MIN QALB 41
*_MQ 41_*
*_Masu karanta book din mu Basu biyaba Kuma sunabinmu da mummunan kalami munbarku da Allah idan kunada rabo Allah ya shiryeku_*
Wani irin bugu zuciyarta keyi me qarfi da sauri hannuwanta
na Yar rawa take kallon anty zarah din da akwatinta datake janye dashi batasan
lokacinda wani qarfin hali da juriya suka shigeta ba ta qaqalo wani talwataccen
murmushi tana ajiye cup din hannunta ta nufi anty zarah din da itama tafi
Amatun dauke wuta tana cewa''
Anty zarah sannu da zuwan bazata.
Duk yanda anty zarah din taso Nemo qaqalo murmushi ta nema
ta rasa sai kawai ta 'dan washe baki Wanda kowa yagani yasan yaqene Tace"
Amatu sannu da gida mun sameku lfy?
Akwatinta Amatun ta karba tana qarasa shigo Mata dashi ciki
tana cewa''
Alhamdulillah anty.
Rasa abinyi tayi sbd ruden datake duk da ba'a iya ganewa sai
kawai ta nufi kicin ta hado drinks da snacks a tray ta fito dasu tana 'dan
satar kallon inda ya zauna Yana sauya layinsa zuwa na qasar ahankali ta ajiye
tray din gabansu tace"
Dady sannu da zuwa.
Qwarewa anty zarah tayi da ruwan data zuba bakinta duk suka
juyo suka kalleta bandashi daya dauke Kai baima Gama juyowarba tace sannu anty
ko ruwan yayi sanyi ne da yawa.
Batareda ya kalletaba yace"
Ki gyaramin dakin and kiban keys din motarki zan fita
urgent.
Miqewa tayi tana Dan Jin wani iri ta nufi dakinta ta dauko
Masa keys din ta miqa Masa ya fice ta juyo ta kalli anty zarah datai saurin
dauke Ido daga kallon datake Binsu dashi tace"
Anty zarah Bari nakai Miki kayan dayan dakin tunda anty
salamatun ma Bata Nan kafin agyara nasa dakin saiki koma can ki shigo kiyi
sallah ki huta idan nagama saina Dora dinner.
Batareda tace komaiba ta miqe tabi Amatun har cikin dakin ta
ajiye Mata akwatinta tareda ficewa tana cewa''
Ina zuwa anty idan akwai Abinda za'a yi Miki ki kirani.
Tana fitowa dakin ta sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya
tareda dafe qirjinta tana Kiran sunan Allah.
Itama anty zarah Amatun ta fita ta sauke numfashi me qarfi
tana cewa''
Ya Salam.
Daukar akwatinsa tayi ta nufi dakinsa ta ita ta ajiye kafin
tafara aikin gyaran dakin tanayi tana sauke ajiyar zuciya akai akai.
Tana gamawa Ta nufi kicin ta Dora girkin pasta da cabbage
source me kidney aciki.
Har lokacin sallar magriba tayi Bata kammala ba sai guraren
7 ta Gama ta jere a dining ta nufi bedroom dinta ta fada wanka sbd ta 'dan
gaji.
Sallah tafarayi bayan tafito wanka kafin ta sanya doguwar
English gown Mara nauyi kwata kwata black ta sanya hula ta fito cin abinci.
Tana fitowa Yana dawowa amatuqar gajiye yake Dan haka Kai
tsaye ya nufi dakinsa Yana cewa takai Masa abinci can Yana Jin yunwa.
Nata tafara zubawa taci ta qoshi tsaf abinta kafin ta hada
nasa a tray tareda komai ta nufi hanyar bedroom din nasa tanayin knocking
yabude Mata sbd tunanin da Kaya a hannunta sai gashi kuwa hannunta dauke yakeda
tray
Daure yakeda towel zaishiga wanka kenan yaji buga qofarta
shiyasa ya bude matan.
Kallo daya tai Masa ta dauke Kai ta nufi table ta ajiye
abincin tana cewa''
Ko amaida ne saika fito wankan Dan kada ya huce?
