MIN QALB 20
MQ 20_*
*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN
JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*
*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*
*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida
tsohuwa yarinya*
*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata
ta daban cikin mata*💆🏾♀️🙎🏽♀️
*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki
gami da tada duk wata komaɗa ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯🏽♀️👯🏽♀️
*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*
*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM
http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*
*ko kai tsaye ta WATSAPP
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*
*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR
WAYAR 08169380189_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*🤞🏾🤞🏾🤞🏾🤞🏾
*************
Jin mutum ta bayansu a tsaye yasa anty zarah Dan dagowa tana
qoqarin juyawa Amatu tasaki wani sabon ihu dayasata dawo da kallonta Kan Salman
cikin damuwa da tausayin Amatun tace"
Salman please ka danyi Mata ahankali kodan juna biyun
jikinta.....
Daga salman din har MD cak tunanin kowannensu ya tsaya da
maganar da Zarah din tafada,
Zame hannunsa yayi da sauri tareda barin gurin kansa na Dan
sarawa sbd ihunta daya cika part din gaba daya,
Yana fita qofar gym dinsa dake maqale data shigowa palonsu
yashiga Yana qoqarin clearing mind dinsa da cewa''
Khalil wane irin shirme kasani aciki¿¿
Matarka ce and she's pregnant....
MAHMOUD just stay out of this.
Geamin din dayazo Yi yafara Yana komawa asalin MD ZABEERA
dinsa.
Salman kuwa shiru yayi Yana nazarin kalmar a cikin kansa duk
da dai ba yanzu ne yasani ba tun kafin yadawo Nuratu ta sanar dashi komai
Kawai abin rudewar anan shine shedan dake saka Masa wasi
wasin hakan sbd Amatun data shiga kansa hakan kawai yake jin bazai Bari Nuratu
ta cutatar da itaba Koda Bata ciki,
Abu daya daya sake tsaya Masa arai shine Sam idanuwansa da
iliminsa na likitanci duk da bana mata ba sun kasa gasgatar Masa da akwai ciki
a jikin Amatun.
Kallon fuskarta yayi ahankali yasaki murmushi ganin hawaye
shabe shabe a fuskarsu su duka ukun,ita da usi harda anty zarah din ma.
Handkerchief dinsa dayake daukeda tambarin asibitinsa da
sunansa ajiki yaciro daga aljihunansa ya miqawa usi yace"
Usman share Mata hawayenta.
Daqyar da fitina da koke koke ta ihu da komai aka dubata
yasa Usman yaje motarsa ya dauko wasu magunguna da allurai yayi Mata da kansa
yabata maganin Yana Mata sannu tareda tsokar yanda idanuwanta suka kumbura sbd
kukan raki.
Saidata ci abinci da sauran maganin yaga anty zarah takaita
daki ta kwanta tafito tace Masa tayi bacci kafin yatashi suka fito tareda usi
dakejin kamar karya tafi yabarta ta bangare daya Kuma kallon koina yakeyi Yana
jaddada daula da dukiya irinta wannan ahalin zabeera.
Sashen Salman din suka nufa cikin motarsa sbd kowane sashe
zuwa sashen akwai 'yar tafiya shiyasa duka yawancinsu da motacinsu suke zuwa
sashen juna sai dai idan kaso motsa jiki kaje da qafa.
A palon Salman din suka zauna Nan USI yaqara ware Ido Yana
kalle kalle badan yayiwa Dr khalil alqawarin bashi ba abin wani har abada ba da
yau Allah ne kadai yasan abubuwan dazai sanfe daga cikin zabeera dinnan Dan tun
a part dinsu anty zarah yaga abubuwan dauka Amma hakanan ya hadiye ya dauke Kai
sbd karya kunyatar da Dr khalil.
Abinci lafiyayye aka aiko daga part din mahaifiyarsa Haj
Maryam aka jera Masa a dining suka zauna ci shida usi dasukai sabo cikin
qanqanin lokaci sbd gano tsananin qauna da kulawa dake tsakaninsu shida Yar
uwarsa Amatu.
