MIN QALB 30
MQ 30_*
Nagode sosai kawu
Allah yaqara girma da Nisan kwana.
Amin Amin" yace Yana cigaba da yimasa nasiha akan
hakuri da rayuwa komai lokacine dashi wata Rana komai zai wuce.
Bai jira sake ganin Amatunba yanayin sallar ishai a
masallaci taredasu kawu yayi Masa Saida safe ya wuce.
Ahanya ya tsaya ya siya cardigan me kauri da sabon bargo me
laushi kafin ya wuce gida.
Sbd sanyi hatta qafaguwansa da hannuwansa Saida ya sakawa
socks bayan yasaka rigar sanyin ya dunqule cikin bargo Amma har lokacin yanajin
sanyi na shigarsa hakanan ya daure har wahalallen barci ya daukesa.
Washe gari da safe ba laifi da kuzarinta ta tashi saidai
kawai sauyi sosai data gani daga iyami har kawu Wanda ya tabbatar Mata da fushi
sukeyi sosai da ita sai taji hankalinta ya tashi duk yanda taso Basu hakuri ko
fuska taqi samu Saida Dr khalil yashigo ne taga sakewar fuskarsu ta kallesa da
Ido ta nuna Masa fushi sukeyi da ita yasakar Mata kyakkyawan murmushi Yana nuna
Mata Babu ruwansa
Suna Nan zaune saiga salman zabeera yazo Yana ganin Amatu
cikin tsananin farin ciki yaqaraso Nan aka hau sabuwar fira inda anan ne
takejin dukkanin Abinda yafaru hadda komai da Khalil din ya rasa bayan aikinsa
da asibitinsa baida komai yanxu.
Jitayi sabuwar soyayyarsa tasake shigarta hartanajin ko
bayada komai zata auresa ta zauna dashi Kuma alqawarine ta dauka saita shiryasa
da familynsa ta maidasa cikinsu.
Koda maganar aurensu sati me zuwa ta bayyana tuni kowa yahau
murna Nan aka Fara shirye shirye musamman iyami data bada himma gurin gyaran
Amatun ga umminsa ma kusan kullum saitazo gurin duba Amatun taso taimakawa
sosai Amma Khalil ya nuna kada tayi Masa komai zai iya iya qarfinsa shiyasa
Dole tabari sai itama ta maida hankali gurin gyaran Amatun sbd 'danta yaji Dadi.
Sauran kudaden dasuka rage Masa yaso Kama wani gidan hayar
dasu Amma duk gidajen babu Wanda zasu iya zama saiya aje kudin da niyar bayan
daura auren Koda da sati biyune zaiyi qoqarin hada kudaden dazasu Samar musu
gida me Dan kyau.
A bangare daya sanyi yayiwa jijiyoyinsa da qashinsa muguwar
shiga a 'yan kwanakin sbd yanxu takai kowane dare Baya iya bacci daurewa kawai
yakeyi cikin mutane baya nunawa Amma ciwonsa yatashi matuqa yanajin yanda lungs
dinsa sukai mugun laushi baya iya Jan numfashi yanda ya kamata duk iya
qiqarinsa yanayi Dan ganin ba'a fahimci halinda yake cikiba.
_GERMANY_
Kallon hoton katin Daurin auren da Khalil yaturo masa
yakumayi da fararen idanuwansa dasukai wani irin laushi lokaci daya ya lumshe
ido Yana sake kallon hoton katin ya ajiye ahankali tareda miqewa ya nufi gaban
qaton window din dakinsa dake kallon swimming pool din gidan ya zuba hannuwansa
cikin aljihun three quarter din dake jikinsa Yana qurawa waje Ido zuciyarsa na
sanyi.
Tunani zuciyarsa keyi Amma ya yakuce hakan Yana lumshe ido
Tabbas zai halarta sbd ranar farin cikin Dan uwansa ce.
Juyowa yayi ahankali tareda dawowa yadauki wayarsa daya
kashe sbd rashin son damuwa ya dannawa PA dinsa Kira Yana dauka Kai tsaye cikin
muryarsa me sautin girma yace"
Ka shirya Mana komawa gida jibi akwai Daurin auren dazan
halarta.
Done sir.