No Bari naci kafin nashiga wankan Ina buqatan abincin zansha
magani.
Zaunawa yayi yafara cin abincin a natse ga ciwon Kai dake
matuqar damunsa sbd stress ta juya zata fice yace"
Zansha magani Ina buqatan ruwa.
Fitowa tayi Dan dauko Masa sai kawai taga anty zarah zaune a
Kan dining turuss ta tsaya wata irin kunya da nauyi yasa takasa daga qafa
saidata ga kamar anty zarah adin hankalinta nakan abinci kafin taja qafafunta
daqyar ta nufi kicin ta dauko Masa ruwan saikuma taji takasa fitowa ta tsaya karba
ruwa ahankali tana tunanin yanda zatazo ta keta anty zarah ta shige dakinsa.
Jin shiru Bata dawoba gashi yagama ci ruwan yake buqata yasa
ya miqe yafito hannunsa daukeda magani
Bai lurada zarah dake zaune tsit ba a dining ya nufi kicin
inda yake hango Amatu tsaye tayi nisa a tunani
Tana ganinsa cikin kicin din ayanda tabarosa daki dagashi
sai towel ta zaro idanuwa cikin tsananin firgici da tsoro ta janyosa da qarfi
sukai gefen fridge ta bayan qofa Ido waje da firgici tace"
Bakaga anty zarah ba a apalo zaka biyoni Nan Kuma ahaka ba
kaya ajikinka me kake tunanin anty zarah zata dauka..
Zuba Mata fararen idanuwansa dasukai laushi yayi Yana
kallon tsoron dake bayyane fili akan fuskarta da bakinta dake
Magana kafin ahankali ya sauke idanuwansa zuwa kallon hannuwanta dake riqe da
qugunsa har hannunta dayama nakan daidai mararsa yaji ahankali gajiyarsa da
ciwon kansa na warwarewa ya maido da kallonsa Kan fuskarta ta ankare da
inda hannunta yake ta zabura zata janye ya riqeta Yana matseta da bango ga
idanuwansa dasuka qarasa hargitsata ta bude baki ahankali murya na rawa
tace"
Anty zarah na Palo kartayi tunanin wani Abu dabam.......
Zancenta yasashi sake matseta jikin bangon tayi saurin
rintse iso zuciyarta na harbawa tasake bude baki maganarta na fita a rarrabe
tace"
Dan Allah anty zarah nake gudun ta.....
Bakinsa kawai taji akan nata sbd firgita batasan lokacinda
ta qanqamesa da hannuwanta ba tana rintse Ido da qarfi.
Qarar faduwar plates yasashi saurarawa daga kissing bakinta
dayakeyi cikin nutsuwa ya saketa batareda ya kalli kowaccensuba yabar kicin din
Dan yasan zarah tariga taga komai yasamu kansa dajin wani iri kamar nauyintama.
Amatu kuwa rawa jikinta ya dauka tahau rawar murya tana
zazzare Ido sbd tsananin kunya ko kallon inda zarah din take bata iya yiba ta
durqusa tahau kwashe plates din tana cewa''
Anty zarah Yi hkr wallahi.....
Katseta zarah din tayi cikin wata irin muguwar dauriya da
danne kukan dake zuwar Mata tace"
Saida safe zanje na kwanta.
Juyawa tayi tabar gurin tana rufe bakinta sbd kukan dayake
Shirin kufce Mata.
Ajiyar zuciya Amatu ta sauke tana miqewa daga durqushen
datake tattara kayan ta ajiye tareda barin kicin din itama tana sake tunano
Abinda ya wakana tsakaninta da MD ZABEERA.
Tana Shiga daki kwantawa itama tayi tana rufe idanuwanta
tana Hana kanta tuno Abinda yafaru Amma kamar bazata hanuba zuciyar.
Washe gari tun 6 tafito tafara aikin breakfast sbd tanada
karatun dazasuyi da annah wata qawarta a school.
