MIN QALB 36
MQ 36_*
Ita kanta Amatun a sanyaye take sbd rashin sanin makomar
abindake cikinta,
Allah yasani tanason babynta Kuma tanason samun Abinda Bata
fatan tayi wahalar banza shiyasama tunda sunce saita kwantarda hankali babyn
zai samu shima lafiyar da akeso tafara iya qoqarin kwantarda hankalin saidai
Kuma Sam tsoro da shakkar halinda babynta ke ciki ya Hana hankalin nata
kwanciya.
Iyami ce ta miqa mata kofin maganin tsiyayewar zaqi tana
cewa''
Karba ki Dan Sha ko kadan ne zai taimaka idan haihuwar ta
taso gaba data.
Kallon kofin tayi tareda karba ahankali ta kurba tana rintse
ido sbd rashin dadinsa ta ajiye cup din tana girgiza Kai tace"
Iyami
bazan iya Sha da yawa ba wannan ya Isa Yana sakani zafin zuciya da yawa.
Fura me sanyi anty zarah ta zuba Mata ta miqa Mata Wanda
itace ke cewa tafisonta da sanyi sosai idan ba hakaba Bata iya Sha abin Sha idan
baida sanyi Sam.
Karba tayi ta shanye atake tana cewa aqaro Mata saidai aka
miqa Mata jug din daya Gama daukan sanyi shima.
Shan furar takeyi sunata kawo Mata firarraki kala kala Dan
dauke Mata hankali kota cire damuwa da tsoron kwata kwata,
Sai dare dukkaninsu suka watse aka barta daga ita sai iyami
sai anty salamatu dasuka Zo taredasu maman junior dasu maman basiru Dan dubata
kowanne dauke da kularsa ta kayan gargajiya na marmarin me ciki,
Maman junior sakwara da jar Miya ta kawo Mata wadda taji
yaji sai maman basiru data kawo Mata danwake dayaji salad da kwai anty salamatu
ma taga soyayyar gyada ahanya da Madara gasassa ta siyo Mata duk saitaji
idanuwanta sun cicciko da hawaye har batasan lokacinda tasakesu tana sunkuyar
da Kai sbd ayau tasake tabbatarda ba jininka ne kawai Dan uwankaba wani Dan
uwanma yafi na jini,
Bata damu da son sanin asalintaba ko jininta wainnan bayin
Allahn sune Yan uwanta sune jininta sbd suna qaunarta tamkar jininta Dan haka
Bata buqatan sanin inda ta fito Dan kula kawu da iyami tareda usinta sune
asalinta hakanma ya Isa rayuwa Alhamdulillah.
Share Mata hawaye anty salamatu tayi tana cewa''
To meyene na kuka Bayan Dr tace ko damuwa ba'a so bare Kuma
kuka,
Wannan abin damukeyi duk yiwa Kai ne sbd mu tamkar zuria
daya ne idan baki manta ba yawancinmu dake gidan bamuda zuria,bamuda dangi mune
Yan uwan junanmu Dan haka meye abin damuwa aciki.
Iyami dai batace komaiba sbd ita wani lokacinma ayanda
takejinsu aranta har mantawa takeyi da ba itace ta haifesuba sbd har cikin
ranta take qaunarsu a haqiqanin gaskia.
Take suka cika dakin da hayaniyar gida dasuka Saba ana
tuttuna baya da irin fadace fadacen dasuka sabayi Wanda haryanxu ba dainawa
sukayiba Nan take ta sake saigata ta washe acikinsu tana walwalarta harda
dariya da qyaqyatawa
Taci sakwara kadan hakama Dan waken taci sosai shikam kafin
ta Dora da masararta tanaji suna firarsu Basu bar asibitin ba sai goma da wani
Abu kafin suka tafi anty salamatu ta rakasu kafin tadawo Amatun tayi bacci
cikin nutsuwa Wanda ta kwana biyu batayiba.
Washe gari da Dr Fatima ta auna BP dinta taga ya sauka sosai
sai abin yabata mamaki takalli iyami cikin Jin Dadi tace"
Tayi bacci ne sosai jiya?
Eh Kam jiya tasamu bacci Dan sallah ma saidai da safen Nan
tayita.
Masha Allah gskia idan da zata riqa samun hakan to da
Inshallah komai zaizo da sauqi yanda mukeso.
Jin hakan yasa iyami ta aika salamatu tayiwasu maman junior
Magana akan su riwa zuwa Dan Allah suna kawowa Amatun firar dare
Ba musu suka amince sbd Suma zasuso tasamu lafiyar.
