Breaking News

SAI A LAHIRA 28


 *🎀SAI A LAHIRA🎀*



              *NA*



*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




            *🅿️age 28*



*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*




.........."Ya kamata mu samawa kanmu mafita akan mutanen Nan sadik. Na tabbata idan satin Nan biyu ya cika ba tare da mun samu mafita ba to tashin hankali ne kwance musamman Garba da bilya. Amma me kake shiryawa?


Ya rungumota Yana kissin goshinta. "Ai Ni ko ma me zai faru yau in dai na tsira dake nafisatu to Zan iya shanye komai. Garba kuwa shi da bilya  nafi kowa son inga yadda wasan kwaikwayon su zai Kare.

So kwantar da hankalinki darling babu me rabamu sai mutuwa da ikon Allah na gama shiri na tsab lokaci kawai nake jira.


"To madallah Ubangiji yayi Mana muwafuqa",


Ya Isa gidan haj Azumi inda ya tura yaro yayi mishi sallama da malam lamis ya fito suka gaisa inda yake duban sadik din,


"Ashe haka Kuma Allah ya kaddaro maku saddiku? Yayi murmushi

"Wallahi kuwa baba yanzu ma nazo ne don in dauki su baby da siyama suyi Mana kwana biyu amaido su. "To Babu damuwa Amma ba tsaya a Nan waje don kar wancen mahaukaciyar ta Gane Kaine mijin AUREN kisan wutan nafisatu don har yanzu Bata Gane Kaine mijin nafisatu ba.

"Sai dai Yaya kake shirin tun karar bilya saddiku? Baba kudin shi kawai Zan mayar mishi nafisatu dama tawace fin karfi ya nuna min to Kuma gashi Ubangiji ya nuna mishi Ni din ne me nafisatu tunda gashi ya maido min ita ta inda banyi zato ba. malam lamis ya Yi murmushi kafin ya shiga gida ya fito mishi da siyama da baby ya tafi dasu inda sukayi karo da mamar su suka makale Mata suna murna. Ya dubeta Yana murmushi sun burgeshi ita da su baby.


"Kinga fa baccin fin karfin da aka nuna min da yanzu yaran Nan nawa ne". "Ko yanzu nakane ta bashi amsa.

Kwana biyu Yana ta hidima da su baby har sukayi sabo me yawa da shi inda ya maido su ba tare da hajiya Azumi ta ga fuskar shi ba inda take masifar Wai in ba tsirfa ba Ina ruwan mijin AUREN kisan wuta da yaran matar da zaku Rabu Nan da kwana bakwai? 


"Nafisatu ta zuba idanu taga irin matakin da  yake fadin zai dauka har kawo yau da yarage saura sati guda wa adi ya cika inda ta kula da shirye shiryen da yakeyi na tattare dukkan kayan su Yana parking din su duk ba ta tambayi dalili ba 


Ranar da ta rage saura kwana biyu sati biyu ya cika yake sanar da ita zata iya binshi Koko zata so ya sallame ta don ta komawa bilya?


Ta dubeshi da wani irin kallo. "Me yasa kayi min wannan tambayar"?


"Saboda in Baki dukkan damarki nafisatu idan kin zabeni ne Zan fice garin Nan ne idan kuwa kin zabi komawa tsohon mijin ki Zan yi Miki adalci ko don Ni din ban kasance me kudi ba me yuwa an sabar Miki da Jin Dadi kinga in nayi haka banyi Miki adalci ba......


"Ko a da can daular shi Bata rudeni ba bare in so shi saboda ita . Abinda na kaddara Rabon su baby ne ya hadamu shi Kuma ya Raba mu. Nima zanyi maka adalcin da kayi min ka bani zabi kaima idan kana ganin Zan zame maka matsala to ka maida Ni inda ka karboni idan kuwa kaji kana da muradina to kasani ko Adawa Zan iya binka in Kuma rungumi Rayuwar da kakeyi.


Ya rugumo ta Yana gode Mata 

"Zan mayar musu da kudin su don Basu da kudin siyen kaunar mu ke nake so ba kudin su ba...


"Nima Kaine zabi na ba bilya ba don haka ka mayar musu da kudin su Zan bika ko ina ne.


Kwana biyu yacika inda tun asubahi suka fice zuwa tashar mota suka Kuma yi sa a kafin gari ya waye motar su ta hau hanya 

Ko ina suka nufa kuma❓❓❓


Tun da farar safiya bilya ya nufi kofar marusa low cost gidan kwaro inda ya iske gidan garkame da kwado mamaki ya Kama shi na inda suka tafi tunda farar safiya.


Ya dauko wayar shi ya Kira sadik Inda yaji wayar akashe ya Kuma Kiran wayar nafisatu itama akashe inda ya fara tunanin wani Abu.

Ya tashi motar Yana Shirin juyowa yaga me gidan dake makwabtaka da nasu kwaro ya fito yanufo shi suka gaisa.

"Yauwa alh dama sadik ya bani sako jiya yace idan kazo in baka don Allah Bari in dauko maka", ya koma gidan ya fito da wasu takardu guda uku ya Miko mishi biyu. "Yace wannan naka ne ita Kuma wannan gudar yace ko Garba zaka bawa? Na dai shafa a da sunan.

Atake bilya  ya farke takardar Yana dubawa.

Ta farko cekc din kudin da ya rubuta mishi ne na ladar aikin auren kisan wuta ne Bai taba komai ba sai takarda ta biyu me dogon rubutu me dauke da bayani kamar haka.......


Bayan sallama irin ta musulunci Ina fatan wannan sakon ya riskeka cikin aminci alh bilya da farko dai Zan baka hakuri akan karya alkawarin da nayi maka Wanda Rashi sani ne ya saka bani auren matar ka akan kisan wuta da kasan nine tsohon masoyin matar ka Wanda Kaine ka Raba mu saboda kudi da kasaka. Ban San hakan ba sai Ranar da muka hadu amatsayin ma auratan sati biyu. To hanga ko Kaine hakan ta faru da Kai shin zaka mayar da tsohuwar masoyiyar ka? To agurguje dai ga cekc din kudin ka Nan na maido maka saboda nafi son nafisatu akan kudin har ma mun shilla wata duniyar da ba lallai ku sake ganin mu ba 

Sai dai ka fadawa Garba shima cikin sakon shi akwai cekc din kudin da ya bani akan shi zai auri nafisatu ba Ni ba Wanda yaso cin amanar ka inda ya fake Dani yake Kuma son yaudarar ka.

To akarshe dai Ina baku Kai da Garba ina fatan Ubangiji ya hada fuskokin mu da alkhairi 

Daga sadik Umar kwaro.........

No comments