Potatoe ball da toasted bread me kwai tayi musu sai lemon
tea Takoma daki tayi wanka ta shirya cikin blue straight skirt da light blue
chiffon top Me Fadi tayi rolling ta fito riqeda handbag dinta tana duba agogo
batason tayi latti gashi key din motarta Yana hannunsa gashi da alama be
tashiba tunda bataji motsinsa ba.
Zaman jira ta dasa tanayi tana kallon agogo har kusan awa
daya sai kawai ta hkr ta miqe ta fice zata hau taxi.
Anty zarah ce tafara fitowa Bayan ta Dade da tafiyarta
ma anty zarah din na zama a palon sai gashi yafito a shirye shima da
kayan zaman gida ta tashi ta nufesa tana qoqarin Hana shedan Sanya Mata tunanin
ko tare yakwana da Amatu ta Dan rungumesa tana qaqalo murmushi tace"
Good morning.
Dafa kanta yayi Yana amsawa kafin suka nufi dining Yana cewa
ta dubo Amatu.
Tayita knocking shiru saita bude kawai ta shiga taga Bata
Nan taje har qofar toilet din dakin takira sunanta shiru saita tura qofar bayin
nanma Bata Nan ganin sanyin toilet din yasa ta fahimci tayi wanka may b ta fita
to
Tazo ta fada Masa sai alokacin yayi tunanin may b tawuce
makaranta.
Breakfast dinsu sukayi anty zarah ta tattare gurin Bayan sun
Gama tadawo gefesa ta zauna tana kallon news taredashi yanayi Yana amsa wayoyi
ahankali.
Da Rana ganin sun buqaci abinci yasa anty zarah dafa Masa
noodles da kwai itakuma tasake cin sauran breakfast din dasuka rage sbd
yafi Mata dadi.
Wanka takuma yowa ta sanyo riga da skirt na atampa tafito
tana waya da ummanta dake sake jaddada Mata tayi hkr da dauke Ido akan duk
Abinda zai Bata ranta Dan Abinda bakada maganinsa gwara ka rungumi hkr da dauke
Ido Dan ita umman batamaso zarah din tabiyosaba da nufin Wai zata Zo duba
Muhammad ne sbd tunda aka taho dashi Bata taba ganinsa ba saigashi suna zuwa
sukuma suna tafiya.
Zama tayi daidai fitowarsa a shirye kamar fita zaiyi ta miqe
tsaye tana Yana kyawu da cikar haibar mijinta Wanda kullum sonsa ke qara Shiga
Yana Kama kowane lungu da saqo na zuciyarta..
Gabansa tazo ta tsaya tana kallonsa shima ita din yake kalla
ganin irin kallon qurullar datake Masa yasan ba komaine ke dawainiya da itaba
sai sonsa sai yaji tausayinta da qaunarta na sake shigarsa ya janyota ahankali
ya rungume cikin jikinsa Yana shafa Bayanta ahankali Jin yanda take sauke
ajiyar zuciya ta dago kanta ta kalli fuskarsa cikin sanyin murya tace"
I love you so very much MAHMOUD ZABEERA..
Dora bakinsa akan nata yayi ahankali Dan nuna godia ga
Abinda tafada din.
Qarar rufe qofa da qarfi dasukaji yasashi dagowa yana kallon
qofar shigowar sukai Ido biyu da Amatu dake Masa wani irin kallon tsana
zuciyarta na harbawa da qarfi saikuma ta maida kallonta Kan anty zarah da itama
takejin wani iri akaro na farko dataji kaman taji kunyar Amatun ta qaqalo
murmushi tana basarwa ta qaraso ciki tana saka wayarta cikin handbag tace"
Anty zarah sannu da zaman gida nafita Baki tashiba shiyasa
na fice bansanarba gashi ma wallahi lattin danai gudu saidanayi.
Ayya bakomai Nima ai nayi tunanin kinjira banfito da wuri
ba.
Hanyar bedroom dinta ta nufa batareda ko inda yake ta kalla
ba batama nuna alamar tasan da mutum ba tana cewa''
Bari nashiga ko sallah banyiba wlh.
Kamar bazai kalletaba saikuma ya Dan juya yabi bayanta
da kallo kafin ya juyo ya kalli zarah yace suje.
