MIN QALB 24
MQ 24_*
Tafiya sukeyi ahankali cikin motarsa Babu me Magana sai
sanyin AC da qamshin turarensa daya Gama Kama motar dama can yake ratsata Yana
Bata wani sabon yanayi cikin zuciyarta Wanda yasata fadawa tunani.,
Tuqinsa yakeyi cikin nutsuwa shima Yana jiyo siririn
sahirtaccen qamshin jkinta na Shiga hancinsa ahankali Wanda kusan shima yasashi
Shiga tunanin banbanta yanayin qamshinta Dana zarah.,
Istigfari yayi saurin Yi cikin ransa Yana Dan tsuke fuska
tareda 'dan qarawa motar gudu.
Ganin sun kamo hanyar blue fox yasata saurin kallonsa
murmushi na sauka Kan fuskarta tace"
Rabin ran Anty Dan Allah muje blue fox akwai abinci me kyau
da dadi acan.......
Wani irin kallo ya juyo ya aika Mata Jin sunan data kirasa
dashi Wanda yasashi qurawa cikin Idanuwanta Ido Yana son sake tabbatarda Abinda
takirasa dashi _Rabin ran anty_ yanda tafada sunan batareda kulawar
komaiba yasashi yimata wannan kallon itama Jin idanuwansa akanta yasata kasa juyowa
ta qurawa waje Ido Yana damqe hannunwanta dake rawa zuciyarta na harbawa.
Jin shiru yasata Dan dagowa tareda juyowa ahankali ta
kallesa hankalinsa na Kan hanya saita qurawa fuskarsa da fararen hannuwansa
dake tuqin motar cikin nutsuwa da qwarewa,
Kan fuskarsa ta tsayarda kallonta tana yaba kyawu da tsarin
fuskarda ubangiji yayi Masa me daukeda da tarin kwarjini da Kamala,
Dogon hancinsa ta kalla zuwa manyan idanuwansa batasan
lokacinda ta lumshe ido ba hawaye na gangarowa daga cikinsu batareda ta gogesuba
cikin ranta tace"
Meyasa zuciyata ta zabi wahalar da rayuwata data Dr ta
hanyar son Dan uwa mafi soyuwa agaresa?
Dukkanin kyawu da Abinda MD yakedashi Dr khalil dinta nadasu
harma yafi MD din kyawawan halaye masu sanyaya Rai hasalima kusan kamanninsu
daya sbd duk mahaifinsu Modibbo suka dauko har Khalil dinta ma yagi MD din
hasken fata saidai MD ya nuna Masa gogewa da hutu irin na Boko da yawan qasashe
suka hudasa sai kalar fatar mahaifiyarsa daya dauko me sheqi.
A harabar blue fox din yayi parking tareda Dan juyowa ya
kalli gefenta tayi saurin share hawayenta tana bude motar ta fito tana washe
baki cikin tsananin farin ciki ta juyo daidai ya zagayo tace"
Yau duk abindake restaurant dinnan saina cire kwadayinsa na
tsawon aikin danayi anan din.
Bai kalletaba yayi gaba ta biyosa tana sake bayyanar da
murnarta ta zuwa gurin.
VIP direct suka nufa inda tuni aka hau sintirin attending
dinsu ga mamakinta kusan Rabin ma'aikatan gurin an sauyasu Nan ta bada odar
abinci kusan kala hudu da tarkacen su fruit salad harda ice cream da furar blue
fox din me shegiyar Madara da Laban yoghurts.
Table dinsu kusan kasa daukan abubuwan yayi sai kawai yayi
odar noodles with veggies salad da power drink yafara ci cikin nutsuwa
Yana kallonta tana cin abincin cikin tsananin Jin Dadi Dan harwani lumshe ido
takeyi tana cika bakinta da Naman kazar chicken rings dataji carrot da spices.
Yana kallo ta Gama yagalgala kazar ta janye gefe ta jawo
shawarma tafara ci itama ta ajiye ta janyo soyayyan dankalin dayaji egg source
Furarta ta janyo ta kurba ta lumshe ido tana cewa''
Wayyo Dadi" kafin ta aje tacigaba da cin noodles Kuma.
Jingina yayi da Bayan kujera Yana zuba Mata iduwansa masu
karya kuzarinta tareda dukkanin nutsuwarsa Yana kallonta kamar ya baby a
gabansa.
