Breaking News

SAI A LAHIRA 21

 


*🎀SAI A LAHIRA🎀*


              *NA*



*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




            *🅿️age 21*



*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*





........"Ina kike mutuniyar banza ? Ai kinje kaduna an Dora ki akan muguwar shawara. To fito ki bani bayanin dake sakaki jayayya da mijinki..


Tun a waje hajiya Azumi ke zuba masifarta kafin ta shigo da zungureriyar bulalarta


Nafisatu ta fito cikin hijabi cikin Shirin ficewa ta dubi Azumi dake kwado Mata harara. "Wato kin cika kin batse kin habake kin Zama mace ta sosai shiyasa Kika fara sa insa da mijinki?

"To bude kunnen ki kijini matukar kikayi sanadin da bilya ya sakeki to sai dai ki nemi wata uwar ba Ni ba ke da Allah bai sa miki kishin zuci ba.....


"Wai Azumi bai fada Miki abinda yake so ayi ba?....

"Karki Kuma ce min Azumi gatsau Baki ga bakina dauke da hakori ba? To hajiya ce Ni me zaman kanta in Kuma layin ubanki Zaki bi don Bai ce min hajiya sai dai Azumi saboda tsabar bakin ciki kuma sai dai ku mutu wallahi ....


"Babu me Miki bakin ciki hajiya ai makka Kiran Allah ne Allah ya sa kinyo makabuliya sai dai gaskiya hajiya na gaji da AUREN Nan Kuma bai fada Miki ya sake Ni ba? To gashi Nan ki tambaye shi ya furta min don haka tafiya zanyi tunda kin kasa fahimta ta ya kamata hajiya ace kece Zan kawowa matsalata ki Taya Ni samun mafita Amma hajiya sai ki rufe idon ki kiyi ta fada da nema min jafa I me yasa? 


Kawai sai Azumi tayi ta zuba Mata bulalar hannunta tana duka tana sababi har sai da bilya ya karbeta 

"Ka barni in nadi ja ira marar mutunci kawai.


Ta dubeshi da gaske ne ka sake tan? "Ai na janye hajiya Babu komai 

Da haka Azumi tafice tana Kara jaddada Mata matukar tayi sanadin da bilya ya saketa to ta nemi wata uwar ba dai ita ba.


Sai aka koma wani irin Zama marar Kan gado Zama irin na kowa tashi ta fishe shi 

Cikin wannan yanayin ne nafisatu ta Kuma haife cikinta inda ta Kuma samu Yar budurwa fara tas me kyau wadda har ta zarce baby don ita baby wankan tarwada ce kwana bakwai yarinya ta amsa sunan siyama  kasancewar sunan yayar Azumi aka saka Mata wato habiba .


Haka nafisatu taci gaba da rainon yaranta inda zaman dai yaki Dadi inda ta Kuma cewa ta gama duk wata mu amala ta auratayya bare ta samu cikin da zai ce sai ta zubar sai dai hakan ne shi Kuma bai Yar da ba inda ita Kuma ta kafe kan Ra ayin ta Aiko ya dauko Mata hajiya Azumi ta Kuma wanketa tas da mugayen kalamai da masifar ta bisa Dole ta sauke komai ta bishi da dukkan bukatun shi inda Kuma wani cikin ya Kuma bullowa tun siyama na da wata Tara 


Ciki me shegen laulayi Wanda yasa yake Jin awannan karon ba zai Kuma yarda nafisatu ta Kuma haifa mishi cikinta ba inda yace lallai sai an zubar matukar tana son zaman gidan shi don duk yadda yake son ta to zai nuna Mata Bai dauki mace abakin komai ba face riga wadda zai sauya aduk lokacin da yaso hakan


Sai dai Kuma agefe Daya zuciyar da tagama azabtuwa da son nafisatu na gargadin shi da ya lallabata azubar da cikin inda Kuma ya karbi shawarar zuciyar shi ya rungumo ta

"Haba nafisatu yanzu ke zubar da cikin ba sauki aka nema Miki ba? Ki duba ki gani kusan fa duk shekara da Dan wani Abu ne kike haihuwa Baki bukatar hutu ne?.... "In dai hutun zubar da ciki ne bana bukata BB don Allah mu bar maimaita magana guda Daya idan ka gaji da yawan haihuwa ta ka sallame Ni  inace da na Daina zuwa dakin ka sai da ka Kai karata wurin hajiya?

To na rantse maka ba Zan tabayi maka biyayya asabon mahalicci ba....


Ya katseta da zafin zuciya don ta gama kaishi karshe.


"Duk yadda nake son ki nafisatu ya zamo Dole in hakura dake tunda ba autar Mata bace ke. A yau Zan nuna Miki ban dauki mace tsiyar komai ba face Riga don Ni Riga ma tafi min mace wahalar sauyawa 

"Kije na tsinke igiyoyin aurena dake kanki duka tunda bazaki bi Ra ayina ba

Ta Mike cikin kullewar ciki saboda wani shegen laulayi da cikin ya zo Mata dashi


"Na gode BB Allah ya baka matar da zata girmama Ra ayin ka Ni Kam zanyi maka biyayya muddin Bata Saba da dokar Ubangiji ba na gode da so da kauna Ina Kuma fatan kayafeni akan Rashin bin umarnin ka Allah ya hada kowa da rabon shi na ALHERI.


Yana kallo ta fice rungume da baby da siyama inda yaji wani Abu me kama da nadama ya soma mamayar shi

Bai tsinke da yayi kuskure ba sai da dare yayi inda ya dubi inda take aje mishi abinci yaga wayam ya kuma kwanta ya ji babu ita a bayan shi inda ya Gane kwabar shi tayi ruwa tsullum Bai runtsa ba har gari ya waye inda ya tafi neman mafiita......

No comments