Breaking News

NI DA KE 29


 ♣️♥️♣️

      _*NI DA KE.....!!*_

          ♣️♥️♣️



```♥️Dole muyi rayuwa.........♥️```









*_wattpad@feebyrh_*







Page 2️⃣9️⃣

"Kin gaya musu Wanda ya baki maganin....???"

   cikeda firgici yayi mata tambayar yana jin xaxxafan xufa na karyo mishi  xama yayi tareda dafe kanshi yana cixon lips d'inshi jim dakin duk ya dauki shiru nunfashinta ne kawai ke fita sama_sama  ta dauki lokaci kafin tace "ban gaya musu ba...."

   cikin daddadan voice dinta tayi maganar tana sunne kai katsa tareda wasa da xaratan faratan hannunta masu matukar kyau da sauri ya juyo yana kallonta kafin yace 

    "kuma basu fahimce komai ba..??"

   yayi mata tambayar yana hararan ta dan guntun tsaki taja tana cewa 

   "Eh"

batayi aune ba kawai taji saukan lafiyayyen mari a beauty face dinta wanda yasata ganin taurari 

    "idan kika koma mun tsaki sai na hallaka ki.."

   yafada yana barin dakin kai da gwiwa ta hada tana kuka me tsuma rai shi kuwa yana fita part d'inshi ya nufa

Kwanciya yayi ya lumshe ido yana furxarda iska me xafi daga bakin shi tunani kala kala yake mikewa yayi ya shiga hada kayan shi cikin trolley phone d'in shi ya dauki yayi dialing number ringing biyu akayi picking 

    "saif ka yanka mun ticket yanxu na London" 

  yafada yana cigaba da hada kayan shi cikin kankanin lokaci ya gama hada kayan fita yayi ya nufi main part a parloun dad d'in shi ya harda mom xama yay yayi tagumi

Kallo daya xaka mishi kasan bakin shi yana dauke da magana Dan murmushi mom d'in shi tayi tana cewa

       "Khalil lafiya kuwa na ganka haka duk ka takura...??"

    ajiyar xuciya ya sauke tareda cewa 

    "Lafiya qlw mom dama inason in gaya muku xan bar kasar nan yau London xani coz baxan iya cigaba da rayuwa a gidan nan ba inhar wannan yarinyar tana nan....!!"

   baki mom ta rik'e dad kuwa koh juyawa beyi ya kalle shi ba aikin gaban shi kawai yake gyaran murya yayi ya dora da cewa 

     "mom nifa koh kadan bana kaunar ganin wannan yarinyar a rayuwata na tsane ta tsana mafi girma kuyi mun gafara xan tafi...!!"

     yafada yana mikewa tsaye 

    "Khalil me ka dauki kanka ne a yan kwana kin nan koh ka fara shaye shaye ne meyasa baka da wani dogon tunani a rayuwar ka....??"

   Cewar dad yana yiwa khal kallon rashin fahimta wani mashi me xafi yaji ya soki xuciyar shi ....anya kuwa ba tsinanniyar yarinyar nan bace ta fara tona mun asiri..??? Khal ya tambaye kanshi hannu yasa ya dafe kanshi yana jin kalaman mahaifin shi na mishi yawo a kai

karfin halin saita kanshi yayi yace 

    "dad ba haka bane kawai dai naji na tsani yarinyar ne kuma baxan iya cigaba da rayuwa a Inda take rayuwa ba.."

     irin kallon mamaki dad ya mishi kafin yace 

     "indai ni na haife ka ban amince maka kabar kohda gidan nan ba balle kasar kuma ita da baka kauna kasan ita d'in jinin ka ce kuma sunanta baxe taba cenxawa ba daga Yar uwarka Don jini yafi ruwa kauri"

    yana fadar hakan ya fice bedroom da sauri khal ya dafe heart d'in shi yana jin yanda yake buga mishi da sauri sauri knell down yayi ya dafa kafar mom d'in shi yana cewa

     "mom please ki taimakawa rayuwata wallahi baxan iya rayuwa a inda wannan bitch din take rayuwa ba"

   dogon tsaki mom d'in shi taja ta tashi tabar wajen ita ma xaune yayi dafe da heart d'in shi yana jin wani irin  tsanarta ya koma karuwa a xuciyar shi

tashi yayi yabar part d'in ya koma nashi xama yayi yana tunani kala kala nan ya tashi yana safa da marwa girgixa kanshi yayi da sauri ya nufi wani drawer bud'ewa yayi ya dauko key nan ya nufi wani show glass Wanda ba'a iya ganin abunda ke ciki yana bud'ewa ya dauko bottle na giya daya ya bud'e ya kafa a baki saida ya shanye shi kaffff kafin ya dire kwalbar ya koma dauko wani half yasha nan ya xauna kasan show glass d'in yana surutai iri iri phone d'in shi yaji  yana ringing hannunshi ya xura a aljihun wandon shi ya dauko wayar ya kara a kannune 

   "Boss komai ya kammala kai kadai ake jira kaxo"

   "na fasa tafiyar kaxo yanxun nan ya dauko wannan shashashar yarinyar a gidan mu so nake Ka batar mun da ita gaba daya cikin da ke jikinta kuwa make sure kun xubarda shi before Ku aiwatarda aikin..."

     "boss kasan da cewar dauko ta a gidanku baxeyuba don ma'aikatan dake gidan naku..."

    "Mtwwwsss saif banason gardama kaxo yanxun nan tareda loko...be karasa maganar ba yaji ance mexan gani haka Khalil.......









Comment & share pls





😘😘feebyrh😘

No comments