Saida tayiwa komai ci rabi aje rabi kafin ta qoshi ta dauki
ice cream dinta ta bude ta diba tana hadiye yawun matsuwa taji sanyinsa ya
sauka a bakinta taji anrike ice cream din
Da sauri ta dago idanuwansu suka shiga cikin na juna
ahankali ya girgiza Mata cikin qaramin sauti yace"
This is not good for your health......
Kasa motsi tayi ta harya zare ice cream din daga hannunta ya
ajiye idanuwansu na cikin na juna Saida waiter din dake tsaye yayi gyaran murya
da qarfi Yana sake miqawa MD din bill dinsu.
Fuskewa yayi Yana Dan tamke fuskarsa ya juyo ya Ciro ATM
card dinsa ya miqawa waiter din batareda ya karba bill dinba.
Bayan andawo Masa da atm din anyi clearing bill dinsu suka
fito suka Shiga mota sukabar gurin.
A mota shiru tayi tana sauraron karatun Qur'an din dayasa a
motar Yana fita ahankali saitaji tana sake samun nutsuwa da yanayin da suke
ciki na kasancewa da juna ahaka.
Koda suka dawo zabeera har bacci yafara daukarta cikin motar
shiyasa da yayi parking sai bai tayarda itaba hakama bai kashe motarba sbd AC ya
zauna ya fiddo wayarsa Yana duba saqon dayaji shigowarsa sunacin abinci.
Ahankali ta bude idanuwanta dake cikeda bacci ta zuba akansa
tana lumshe ido ahankali ta furta"
Tabbas Ina cikin tsananin son MAHMOUD ZABEERA Kuma so me
qarfi Wanda nakejin kamar ruhina zai rabu da gangar jikina idan nayi nesa
dashi,
Lumshe ido takuma Yi tareda budesu akansa cikin sauti me
taushi dazai iya jinta tace"
Nagode.
A natse ya juyo ya kalleta da nasa idanuwan dasuka nuna
sunfara Jin bacci taji zuciyarta na qara narkewa da sonshi tayi saurin dawowa
hayyacinta tareda tashi zaune tabude motar da sauri ta fice hartana hadawa da
Dan gudu tayi ciki.
Kai tsaye bedroom dinta ta nufa ta fada Kan gadon tana sakin
hawayen dataketa riqewa tace"
Amatu kidawo hankalinki Mana,
Kidawo Amatunki da kowa yasani,
Amatun Dr khalil matar Dr khalil,
Babu kowa a zuciyarki sai Dr khalil sbd shine Wanda zuciya
da ruhinki keson aure.
Ta jima ahaka kafin ta miqe tafada toilet ta wanko fuskarta
tayi fitsari tazo ta kwanta tareda lullubewa tana qudurtawa ranta gobe zata
amayarwa Salman abindake zuciyarta kafin ta rufe zuciyar gaba daya ta mallakawa
Dr khalil dinta Wanda idan har tana Raye Inshallah batada miji sai Dr khalil.
Washe gari tunda wuri ta tashi yau da kanta ita tafara Kiran
Dr
Meeting zasu shiga Amma ganin kiranta Saida ya tsaya ya
dauka yaji lafiyarta kafin yace idan yafito zaikirata.
Wankanta tayi ta shirya cikin riga da skirt na atampa kalar
blue tayi Mata kyau sosai ta yafo gyalen akanta sbd Bata dauro dankwalin
kayanba.
Palo ta fito ta nufi kicin da kanta yau ta dafawa kanta
indomie da dafaffen kwai guda biyu sai custard data hado Wanda yaji uwar Madara
takoma dakinta acan tayi breakfast dinta tana gamawa ta fitoda kayan ta maida
kicin Takoma daki ta sake kwantawa tana tunanin Dr da irin dibbin soyayya da
qaunar daya Bata,
Ya juyawa iyayensa baya akanta alokacinda aka koresa ya
amince zaibar komai da komai ciki hadda iyayensa da 'yan uwansa da rayuwar daya
taso ciki duk sbd ita
To menene Dan itama ta danne zuciyarta ta tauyeta daga
Abinda takeso ta bashi koba komai Al'amarin da zuciyarta ta dauko me girma ne
sbd mijin anty zarah ta haramtawa kantashi Koda sonsa zai kasheta har abada su
biyun Nan anty zarah da Dr bazata taba barin susan halinda zuciyarta ta Shiga
akan mutuminda sukafi qauna da komai arayuwarsu.....
Kiran Salman ne yashigo wayarta cikin nutsuwa ta daga tana
qoqarin kawar da damuwarta tace"
Likitan qashi na duk Nigeria""ta qarasa tana Yar
dariya.