Kashe wayar yayi ya ajiye Yana sake karanta sunan dake
rubuce 6aro 6aro akan hoton katin KHALIL DAHEER ZABEERA da AMATULLAH K SALEH.
sake dauke Kai yayi yana lumshe ido tareda sauke ajiyar zuciya
ya juya yabar gaban labtop din.
_NIGERIA_
da kanta ta shirya tsaf Babu Wanda yasani ta fito suka fita
da salman zuwa zabeera mansion.
A sashen Andi sukai parking tafito ahankali tana kallon
koina komai na dawo Mata sabo tana tuno yanda tabar anty zarah dinta cikin kuka
da damuwa take taji idanuwanta sun ciko da hawaye Bata damu da tsaidaduba Saida
suka gangaro tasaka hannu ta gogesu ta nufi qofar shiga palon Andi din ta tura
tashiga da sallama dama Salman ya tabbatar Mata da a irin wannan lokacin Modibbo
na gurin Andi.
Modibbo ne yafara gabeta ya zuba Mata idanuwansa masu
kwarjini da Khalil da MD suka dauko ta qaraso ahankali ta zube qasa gabansu sai
alokacin Andi ya dago ya lura da waye.
Cikin tsananin biyayya da nuna damuwarta a fili tace"
Ina miqo gaisuwata ga Andi da Modibbo tareda neman afuwar
babban kuskuren Dana aikata Wanda ya shafi 'da mafi biyayya da gujewa
zuciyarku.
Kallon mamakin rashin tsoronta da gwarin gwiwarta suke Mata
su duka din ta sauke Kai cikin nutsuwa da girmamawa tace"
Wallahi tallahi Dr khalil zabeera baitaba aikata laifin da
kuke tunanin ya aikataba koma wane irine,
Taimako ya hadani da Dr khalil Kuma shine yasa yayita
ajiyata acikin zabeera,
Ni marainiya ce kuma Yar bola kamar yanda kowa ke fada Amma
Kuma banice nakai kaina bolarba harnayi rayuwa acikinta na tashi acikin
Rayuwa da jarabawar rayuwace takaini wadda itace tabaku
girma da matsayi tareda sunan dakuke ganin yafi Dan Adam daraja,
Nayi rayuwar maraici da tozarci irinku masu arziki Baku
dubemu ba kuka taimaka Mana saidai maigadin makarantane Wanda yake karban dubu
bakwai a wata ya taimakemu,
Nayi rayuwar almajiranci Ina matsayin mace sbd kawai na
rayu,
Nayi rayuwar wahala da qasqanci duk Dan sbd na rayu,
Munkwana da yunwa muntashi acikinta,
Lokacinda yaranku da jikokinku suke karatu mu bara mukeyi
alokacin sbd muci,
Da kaina na koyi yanda zanyi yaqi da maza na qwaci kaina
daga sharrinsu tun inada qananun shekaru
Shin nayi dukkanin wannan ne sbd nazama karuwa a rayuwa????
Nice na zabarwa kaina yin sata amaimakon karuwanci Dan kawai
na rayu sbd sata Zan iya rokon me Abu ya yafemun wata Rana Amma Zina fa???
Dr khalil zabeera shine mutum me arziki na farko daya shigo
rayuwarmu,
Yakawo Mana walwala da farin ciki a zukatanmu,
Talakawan bangarenmu wainda Dr khalil zabeera yakawo farin
ciki akan fuskokinmu da rayuwarmu basa qirguwa,
Meyasa mutum me zuciya irinta Khalil maimakon ayi alfahari
dashi za'ayi fushi dashi?
Shin Kuna tunanin ladar aikin Khalil kawai Bata Isa takawo
qarin haske da walwala acikin zabeera ba??
'yayan da Allah yabaku dukkaninsu amanace agurinku Allah
zaitambayeku alaqarku dasu idan da akwai cutatarwa,
'yayanku ne Amma Kuna gudanar da rayuwarsu kamarta
dabbobinku kokuma bayinku,
Wasunsu da dama a tauye suke basa rayuwar farin ciki,
Zaman auren Dole da qunci sukeyi duk sbd bin umarni da
qaidojinku,
Shin haramun ne neman farin ciki a wani gurin kokuwa
musulunci ne ya hana?
