MIN QALB 29
MQ 29_*
Su kawuma duk shi suka tsurawa ido suna jiran jin Abinda
za'a fada Masa.
Ahankali ya lumshe ido tareda sakin boyayyan numfashi jin
Abinda garban yafada Masa ya katse wayar tareda kallon kawu dayayi zuru zuru
cikin farin cikinsa daya kasa boyuwa yace"
Tana central ta hanyar zaggen.
Ajiyar zuciya kawu yasaki tareda Dan rufe Ido batareda yace
komaiba hakama iyami numfashi ta sauke sbd harta yanke hukuncin yau dai zata
fadawa usi yasan halinda ake ciki.
Miqewa Dr khalil yayi Yana zura takalminsa yana cewa''
Kawu muje inshallah yau Amatu agida zata kwana.
Zabura kawun yayi dama jira yake ace yatashi din.
A mota Dr khalil kasa nutsuwa yayi wani irin yanayi yakeji
na tsananin kewar Amatun
Inama ace Amatu mallakinsa ce da tabbas ayau rungumeta zaiyi
ajikinsa saiyaji dukkanin kewarta ta sakesa,Amma ko yanzu wannan alamarin daya
faru bai barsa da zabin komaiba face na aurenta cikin qanqanin lokaci sbd samun
Bata kariya daga kowanne irin barazana.
Doguwar tafiya sukayi Mai Dan tsayi takaisu central din inda
daqyar aka barsu suka Shiga sbd tsaro.
Yana yin parking suka fito kawu na qarewa gurin kallo cikin
tsananin tashin hankali ace anan Amatu take zaune akan qanqanin laifi irin
wannan Wanda ko zagi da bannar suna da gorin da mutane suke musu aka barsu
dashi sun hukuntu,
Amma ace ankawota irin gurin Nan dasai masu laifin babbar
kisar gilla ake kawowa sbd kawai tayi Abinda ba laifinta bane,
Wani irin kunci da bacin Raine ya cika zuciyarsa yanajin
ba'a taba yimusu rashin adalci ba tun takaicinsu irin wannan,
Yarinya qarama mace budurwa za'a kawo irin gurin Nan?¿
Yanda yakejin tsananin bacin Rai wallahi daba mahaifiyar
Khalil ce tasata a wannan halinba wlh dasai yayi shari'a da duk Wanda yake
cikin zuriar zabeera sbd arziki ba hauka bane hakama talaka ba dabba bane.
Shi kansa Dr khalil Jin yayi dukkanin gwiwoyinsa na sanyi
zuciyarsa na cika da baqin ciki da bacin ran ganin anan Amatu take,anan aka
kawota cikin masu manyan laifuka sbd kawai tayi qaramin laifinsa baifi ayisa
agama cikin gidaba...
Babu Wanda ya iya yiwa wani Magana acikinsu sbd halin
tsananin baqin cikin dasuka Shiga na ganin irin cin zarafi da wulaqantawarda
akayiwa Amatu.
Koda suka Isa bakin office din commissioner Saida aka Shiga
aka isarda zuwansu shima sbd Khalil din 'dan Zabeera ne da Babu wanda zai Bari
ko hanyar office din su Isa.
Daga cikin office din commissioner kuwa Bayan anzo ansanar
Masa da zuwansu waya ya dauka ya dannawa alhaji qarami Kira Wanda akaci sa'a a
lokacin Yana gurin Andi.
Shiru alhaji qarami yayi bayan yagama sauraran Abinda
commissioner ke fada Masa cikin mamaki yace"
Ya akayi yayi saurin ganowa Bayan kabada tabbacin aqalla har
maganar taje court bazai gano inda takeba.??
Yanzu dai Bari na sanarda Andi saina kiraka kafin ka gansu.
Aje wayar yayi ya kalli Modibbo kafin ya kalli Andi cikin
nutsuwa da girmamawa yace"
Andi khalilu ne yasamu gano inda take Yana bakin office din
commissioner ma yanzu haka.
Dagowa yayi ya kalli alhaji qarami din da mamaki a fuskarsa
kafin ya kalli Modibbo cikin bayyanarda mamakinsa yace"
Me Khalilu yakeson komawa ne akan mace????
Shiru Modibbo yayi Yana sauke Kai cikin takaici da mamakin
Khalil din.