Shima 'yar dariyar yayi Yana gyara zama cikin motarsa
yace"
Zakije mukai usi airport kokuwa na tafiyata?
Wuntsilowa tayi bakin gado tana janyo dankwalinta da
gyalenta ta fito tana cewa''
Ai karma kamin haka idan ban takasa a matsayin 'yar uwarsa
da bamu taba rabuwaba arayuwa sai yanzu to zan takasa amatsayin matar Dr khalil
tunda bayanan Dan shine yafi kowa cancantar ganin wucewar usi Dan shine yakawo
wannan murmushin akan fuskarsu na samun cikar buri su samu ilimi kamar sauran
'yaya.
Ganinta kawai yayi tana bude gaban motar ta shigo ta zauna
tana kashe wayar tace"
Muje ko¿
Dariya tabasa ya girgiza Kai Yana cewa'
Amatun likita bokan turai.
Kallonsa tayi tana cewa''
Nidai muje tun kafin na huce da zafi zafina nafito Dan yiwa
USI huduba.
Jan motar yayi suka fice suna Dan taba fira ahankali har
suka Isa gida inda su kadai ake jira suzo dauki usin.,
Tunda tashigo gidan idanuwanta suka sauka Kan 'yan gidan kaf
a tsaye cirko cirko tsakar gidan kowanne fuskarsa cikeda yanayin damuwar rabuwa
da USI din ta juya ta kalli kawu dake zaune radionsa a kunne Amma yanayin
fuskarsa yasa taji idanuwanta suna qoqarin cikowa da hawaye tana kallon iyami
sai kawai ta qaraso da sauri Yana sake hawayenta ganin yanda Usin yake tsaye
riqeda hannun iyami Yana Bata qwarin gwiwa.
Usman din ta kalla tana share hawayenta tasaki murmushi Dan
cirewa kowa damuwa takai Masa duka a baya tana cewa"
Ki yanda kasa kowa cikin damuwar tafiyarka bayan duk hutawa
zamuyi da rashin Jin ka musamman maman junior da anty salamatu
ko???""tafada tana kallon maman junior da anty salamatun dake
qarasowa da jakarsa data fito Masa da ita.
Murmushi maman junior tayi tana cewa''
Usi Allah yabaka sa'a kamaida hankali kayi karatu ko zaka
tallafa Mana wata Rana idan lokacin cin amfanin karatun yazo sbd Kaine kasan
wahala da gwagwarmayar rayuwa damukeyi anan gwamnati batamasan da ire irenmuba.
Maman junior kada ki damu daya bayan daya dukkaninmu sai usi
yakaimu Hajj da umrah da albarkar wannan karatun dazaije Amma idan kuka tsaya
Kuna Masa wannan fuskar ta marayu ta Yaya zaije da gwarin gwiwarsa ai kawai ki
Masa tashin hankali da hayaniyar da kuka Saba shizaisa yaje Yana tuno kowa
ayanda halayyarsa take....
Dariya dukkaninsu suka dauka Nan aka hau hayaniya ana Masa
Allah ya kiyayaye shima sai hakan yasashi Jin Dadi ya saki fuska Yana amsa musu
kowa ana Masa alqawarin Abinda za'ayi Masa idan akai kudi.
Kawu da iyami dasu akeje har airport inda suka taru su duka
da hayaniyarsu suka cikawa Salman motar da hayaniya sai suke qara burgesa
musamman Amatun dake qoqarin Hana kowa shiga damuwar tafiyar Usin bayan ita
Yana iya hango tsananin damuwa da fargabar rabuwa da Usin a idanuwanta tana
daurewa ne kawai.
Suna Isa ko zama basuyiba aka Kira jirginsu Salman ya
kallesa Yana basa sauran dukkanin bayanan da Dr yace yayi Masa tareda basa
takardun komai Dana atm card na account din da aka bude Masa tareda wadataccin
kudi aciki ya miqa Masa tareda Dan rungumesa Yana cewa''
Zaka ringa ganina akai akai inshallah har sai kagama sanin
komai da komai just take care brother,
Kuma Ina fatar zaka saka mijin 'yar uwarka alfahari dakai
wata Rana.
Kallonsa yayi ya kalla Amatu Yana qirqiro murmushin qwarin
gwiwa yace"
Inshallah Dr khalil saiyayi murmushi ga wannan aikin
alkhairin nasa.
Gyada Masa Kai tayi tana qoqarin maida hawayen dake subuce
Mata
Suka rungume suna tana sakin hawayenta gaba daya suna zubowa
ba tsayawa.