Shi mutunci da girma Allah ne yake badawa Kuma shiya Baku
Idan Allah yabaku suna duk Abinda wani Dan Adam zaiyi bazai
Bata hakanba Koda kuwa me zaiyi.,
Nazo zabeera ne sbd son kudina dakuma rashin sanin ciwon
kaina Amma sbd tseratar da mutuncinku yasa ya karbi laifi da bacin sunan da
baisan lokacinda aka hadosaba,
Wallahi niba karuwa bace,
Bantaba aikata zinaba,
Bansan ta Yaya ake aikataba,
Aikin gidajen abinci danayi nayine Dan neman halak Dina
Wanda haryanxu Ina alfahari da hakan sbd Allah bai bani matacciyar zuciya ba.
Dagowa tayi da idanuwanta dasukai jajir ta ajiye katin
Daurin aurensu cikin sanyin jiki tace"
Babban burinsa shine aurena yakawoni gabanku Dan neman
yafiyarku da gafararku nikuma babban burin danakeson cika masa shine bashi
kaina amatsayin mata dakuma sasantawarsa daku iyayensa,
Hawaye masu tsananin zafi suka gangaro Mata cikin daci da
damuwa tace"
Dan Allah Ina roqan gafarar ku yafe Masa kodan kasancewarsa
'da me biyayya da gudun zuciyarku a baya,
Ku basa farin cikin dabai taba samu daga garekuba tun
haihuwarsa....
Umme dake bayanta tuntuni a tsaye batasan lokacinda tafashe
da kukaba tana sake Jin qaunar Amatu ta qaraso gabansu Modibbon ta zube itama
cikin kuka tace"
Andi Dan Allah ku yafewa khalil kubarsa ya aureta wlh
dukkaninsu ba laifinsu bane nice me laifin sbd nice na kawo Amatu zabeera da
wata manufarda rashin wadataccen ilimina yabani.
Zayyane musu komai tayi sukai tsit Babu me motsi musamman
Andi dashi maganganunsa Amatu ne sukafi shigarsa,
Shin dukkanin yawancin 'yayansu rayuwar kunci sukeyi sbd
gudun zuciyarsu???
Tabbas tunda yake tsawon rayuwarsa Babu Wanda yataba
kallonsa yafada Masa haqiqanin gaskia sai yau yaringa qanqanuwa daya Isa
haihuwar ubanta koma kakanta ta kallesa tafada Masa quncin dayake saka 'yaya da
jikokinsa shekaru wa shekaru.
Modibbo Kam dama tuni Amatu ta Dade dashiga ransa bazai iya
nunawa bane sbd bacin ran Andi Amma tuni yajima da sanin yarinyace me fadar
gskia batareda tsoro ko shakkaba.
Miqewa tayi ahankali ta juya ta fice tana share hawayenta
daketa fita da gudu ta fada mota suka bar zabeera.
Kwance yake yau kwana biyu kenan ciwonsa nacinsa harya Fara
cin qarfinsa ko fita daqyar yakeyi sai dare cikin duhu yake zuwa gidansu kawu
sbd kada agano halinda yake ciki magungunsa yasiyo dasu inhaler Amma Sam kamar
basa Masa aiki sbd kullum sanyi sake shigarsa yakeyi a gidan.
Yau laraba saura kwana daya Daurin aurensu Amma abin yaci
qarfinsa tuni aka gano baida lafiya sosai sbd Koda Ibrahim yaje gidan tuni ya
Dade da fita hayyacinsa hankali tashe ya kwashesa sai asibiti.
A asibiti Koda aka karbesa numfashinsa yayi nisa sosai cikin
gaggawa akai emergency dashi ana qoqarin saka Masa oxygen.
Su kawu Ibrahim din yafara fadawa kafin yakira salman yafada
Masa cikin qanqanin lokaci duk suka halarto asibitin hankalinsu duk atashe.
Kallo daya Amatu tayi Masa hankalinta yayi mummunan tashi
sbd lokaci daya sanyi ya kumburasa
Numfashinsa Sam kwata kwata Babu saidai oxygen dinne ke
janyo Masa ahankali idanuwansa a rufe fuskarsa tayi haske hakama bakinsa yayi
haske sosai ya bushe.