USI na Ido biyu da kayan Dadin dake jere a dining din take
yaji hakurinsa na Kama mutuncin Kai ya qare take ya washe baki Yana cewa''
Allah ya taimakeni saura kadan yau nadauki azumin alhamis da
Dr ya doramu akai nidasu kawu
Kawuma yau dayaji Dr yayi tafiya wlh win dauka yayi yace mu
huta kwana biyu kafin Dr din yadawo sbd duk litinin da alhamis taredamu
yakeshan ruwa acan gida.
Dariya sosai Salman yayi Yana sakejin Usin na burgesa sbd
baya boye boye yace"
Kace yau dai akwai ciye ciye sai ciki yakasa dauka.
Lumshe ido USI yayi bayan yazuba kakkauran soyayyan kwai
cikin bakinsa dayaji kayan qamshi da albasa take yasaki murmushi Yana sakawa Dr
khalil da adduar samun nasara a rayuwa Dan komai suke samu a rayuwa sbd shine
Yagama Basu duk wani Abu da suka kasa samu a rayuwarsu ta
kadaici, talauci,garari da rashin sanin daraja.
Sosai salman yaji tausayi da qaunarsu tareda son samun Lada
da adduar da Dr khalil ke samu daga garesu sbd kyautatawa da kulawar dayake
Basu amatsayinsu na wainda basuda shi,
A iya firar da yayi da USI ya fahimci su din talakawane masu
tsananin buqatar taimako Wanda yasa Dr Khalil shigowa rayuwarsu ya taimakesu
har suke ganinsa a Wanda yafi musu kowa da komai,
Idan baiyi kuskuren tunaninba yanasa ran sbd tallafawa
rayuwarsune yasa ya auri Amatun batareda sanin iyayensu ba,
To Amma Kuma a yanda labari yazo a zuwan Amatu zabeera ance
batada mahaifi ita din marainiyace,
To shi kawu waye tunda ba'a ce sunada kawun ba a takaice
cewa akayi basuda kowa,
Gashi yanzu yanatajin sunan kawu a bakunansu,
Da akwai inda wani Abu ya maqale to,
Akwai Abinda dagasu sai Dr ne suka San abinsu koma dai
menene yasan Dr khalil ya boye ne sbd wani dalili me kyau.
To gashi shima Amatu da USI sunshiga ransa alokaci daya,
Yaji yanason kasancewa acikin farin ciki da walwalar da
Amatu da ahalinta zasu samu.
Bayan sun Gama cin abinci shigewa yayi ya kwanta yabar USI
yanata faman kallon wani action film Yana cin wani lafiyyan dabino me laushi
daya Gama daukan sanyi a fridge.
Sai azabar salman din yatashi bacci zuwa lokacin shima usi
ya Dan miqe a kujera yayi baccinsa sanyin AC na hudasa hankali kwance.
Tayar dashi salman yayi tareda nuna Masa dayan bedroom dinsa
yace yaje yayi wanka zai kawo Masa Kaya.
Dakinsa yakoma ya hadowa usi din manyan kayansa designers
masu kyau da tsada kusan kala shida da takalma na alfarma da agogai ya hado
Masa tareda wata qaramar akwati yasa aciki yakawo Masa
saiga usi yayi wanka ya shirya tsaf cikin qananan kayan
dasuka fiddo da ma'anarsa da kyawun dayake dashi shima hardasu feso turaren da
duk ya shaqa a jikinsa saiya saki murmushi abinsa Yana sake godewa Salman da
yiwa Dr khalil addua.
Dasuka fito Saida suka koma yasake dubo Amatu zuwa lokacin
har ta tashi bacci itama tayi wanka taci abinci tasha magani tana zaune Palo
anty zarah na gefenta tana miqo Mata yam balls datasa akai Mata tana ci tana
tunanin Dr Khalil da har lokacin basuyi Magana ba.
Kwankwasa qofa akayi hafsatu tazo daga kicin tabude suka
shigo suna yar fira kamar wainda sukai shekaru atare duk da Dr salman ne me jan
usi din da firar sbd yasake sosai dashi Dan dama can shi Dr Salman yanada
Magana sosai da son raha da Wasa.
Tunda taga USI da kayan dake jikinsa ta sake baki tana
kallonsa cikeda mamaki tana cewa''
Usi a Ina ka......
Da sauri yace"
Dr Salman ne ya......