Daki taje ta dauko mayafi da wayarta ko jaka Bata daukaba
suka fice.
Tunda tagama sallah tayi wanka ta fito taci abinci take
zaune Palo tayi waya dasu iyami,tayi da kawu,tayi da umme,tayi da Dr salman
zabeera tayi da USI Wanda sukafi awa suna Magana duk Dan tasamu sauqin Abinda
takeji aranta Amma takasa samun salama sai kawai ta kunna TV tafara kallo tana
dariyar qarfin hali kamar wata wawuya.
Kallon agogo tayi taga qarfe goma harda minti arba'in ta
miqe taje kicin ta hado tea tadawo ta zauna tana durawa cikinta idanuwanta akan
kallo.
Goma da Sha daya da minti Tara taji bude qofarsu ta Dan
kalli agogo taga lokaci taci gaba da kallonta tana Shan tea suka shigo ta Dan
dago ta kalli anty zarah ta saki murmushi tace"
Lah anty Ashe fita kukayi banma Ankara ba wlh na dauka kina
ciki kina bacci.
Kallonta yayi da mamaki saidai ko inda yake batada niyyar
kalla ta tashi tana cewa''
Anty kawo kayan na riqe Miki.
Ta karbi kayan hannun anty zarah din yakai Mata har dakinta
ta fito tana cewa''
Bari naje na kwanta gobema inada zuwa makaranta da safe.
Shigewa tayi ta rufo qofa ta Isa bakin gado ta zauna tareda
sauke ajiyar da numfashi me qarfi idanuwanta na cikowa da hawaye batasan
lokacinda ta kifeba Tana sakin kukan kewar Dr khalil dinta.
Washe gari ko abincin breakfast qin Yi tayi ta wucewarta
makaranta taga keys dinta na mota ya ajiye Mata a palon taqi dauka ta
tafiyarta.
Bata dawoba sai yamma tayi shigewarta bayan tashiga har
dakin anty zarah sungaisa.
Washe gari ma haka takuma ficewarta ba Wanda yaganta sai
abin yazama kamar tana wasan buya dasune Dan tasawa kanta zama very busy kullum
Babu me ganinta take fita har gwara idan tadawo sukan gaisa da antyn tata ogan
gidan kuwa Sam taqi Bari suga juna tuni kewar su Anty salamatu da Muhammad suka
sanyota gaba gashi meenat batanan bare taje gidanta,
Wata Rana idan tafita shopping kawai take zuwa idan ba
makarantar sbd kawai ta Hana kanta zama gidan.
Kusan kwana takwas kenan tana wannan wasan buyan dasu duk da
itama ta matuqar gajiya da wannan yawon hutu take buqata Amma bazata iya zama
gidan ba matuqar ba tafiya sukaiba sbd har yau fama take da ciwon zuciyar
Abinda idanuwanta sukai Mata gani shiyasa ta zabi raba kanta da zaman gida.
Yau sai magriba tadawo gidan amatuqar gajiye take Bata
tararda kowa agidan ba da alama sun fita basa Nan Dan har dakin anty zarah
tashiga Bata nan sai kawai tayi wankanta tayi sallah ta sanya wata qaramar riga
Mara hannu red da bumshort baqi wanda ko cinyarta bai saukaba sosai tafito ko
dankwali Babu akanta taje ta sanyawa qofar shigowa key tana sakin numfashi Dan
rabonta data sakata acikin gidan tun ranar dasuka Zo tasaba Bata cika son Kaya
masu nauyiba yanzu kullum kayanta gajeru ne dasuna sukadai Amma tunda sukazo
take a takure.
Kicin ta nufa ta hada celeals din Muhammad Tasha acan kicin
din Tasha ruwa tadawo Palo zata zauna sai ganin mutum tayi zaune Yana waya a
natse cikin tsananin firgici da tsoro ta bude baki Yana lurada Abinda zatayi ya
janyota ta Fado kansa ya sanya hannu daya ya rufe Mata bakin Yana kallon cikin
tsakiyar idanuwanta dake kallonsa ahankali yace"
Shihhh wayana me mahimmanci ne don't make a sound..
