SAI A LAHIRA 20
*🎀SAI A LAHIRA🎀*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
*🅿️age 20*
*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*
*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*
_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE 1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_
_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
.........Batayi niyar zuwa Asibitin ba sai dai amai da ciwon Kai su suka fi damunta bisa Dole ta bishi Asibitin Yana ta cin daci itama sai ta soma cin dacin Wanda yafi nashi. Haka suke tafe amota Amma kowa na daukar kanshi har suka karaso Asibitin kudi na nanso pravert clinic suka shiga inda jiri ya kusa kayar da ita da sauri ya rungumo ta ya rike har cikin office din likitan inda ya soma yi Mata tambayoyi tana amsaba har dai ya nemi da ta shiga tayo fitsari ta kawo don ya auna.
Ta shiga bayin tayo ta kawo mishi ya shiga awo har dai daga karshe ya gano ciki har na tsayin watannin auren su wato wata shida.
Su duka sunji batun ya Kuma naushe su akirji inda ya bita da wani kallo me kama da kwayar idon zata fado kasa.
Itama mamakin yadda cikin ya Kai har wata shida ajikinta take ba Kuma tare da ta Gane hakan. "Dama yaudarata kike ba Kya Shan maganin da nake Baki ko? "Ban fada Miki ban shirya haihuwa yanzu ba? Amai ya tukota tayi ta kelaya shi inda yacewa likitan azubar da cikin baya bukata.
Ta gama Aman inda likitan ke nuna Mata dakin da zata shiga ayi aikin zubar da cikin
Ta dubi bilya
'sai dai kayi hakuri BB Amma ba Zan biyeka na halaka ba sai dai ko ka nuna min yadda kake sauya Mata tamkar Rigar da kake fadar kana sauyawa koma ka tsinke igiyar AUREN gaba daya.
Don haka sai kawai ta fice ta bar mishi Asibitin ta nufi gidan inda Azumi ke tambayar abinda ke faruwa ta haye gado ta bar Azumi da sababin da ta Saba inda Kuma bilya ya biyo sawunta inda shi bai boyewa Azumi ba Kan cewa akan zubar da ciki ta taho.
Inda Azumi ta hau sababi Wai Bata yiwa mijinta biyayya inda Azumi ke cewa ya Zama dole tabi abinda mijinta yake so tunda baya son haihuwar Dole ne? Da dai ta Gane Azumi ba gaskiya take so ba sai kawai ta fice tayi tafiyar ta kaduna gidan baba shitu inda suka nema ta kaura wambai suka rasa har dai daga karshe Azumi ta gano can kaduna ta tafi inda suka tafi ita da bilya can kadunan suka iskota
"Yar duniya Nan Kika taho inda za akashe Miki Aure ko? To fito maza sai kin koma gidan bilya ko duk mutanen katsina zasu Kare. Baba shitu ya soma wanke Azumi da tashi masifar wadda Bata taba sanin ya iyata ko Yana da ita ba inda bilya yake ta bashi hakuri har sukayi nasara ya Basu nafisatu suka juyo Inda Azumi ta rufeta da duka tun acikin mota.
"Kaga Yar banzar yarinya marar mutunci. Wato kinji dadin aure shine kike tata Rashin mutunci son ranki to ki maida hankali ki kure shi idan ya sakoki sai ki nemi wurin zuwa don ubanki ma alfarma nayi mishi yake zaune gida na idan na koreshi ya koru. Bilya ne ya karbeta daga hannun Azumi har suka shigo katsina Azumi batayi shiru ba ya fara sauke Azumi kafin ya wuce gida inda shima suna zuwa gida ta balle hancin tsiya. "Na rantse maka da Wanda Raina yake hannun shi ba Zan taba yin abinda kake so ba don ba Zan taba yarda ka halakar Dani ba. Idan har da gaske kake to Ina so Nima ka sauwake min auren ka don in bi sahun matan da baka dauke su atsiyar komai ba face Riga don tafiyar mu da Kai ba iri daya bace don yadda kake da tsanar haihuwa Nima haka nake da tsanar zubar da cikin kaga mun samu sabanin Ra ayi don na rantse maka ba Zan Kuma Shan wani magani daga gareka ba ciki goma zanyi agidan ka to Zan haife shi sau goma idan kaji ranka Bai dauka ba rubuto min kawai in wuce don Wallahi tallahi da sakin auren ahannu na yake da tuni na sallame ka
Ta shige daki ta barshi sake da Baki shi kanshi yayi mamakin yadda ta dankara mishi wadan Nan magan ganun Kuma ya kyaleta batare da daukar mataki ba wani Abu da ya kasa ganewa ma shine wani azababben so yaji Yana yi Mata don haka duk wani zafi da hargowa nashi sai ya nemesu ya rasa sai ma rarrashi da yake inda ita Kuma ta murda kambunta ta Kuma dare Kan kujerar naki.
Haka ya jure ya Kuma daure ba don yaso ba har ciki ya shiga watannin haihuwa ta Kuma haife abinda ke cikin inda ta haifo Yar budurwa me shegen kyau wadda ta amsa sunan mahaifiyar shi wato zainab tana ce Mata baby sai dai baya shiga cikin lamarin baby ko sunanta bai sani ba bare yasan awane hali take ciki.
Haka dai ake ta wannan Zama Wanda shi yafi kowa ji ajikin shi inda kullum kafar Garba na tafe da sunan yazo ya Shari girki inda azahiri kuma nafisatu ke kawo shi inda ita Kuma ta gaji har ta gajiya da kallon da garban ke Mata bayan ya tafi ta iske shi har dakin shi abinda ta Dade Bata yi ba.
"Kayiwa abokin ka magana gaskiya bana son yawan kallon da yake min idan nemanka yake ya tsaya can waje ka iske shi ko Kuma idan ya shigo ka Daina kirana bare ya ganni ya zuba min idanu tamkar anyi barin kwai a titi.
Ya dubeta inda shi da kanshi yasan Garba Dan duniya ne na sosai sai yaji wani matsiyacin kishi ya turnike shi Amma sai ya Bata hakuri yace zai yi mishi magana ba zai sake shigowa ba.
Lamirin Allah bawa ya zuba ido kawai yayi kallo duk Wanda yace zai shiga hurumin Ubangiji Babu ko shakka kunya ce zai Sha inda watan baby bakwai ta Kuma samun wani cikin inda ita da kanta ta Gane sai dai Bata fada mishi ba sai da cikin ya soma girma kafin ya farga dashi Aiko ya soma tijara Yana fadin sai an zubar Wallahi wannan dayar ma kaddara ta kawota inda ita Kuma tace Bata San zancen ba idan dai ya gaji ya sauwake Mata kawai inda yace taje ya saketa saki.....
Sai Kuma yayi shiru Don yanajin yin sakin shine kuskure na karshe da zaiyi a Rayuwar shi inda ita Kuma tace tunda ya furta sakin ta gama Zama dashi sai ta shiga hada kayanta inda shi Kuma yaGane ya kusa ballo ruwa don haka ya fice ya dauko Azumi wadda ta je makka ta sauke farali bakinta dauke da Jan hakorin makka suka nufo gidan....

No comments