MIN QALB 25
MQ 25*_
Saurin dauke idanuwanta tayi tana juyar da kanta zuwa wani
gefen tana cigaba da dariyarta ta firar dasukeyi da Salman Wanda shima ya lura
da yanayinda Amatun tashiga sai ya basar kamar yanda itama ta basar suka fito
suna cigaba da zancensu.
Gurin MD din ya nufa ya bude Masa mota ya fito Yana gaidashi
tareda fada Masa saqon Dr khalil daya basa sbd yakasa samun wayoyin MD din
duka.
Itadai gaba tayi tashigewarta ko Palo Bata tsayaba sbd sanin
ciki sukayo
Anty zarah ce ta tsaya tai Masa sannu da zuwa ganin Salman
yasata itama wucewa sbd yanda ya amsa kamar bazai amsa ba karya kwafsa Mata
gaban Salman din itama bedroom dinta ta wuce Kai tsaye sbd dukkaninsu suna
buqatar wankene kawai Dan ko yunwa basa ji Dan Babu kalar cimar dasuke buqata wadda Salman be
siya musu ba Wanda kusan hakan yasa tafarajin qaiqayin ciwon Abinda rayuwarta
take ciki na rashin kulawa daga kowa musamman mijinta Wanda shine yakamata ace
ya jiyar da ita dadi da nushadin rayuwa amma Bata samu hakan daga kowa ba sai
yanzu sanadin Wanda batamasan meye ake Kira gata da arziki ba a rayuwa gashi ta
sanadinta suna nishadantuwa da rayuwarsu da Basu San komaiba sai bin umarni da
oda.
Wanka tayo ta shirya cikin kayan baccinta ta sanya dogon
hijab tayi sallah tana idarwa taje ta dauko yoghurts a fridge ta zuba cikin cup
ta qara Masa madarar gari sosai ta juya sosai tadawo daki tana Sha tana
daukarwa Dr khalil hotunan lallenta tana tura Masa saigashi yakira.
Daukar wayar tayi tana murmushi qasa qasa tace"
Kai Dr baka shanye rada ba.
Wani siririn numfashi ya sauke Wanda yasata aje spoon din
hannunta cikin kulawa tace"
Yadai???
Lafiya najika kamar kana bacci?
Murmushi me sauti yasako Mata Yana gyara kwanciyarsa da
lullubinsa yace"
Lafiya kalau kawai sanyin garin Nan ne yafara tabani tun
satin daya gabata garin qasar ta daina
shafamin lafiya Amma ai alhmdlh tunda gobe zamu dawo.
Ajiyar zuciya ta sauke tana cigaba da Shan yoghurts din
tace"
To Meyesa zaka zauna harka Dade haka a inda baya shafa maka
lfy???
Gwara da gobe zaka dawo da yau saina daga maka hankali
kabaro.
Murmushin qarfin hali yayi Yana cewa''
Gobe idan nadawo me Kika ajemin?
Wani juyi tayi tareda kifewa kan carpet tace"
Saika dawo zaka gani.
Fira sukeyi ahankali sbd yanayin yanda yakejin jikin nasa
sbd sanyi ya shigesa sosai Wanda yafara yiwa lafiyarsa barazana Dan yanaji
ciwonsa yafara tashi ahankali.
****Miqewa Nuratu zabeera tayi daga zaunen datake a cikin
restaurant din blue fox tana juya envelope din data karba tana sakin wani irin
qyayataccen murmushi tace"
Manager kayimin Abinda zai juya rayuwata nasamu Abinda
nakeso kaima kasamu wadda kakeso,
Wannan taimakon naka yabani farin cikin danayi shekaru
bansamu ba sbd Dr khalil zabeera shine farin cikina,burina dakuma zuciyata...
Kallonta yayi tareda miqewa tsaye yace"
Ina fatar zan mallaki Amatu kamar yanda kikaimin alqawari??
Karka damu idan ka iya takunka zakayi amfani da damarka ka
sameta daga lokacinda aka watsota daga rayuwar farin cikina da zabeera ma
gabaki daya.
Barin gurin tayi tana sake riqe envelope din farin cikinta
na qaruwa ta nufi motarta tashiga ta rufe..