Sake bayyanarda mamaki da takaici Andi yayi Yana cewa''
Tabbas khalilu Yana buqatar hukuncindazai dawo dashi
hankalinsa tunda yazabi wulaqanta hukuncina akan mace..
Dan gyara zama Modibbo yayi tareda gyaran murya cikin
girmamawa yace"
Allah ya huci ranka Andi Amma sai Inaga tunda yariga yayi
nisa duk wani hukunci sake tsaurara abin zaiyi tunda Babu wani a zabeera daya
taba take hukuncin Manya sai akansa gashi yanzu kowa yafara ankarewa da hakan
da azo ayi Abinda zaisa agano bijiewa yayi yayi watsi da hukuncinka asamu masu
Goya Masa baya abun yayi yawa.
Shiru Andi yayi Yana sauraronsa cikin qoqarin son fahimtar
zancensa
Ya dago ya kalli alhaji qarami dakeson Magana shima
yace"
Kaikuma meye naka hasashen?
Gyara zama yayi Yana tausasa murya yace"
Inaga akashe maganar
a idon duniya ma'ana a janye qarar amatsayin munduba maraicinta mun qyaleta
idan yaso sai commissioner su saka kudin belin da Khalil din bazai iya biyaba
idan yayi yayi Dole zai hkr kokuma ace za'a biya kudin belin Amma saiyayi
alqawarin rabuwa da yarinyar
Hakan shine mafita a yanayin da ake yanzu sbd Khalil idan
baa janye qararba zai iya dagewa qarshe ya aikata Abinda zai saka zabeera
kunya.
Jinjina Kai Andi yayi Yana na'am da bayanin alhaji qaramin
yace"
A aikata hakan Amma kafin Nan ayau nakeson Modibbo dukkanin
Abinda Khalil ya mallaka na zabeera a karbe.
Kallonsa Modibbo yayi da sauri saikuma ya sauke Kai Yana
jinjina hukuncin sbd kaf 'yayansa bama
shikadaiba kusan duk yayan zabeera da arzikin Zabeera suke tinqaho MAHMOUD
ZABEERA ne kawai Babu qwandalar zabeera acikin dukiyarsa da guminsa da
wahalarsa yatara arzikinsa,
Idan akace akwace komai na Khalil to motarsa ta hawa da
kudaden account dinsane kawai zai tsira dasu Dan kuwa ko asibitinsa dayake
tinqaho da ita MAHMOUD ne ya Gina Masa ita amatsayin tayasa murnar zama
cikakken likita.
Koda commissioner yabasu izinin shiga bai nuna musu komaiba
suka gaisa kafin Khalil yafara Masa bayanin Abinda yakawosu Babu dogo musu yacewa
Khalil din an janye qara belinta kawai
zasuyi akan kudi naira miliyan daya sai kudin tarar bacin suna miliyan daya da
rabi duba da yanayin gidan da akayiwa bacin sunan.
What?????"""Khalil yafada cikin tsananin
mamaki da yiwa commissioner din kallon rashin hankali yace"
Beli ne wannan kokuwa hukuncin Rai da Raine wannan???
Murmushi commissioner yayi Yana gyara zama yace"
Dr khalil zabeera zaka iya Kiran lawyer dinka zamu basa
komai a rubuce sbd samun qarin fahimta.
Kallon bakinsa kawu keyi cikin yanayin tsoron dayafi
mamakinsa miliyan biyu kudin beli?gwarama su fito su fada musu bada itane
bazasuyiba.
Koda lawyer din Dr khalil ya iso aka miqa Masa takardun
belin da aka bugo cikin qanqanin lokaci ya karanta yasake karantawa zuciyarsa
na tafasa ko ba'a fada yasan shirine akayi Dan quntata Masa shida su Amatun,
Koma menene akayi Dan a cimma bazai taba rabuwa da Amatu ba,
Idan anyi ne Dan aga gazawarsa tabbas bazai taba gazawaba
zaiyi komai iya iyawarsa zaikuma qwatar Mata mutuncinta da yancinta.
Dagowa yayi ya kalli kawu da idanuwansa sukai jajir sbd
tashin hankali saiyaji zuciyarsa ta sake karyewa ya waiwayo ya kalli
commissioner cikin yanayin na nuna rashin gazawa yace"
Ahada takardun belin su zama ready zuwa gobe zankawo kudin.