Tsit tayi tana kallon bakinsa dake Magana da Wanda yake
wayar cikin burgewa da rashin garaje.
Maida kallonta tayi Kan qofar shigowa taga tananan rufenta
to kenan Yana dakinsa Koda tayi tunanin basa gidan.,
Qofar dakinsa ta kalla batasan lokacinda tace"
Ina anty zarah??
Wani kallo ya juyo yayi Mata na tsawon mintuna kafin ya
datse wayar dayakeyi ganin yafara rasa gane Abinda suke tattaunawa ya ajiye
wayar Yana kallon fuskarta da ba annuri ya sake matseta cikin jikinsa
yace"
Mezaki Bata da kike tambayarta?
Qin kallon fuskarsa tayi tafara qoqarin qwacewa tana cewa''
Sakeni kada ta fito ta......
Menene koyaushe kike cewa kada ta fahimta?
Kallonsa tayi a gundure tana sake qoqarin qwace jikinta
tace"
Matarka ce Dan haka bazataji dadin ganinka da wata ba..
Bakinta ya kalla cikin taushin muryar son qureta yace"
Hakan kikeji shiyasa kike ganin kaman itama hakan takeji.
Da sauri ta kallesa tace"
Menene?
Ni banma San me kake cewaba.
Matsota yayi ta qarasa mannewa jikinsa ya kalli fuskarta
zuwa bakinta dazaiyi kissing saikuma ya fasa ya miqe da ita a jikinsa ya nufi
hanyar dakinsa sbd dukkaninsu idan ya fahimci matsalarsu ta baifi kowacce data
Ganshi da 'yar uwarta ba Amma na Amatun yanason tabbatarwa ne idan yashiga
zuciyarta kamar yanda yake tunani sbd zafin kishi me tsananin daya hango a
idanuwanta.
A tsakiyar gadonsa ya kwantar da ita tareda sakar Mata
dukkanin nauyinsa ta rintse Ido sbd idanuwansa dake son karya kuzarinta tadan
juyarda fuskarta ta bude baki daqyar sbd mutuwar jiki tace"
Anty zarah zata.....
Rufe Mata baki yayi Ahankali da nasa Yana Dora hannunsa Kan
wuyanta zuwa kirjinta dake harbawa da sauri har batasan lokacinda ta qanqamesa
ba tana bude idanuwanta akan nasa idanun dake kallonta cikin wani irin yanayin
daya qarasa kashe jikinta
Ya saka hannu yafara zare qaramar rigar jikinta ahankali
tayi saurin rufe Ido sbd rigarce kawai ajikinta batada ko bra...
Qarar doorbell ne yasata bude idanuwanta ahankali ta Dora
akan nasa idanun dasuka sauya kala ta janye jikinta ahankali tareda mirginawa
gefe tana Jan duvet ta rufe qurjinta ya saki wani qaramin numfashi tareda tashi
zaune yafara daidaita kansa ya miqe ya fita dakin.
Kobaa fada ba yasan zarah ce tadawo daga gidan qawarta
dataje Dan haka Kai tsaye ya bude qofar fuskarta daukeda murmushi ta shigo
zatai Masa Magana yanayinsa yasa gabanta mummunan faduwa ta kalli fuskarsa da
sauri zatayi idanuwanta na cikowa da hawaye ganin hakan yasashi Dan dafe goshi
Yana cewa''
Wat a hell""zama da Mata fiyeda daya.
Kallonta yayi Kai tsaye sbd bai iya kame kame ba yace"
Zan kwanta and kada ki nema AMATULLAH zata Kwana adakina
after 2 days Zaki kwana so please don't make it too difficult for me kije ki
kwanta I know you're tired.
Kadan ya rage anty zarah ta Dora hannu akai ta zunduma ihu
Tafi kowa sanin MAHMOUD din Dan Kai tsaye ne bai iya kwana
kwana ba Amma Bata dauka rashin kwana kwanarsa yakai hakaba da zai iya
haikatata wata ran.
##mamuh#

No comments