Aikuwa tuni asibitin Takoma majalisar 'yan gidansu Dan kuwa
idan sunayi dariyar Amatun har qofan daki anaji umme ma data ga hakan saita
qarawa zuwan nasu armashi ta aiko musu da lafiyayyan abinci da pepper chicken
na kaji kullum aikuwa Suma ganin wannan dadin yasa suka sake dagewa da kullum
gida suke kwaso abinsu sai sun iso gida araba abawa kowa nasa Kuma kajin ba
'yan kadan ba ga drinks gakuma kudin abin hawa da anty zarah ce itakuma ta Basu
Wanda zasu riqa amfani dasu Dan da farko kawu ne duk sukazo yake Basu na komawa
sai anty ZARAH ta dauke Masa wannan nauyin.
Kwananta takwas a asibitin ranar na Tara ta tashi da wani
mummunan ciwon kai wanda yasanya jini da ruwa 6alle Mata take hankalin dukkanin
likitocinta tashi musamman Dr Fatima
Su kansu su umme dasu kawu kowa yashiga tashin hankali
musamman ganin yanda take wani wani Abu kamar jijjiga haka aka kwasheta akai
labour room da ita aka barsu tsaitsaye suna Kai kawon jira cikin rashin
hankali.
Kafin qarfe hudu na yamma dukkanin 'yan uwanta da wasu daga
cikin familyn ZABEERA suna asibitin Babu me wata walwala acikinsu sbd har
lokacin Babu wani labari daga likitoci sai yawo ake ana fita ana shiga.
Dr Fatima ce ta fito Bayan tayi waya da Modibbo ta sanar
Dasu komai na halinda ake ciki ta kalli kawu da umme da iyami dake gabanta
cikin office dinta dake cikin labour room cikin tsananin damuwa da sanyin jiki
tace"
Wato Abinda ake ciki shine Amatu bazata iya haihuwa da kanta
ba sbd lokacin haihuwar baiyiba gabanta ko kadan bai Fara budewaba gashi baza'a
iya jiraba sbd qarfinta zai qare hakama babyn ruwan dayake ciki kowane lokaci
zasu iya tsiyayewa Wanda hakan na faruwa hadari ne Mai matuqar girma Kuma
barazana ce ga rayuwarsu su duka,
Dan haka bazamu Bata lokaci ba na sanarwa su Modibbo zamuyi
Mata aiki saidai Abinda zata Haifa din zamu sakasa a kwalba sbd rashin isarsa
haihuwa idan Allah yasa andace...
Tsit sukayi kamar wainda sukaji mugun labari,
Koda yake kusan hakan ne Dan umme tuni tafara hawaye sbd
tasan rasa babyn zatayi kamar yanda ta rasa Khalil dinta.
Numfashi kawu ya sauke cikin jarumata yace"
To shikenan likita ba damuwa ayi aikin Allah yasa hakan
shine mafi alkhairi yasa Kuma ayi cikin sa'a.
Amin tace tana qoqarin amsa wayarta da Kiran MAHMOUD ZABEERA
ke shigowa Dan takirasa dazun bai dagaba.
Itace tafara Magana sbd tadan fahimci bai cika maganaba yafi
saurare Dan haka Bayan ta Masa ya aiki saita Fara koro Masa bayanin halinda ake
ciki ta Dora da cewa''
Modibbo yace Kaine zaka saka hannu a file din gashi Kuma
bakanan and bazamu iya wuce Nanda 20min ba bamu Shiga da itaba ba sbd.......
Kai tsaye cikin wata murya me sanyi ya katseta da cewa''
I will be there in 10min yanzu nake baro airport.
Kafin tayi Magana ya datse wayar ya ajiye gefensa ya sauke
sanyayyan numfashi tareda rufe Ido ya bude ya kalli Mal Umar yace"
Mal Umar Yi parking.
Ba musu yayi parking din saiyaga ya fito daga Bayan motar ya
zagayo gurin sit din driver ya bude yace"
Fito ka koma baya zanyi tuqin.
Fitwo Mal Umar yayi da sauri batareda yace komaiba duk da
Yana cikin mamaki Amma dai sanin ba Abinda yafi tsana wani lokacin kamar
tambaya yasa baice qalaba ya zagaya ya Shiga dayan gefen ya zauna.
Batareda ya kalli gefen mal Umar dinba Bayan ya shiga ya
tayarda motar yace"
Saka seat belt dinka.
Da sauri ya janyo ya saka.