Cikin kunnenta yace"
Amatu Ina Miki fatar samun Abinda kikeso arayuwa Wanda
zaisaki farin ciki,
Inaso Kuma kimin alqawarin Babu wani Abu dazai sauya
matsayin Dr acikin rayuwarki kimin alqawarin da ke da kanki zaki kirani Dan
sanar Dani aurenki da Dr Khalil idan lokacin yayi.
Rintse ido tayi hawayenta na sake gudu ta janye jikinta tana
kallon qasa tace"
Usi zuciyata takamu da son wani Wanda ba Dr khalil ba so me
girma Amma wlh shima son Dr khalil bai sauyaba a zuciya da rayuwata,
Ba laifina bane sbd bansan yaushe hakan yafaru ba,
Bansan ta Yaya zan kankare wannan son daga zuciyata ba Amma
nasan ta yanda zan dannesa dannewar da har abada bazai tasoba bare wani yasan
dashi zanbarshi cikin Raina har mutuwata,
Jan kuka tayi ahankali tana cigaba da cewa''
Usman ayau ni Amatu nayi maka alqawarin bazan taba auren
kowaba sai Dr khalil,
Nayi alqawarin Dr bazai taba fuskantar sauyawa daga gareniba
sbd shi kadai na zaba amatsayin mijina Inshallah...."wani siririn kuka
taqarasa maganar dashi zuciyarta na wani irin nauyi.
Baiyi mgn ba ya juya gurinsu kawu yayi musu bankwana ya wuce
Yana danne zuciyarsa dake Jin tsananin damuwa da tsoron Abinda Amatu ta fada,
Shin yayi Mata adalci satayin alqawarin auren Dr Bayan
tafada Masa akwai Wanda zuciyarta ke tsananin so???
Baya tunanin baimata adalciba sbd a nasa gani da sanin Babu
Wanda zata aura ya sota ya qaunaceta yabata farin ciki da kulawa fiyeda Dr
khalil zabeera Dan haka koma waye zuciyarta keso farin cikinta da kulawar
dazata samu daga Dr yafi matasu ahankali zata manta sonta zuciyarta ta koya son
KHALIL din.
Ahanyarsu ta komawa Babu me mgn acikinsu kowa yayi shiru
Yana tunani kamar basune suketa hayaniya ba a hanyar zuwa.
Su kawu tunanin rahuwarsu dasu Usin sukeyi sbd dukansu basa
gabansu yanzu sai sukejin kamar rabuwa sukayi dasu gaba daya musamman iyami
datakejinsu kamar itace ta haifesu gashi yanxu ta tashi Babu ko daya a gabanta.
Shikuma Dr Salman yasan irin ciwo da radadin datake ciki na
zabar danne sonta tabi Abinda rayuwarta da 'yan uwanta keso.
Ajiye su kawu sukayi suka nufi gida har lokacin Babu me
Magana acikinsu Saida yayi parking qofar part dinsu anty zarah sai ga MD
ZABEERA yafito Yana amsa waya fuskarsa sai sheqin kwarjini takeyi ya nufi
motarsa ya bude ya shige drivernsa na ciki yaja sukabar gurin idanuwanta na
binsa da kallo har motar ta bace Salman na lure da ita ya saki numfashi
ahankali yace"
Duk zabin dazakiyi Amatu kisani ni Salman zabeera Ina
bayanki dari bisa dari saidai bazanso ki zabi Abinda zai kawo damuwa da qunci cikin
rayuwarkiba,
Soyayyar MD ZABEERA Babu Abinda zata baki sai damuwa sbd
bazai baki soyayya da kulawar da kike nemaba infact baimasan kinayi ba Koda
yasani Babu so agabansa sbd keda idonki Kinga hakurinda matarsa keyi akansa
Wanda mu bazamu iya ganinki kina irin wannan rayuwarba so please AMATULLAH for
our sake kadaki saka kanki cikin quncin dazaki sakamu muma.
Share hawayenta tayi tasaki murmushi me ciwo tace"
Dr Salman zabeera daga yanxu anan munrufe maganar MD ZABEERA
sbd soyayyarsa ba Abu bane Dani Amatu zansamu,
Soyayyarsa wani bangarene me girma a zuciyata da bazan iya
cirewa ba saidai Kuma illace ga mutane da dama Dan haka na zabi azabtuwa da ita
ni kadai acikin Raina bazan Bari ta azabtarda masoyanaba dan haka daga yanxu
Babu mgnar MD ZABEERA da AMATULLAH,
Zuwa yanzu nasan kagama sanin Abinda yake faruwa kasan
banida aure da Dr Khalil dan haka idan har ka daukeni kamar Yar uwa wadda kake
tsananin qauna to ka nesantani duk Abinda zai cigaba da zurafaf soyayyar MD
ZABEERA ka tayani nitsawa da kutsawa cikin son KHALIL ZABEERA sbd na riga na
yanke shi na zabarwa kaina.
