Breaking News

NI DA KE 26

 


♣️♥️♣️

        *_NI DA KE...!!!_*

                  ♣️♥️♣️



```♥️Dole muyi rayuwa........♥️```





_*Wattpad@feebyrh*_







*Wannan page din sadaukarwa ne ga yan kungiyar mu  SHINNING STAR'S WRITER'S ASSOCIATION*








page 2️⃣6️⃣

    "Khalil ka barni da bakin cikin da ke neman dauke rayuwata idan ka kuskura ka sake yarinyar nan wallahi bani bakai har abada......

      Har cikin kanshi yaji wannan kalaman dad ajiyar xuciya ya sauke yace

      "dad bafa wannan auren...."

      Da sauri dad ya dago da kanshi yana kallon khal cikeda bacin rai

      "Me kake nufi a daura aure yanxu kuma kace ba auren...!!???"

    Ba tareda ya tsaya bawa dad amsa ba yabar dakin direct parking space ya nufa inda ma'aikatan gidan da baki take taya shi murna wani bala'in haushi yakeji hakan ya shiga mota yabar gidan direct guest house d'inshi ya nufa yana shiga gidan yayi parking d'in motar bud'e murfin motar yayi ba tareda ya tsaya rufewa ba ya kutsa kanshi cikin gidan kai tsaye dakin da take ya nufa har yanxu tana bacci kujerar dake facing d'inta ya xauna akai cikeda fusata da tsanananin bacin rai xama yayi tareda crossing kafar shi daya kan daya yana furxarda xaxxafan iska daga bakin shi ganin batada niyar tashi yasa, ya tashi ya nufi fridge bottle water ya dauko me mugun sanyi wanda ya fara kankara da sauri ya dawo dakin tun daga kanta ya fara xuba mata ruwan har xuwa tafin kafarta a firgice ta mike a kanshi ta sauke dara daran sexy eyes d'inta mugun xafinda taji a kasanta ne yasata komawa gefe ta hade jikinta tana xan blanket ta rufe jikinta  hada kai da gwiwa tayi tanata shashsheka gabanta kuwa sai faman bugawa yake dappppp da ita yaxo ya kama kunnenta da karfi a hankali ta dago da kanta tana kallonshi cikeda tsantsansar tsana da karfi ya aika mata mari wanda yasata ganin stars yace

          "xaman me kike mun a gida abunda nake nema nasamu sai ki tashi kije gidan ubanki kuma karki kuskura ki koma gidan ubana......."

      yayi maganar yana huci kamar wani xaki

wani kololon bakin ciki ta hadiye idonta sai hawaye me xafi yake fitarda....me wannan macucin mutum ke nufi ne yaxata da rayuwarta.....???

     "karki kuskura in koma hada ido dake....bana kaunar koma ganin me irin wannan mummunar fuska naki....."

     yafada yana janta da karfi saida ya kawota bakin kofar parlourn kafin ya tsaya kallonta yayi up and down yace "ki fitar mun daga gida tunda bana ubanki bane....."

   Durkushe kasa tayi tana rushewa da matsanacin kuka me tsuma rai sake kallon kanta tayi a xindir take ba komai a jikinta kuma a hakan yake nufin ta fita tabar mishi gida voice d'inta na cracking tace "ka tai....maka...mun in dauki kayana.....nima....bana fatan....in koma....kara numfashi a doron....duniyar nan....balle a gidan ka....."

     ba tareda ya tsaya jin maganarta ba ya fice daga wajen a fuskarta ya cilla mata kayanta yana cewa         

      "Minti biyu na baki kibar gidan nan...."

     Jikinta na rawa ta saka Yan kayan baccinta tabar gidan ta dauki lokaci tana tafiya duk inda tabi sai an bita da ido hakan yasa ta saida me Napep ta gaya mishi gidan da xe kaita dappp da gate din yayi parking ganin an dauki lokaci bata sauka ba yasa ya juya summamiya ya ganta cikin tashin hankali ya soma kiran mutane

     Nan akayi kanta direct asibity aka wuce da ita....




B'angaren khal kuwa cikeda tashin hankali ya yini ranar tsoron shi daya karta sanarda su dad abunda ya faru yayi nisa cikin tunani yaji wayarshi na ringing saida akayi wajen 5 missed call kafin ya dauko wayar xe kira saiga kiran yashiga Watan daddan murya yaji tana gaida shi cikin sanyayyar murya ya amsa B'angaren ta kuwa murmushin mugunta tayi tana cewa 

       "nasan Baka gane me magana bako....??"

     Jim yayi kafin yace 

     "eh wacece...??" 

   dan murmushi tayi tana cewa 

     "Khalil da wuri haka koh toh leenah ce kawar Salma..."

    Xumut ya tashi da kwancenda yake coz yana son yaji labarin Salma daga bakinta don yaje gidansu ance ba'a San inda take ba da sauri yace

       "Ina Salma..."

    "kwantarda hankalin ka Salma na nan...."

     "a ina take..."

Ya tambayata da sauri

      "inason in ganka ne muyi magana xan gaya maka komai....mu hadu emerald suit anjima karfe uku....."

      "alright....."

nan ta kashe wayar tana sakin shu'umin murmushi Tun 1:00pm ya shirya yaje cen a garden ya xauna yana xaman jiranta



B'angaren Firdausi kuwa an samu ta farfado har an sallame su sun bar asibityn bayan duk mutanen da sukaxo bikin sun watse nan suka tasata a gaba suna tambayarta yanda akayi abun ya faru Jim tayi tana naxarin abunda xata sanarda su a hankali ta bud'e bakinta tace 

         "da dare ina xaune a bedroom dina ina shirin yin bacci sai naji knocking ina bud'e kofar ban koma sanin inda nake ba sai gani na nayi a asibity tareda Ku......"

   Jikinta na rawa tayi maganar ajiyar xuciya suka sauke koh wanne da irin tunanin da yake 

Khalil kuwa sun hadu da leenah nan ta shaida mishi komai har kashe khairat da Salma tayi nan suka dukuma nemanta don ba wanda yasan duniyarda take kusan kullum kuwa sai sun hadu da leenah har sun fara shakuwa....





Bayan wata daya

   Firdausi ce durkushe a gaban iyayen nasu sai kuka take faman yi

       "Kiyi magana kinyi shiru kin maida mutane sakarkaru waya miki ciki.....????"

         mamanta tayi mata wannan tambayar cikeda fada da tsananin bacin rai 

         nan ma shiru tayi bata Basu amsa ba lafiyayyen mari mamanta ta aika mata wanda yasa ta rikice tana koma tambayarta voice d'inta na mugun cracking tace

        "Khalil....ne"

wani irin mugun damka mamanta takai mata ta rike wuyanta da kyau tana cewa 

     "karya kike yanxu ki rasa wanda xakiyiwa karya sai khalil ki rasa wanda xaki cuta sai shi....??"

     dad ne yayi sauri riketa yana cewa

       "kiyi a hankali mana ai ba'a shaidar yaro...."











*gaskiya kun bar sharhi da dogon comment shiyasa nabar typing*

No comments