Wani lafiyyan speed yabawa motar Wanda yasa Mal Umar saurin
hade qafafunsa Yana hadiye yawu tareda damqe qofa Yana zazzare idanuwa dan ba
halin Magana bare ya nuna tsoronsa,
Allah ya kaimu inda zamu lafiya yafada cikin ransa Yana
satar kallon MD din dake sake bawa motar wani mugun speed din Wanda yamanta
rabonsa da irin wannan tuqin qila tun Yana cikin samartakarsa idan Khalil ya
matsa Masa Akan suyi tseren mota a Sudan idan yaje gurinsa.
Fitowa Dr Fatima tayi daga labour room sanyeda kayan CS tana
duba agogon wayarta datakeson kashewa kafin Shiga CS din taga minti Tara kenen
da wayarsu da MD Amma haryanxu shiru ga kowa jigum jigum shi ake jira yazo yasa
hannun ga Modibbo ma ya iso asibitin Amma baisaka hannunba yace ajira MAHMOUD
din tunda yace abasa mintuna kadan...
Kamar daga sama har zata juya cikin room din saigashi ya
doso gurin cikin tafiyarsa me nutsuwa da cika Ido take kowa ya juya Yana
kallonsa Yana tahowa in calm Sam baka ganin gaggawa ko sauri ko firgici
ataredashi shi mutum ne daya iya controlling yanayinsa duk qwaqwarka baka
ganewa saidai idan ka kalla cikin idanuwansa kake iya gane Abinda yake ciki
saidai Sam ganin idanuwansa ba Abune me yiyuwaba ga kowa Dan baya Bari.
Yana qarasowa ba wata Magana Dr Fatima ta miqa Masa file da
biri yayi signing tareda juyawa zuwa blood bank dinsu sbd tun a waya yafada
Mata basa buqatan jinin asibiti.
Anshiga tiyatar da qarfe biyar na yamma shiyasa gabaki daya
ward din cike yake da familyn ZABEERA ko biyowa ta gefen ba'a yi sbd ba'a
buqatan hayaniya suna buqatan silence sbd suji da damuwar dasuke ciki,
Damuwar iyami da kawu tsakaninsu da Allah tafi karkata ne
Akan su samu 'yarsu tukuna kafin suyi maganar abindake cikin shiyasa sukafi
kowa damuwa ga USI da Dr Salman sai Kira sukeyi sun Hana kowa sukuni qarshe ma
dai kusan wasu kashe wayoyinsu sukayi wasu Kuma suka sanyasu silent.
MAHMOUD na tareda Modibbo a office din Dr khalil zabeera
Wanda haryanxu wani bai shigaba tukuna suna jira Modibbo ne Dai ke wayoyinsa
shikuwa MD ZABEERA Yana zaune ne yayi crossing legs idanuwansa a lumshe yana
karkada qafa.
Ana fitowa sallar magriba nurse na fitowa daga theatre ta
cikin labour room fuskarta daukeda da murmushi da farin ciki tun Kan ta qaraso
duk suka miqe suna kallon bakinta tasake sakin murmushi tace"
Ansamu baby boy.......
Masha Allah, Masha Allah, Masha Allah alhmdlh,
alhmdlh" Sune kalmomin da suka
karade gurin atake kowa na fada Yana washe baki
Umme Kam tana fada idanuwanta na cikowa da hawayen farin
ciki hakama iyami da kawu daya kasa zama guri daya yafita waje yadawo.
Anty zarah kuwa karo na farko dataji idanuwanta kamar zasu
ciko da hawayen kwadayin samun dukkanin Abinda Amatu ke samu musamman irin
wannan soyayyar daga kowa ga Kuma babynta tasamu.
Hamdala Modibbo yayi lokacinda nurses biyu suka fito da
jaririn dunqule cikin wani qaton farin bargon jarirai acikin kwalba.,
Babu Wanda aka Bari yashiga dakin kwalbar jariran sai
Modibbo da MAHMOUD din sbd jaririn baida lafiya sosai Dan gabaki dayama kalar
fatarsa ta Dan sauya saidai tubarkalla jaririn Yana haske sosai da dogon hanji
kamar dukkanin iyayensa.
MAHMOUD Modibbo ya miqawashi Yana tayasu murnar samun qaruwa
tareda addua ya fice yabarsa.
