SAI A LAHIRA 31
*🎀SAI A LAHIRA🎀*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
*🅿️age 31*
*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*
*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*
_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE 1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_
_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
........Yaro ya shigo yace Wai ana sallama da baby
Ta dubi yaron
"Waye ke sallama da baby"?
Yaron yace Bai sani ba
Ta yafo gyalenta ta biyo yaron inda ta iske wani saurayi cikin shiga ta Kamala dogayen Kaya da hula akan shi
Ta coge bakin kofar tana mishi kallon da wa yazo kaduna. Ya karaso yana murmushi "Ranki ya Dade barka da fitowa...
"Yauwa ta tare shi tana harara
"Sunana Bello mu azu na ganki ne jiya kinzo malali shine nabiyoki.....
Tayi saurin katse shi ta hanyar daga mishi hannu. "Da Allah malam dakata wa ya nemi Jin sun sunanka da zaka tsinke da magana tamkar tsinkakkiyar carbi ", kawai sai ka sallama min da Rana tsaka kace wani ka ganni kana so. To Ni ban tashi aure ba sai ka saurara min ka Kara birnin gaba kar in sake ganin kafar ka anan idan Kuma na sake ganinka duk abinda nayi maka Kai ka siya
Taja tsaki ta shige gida ta barshi
Bawan Allah da haka shima ya wuce
********************
Jirgin Azman ya sauka a filin sauka da tashi abirnin tarayya Abuja inda matafiyan suka soma saukowa inda wani matashi ya fito fari ne tas me suffar kyau dogo me kyakkyawar fuska sumar kanshi tamkar balarabe inda matar tayi saurin Isa gareshi suka rungume juna
"Sannu da sauka my son .
"Yauwa my momy fatan na sameku lfy Ina dady ne Bai zo tarbata ba? "Baya gari ne Amma yau din zai dawo da atiku direba zai taho daukar ka nace ya Bari Ni zanzo fatan an Kare karatu lafiya"?,
"Lafiya Lau momy bayi mission dinku. Ai gashi ka dawo gida Salim sai dai don Allah Zan so ka fitar da Mata kayi aure tunda baka rasa masoya ba yanzu haka su Aliya da munayya har da su safina da surayya kowacen su tasa anyi maka abinci na garari saboda tarba don sunji yau zaka dawo.
Ya shafi sumar kanshi Yana murmushi
"Gaskiya Momy ba Zan boye Miki ba Ni kaf dinsu Babu wacce tayi min saboda Rashin kamun kansu suna Kuma ganin iyayen su masu akwai ne Amma in Sha Allah da na samu wadda tayi min zanyi aure ayi ta tayamu da addua dai momy.
"To Allah ya kawo ta gari Salim Amma naso ka auri daya daga cikin su munayya tunda iyayen su manyan mutane ne daga Yar senator sai ta Dan majalissa Allah yasa kar ka kwaso min diyar talaka.
Bai San me yasa momy Bata son talaka ba don haka sai ya sauya firar har suka karaso gida inda ya iske girke girken da aka Tara mishi Banda Wanda momy ta hada mishi da kanta sai kawai ya ci na momyn Wanda har gobe Babu wani abinci dake gamsar dashi irin momy inda Kuma Yan Matan dake mutuwar son shi suka soma yi mishi zarya da son ya fidda gwanar shi cikin su Amma da yake ya tasirantu da addini sai ya sallame su cikin hikima ya kuma dakatar dasu daga zuwa gareshi
Abokin karatun Salim da suka hadu dashi acan rasha wato sulaiman wani kamammen mutum me ruko da addini Wanda taren su ta koyawa Salim abubuwa da yawa har wata Rana yake tambayar sulaiman Wai Ina yayi karatu? Ya fada mishi Zaria yayi karatun addinin shi yakuma fada mishi Zaria ta Tara manyan malamai masana addini shiyasa ma Zaria tayi fice akaf fadin Nigeria wurin Tara malamai masana daga Zaria sai barno sai hakan ya zamo wani buri ga Salim na son ya ziyarci Zaria ya Kuma Ravi malaman don ya Kuma karuwa da baiwar ilimi sai dai Yana tsoron momyn shi saboda yasan ta tsani talaka tamkar ita tayi kanta sai dai yanajin Babu gudu ba ja da baya.
Don haka Bai tunkare ta da batun ba sai dai da dadyn shi ya dawo bayan sun gama gaisawa yayi mishi fatan alkhairi shima ya Dora da batun aure inda Bai boye mishi ba ya fada mishi gaskiyar abinda yake buri inda da farko uban Bai yarda ba Amma da Salim din ya fahimtar dashi sai ya Gane akan cewa sun fa bashi ilimin Boko me yawa Amma badon ya Raina na addinin da suka bashi ba sai don sunfi bawa bokon karfi Boko kuwa iyakar shi Nan idan ma ka mutu kwalin bokon ka baya amfanar wanin ka
Bisa Dole ya yarje mishi don ya tabbatar yafisu gaskiya
Sai dai Kuma momy tace Bata yarda ba me ke akwai cikin Rayuwa da talaka in Banda Rashin sanin kimar Dan Adam?
Sai da aka turza kafin ta yarda da sharadin duk sati yazo gida ta ganshi Kuma sai dai ya sauka agidan su dake kaduna Wanda daga cikin shi suka taso shekaru masu yawa kafin su dawo Abuja in yaso sai ya Rika zuwa can Zaria wurin daukar karatun Yana dawowa tunda ya saka kanshi Wai me zai karanto tunda dai ya iya karatun sallah? Kunji fa?
Da haka dai Salim ya taho kaduna a tsohon gidan su inda ya Kira sulaiman dake can Zaria ya sanar dashi gobe zai shigo Zaria city domin ya hada shi da malaman shi Yana son ya Kara fahimtar Ubangiji da yadda zai bauta mishi har yasamu rabauta Ranar gobe kiyama.
Da haka suka gama wayar
Washe gari yanufi Zaria wurin sulaiman Wanda ya hada shi da malam imam wani mutum me tsoron Allah da Kuma tarin ilimi na addini ya Kuma karbi Salim da karamci suka fara karatun tundaga kawa idi da ahalari da Kuma ishmawi sai nahawu da Kuma alkur ani. Salim yaji Rayuwa ta Kara yi mishi Dadi
Lallai jahilci duhu ne acikin duffai
Ya dawo daga Zaria agajiye Yana Kara maimaita karatun shi da malam imam dake kusfa sunan unguwar ma ya burge shi.
Yayi wanka yaci abinci inda yajj Yana son zaga garin kaduna.
Haka ya Tako akasa Yana ganin yadda mutane ke ta hada Hadar su
Cikin sa a ya hangota tana tafiya sannu Kan hankali cikin tafiyar ta me kama da yanga. Gaban shi ya Sara inda ya bita da kallo har ta kusa kurewa ganin shi sai Kuma ya bita abaya har yaga gidan da ta SHIGA
Ya Dade atsaye kafin ya wuce Yana waiwaye
Ko da Bai San so ba ya Gane sonta yake Bai ida Gane hakan ba sai da ya kwanta bacci yayi ta mafarkin ta inda yaje Zaria ya dawo da BURIN zuwa gida ya nemi sonta don ya gama Gane zuciyar shi ba zata taba barin shi Zama lafiya ba matukar ba Kai kanshi gareta yayi ba don haka yayi wanka cikin shigar jallabiya da hula tashi ka fiye naci ya tunkari gidan su.......

No comments