Katsesa shima Salman din yayi da cewa"
Wai Kai itace yayarka ko Kaine yayanta da kake Jin shakkarta
ne.,
Sosai Kai usi yayi Yana murmushi yace"
Dr bakasan Amatu bane da zafin Rai yanzu Nan saitace zata
fasamin Kai ko baki.
Dariya Dr da anty zarah suka sake
Anty zarah tace"
To lallai Nima naji tace zata fasa maka Kai da baki yafi so
goma Amma bantaba ganin anyi ba.
Kallon Amatun usi yayi Yana cewa'
Anty zarah dafa tanayi yanxune anan batama ganni ba bare
tayi
Amma ada tsaf zata saka wata Jakarta me kama data wanzamai
ta kwadamin akai ko baki
Jakar Nan yanda kikasan da qarfe akayita tsabar qarfi.
Dariya duk su duka suka sake sosai hadda hafsatu dake jera
abincin Rana a dining
Itama Amatu dariyar tayi tana cewa''
Usi tashi kabar Nan kafin na fasa maka baki wlh...
Kinji ko anty zarah tasake fada
Ai a yini tana cewa zata fasa bakina da kaina yafi so
ashirin
Kawu ne duk ta fada sai yayi sadakar ruwa wa qadangaru su
Sha Wai yana fidda Mata baki kada fada Babu cikawa ya fado Mata.
Filon kujerar datake ta dauka ta jefa Masa da qarfi tana
cewa''
Kamar anyi a kunnen kawu
Kuma Allah saina fadawa Dr yau bakayi azumi ba dan Banga
alamarsa atare dakaiba yanda nasanka kamar mace da mugun Jin azumi.
Kallonta yayi da sauri kafin ya kalli Dr Salman yana Dan
nutsuwa yace"
Idan Kika fada Masa to kisani banine kawai banyiba
Kawuma ya ajiye yace wlh saiya huta.
Zaro Ido tayi itada anty zarah tace"
Kawu ma ya ajiye?
Eh Mana iyami ce kawai ta dauka abinta sai kwadayayyun gidan
dasuka Saba duk akayi ana raba musu abubuwan abinci basusan yayi tafiya ba
sunacan duk sun dauka.
Shiru Amatu tayi tana sakin murmushi kewa da tsananin qaunar
Dr khalil da girmansa na sake cikata sbd ya kawowa gidansu rayuwa me inganci da
samun tsira,
Duk litinin da alhamis yakeyin azumi harya koyawa su kawu
Suma sauran Yan gidan tuni suka dauka sbd duk litinin da
alhamis din Yana kawo kayan abinci a raba gidan Dan Shan ruwa Wanda wasu suna
musu kwana biyu Basu qareba,
Da farko sbd samun kayan dayake kawowa suke azumin Amma
yanzu kusan dukkaninsu abin yafara zama jikinsu Kuma kowannensu yasha ruwa
takanas sukewa Dr khalil adduarsa ta daban sbd yakawo sauyi da walwala a rahuwarsu
gidan gaba daya.
Anty zarah ma cikin jinjinawa Dr khalil tace"
Allah ya biyawa dr buqatocinsa na alkhairi sbd wannnan aikin
ladar dayayi.
Amin Amatu tace tana kallon Dr Salman dashima yaji yana sake
ganin girman Dr khalil zabeera tareda yiwa kansa kwadayin Lada da kyautawa su
Amatun.
Anan sukaci abincin Rana taredasu Amatu kafin suka fito suka
wuce Salman zai maida usi gida.
Bayan tafiyarsu cikin kulawa anty zarah tace"
Nagode Amatu.
Juyowa Amatu tayi ta kalleta cikin rashin fahimta tace"
Anty zarah me akayi?
Murmushi tayi tana kallon Amatun gaba daya tace"
Amatu kinkawo dariya da walwala acikin rayuwar kadaicin Dana
samu kaina acikin gidan nan,
Tsawon shekarun aurena Banda ranar Dana taba zaunawa acikin
gidan nayi fira nayi dariya harda qyaqyatawa saida Kika shigo cikinsa,
Banda abokin fira,abokin nishadi acikin gidana,
Maimakon nakawo sauyi da walwala acikin gidan Nan da rayuwar
MD sai Nima kadaici da rashin walwala da rashin farin ciki suka aureni sai
gidan yaqarasa zama cikin duhun dayake ciki tuntuni.,
Amma zuwanki amatu yakawo walwala da annushuwa acikin gidan
Nan Wanda ko hafsatu datake amatsayin me aiki na hango walwala atareda ita
bayan zuwanki cikinmu
Shiyasa nake Miki godiya sbd ko ahaka kin shayar damu yanda
walwala da nishadi sukeda Dadi a rayuwa.