Hawaye ne suka kufce Mata ta saki siririn kuka ahankali tana
cewa''
Meyasa zaka boye bakada lafiya harsaida abin yayi tsanani
haka?
Zaman rashin hankalin kurame sukeyi a asibitin daga ita har
kawu da iyami duk suna asibitin da salman sai ummensa dasu Nuratu dasuka iso
kowa cikin tashin hankali bama kamar umme datasha kuka idanuwanta sukai jajir.
Sunanan zaune har magriba saiga anty zarah da MD ZABEERA sun
iso tana ganin anty zarah suka tsaya kallon juna cikin tsananin kewa da qaunar
juna tazo da gudu tafada jikinta tana fashewa da sabon kukan datake ta riqewa
tuntuni na ganin har lokacin sai Abinda yayi gaba ajikin nasa.
MD ne dakansa yaje yayi mgn da likitocin suka sake yimasa
bayanin sanyine yayi mugun shigarsa Wanda yasa gaba daya jijiyoyin huhun Jan
numfashinsa sun daskare ya tayarda ciwonsa gaba daya harya basa attack Sam
numfashinsa yaqi dawowa ta oxygen dinma alamarin sai ahankali.
Tsorone yashigesa akaro na farko rayuwarsa
Dawowa yayi dakinda Khalil din yake ya tsaya akansa Yana
kallonsa yaji zuciyarsa na neman karyewa da sauri ya juya fice.
Anan ta kwana asibitin itada ummensa da iyami har gari ya waye
be farkaba zuwa lokacin Kam ko mgn basa iyayi da junansu sbd damuwa zazzaune
kawai suke suna rarraba idanuwansu dasuka kode sukai zuru zuru.
Da yamma tayo alwalar magriba tazo gefensa ta tayarda sallah
tayi tagama tana cikin addua taga kamar ya motsa hannunsa kadan ko shafa adduar
batayiba ta zabura ta miqe sai taga idanuwansa a bude sunyi fari tas dasu cikin tsananin farin ciki ta fada kansa ta
rungumesa tana sakin hawayen farin ciki.
Umme data fito toilet din dakin tana ganin haka tayo kansu
da gudu har sanyin ruwan qafarta na zameta itama fadawa tayi kansa ta rungumesa
Ya lumshe ido ganinsu su biyun ba qaramin farin ciki yasashi
ba yasake lumshe ido cikin azabar ciwo yanason motsawa Amma sun dannesa
MD daya shigo yayi gyaran murya itace tafara juyowa sukai
Ido biyu tayi saurin dauke Kai tana maido da kallonta Kan Khalil cikin tsananin
farin ciki tace"
Dr Dan Allah karka sake rufe idonka.
Qarasowa yayi ahankali Yana kallon fuskar Khalil din yau
farin cikinsa dai Kam ya bayyana
Shima Khalil din shi yake kallo fuskarsa nason bayyana farin
cikin ganinsa Amma azabar ciwo ya hana.
Cikin sautin murya me taushi yace"
Kun sakar Masa nauyi da yawa inaga.
Da sauri dukkaninsu suka dagasa kafin suyi wata Magana saiga
Andi da Modibbo tareda alhaji qarami sun shigo salman yakawosu take umme da
amatun suka saki hawayen farin ciki suna kallon fuskar Khalil din da idanuwansa
suka nuna zallar farin ciki ganinsa hawaye masu dumi suka gangaro ta gefen
idonsa
Andi da kansa ya matso gefen gadon ya dafa kansa yasaka
tissue ya share Masa Yana jinjina Masa Kai.
Salman da MD ne suka tayar dashi zaune amatu ta hado ruwan
zafi da towel suka gyara Masa jikinsa tareda Sanya masa shirt Mara nauyi aka
basa tea yasha kadan har lokacin da oxygen a hancinsa Kuma har lokacin bai iya
mgn sbd bai iya jan dogon numfashi.
Kafin dare yadan warware ba laifi sbd Yana Dan magana
ahankali tareda zuwa toilet idan ankamasa.
Da kawu yaso daga Daurin auren a gobe Amma Andi yace abarshi
kada a daga tunda anriga anyi sanarwa.