Bayan ta zauna cikin motar kallon envelope din tayi tana
cewa"
AMATULLAH K SALEH wannan shine asalinki tun kina Yar bolarki
har zuwa yanzu,
rayuwar alfaharinki
tazo qarshe,
Kinyi kutse a tsakanin masoyanda ba'a iya rabawa sbd son
danakewa khalil hankalinkima bazai daukaba bare ki iya rabamu,
Kina alfahari da kanki dakuma gatan da Kika samu daga
Khalil, Modibbo da Andi ma gaba daya
Zan ruguza rayuwarki gabaki daya sai nasaka kowa ya tsaneki
fiyeda yanda tunaninki zai dauka,
Ki shirya komawa rayuwar sata da dauke dauken da Kika fito
bayan kinyi shari'a da familyn ZABEERA na Bata sunan da kikaso yimusu.
Cikin handbag dinta ta sakashi ta ajiye jekar gefenta tareda
tayarda motar tabar gurin cikin mugun speed Dan amatse take data Isa zabeera
sbd so takeyi kafin Dr khalil zabeera ya iso an dade da korar Amatun daga
rayuwarsu,
Agogon motar ta kalla taga qarfe biyar ta yamma takusa gashi guraren yamma jirginsu
Khalil ake sakaran zai sauka,gudu taqarawa motarta tana kallon titi.
***Cikin riga da skirt na lace maroon tayi adonta tareda
daura dankwalin lace din ta sanya Yan kunne marasa tsawo sosai kalli agogo tana
zama bakin gado da wayarta a hannu tana daukar hoto tace"
Kowane lokaci yanzu Salman yace Dr zasu iya saukowa Meyesa
yau nakejin wani iri cikin raina kamar inajin kunyarsa ne kokuwa wani abin
daban.
Shiru tayi gabanta na 'dan faduwa taji duk batajin sukuni ta
miqe tana ajiye wayarta gefen gadon ta miqe tareda fitowa zuwa Palo gurin anty
zarah ko zata debe Mata yanayin da fira.
Tana fitowa anty zarah na fitowa daga nata bedroom din sanye
da doguwar Turkish abaya red itama tayi kyau sosai sai qamshi takeyi kamar
Amatun sai abin yabasu Daria kusan atare suka saki dariyar Zarah na cewa''
Wannan da kishiyoyi muke bansan wa mijin zai Fara kalla ba
sbd kalar duk jajaye ne Kuma kalar ja idan ba mantawa nayiba tana cikin kalar
da MD ke tsananin so sbd ance kalar kayan mahaifiyarsa kenan kafin ta rasu sbd
sarautar da mahaifinta yataba Yi.
Kallonta Amatu tayi tanayin shiru cikin tunanin kalamanta
aranta tace"
Anty zarah Allah yasa kada 'yan Amin na kusa su karba Miki
zancenki sbd ita Magana ana fadarta ne da fatar 'yan Amin su amsa shiyasa ake
cewa kafada alkhairi ko Kayi shiru.
Wucewa gaba anty zarah din tayi Amatu naci gaba da binta da
kallo zuciyarta na sake shiga fargaba saita kuma komawa daki zata zauna kenan
saiga Kiran wayar Salman da sauri ta dauka Dan dama shi zata Kira ya debe Mata
kewar tunaninta..
Salman ka......
Muryan Dr khalil taji yace"
AMATULLAH.
Wani irin sanyi da farin ciki taji ya kwaranya cikin ranta
batasan lokacinda tasaki wani irin qaya taccen murmushi ba tana furta"
Alhamdulillah ya Allah.
Har cikin ransa yaji dadin hakan ya kashe wayar tareda
miqawa Salman batareda yace komaiba suka kamo hanyar gida.
Koda suka iso gida a gurin ummensa ya sauka Dan itama a
matse take da ganin Dan nata musamman sbd kwanakin wata sabuwar qauna da kewar
danta ke kamata shiyasa itama a matse take da taga abinta Nan aka hau hidimarsa
kayan abinci da snacks kala kala anyi Masa taredasu fruits dasu fura duk dai
wasu kayan marmarin kewar gida anyi Masa Nan yaci abinci tareda ita da Haj
maryam da salman da Nuratu wadda koda ta iso gida kusan ataredasu Khalil din ta
shigo Dan motarsu na gaba kafin Tata
Ganinsa yasa takasa riqe farin cikinta da zumudinta tama
manta da Abinda tadawo dashi Nan ta zauna cikinsu anacin abincin tana faman
kula da duk motsinsa da Abinda yake so iyayensu kuwa sai washe baki sukeyi sbd
dama shine burinsu hada Khalil din da Nuratu.
Bai bar gurin umme ba sai magriba ya wuce gurin Modibbo acan
sukai sallah taredashi da salman da MD ma Wanda ya shigo ana magribar.
