siyama sallama ya tafi Yana diga 

Tana tsaye tana kallon shi inda ta tabbatar da so baiyi mishi adalci ba da yayi mishi adalci sai ya sauka inda za a karbeshi

Sai taji tausayin shi ya kamata har dai wannan tausayin ya juye ya koma wani Abu na daban Wanda Bata yarda tausayin shi ya koma so ba

Tayi ta fatan ta sake ganin shi Amma shiru Bai Kuma zuwa ba inda tayi fatan Ubangiji ya yaye mishi son maso wani koshin wahala da yakeyi Amma Kuma agefe guda tana son ganinshi sai dai ko a mafarki Bata Kuma ganinshi ba.


Tsayin lokaci Babu labarin salim inda Kuma a yau goggon ta aike su kasuwa siyo Mata wasu Kaya a kasuwar bacci bayan sun siyo kayan sun taho inda siyama ke gaba baby na baya tana tafe tana rausaya tana taunar cingam 

Siyama ta waiwayo ta hangota bayanta

"Don Allah kiyi sauri anty baby Sai kace me tafiya akan kwai?

"Kar ki uzura min idan sauri kikeyi yi tafiyar ki na San hanya.

"Gaskiya Kam sai ince sai kin taho 

Siyama tayi gaba inda wata katuwar mota me numfashi Tasha gaban siyama inda baby tasaki kafa ta karaso da sauri don taga me wannan mota

Ta karaso dai dai da me motar ya fito cikin shadda wagambari me walkiya kamshin turaren shi ya bulale hancin su......

No comments