Kallonsa sukayi da sauri duk su duka commissioner na boye
mamakinsa akan Khalil din yace"
Shikenan Dr khalil zabeera muna jiranka goben.
Miqewa yayi ya fice kawu da Barr Bashir na bayansa
kowannensu cikin damuwa Yana Isa bakin mota ya tsaya ya juyo ya kalli Barr
Bashir da idanuwansa dasukai jajir yabude busashen bakinsa yace"
Barr zankiraka gobe muhadu anan abasu kudin inshallah.
Kallonsa Barr yayi cikin kulawa da jimami Yana cewa''
Dr khalil kana ganin zamu karbi belin Nan ahaka?
Inaga muje can zabeera aroqi maganar tarar ajanye Mana ita
zaifi....
Girgiza Kai yayi Yana qoqarin boye rauninsa yace"
Ba buqatar hakan zanhada kudin zuwa goben Inshallah.
Shikenan tunda zaka iya biya ba damuwa Allah yakaimu goben.
Suna Shiga mota yayi shiru cikin tsananin damuwa da tashin
hankalin ta inda zai Fara hada kudin sbd dukkanin kudin account dinsa ya rabesu
gurin case dinnan cikin kwanaki kadan
Duka duka abindake account dinsa baifi dubu dari bakwaiba
Kuma gidan haya yayi niyar kamawa dasu ya ajiye Amatun.
Bayan kudin account dinsa da motarsa baida wata babbar
kadara sai tsadaddun agogunansa da wayoyinsa,
Asibitin dayake tinqaho da ita bata cikin lissafi sbd tamkar
alamar qaunarssuce me qarfi dake tsakaninsa da 'dan uwansa.
Kallonsa kawu yayi cikin tsananin damuwa da sarewa yace"
Khalilu kada ka takura kanka da hada wainnan kudaden daba
haduwa zasuyiba,
Qaddarace wannan me girma ta samemu wadda Allah zai fitar
damu inshallah.,
Zamuje muyita addua Allah yabamu ikon cinye jarabawa sbd
koba komai munqara bambamce halaye irin na wasu masu arzikin Wanda bayan suna
Babu Abinda suka damu dashi,
Farin cikin yayansu da walwalarsu bai damesuba kamar yanda
sunansu da girman kansu ya damesu.
Ahankali yaja motar suka bar gurin suka kamo hanyar gida har
lokacin bai iya cewa ko qala ba sbd nisa da yayi a tunani.
Koda suka Isa ajiye kawu yayi ya wuce zuwa zabeera.
Parking yayi daidai sashen Modibbo yafito ya nufi ciki
jikinsa da zuciyarsa amatuqar sanyaye.
Sallama yayi palon yashiga cikin sa'a Modibbon na zaune
shikadai Yana kallon labarai Koda yaga khalil din Saida yaji tausayinsa Amma
bai nunaba sbd ya dauke Kai Yana cigaba da kallon labaransa.
Gabansa ya zube tareda sunkuyar dakai wasu irin hawaye masu
zafi suka gangaro daga cikin idanuwansa akaro na farko daya nuna gazawa cikin
wani irin sauti Mai tsananin sanyi yace"
Modibbo Ina roqon yafiyarku akan dukkanin Abinda yafaru Dan
Allah ku sassautawa Amatu wlh batada
laifi akan hakan kuskure ne da rashin sanin ciwon Kai wlh batayi Dan wata
manufar Bata suna ko wani Abu ba dabam tayine kawai sbd kudi Wanda tsananin
rayuwa yakaita ga hakan.,
Modibbo Dan Allah Ina roqon gafara da yafiyarku Dan Allah ku
duba maraicinta kada ku tsaurara Mata.
Juyowa Modibbo yayi ya kallesa sosai ganin yanda babban
namiji jajirtacce kamarsa ke kuka ya sauke ajiyar zuciya Yana cewa"
Khalilu zancenka ba'a hannuna yakeba Amma amtsayina na
mahaifinka zanfada maka Abu daya,
Kada kayi Abinda zai kawo maka matsalarda bazaka iya tsayawa
kaga wucewartaba,
Idan kanason yarinyar Nan tsakani da Allah Dan tallafawa
maraicinta to tabbas na amince maka ka aureta sbd aurenta ne kawai zaisa Andi
ya iya sassautowa tunda tariga tazama Zabeera Amma idan kasan tsakani da Allah
yarinyar Nan batada nasaba to Ina baka shawara kayi gaggawar cireta daga
rayuwarka shine kawai sauqi da mafita agareka..