Da daddaren ranar duk yanda ta nace hanata kwana asibitin
akayi akace Takoma gida Salman zai kwana dashi tunda washe garine Daurin auren
Dole ta koma bayan tayi Masa bankwana yabiya da Ido cikin kewarta tun Bata wuce
dinba.
A gida duk wani hidimar al'ada sunyi abinsu hatta lalle anyi
Mata a blue fox anty zarah takaita akayo Mata tareda gyaran Kai dana jiki
Daurin auren kawai suke jira a goben akaita zabeera.
Tunda ta kwanta mafarkin Dr kawai takeyi sai kawai ta tashi
tayo alwala tazo ta tayarda sallar nafila.
Tunda gari ya waye takejinta batada qarfin jiki sbd barin
gida dazatayi.,
Qarfe daya da rabi dubban JAMA'A suka shaida Daurin auren
KHALIL ZABEERA da AMATULLAH SALEH Wanda ya bayarda tarihi me girma sbd itace
mace ta farko da aka auro daga waje.
A asibiti dagashi sai MD ZABEERA ne Wanda yace zai zauna
dashi tunda kowa na gurin Daurin auren.
Bacci yakeyi sbd alluran da akai Masa bada jimawaba sbd
jikin daya dawo Masa sosai.,
Bayan Daurin auren JAMA'A duk asibiti sukaita zuwa dubasa
sai yamma lilis ya farka cikin ikon Allah saiya tashi da qarfin jiki haryana
iya Magana tana Kuma fita sosai.
Wanka MD ya taimaka Masa yayi ya sanya farar jallabiyar
datai Masa kyau matuqa yayi sallolin da ake binsa yazauna kenan saigasu umme da
Nuratu wadda idanuwanta sukai luhu luhu sbd kukan data kwana tanayi.
Abinci ta zuba Masa ta zauna gefensa ta miqa Masa kanta a
sunkuye batareda ta kallesaba.
Karba yayi tareda sauke numfashi cikin sanyin muryarsa dake
fita ahankali yace"
Nuratu inshallah zaki samu Wanda zai wadata rayuwarki da
farin cikin Dana kasa baki.
Kallonsa tayi idanuwanta na cikowa da hawaye murya na rawa
tace"
Meyasa kakeson Amatu???
Lumshe idanuwansa dasuke a 'dan galabaice ahankali
yace"
Allah ne yasamin sonta fiyeda komai
Kuma Ina fatar zaki qaunaceta kodan sbd ni.
Murmushi me ciwo tasaki hawayenta na sake gudu tace"
Zangwada.
Murmushi shima ya sakar Mata tareda juyowa ya kalli MD dake
amfani da wayarsa yace"
Kaifa MAHMOUD???
Zaka gwada qaunar matata ko Dan sbd ni?
Juyowa yayi ya zuba Masa idanuwansa batareda yace qala ba.
Abinci umme ta matsa Masa ahankali yaci kadan Tasha tea me
zafi har zufa yadan karyo Masa aka kunna Masa AC kadan.
Ganin yanayin jikin nasa dakuma shi kansa daya nema sallama
yasa suka sallamesa bayan sallar magriba zuwa ishai Koda suka Isa zabeera
daidai isowar motacin dasuka je dauko amarya Amatu.
A gurin Andi aka kaisu duk su duka yayi musu nasiha sosai
kafin aka wuce da ita gurin zamanta wato sashen Khalil din Wanda aka sauyawa
komai sabo.
Iyami da kanta taredasu maman junior suka kawota har cikin
dakinta suna jinjina arzikin duniya irin na familyn ZABEERA kafin aka maidasu
gida.
Ahankali yashigo dakin datake zaune zugum bakin gado tana
tunanin da batamasan tanayiba...
Ji tayi anzauna kusada ita ahankali ta juyo sukai Ido biyu dashi
gabanta taji yafafi ahankali ta dauke Kai zata sunkuyar ya riqo fuskarta
ahankali tareda girgiza Mata Kai ya rungumeta cikin jikinsa ahankali tareda
sauke ajiyar zuciya batareda yace komaiba.
Sunjima ahaka kafin ya saketa tareda cewa ta tashi suyi nafila.
Tashi tayi Babu musu sukaje toilet din tare sukayo alwala
suka fito yakama hannunta suka nufi dakinsa.