Kallonta ya tsaya Yi zaiyi Magana tayi saurin girgiza Masa
Kai tana share fuskarta da tissue din motar tana murmushi tace"
Zancen ya wuce Kuma ai"" dan sake batarda zancen
ta Dora da fadin"
ni yanzuma so nakeyi kafara koyamin wannan turancin naka na
turawa idan Dr yadawo so nakeyi nabasa mamaki.
Dariya yayi Yana jinjinawa gwarin gwiwarta na kawo dariya
Kan fuskarta da boye abindake zuciyarta Wanda hakan na daya daga cikin Abinda
yake burgesa gameda ita.
Fitowa sukayi suna fira sama sama suna dariya kamar Babu
Abinda yafaru.
Anty zarah na ganinsu ta daga wayar hannunta tana cewa''
Cikinku fa daya zankira sbd Ina ganin bangantaba nasan Kaine
kawai zaka fita da ita.
Ko zama beyiba suka gaisa da anty zarah din ya juya ya fice
sbd mum dinsa daketa qwalo Masa Kira.
Fes ta sakewarta Takoma Amatun ta me rayuwarta cikin Raha da
Jin Dadi,
Duk wani Abu ko inda tasan zata hadu da MD ZABEERA ta
tosheta gaba daya data fahimci lokacin dawowarsa yayi take komawa daki takira
Dr ko USI ko Salman suyita firarsu cikin nishadi.
Kulawa kuwa da qaunar da anty zarah take Mata sai ninkuwa
sukeyi sbd yanzu kwata kwata ta daina cire cikon datakeyi sbd umarnin Dr khalil
ne Dan shima yanzu so yakeyi daya dawo Susan dubarar Yi maganar cikin Nan
yaqare su fuskanci reality itakuma anty zarah data qwallafawa cikin Rai har MD
ZABEERA yiwa zancen takeyi idan tasamu fuska sai hakan yafara basa tunanin Dole
daman Suma wata ran suyi sha'awar samun 'da ko 'ya.
Sannu ahankali sabo da shaquwarta da Dr Salman yayi qarfi
Dan shima saitakejinsa kamar usi da baya kusa duk wani gurbi na 'dan uwa me
kulawa ya cike matashi Dan dukkanin
shawararta da sirrinta dashi takeyi ta yanda shima baya boye Mata komai
sai suka zama tamkar wasu best friends kokuma Yan uwan dasukafi kusanci da
kowa.
A bangare daya Kuma yanzu su umme sun Dakota gaba itada Haj
maryam sbd ganin dukkanin yayansu sun qare
da rawar qafa agunta sai suka sanyota gaba ba itaba ba anty zarah ba tun
abin baya damunsu harya Fara damunsu zancen yajewa ummah mahaifiyar anty zarah
tazo tayi musu mgn sai abin yazama fitina akayi tashin hankali tun abin na
dagasu sai yayi tsanani akai kusan qaramin yaqi a familyn Wanda yasa akayi taro
na musamman Amma duk da haka sai abin yaqara jawowa Amatu baqin jini sbd ganin
kamar itace takawo fitina cikin familyn ZABEERA sai aka Fara camfata ga nuratu
data sanyota gaba sosai tafara bincike a kanta sbd gano haqiqanin gaskia Dan
bazata taba Bari Dr khalil ya auri wata banzar karuwa ba yabarta.
Zuwa yanzu satin Dr khalil uku cikin na hudu da tafiya suna
saka ran dawowarsa gobe shiyasa take cikin farin cikin data kwana biyu batayiba
sbd tashin hankali sbd wannan fitinar da akayi yasa Andi saka doka me tsanani
akanta akan kullum taje ta gaida uwar mijinta Wanda duk taje da bacin Rai take dawowa.
Blue fox sukaje akayo musu gyaran Kai da qafafu akaiwa
Amatun Jan lalle a hannuwa
Basu bar gurinba sai yamma sosai sukayo gida Salman ne ma ya
daukosu suna yin parking motar MD ZABEERA nayin parking akusa dasu ita tafara
juyowa daidai shima ya juyo idanuwansa suka sarqe cikin na juna
##mamuh#

No comments