Breaking News

NI DA KE 21

 


♣️♥️♣️

        *_NI DA KE...!!!_*

                  ♣️♥️♣️



```♥️Dole muyi rayuwa........♥️```





_By 😘😘feebyrh😘✍️_





page 2️⃣1️⃣

      "Rufa mun baki shashasha ita Firdausi da nake aikawa Neman kudin kinga tayi ciki ne.......??sai ke shashasha wacce batasan yanda xata Kare kanta ba....."

    "to umma ai ina ganin laifin ki ne Ke yakamata ki bani maganin bani xan nemawa kai na tunda bani na saka kaina ba saka ni akayi...."

    "mtssw kaji mun munafukar yarinya ai sai kisan yanda xakiyi da cikin dan yau dinnan xaki fitarda cikin wallahi"

     "gaskiya ni umma inason cikina baxan iya xubda shi ba da wanne xunubin xanji na aikata xina koh na xubda cikin.....??

   tsaye luba ta mik'e tana rik'e waist d'inta ta finciko wuyan maryam da karfi ta rik'e " wallahi baki isa ba yau saina ci ubanki har sai cikin nan ya xube kuma baxaki bar nema mun kudi ba koh gobe sai kinje in yaso kuma ki koma bud'e kafa ayi miki wani cikin ni kuwa baxan gaji da cin ubanki ba har sai ya xube.....ita shegiyar kuwa anxo an tafi da ita gashi duk abubuwa sunyi mun yawa a kai"

    Tana fadar hakan tacigaba da xabgar maryam








B'angaren khal kuwa bayan fitan su dad yaci axaba sosai hannun momy a ranar ne hauwa mahaifiyar momy ta sauka Nigeria sunyi matukar murna da dawowarta nan tace ta dawo da aikinta a nan coz tana son tayiwa kasarta aiki dama dalilin daya sa tabar kasar don a ganinta batada kowa shiyasa xaune suke kan dinning table suna lunch mom ce ta juya bataga momy "lafiya wai ina momy....??" murmushi dad yayi yana cewa "kinsan ai baxata wuce dakin yayanta ba...."

    "nikam Alhaji ina mamakin irin wannan kauna da tausayi dake tsakanin su...??"

     "hakane mine kinsan ai jini yafi ruwa kauri"

   "hakane Alhaji kullum babban fatan ta Allah yabashi lafiya"

     


ASALIN SU 


   Alhaji Muhammad d'a ne ga Alhaji umar yaran shi biyu Muhammad da hauwa Allah ya axurtashi da dukiya wanda yayi gadon shi tun kakanni shikadai Allah yabawa iyayenshi Muhammad da hauwa sun girma cikin kulawar iyayen su da tarbiyyah me tsabta sunyi karatu na islama da boko sosai inda tun kafin mahaifin nasu ya rasu ya mallakawa Muhammad dukiyar shi me dunbin yawa nan yashiga juya dukiyar ya dawo sokoto state da xama yana kasuwancin shi iyayenshi kuwa da hauwa suna Abuja a nan ne Muhammad ya hadu da matar shi basu wani yi soyayyah ba sukayi aure sun dade sosai kafin Allah yabasu haihuwa iyayen nashi sunyi matukar murna daren suna ne mahaifin nashi da mahaifiyarsa suka shirya xuwa ganin wannan jaririnda Allah ya axurtasu da a hanyar su na xuwa ne jirgin su yayi hatsari inda duk wa'inda ke jirgin suka rasu Muhammad yayi bakin ciki sosai ranar suna Yaro kaci sunan kakan shi shine aka saka mishi Khalil yaronda ya tashi cikin gata da soyayyar iyayenshi fiyeda yanda ba'a sammani lokacinda hauwa taji labarin ta kusa xaucewa hakan yayi daidai da kammala karatunta a U.S.A bayan ta dawo ne suka hadu da Yusuf nan suka kulla soyayyah harta kaisu ga aure saidai kash Sam tabaji dadin auren ba don matar Yusuf tabi ta addabeta saida ta shekara goma sha biyar da aure kafin ta haihu ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyarta wato Firdausi haka a lokacin ne taji mummunar labari cewar yayanta ya rasu tacigaba da rayuwa cikin kunci ranar juma'a da rana kishiyarta ta tura mata Yan daba haka suka risketa a gidan Allah yabata iko ta fita tayi gudu har xuwa wani unguwa lokacin yarta na shan nono a hanya sukaci karo da wani mutum yana fita daga gidanshi tana haki ta mika mishi yarta tana nuna mishi mutanen da ke binta tace "bawan Allah ka taimaka ka rike mun yata xasu kasheta xan dawo karbarta ka shiga karsu xo...."

voice d'inta na cracking tayi maganar nan tacigaba da gudu a hanya ne suka hadu da mijinta tayi sauri ta Shiga motar cikin rudani yake tambayarta ita kuwa sai ajiyar xuciya take duk ya mayarda hankalinshi a kanta garauuuuuu sukaji wani babban mota ya buga su ana isa asibiti koh da akayi bincike mijin ya dade da mutuwa ita kuwa tayi losing memory d'inta me motarda aka kad'e su da ita ne ya dauki nauyin kaita Indian ayi mata magani nan tacigaba da rayuwa a cen har tasamu lafiya inda har aiki tasamu a cen kafin ta dawo Nigeria ta dade tana Neman wannan mutumin dakyar ta gane gidan tana xuwa gidan kuwa ta iske shi ga mamakinta da xuwanta har ya ganeta nan ya kira Firdausi ya xaunarda ita ya gaya mata komai tayi kuka sosai najin ba Malam ya haifeta ba dakyar ta yarda tabi mahaifiyar ta kudi sosai mamata taba shi amma firrrr yaki karba......





Cigaban labari

     momy ce ta fito cikin shirinta na gown pink colour tayi rolling d'in Vail light pink ba kadan tayi kyau nufar dinning area tayi tana cewa "mom xani wajen  baba............


















😘feebyrh

No comments