Bayan sungama sallar hannunta ya riqo cikin nasa ahankali
yace"
Zakici abinci ko wani Abu?
Akwai abinci da umme da antynki suka kawo gashi can a
dining.
Dagowa tayi ta kallesa ahankali kafin ta girgiza kai.
Murmushi yasake ganin yau itama tazama kurma kamarsa tunda
yafara ciwon baya iya doguwar Magana.
Miqewa yayi tareda tayarda ita tsaye Yana zame Mata
mayafinta kyakkyawar fuskarta ta bayyana da kyau cikin qarfin hali yace"
Alhamdulillah.
Sunkuyar dakai tayi tana qaqalo murmushi ya janyota ya sanya
cikin jikinsa ya rungumeta Yana lalubar zib din goguwar rigar Julius Holland
din dake jikinta me laushi ya bude rigar ta Fadi qasa tabarta daga ita sai
farar bra din dake jikinta da farin under.
Saurin rintse ido tayi zata durqushe ya tareda tareda
rungumeta cikin jikinsa baida qarfin jiki sbd ciwo Amma hakanan ya cirata tana
qanqamesa ya kwantar da ita Kan lafiyayyan gadonsa tareda rage hasken wutar
dakin ya zare jallabiyarsa ya hau gadon ahankali tareda jawota jikinsa Yana
kallon fuskarta ya Dora bakinsa akan nata tareda 6alle hook din bra dinta Yana
cillowa qasa.
Qarfe ukun dare taringa Jin wani irin Nishi sama sama cikin
kunnuwanta ta bude idanuwanta ahankali tana kallon inda take saita tashi zaune
da sauri tana kallon gefenta a firgice tagansa numfashinsa na qoqarin daukewa
cikin tsananin firgici ta diro gadon ta zagayo gabansa tana Kiran sunansa cikin
tashin hankali Amma Sam tayi nisa a kidime ta janyo jallabiyarsa ta zura sbd
itakadaice zata shigeta alokacin sbd firgici
Sam Bata damu da tsakiyar darene ba ta fito da gudu tayi
hanyar sashensu anty zarah dake kusa da nasu a kidime tahau buga musu kofa tana
Kiran sunan anty zarah da qarfi.
MAHMOUD dake zaune daram acikin Daren yakasa ko rintsawa sbd
tsananin ciwon Kai yafara jiyo bugun qofar ya sauko daidai itama zarah tafito
daga dakinta Dan taji bugun qofar itama.
Shine yafara cewa"
Waye??? ta jikin qofar
Cikin sauri da tashin hankali tace"
Nice Amatu Dan Allah kuzo Dr ne......
Tun kafin ta qarasa ya bude qofar yanayin datake ciki
yasashi Kama hanyar sashen nasu batareda tagama fadar Abinda zata fada din ba.
Koda suka iso tuni Dr khalil zabeera yayi nisa shima yau
gigitar yashiga ya janyo wata jallabiyar da sauri ya sanya Masa ya daukesa da
dukkanin qarfinsa yafito dashi suka biyosa
Zuwa lokacin Amatu kukanma takasa Yi suka fada mota Banda
zarah dayace taje hafsatu ta Rakata ta fadawasu umme.
Koda suka Isa asibiti cikin gaggawa aka karbesa akai ciki
dashi zuwa lokacin Amatu idanuwanta neman qanqancewa sukeyi kamar wainda ke
bayansu saiga umme da Modibbo harma da Salman sun qaraso asibitin Babu me
nutsuwa Hakanan yau ciwon nasa yasasu cikin wata irin rashin nutsuwa da
firgici.
Dr ashir ne da Dr Fatima suka fito daga dakin emergency din
idanuwansu kowanne jajir Dr Fatima tuni idanuwanta suka kawo hawaye rauninta na
bayyana Dr ashir ya sauke Kai gaban Modibbo yace"
Saidai hakuri Allah ya karbi Dr khalil zabeera.
Wuta kowannensu ya dauke musamman Amatu da umme
Amatu qyafta idanuwa tayi kusan so biyu kamar zata makance
sbd duhu dake mamaye idanuwanta suka yanke jiki a some kusan atare itada umme
wadda Modibbo ya tare ita kuwa MD ne ya tareta ta zube jikinsa dukkanin jikinta
ba saki.

No comments