MIN QALB 22
*_MQ 22_*
*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN
JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*
*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*
*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida
tsohuwa yarinya*
*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata
ta daban cikin mata*💆🏾♀️🙎🏽♀️
*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki
gami da tada duk wata komaɗa ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯🏽♀️👯🏽♀️
*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*
*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM
http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*
*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*
*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR
WAYAR 08169380189_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*🤞🏾🤞🏾🤞🏾🤞🏾
************
Cikin kulawa yake tambayarta ya jikin nata itama cikin
kulawar take amsawa tanason fada Masa komai na Abinda yafaru tun zuwansu
asibiti tanajin nauyin anty zarah
Ganin hakan yasa anty zarah miqewa tayi toilet Dan taimakawa
ta hada Mata ruwan wanka tana hamdalar cikin dayake lafiya kalau Babu Abinda ya
samesa.
Tun tanayin wayar a zaune harta Dan jingina da Kan gadon
tana rufe idanuwanta tana sauraran abubuwan da Dr ke fada Mata tana murmushi
sbd sbd girmqn mahimmancinta a rayuwarsa yake fada Mata Yana Mata fadan ta rage
ciye ciyen kayan shiririta.
Ganin ba gamawa zasuyiba yasa anty zarah karbe wayar tareda
kashewa Tana cewa''
Tashi kije kiyo wanka yanda jikinki zai qara warwarewa,
Miqewa tayi tana murmushi har lokacin ta cire kayanta tareda
daura towel ta fada toilet din.
Ahankali take wanka tana tunanin Rabin ran Anty zarah ta
yanda zai iya wanke jinin daba na matarsa ba,
A yanda yakeda tsafta da Shan qamshin Nan Bata tunanin zai
iya taba rigar bare ya wanke da kansa,
Duk yanda za'ayi ita zata karbo rigar ta wanke da kanta
tunda jinin natane koba komai abin kunya ne gareta wani ya taba jinin al'adarta
Wanda ba mijintaba.
Kodata fito wanka anty zarah na dakin tana sauke abincin da
hafsatu tashigo dashi Wanda akayi domin Amatun kawai.
Tasamu qarfin jiki matuqa sosai datayi wankan shiyasa cikin
walwala ta shirya bayan tafara shafa Mai kadan ta sanya doguwar riga me Fadi
sbd ganin anty zarah nata kallon cikinta cikin kulawa itadai lafiyar cikin ce a
gabanta.
Zama tayi suka hau breakfast tareda anty zarah din suna 'dan
taba firar Dr daya damu da haryana cewa zai dawo yau daqyar ta hanasa.
Suna gamawa ta hau gadonta ta mimmiqe Anty zarah takira
hafsatu tana Mata tausa ahankali ahankali har bacci ya dauketa sai alokacin
Anty zarah tasaki ajiyar zuciya tareda miqewa tabar dakin.
Dakinta tafara zuwa ta sauya kayan jikinta tareda qara
shafawa jikinta body mist ta fito tana gyara zaman qaramin qyalen dake daure
akanta Wanda yaqarawa kyakkyawar fuskarta kyau ta nufi dakin mijinta.
So daya tayi knocking tareda bude qofar bedroom dinsa
tashiga bakinta daukeda sallama Mai sanyi.
Tsaye yake gaban mirror daureda brown towel iya qugunsa Yana
shafawa jikinsa spray din Hugo boss fuskarsa a fuske kamar dai koyaushe.
Kallon budadden bayansa tayi dayake fari tas Babu tambon sai
qyalli yakeyi kamar na mace har zuwa wuyansa da faffadan qirjinsa datake gani
ta jikin mudubi Wanda tuni yaji ajikinsa shi take kallo saiya juyo ahankali
yayi Mata kallo daya yaga yanda take kallonsa cikeda so da qaunarsa saiyaji
zuciyarsa ta danyi sanyi sbd yasan zarah mace ce me tsananin hakuri da juriya
Wanda yasa yake matuqar respecting dinta akan hakan,.
Gabanta ya qaraso ahankali ya tsaya Yana kallon fuskarta
itama shi take kallo tana jin sabuwar soyayyarsa na shigarta ahankali ta matsa
ta shige jikinsa tareda zura hannuwanta bayansa ta rungumesa ahankali tana
kwantarda kanta akan qirjinsa tareda lumshe ido tana sauke boyayyar ajiya
zuciya.
Sai daya jima shiru Yana sauraran bugun zuciyarta dake dukan
qirjinsa kafin ya daga hannuwansa ya rungumeta ahankali tareda lumshe ido ya
sauke numfashi,
Sun dauki kusan mintuna biyar ahaka shiru Babu me
motsi kafin ahankali ya dagota daga jikinsa ya dauketa gaba dayanta ya nufi
gadonsa da ita Yana kallon fuskarta data soke cikin qirjinsa,
Yana kwantar da ita Kan gadon yayi Mata rumfa da fadadden
qirjinsa Yana Kai hannu Kan zib din gaban jallabiyarta.
Bayan wasu lokuta haryayi sabon wanka ya fito ita alokacin
take qoqarin saukowa daga gadon tayi saurin daukar fadawa toilet din nasa duk
da shi mutum ne dabai cikason wani na amfani da toilet dinsaba Amma kasancewar
yanzu Basu kadai bane Dole bazata iya fita ahakaba kamar da wani zai iya
ganinta.
Wanka tayo tafito lokacin harya shirya cikin farin filtex
transparent da hular qube coffee brown Yana fesawa jikinsa turarensa na
IMPERIAL MAJESTY.
Kayanta ta maida bayan tagama goge jikinta ta shafa oil
kadan tareda turarensa.
Sai alokacin ta tunoda Abinda yakawota ta kallesa Yana
qoqarin daukar wayarsa dake Kan bedside cikin taushin murya tace"
Am...amm dama rigar dazu ta jikinka nace ko zaka kawo na
bayar a wanke sbd Naga ta samu lalacewa....
Cak ya tsaya daga Abinda yayi niyar Yi hakanan yaji maganar
Tata kamar ta ciza ransa,
Idan tunaninsa na aiki daidai yasan me wankin zarah din
namiji ne Wanda kusan duka familyn shike yiwa wasu da yawa daga ciki wanki,
Tana nufin shi gardin zata bawa jinin dayake sirrin Amatune
ga wani gardin ya wanke???
sake 'dan tamke fuska yayi tareda juyowa ahankali kamar zai
kalleta saiya fasa ya juya ya dauka wayarsa batareda yabata amsaba yafara
qoqarin barin dakin.
Saurin biyosa tayi tana cewa''
Nace bakajiba rigarka ta yau da safe nakeso kabani zanbawa
wa....
Kallon daya dago yayi Mata yasata matsawa baya kadan tana
sauke Kai zuciyarta na bugawa da sauri.
Kamar zai wuce baiyi Magana ba saikuma ya tsaya batareda ya
juyo ya kalletaba cikin sautinsa me daukan hankali yace"
Karki sake kawo maganan riga da Abinda yasamu riga agabana
ok????
Kallonsa tayi tana son sake maganar Amma ganin yanayinsa na
Babu Wasa ko sakin fuskarsa yasa ta 'daga Masa Kai tana cewa''
Adawo lfy.
Can qasan maqoshinsa yace"
Thank you"tareda wucewa ya sauko qasa tareda ficewa
zuwa office.
##Mamuh#
Gashinan please yauma kuyi manage gobe Inshallah zamu koma
pages dinmu masu tsawo yauma uzurine ya riqeni kuyi hkr da wannan din🙏🙏🙏

No comments