Da jajayen idanuwansa ya dago ya kalli Modibbon Yana
nazartar zancensa wani irin sanyin sassauci na shiga zuciyarsa sbd ya fahimci
zancen mahaifin nasa take sabon qwarin gwiwa yasake shigarsa ya sunkuyar dakai
cikin sanyi yace"
Nagode Modibbo Allah yaqara tsawon Rai.
Yana fitowa sashen ummensa ya nufa inda ya tararda ita zaune
tayi tagumi kamar koyaushe cikin kwanakin tana ganinsa tayi saurin miqewa ya
hanata ta hanyar mayarda ita zaune yana girgiza Mata Kai murya a mace
yace"
Umme zanbar zabeera......
A firgice ta kallesa idonta na cikowa da hawaye zata fashe
da kuka yace"
No umme karki manta kinmin alqawarin bazakiyi kukaba Kuma
kinyi alqawarin bani support adukkanin Abinda Zan yanke.,
Umme albarkanki nake nema a rayuwar dazanyi wajen zabeera
dan Allah umme kimin alqawarin bazaki saka kanki cikin damuwar dazata cutatar
dakeba.
Kasa riqe kukanta tayi ta fashe dashi tana cewa''
Khalil Dan Allah kada kabar zabeera kabarni katafi Dani Nima
Wlh bazan iya zama baka nanba,
Katafi Dani duk inda zakaje zanzauna acikinku,
Zan zauna taredaku zanyi renon 'yayan dazaku haifa........
Kasa hkr yayi ya rungumeta Yana girgiza Mata Kai Yana cewa''
Umme Zaki zauna anan gidan aurenki sai mutuwace kawai zata fiddaki zabeera.
Aa khalil zanbika Dan Allah kada ka tafi kabarni.
Ganin yanda ta daga hankalinta yasashi zamewa da sauri ya
fice Yana danne zuciyarsa dake neman fashewa yayi hanyar sashensa.
Kayansa ya diba a akwati tareda kwashe agogunansa da
takalmansa masu tsada sosai da duk abubuwan dazai buqata ya saka cikin mota
tareda dukkanin takardunsa yafito yaja motarsa yabar zabeera.
Daga zabeera gidan Ibrahim yaje yafara ajiye kayansa acikin
dakin farkon Shiga ya rufe dakin da mukulli ya fito yarufe gidan ya wuce.
Tareda Ibrahim din sukaje gurin masu Saida agogo akayiwa
agogunansa kudi kaf aka shiye suka hada kusan dubu dari uku daganan gurin Wanda
zai siye motarsa suka nufa aka Fara cinikin saidai abin son Rai yayiwa mutane
yawa Dan siyan wulaqanci sukaiwa motar har kusan mutum shida sukaiwa motar siyan
wulaqanci qarshe Dole ya saidata miliyan daya da dubu dari suka karba ya hada
hadda kudin account dinsa suka tashi 2.6.
Mashin yahau Abinda baitaba hawaba a rayuwarsa ya nufi
gidansu kawu anan yafadawa kawu ya hada kudin daga iyami har kawu basusan lokacinda
suka fashe da kuka ba.
Murmushi me ciwo kawai yasaki batareda yace komaiba anan
yayi sallar ishai iyami tasashin tuwon Dole kafin yatashi yatafi.
Mashin yasake hawa yakoma gidan Ibrahim Yana Shiga Allah ya
taimakesa ana kawo nepa Nan ya tube yayi wanka da ruwan rijiyar gidan da
Ibrahim yacika Masa durum da kansa masu shegen tsananin sanyi Wanda Saida suka
saka numfashinsa kusan daukewa daya watsasu.
Boxer da singlet kawai yasaka yadawo ya kwanta Kan sabuwar
katifar da Ibrahim din yasiyo yau yakawo Masa.