Shiru yayi akaro na farko yaji hannuwansa na rawa game da
daukar Abu sbd kaf rayuwarsa Yana sakaran wannan ne karo na biyu daya taba
daukar jariri sbd baida Wanda zai haihu yabasa danshi ya dauka,
Karon farko daya taba daukar jariri shine lokacinda wani
babban abokin kasuwancinsa ABDUL LAYE da matarsa ta haihu suna Greece shine
yayi Masa huduba ma sbd shaquwarsu sai yau da Allah yabasa ikon daukar 'dan Dan
uwansa Wanda yake shine ubansa yanzu Koda kuwa ace Khalil din na Raye yasan
shine zai Masa huduba bare yanzu dayakeda gaba daya responsibilities din na
yaron,
Fuskarsa yadan bude ahankali ya kalla wani sanyi da nutsuwar
zamowa uba na shigarsa
Sai yanxune yakejin Abinda zarah ke fada nason zamowa uwaye
suma wata ran,
Haka kawai sai yasamu kansa da murmushin dayasa nurse din
dake tsaye kusan sumewa tana kallonsa da dukkanin girman idanuwanta kamar zata
cinyesa baki sake.
Dagosa yayi yakai fuskarsa gurin kunnen jaririn ya karanto
Masa Kiran sallah da addua tareda Sanya masa dukkanin albarkarsa dakuma yiwa
Khalil addua.
Saida ya Dan jima kafin ya miqawa nurse din aka maidashi
cikin kwalba ya fice.
Office din Dr Fatima data gama sauyawa tagama signing na
fitowa tiyata tana zaune tana harhada kayan tafiya gida saigashi yashigo Nan
tasake Masa bayanin Alhmdlh Amatu insha Allah komai lafiya data wartsake
shikenan ba wata damuwa saidai jaririn Kam baida lafiya sosai saidai yanzu ita
matsalar jaririn ba nata bane yanzu Dr fatihu ne zaiji da matsalar jaririn
shizai Basu bayanin komai zuwa da safe Dan haka tana tayasu murna da fatan
Allah yakawo abin da sauki.
Kusan atare itada MD din suka bar asibitin zuwa gida Dan ko
dakin da amatun take bai jeba ya wuce gida Modibbo ma tuni ya wuce.
Sosai suke ta hidimar kulada Amatun tun cikin dare data
farka tuni nurses suka sake gyarata aka kimtsa komai Koda qarfe goma na safe
tayi kowa yazo ya tararda ita a zaune sai abin nasake Sanya kowa farin ciki.
To kusan dai murna komawa ciki takusa Yi sbd bayanin da Dr
fatihu yayi musu dangane da jaririn Wanda yanzu haka da oxygen yake numfashi
kadan kadan baya iya shaqar numfashi da kansa,
Sanyi ne da rashin motsawar jijiyoyin yawon jini ajikinsa
sukai Masa mugun qarfi gashi ko qarfin kuka yarin baida a taqaice dai Yana
buqatar blood transfusion.
Babu Wanda yakai MAHMOUD da Amatu tashin hankali sai umme ma
da abu yadawo na damuwa shiyasa duk abin yakoma ba murna kamar ba haihuwa
akaiba.
Ahankali ita ta warware tasamu sauki sosai Dan kullum da
kanta take zuwa dakin da yake tadubosa,
Kwana shida dayin CS din ta murmure matuqa sai Dr Fatima
tabata sallama Amma sbd jaririn sai jinyarsa ta dawo musu sabuwa saidai kullum
tana zuwa gidansu tayo wanka ta huta tadawo.
Batareda sanin kowaba MAHMOUD ya bincika wani qwararran
asibitin Yara dake Greece take yasa ayi musu Shirin tafiya
Ya sanardasu Modibbo Nan Suma sukai na'am da hakan Dan dama
tuni Andi shima yafara bincikawa wasu qasashen.,
Da Amatu da anty salamatu sai umme datace zata aka hada
tafiyar shi MAHMOUD zasu rigasa zuwama sbd baya iya tafiya da Mata sam.
Andi dayazo har gidan kawu da kansa da Daren laraba ya gyara
zama Kan tabarmar da aka shimfada Masa bakin masallacin qofar gidan yace"
Mal Saleh maganar tafiyar yaran Nan inaga zaifiwa kowa
kwanciyar hankali idan aka daura auren kafin sutafi sbd su samu isashen lokacin
nemawa KHALIL qarami lafiya daga Nan har lokacinda Allah zai basa batareda mu
munshiga wasi wasiba Suma Basu Shiga takuraba
Shiyasa nace amatsayinka na mahaifinta Zan Sanar maka idan
ka amince a daura Bayan sun dawo sauran abubuwan sa biyo daga baya.
Numfashi kawu ya sauke Yana muskutawa cikin jinjina kai
yace"
To Nima dai da bakazoba inada niyyar zuwa da safe sbd zuciya
data kasa yardarmin tafiyar hakanan sakaikai duk da ba ita kadai bace Amma
hakanan nayita wasi wasin su sauran idan sungaji dawowa zasuyi abarota ita
kadai sai hakan bai wani kwantaminba gwara a daura Kam Nima yafimin nutsuwa.

No comments