Bayan sungama sallah anan suka zauna tareda Modibbo Yana
tambayar MD Amatu sbd duk yau da jiya Bata Zo ta gaidashiba kamar yanda ta Saba
shiru MD din yayi Yana Dan sauke Kai yace"
Inshallah duk suna lfy sbd Nima na kwana biyu bana zama gobe
ma insha Allah Nima zanyi tafiya zuwa Germany.
Allah ya taimaka ya tsare yabada sa'a Kuma.
Amin dukkaninsu sukace suna qoqarin miqewa cikin sautinsa me
saka nutsuwa yace"
Khalilu matarka Ina saka ran a lissafi saura wata uku
haihuwarta ko???
Tsit sukayi dukkaninsu su ukun
Take zufa tafara Dan tsatsafowa Khalil din MD kuwa fararen
idanuwansa ya zuba Masa Yana jiran jin amsar da Khalil din zai bada sbd shidai
wadda ake maganar cikin akanta tana zaune gidansa Amma baitaba ganin ciki a
jikinta ba gashi ana maganar saura wata uku haihuwa.
Dan gyara murya Khalil yayi cikin girmamawa yace''
Inshallah haka ake saka Rai saidai cikin yazo da tangarda ne
sbd rashin girmansa ya bayyana cikin baida lfy inasaka ran ma gobe zanje da ita
asibiti musake dubawa.
Cikin watanni da dama baa fada baida lfy ba sai yanxu?
Sarqewa Dr khalil din yayi Yana Dan gyara murya yace"
Ayi mini afuwa Modibbo nayi kuskuren rashin sanarwar.
Shikenan ba damuwa kuje Allah ya Bata lfy.
Amin"Khalil din yace suka miqe suka fito tare suna
tafiya zuwa hanyar sashensu dayake direction guda.
Tafiya sukeyi su biyu Banda salman daya wuce ya nufi motarsa
yafita zabeera ahankali kowannensu shiru Babu me mgn dama sun Saba haka suke
koyaushe idan suna tare saisun jima shiru kafin su Fara mgn Wanda MD ne me
wannan halayyar shikuma Dr khalil Yana girmama kowane irin Hali da MD ya zabawa
kansa da rayuwarsa.
Tsayawa yayi ahankali batareda ya juyo ya kalli khalil dinba
yace"
Bansan wane mataki ka dauki wannan alamarin ba Amma ya
kamata kasan kana saka kanka cikin hadari along with her.. 'dan shiru yayi
kafin ya juyo ya kalli khalil din cikin wani irin yanayi yace"
Atleast kayi tunanin Hali da Abinda zata fuskanta kafin
kasata a irin wannan tight spot din sbd yanxu ku duka Kuna situation dinda only
God can help so kafin komai ya fita hannunka kasan Abinda kakeyi ka dawo
daidai,the truth doesn't cost anything but a lie could cost you everything.
Kallonsa Khalil yayi tareda sauke ajiyar zuciya cikin damuwa
yace"
Bansaniba ko kasan Abinda nake qoqarin boyewa Amma bazaka
iya fahimtar dalilina nayin hakan ba sbd komai yazone alokacinda banyi
tsammaninsaba Babu mafita bayan wadda na dauka a wancan lokacin da yanzu ma..
Denying the truth doesn't change the fact cewa ka dauki
hanya Mara bullewa,
Ka zauna kayi tunani zaka samu wata mafitar wannan batayi
ba.
Yana Gama fadar haka ya wuce gaba batareda ya juyoba yayi
hanyar sashensa.
Shiru Dr khalil zabeera yayi yana tunanin maganganun MAHMOUD
din wainda suka sakashi zurfin tunanin sbd tabbas qaryarsu takusa qarewa wadda
idan bai nemo mfitaba asiri ya tonu to daga Ummensa har Amatu dashima suna
cikin matsalarne,
Babban burinsa daya dawo dashi shine maganar auren Amatun
tukuna sbd duk wasu kayayakin aure na akwati ya siyosu yazo dasu saitin
akwatinsa cif ya hado kayan aurensa Wanda ko gidan bai kawosu ba daga airport
gidansu kawu suka Fara ajiyesu kafin su qaraso gida.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin shima yabi Bayan MD din zuwa
ganin Amatu da tun Yana gurin umme take kiransa yaqi dauka sbd kada farin cikin
ummen ya gushe.
##Mamuh#

No comments