Kiran salman ne keta shigowa wayarsa Yana qin dagawa sbd duk
kwanakin ya tashe duk banyarda salaman zaishigo cikin Al'amarin sbd bazaiso
laifin ko wani Abu yasamesaba kodan yanda Amatu ta daukesa kamar usinta.
Kiran MD ZABEERA ne yashigo wayar ya qurawa wayar Ido tsawon
sakanni kafin ya dauka Yana boye damuwarsa Nan suka hau Maganar shi cikin sanyi
MAHMOUD Kuma cikin nutsuwa da miskilanci.
Koda asuba tayi daqyar ya iya dafawa ya tashi zaune sbd
tsananin sanyin daya Gama shigewa ya Kama dukkanin qasusuwansa.
Daqyar yayi sallah ya jingina da bango Yana makure jikinsa
guri daya sbd kaf gidan gaba daya koina sanyi yake fitarwa sbd gaf suke kusada
ruwa.
Daqyar yaga qarfe Tara na safe tayi ya miqe yasake zuwa bayi
ya watso ruwan sanyin yafito jikinsa na Dan rawa yashigo daki ya shirya cikin
qananan kaya masu Dan kauri ya bar gidan sbd Jin kamar zai iya suma da ciwonsa
dake gaf da tashi.
A gidansu kawu yaci biredi da kunun tsamiya tareda waina da
iyami tasiyo Masa me kyau ta shinkafa.
Kobai fadaba sungama gano halinda yake ciki sbd kada su qara
Masa damuwa sukaqi yimasa maganar sai tattalinsa dasukeyi.
Qarfe goma da rabi a central tayi musu shida kawu suka zauna
zaman jira har qarfe goma sha biyu commissioner bai buqaci ganinsuba sai daya
da rabi Bayan anyi sallah anfito tukuna aka kirasu suka Shiga.
Barr Bashir ne yacire kudin beli da Tara ya bayar akayi
rubuce rubucen daza'ayi aka gama kafin akace afiddo Amatun.
Lokacinda aka kawota suna ganinta kowannensu idanuwansa suka
ciko da hawayen baqin cikin ganin halinda take ciki Amma ita ganinsu yasata
qaqalo qarfin hali tana danne azabar cizon sauri da galabaituwar yunwa da
dau'dar datake ciki Danma tunda tazo koda Wasa ba'a taba dukantaba Wanda
umarnin Andi ne kada a daketa ko so daya.
Babu Wanda ya iya mgn acikinsu aka Bata gyalanta da
takalmanta suka fito tana tafiya daqyar a galabaice.
Suna fitowa titi taga suna qoqarin taron adaidaita ta kalli
Dr khalil din da mamaki Kan fuskarta saidai batayi maganaba suka tare adaidaita
biyu ita dashi suka shiga daya kawu yashiga daya.
Ahankali ya juyo ya kalleta cikin tsananin kulawa da damuwa
akan fuskarsa yace"
Are you ok?
Kallonsa takeyi tana mamakin sauyawar dayayi
Yayi duhu tayi Rama hakama kamar Wanda baida lafiya sai
Nishi Nishi yakeyi kamar Wanda yayi aikin wahala.
Kai ta daga Masa ahankali tana lumshe ido a wahalce.
Koda suka iso gida tuni mutanen gidan suka rude da murna da
yiwa Allah godiya take aka hada ruwan wanka masu zafi aka Kai Mata
Maman junior hadda tayata wanka kamar me haihuwa haka aka
gasata tasamu 'dan qarfin jiki aka Bata abinci taci tareda magungunan da Dr
Khalil din yasiyo Mata ta kwanta take baccin wahala ya dauketa.
Da daddare kafin ya wuce Bayan yaci tuwon iyami cikin
nutsuwa ya zayyanewa kawu duk halinda yake ciki yanxu tareda gabatarda
buqatarsa na auren Amatun
Kawu ya sauke numfashi me sanyi yace"
Khalilu ko bakayi mgn ba nayi niyyar aura maka Amatu kobabu
danginka ko daya sbd aduniya Babu Wanda ya cancanta yazama Dole yazama mijin
Amatu idan bakaiba Dan haka wlh khalilu nabaka Amatu amatsayin Mata ka shirya
nida kaina zanje masallacin juma'a nayi sanarwa ranar juma'ar Nan Inshallah
za'a daura muku aure.
##Mamuh#

No comments