Breaking News

SAI A LAHIRA 15

 


*🎀SAI A LAHIRA🎀*


              *NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




            *🅿️age 15*



*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*





........Fitar malam lamis yaro ya shigo yace ana sallama Azumi ta dubi yaron "tace waye ke sallamar? 

Ya amsa da wani me motane a kofar gida

Azabure Azumi ta Mike daga kwancen da take tace "Kai kace me mota ne manu"? Yaron ya amsa da eh Azumi tayi galau da Baki tana duban manu kafin ta Mike ta yafo gyalenta don ta San Babu wani me  mota da zai zo musu abinda ta kawowa ranta shine ko zakka ce kalamu Waheed ko Alh A Y suka kawowa malam lamis don haka ta fice tana fatan hakan don tayagi rabonta  

Taleko tayi arba da motar bilya barda ta washe Baki 

"Alh sannu da zuwa ina wuni?

Ya fito da sauri Yana rusunawa Yana gaisheta inda tace ya shigo daga ciki Wai kar ya Bata kayan shi

Aguje ta koma ciki ta yayo mishi tabarma ta shi baza mishi suka sake gaisawa inda take fada mishi me gidan baya Nan Amma idan sako ne  ya kawo a aje mishi Wai ba nisa yayi ba


Ya sunkuyar da kanshi kafin ya soma magana "wato hajiya dama Allah da ikon shi ne jiya na hadu da nafisatu inda Ubangiji ya jarabeni da kaunar ta har nazo gareta sai dai ta fada min wai anyi Mata miji Ni kuma Allah yasa ban taba Jin so a Rayuwa ta ba irin na nafisatu shine nazo don mu gana da mahaifinta in roki arziki idan ma Wanda nafisatu ta tsayar yayi Mata wata hidima Ni Zan lunka mishi ribi biyu don ya bar min nafisatu don har ga Allah bazo adubun ko nawane Zan iya kashewa akan ta.....


Azumi ta tare shi  "haba alhaji ai me son naka ya gama maka komai a Rayuwa Kuma Ni dama Wanda nafisatu ke so bai kwanta min ba saboda fakiri ne me fama da kanshi tunda Kuma Allah ya kawo ka Ni dama nafi sonta da auren irinku don kunfi yaran rikon Aure don haka kasaka ranka a inuwa in kaga baka auri nafisatun ba to sai fa in bani da Rai na ma baka aurenta fakat!


Ya rusuna Yana gode Mata kafin ya zura hannu aljifu ya dire Mata rafar dubu hamsin Aiko Azumi ta gigice  har ya Gane idon ta na kudi ne don Bata boye murnar ta ba  da haka sukayi sallama ya tafi Yana fadin sai ya dawo 

Fitar shi yaba Azumi damar fashewa da kuka tamkar wadda akayiwa mutuwa kuka takeyi hada sharbe majina inda nafisatu ta iso ta risketa tana ta sharar kuka


"Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un" Azumi wa ya mutu? Ta dago kanta tana share hawayenta. "Wa fa ya mutu in Banda Dadi . Ashe Dadi na saka kuka? "Kai Ubangiji ya yarabamu da talauci  don kabarin shehu Dan hodiyo . Nafisatu tabita da kallo tana nade tabarma inda kudin hannunta suka fado  nafisatu takaiwa kudin cafka inda azimi ta damke abinta 

"Kudi Kika samu haka Azumi ? Ko zakkar su kalamu Waheed ce? 

"Ko daya Allah NE ya dubeni da Rahama ya kawo min wani alhaji guda Wai ke yake son aure har yayi min kyautar kudin Nan abinda bantaba  rike ko Rabin su ba yau nice da dubu hansin.

Gaban nafisatun ya rikito ya fado don tasan zancen waye yazo ga Azumi don haka sai tayi maza ta tareta

"A a Azumi wallahi bana sonshi karma kici kudin shi sadik nake so ......

"In bakiyi haka ba Ashe Baki fito daga cikin su shitu da lamis ba" ke Bari kiji Ni ba zanyiwa arziki kullin da zai tarwatse ba matukar dai nice uwar ki Kuma albarka ta kike so to Baki da mijin da ya wuce barda wallahi lamis ma ba zai tada wannan maganar ba kinji na fada Miki. 'in Banda tsiya yaushe kike zabar talauci akan arziki? Tunda na fara soyayya da lamis ko dubu biyar bai taba bajintar bani ba bare dubu hansin shine saboda kin kware akan bakin ciki shine zakice Baki son barda don kar ki agaje mu to ki sani idan har Kika auri barda kaf zuriyar ku kece hamshakiya mandiya don duk cikin dangin ubanki Babu alhaji cikin su bare hajiya don haka sai ki biye wa soyayya ki Kare da cikon cefane kamar yadda nakewa ubanku ko Kuma ki bi yarima Kisha kida inda za a yi Miki komai......


"Azimi Ni dai bana so don Allah ki kyale ni  kwadayi mabudin wahala ne baban Kuma ai da kike yi mishi cikon Banda yanzu Kuma Ni irin shi nake so don ko da yunwa zanjure a gidan sadik don shine muradina ba kyalkyali ba 


Azumi tabita da kallo baki sake  sai dai ta lashi takobin ko za a mutu sai ta Mika nafisatun gidan  barda 


Sai dai nafisatu da gaske take domin kuwa da dare da aka Aiko  kiranta tana fitowa taga bilya barda sai tayi maza ta dawo inda Azumi ta Gane da gaske takeyi don haka ta  maida ita inda bilya ke ta aikin rarrashin ta don da gaske yake Bai taba so irin na nafisatu inda ya Miko Mata ledoji masu dauke da Kaya na girma sai dai Bata amsa ba ta taho ta barshi inda yaro ya biyota da su Azumi tayi ta bare bare 


Sai dai Kuma ko da wasa malam lamis bai San zancen barda ba  inda washe gari Azumi ta ke sanar dashi Wai wani daga cikin danginta Yana son nafisatu 


Ya dubeta "dangin naki ne Kika yarda da auren Amma nu nawa dangin Kika rufe ido kina cin mutunci na ? Anya kuwa Azumi kina yiwa kanki adalci...


"To sannu adali Kai adalcin ne kake barmin cefanen gidanka?  Kuma Kai ko auren ya tashi me kake dashi da za ace kafito kafito? Koko kayi gwale da ido shitu yayi maka komai shiyasa kake kokarin bawa mujahid? To Sha kuruminka bawan Allah ba nason kayi komai ka zuba ido kawai kayi kallo a wannan karon lamis ya soma nuna kwanjin shi irin na me gida inda yace shima bai yarda Azumi ta bawa Dan uwanta auren nafisatu ba shima mujahid ya sani sai dai ko su tsaga nafisatun biyu kowa yaja nashi kason Aiko rigima gagaruma Azumi da lamis akan AUREN nafisatu kowa yaja ya kafe kan ra ayin shi.......

No comments