Breaking News

SAI A LAHIRA 29


 *🎀SAI A LAHIRA🎀*



              *NA*



*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




            *🅿️age 29*



*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*





..........wani mahaukacin tashin hankali ya ziyarce shi bayan gama karanta sakon kwaro.

Ya fafari motar aguje inda ya dire akofar gidan Garba don yafi Jin tsanar garban akan kwaro don ko shine abinda zaiyi kenan.


Ya shiga gidan inda ya samu Garba Yana Karin kummallo. Ya tarbe shi inda yayi saurin dakatar dashi da hannu.

"Garba ka bani mamaki ban Kuma taba zaton haka abotar mu ko aminci ya koma ba.

Garba ya kidima da Jin abinda yake fada

"Wani Abu ya faru ne abokina?

Ya zaro takardun ya Miko mishi ya soma karantawa 

Sai da ya karance su tsab inda gumi ke wanke mishi fuska


"Nayi Zaton yadda na amince da Kai haka ka amince Dani Ashe dama da biyu kake kallon nafisatu",

To wannan sakon kwaro ne ya bada abaka ya Kuma dauki nafisatu sun bar garin sai dai duk inda ya shiga Zan Nemo shi domin in nuna mishi ba iri na ake yaudara ba . Kaima na gode da cin amanar ka  duk da Allah bai baka nasara ba sai kashiga sahu mu gwada sa a ni da Kai akan nafisatu...


Ya fito daga gidan Bai tsaya Jin abinda garban zaice ba Kai tsaye ya nufi gidan haj Azumi inda ya fashe da kuka Azumi ta rude.


"Na SHIGA UKU Ni Azumi bilya wa ya mutu Kuma"? Ya zayyane Mata yadda nafisatu tabi mijinta suka gudu suka bar garin.

Azumi ta Dora hannuwan ta biyu aka tana kokarin kurmo ihu.


"Kar ki damu hajiya Zan shiga in fita  har sai na Nemo kwaro na karbe nafisatu Kuma duk wani abinda ya same shi kar ya tuhumi kowa sai kanshi.


Da haka yabfice ya bar gidan inda lamis yabdawo Azumi Bata fada mishi abinda ke faruwa ba sai nafisatu ta kirashi da dare take sanar dashi yadda suka tsere.


Yayi murmushi"madallah nafisatu Ubangiji yayiwa Rayuwa albarka yasa Kuma ki gama lafiya  idan kun sauka ki kirani kinji ? Ki gaida saddiku Allah ya sauke ku lafiya.


Azumi na zaune tana Jin su inda ya gama wayar ya dubeta

"Nafisatu tace agaishe ki....

"Gaisuwar banza gareta da zatayi min? Ai nagama Gane duk wannan mugun qullin kai ka shirya musu shi saboda bakin ciki to albishirin ka sai kace min goro wallahi duk inda nafisatu ta tafi zata dawo ta komawa bilya Ina Nan Kuma ita nafisatun zata iskeni sai naci mutucin ta wallahi....


Malam lamis yayi murmushi.....

"Au har na Zama abin dariya ko? Wato na Zama mahaukaciya 

"Ai Baki da maraba da hauka Azumi Ni wallahi nafisatu ta burgeni da ta nuna muku kune sakarkari ke da bilyan na kula soyayyar da kikewa bilya me yawace tunda har kike kin Yar cikin ki akan shi saboda Yana Baki kudi Yana kaiki makka. Da Zaki yarda sai in sauwake Miki kije ki aure shi...


Aiko Azumi tayi ta sheka ruwan tijara tana fadin duk bakin cikin shi dai ba zai kankare Mata faralin da ta sauke ba.


"Azumi kenan Ni bana bakin ciki da faralin ki domin kuwa nasan zuwan ki saudiyya da hajin ki ta karbu to da kin sauya hali Amma maimakon sauyi sai Kika Kara durmiyewa bani ko tan Tama jifar da kikayiwa shaidan Baki same shi ba shine ma ya jefeki...


Aiko Ranar Azumi tayi tijara me amsa sunanta har taci damarar yin dambe da malam lamis Wai ya CE mata shaidaniya

Bai biye Mata ba ya kyaleta tayi tijarar ta tagama inda ya Kuma hayaka ta da batun auren badariyya da Khalil a wannan Rana Azumi kusan da ciwon zuciya ta kwana inda ya kwashe su siyama ya kaisu kaduna wurin baba shitu Wanda ya bukaci hakan saboda me dakin shi Hime ke son yaran 

Abinda ya Kara bawa Azumi haushi ta Kuma tsanar Hime da dukkan ahalin ta Wai ta shanye shitu ta Kuma shanye Mata danta khalil tunda har ta jona mishi badariyya....

No comments