Murmushi tasaki tana gyara zama tace"
Anty zarah banbaki kwatan Abinda kikamin arayuba,
Kin qaunaceni a yanda nake Kika Kuma karbeni hannu biyu
bayan kingama sanin waceceni,
Kinbani matsayin qanwa kamar ta jini bayan baki hada komai
Dani wannan shine babbar kyautar Dana samu a rayuwata ta samunki keda Dr
khalil,
Dr khalil shi yariga yazama wani jigo atare Dani da bazan
iya Babu Shiba Wanda nake fatar dagake harshi mutuwace kawai zata rabamu,
Farin ciki Kuma Babu Wanda yake bawa wani farin ciki a
rayuwa sai Allah saikuma Kai da kanka idan ka ture komai ka bawa kanka
mahimmanci,
Anty zarah kece da kanki zaki kawo walwala da sauyi a gidan
aurenki idan kinso,
Bansan meye zaman aureba tunda banzauna da Dr ba saidai ni
nawa tunanin daga lokacinda Kika auri mutum to duk mulkinsa da dukiyarsa da
muqaminsa da duk wani Jin kansa to fa anzama daya
Idan bai aje Dan kansa ba ke zaki aje masa,
Anty zarah kinsa tsoro da shakkun mijinki fiyeda sonsa
acikin ranki Wanda shike sa kiga an tsufa da jikoki da 'yaya da komai saikiga
mace mijinta na Mata fada ko dixgawa a gabansu Wanda ita ta daukar Masa hakan
tun anada kuriciyar aurensu.,
Mijinki mijinkine baida wani suna bayan wannan hakama kema
bakida wani suna bayan na matarsa ko bayaso Dan haka anty zarah ki aje tsoro da
shakka ki gyara rayuwar aurenki sbd bazan zauna Nan dakuba dazanta kawo dariya
a fuskarki kece zaki kawo dariya a fuskarki data mijinki,
Dan haka Dan Allah anty zarah ki gyara sbd kada lokaci ya
qure Miki.
Zugum tayi tana sauraren Abinda Amatun ke fada tanajin kamar
da wuya al'amarin.
Murmushi Amatu ta sake tana cewa''
Anty zarah tunanin me kikeyi?
Miqewa tayi tana cewa''
Sam ni Banga abin tsoro ko shakku ba agun Rabin ranki
a takaice ma ni tsaf zan gyare Miki zamansa matsalar da aka samu itace ni ko
qamshinsa na jiyo gabana faduwa yakeyi sai naji zuciyata tana bugawa da sauri
kamar zata fito daga qirgina,
Idan na kalli fuskarsa kuwa rasa nutsuwata nakeyi,
Bansan meyasaba shikadaine nakejin hakan akansa,
Shi kadaine bana iya yiwa fuskarsa kallo biyu sbd dukan da
zuciyata takeyi,
Meyasa idan.........
AMATULLAH"""yakira sunanta gaba daya batareda
yasan yayi hakan ba sbd zantukanta dake juya kansa da tunaninsa....
Juyowa sukayi su duka hadda anty zarah datai qaramin suman
zaune Jin abubuwan da Amatu ke fada akan MD Wanda idan shedan ya Rudi
fahimtarta to zata ce ne wannan so ne me zafi.....
Saurin girgiza kanta tayi tana Dan bugawa tace"
Tunani ne
Amatu matar Dan uwan MD ce
Tanama daukeda cikinsa
Bazata taba son wani ba bayan Dr khalil bare Dan uwansa
MAHMOUD tunanin banxana ne kawai.
Ganin Dr Salman ne yakira sunanta yasa anty zarah sakin
ajiyar zuciya a boye
Ita Kuma Amatun murmushi ta sakar Masa tana cewa''
Harka dawo¿
Gabaki daya kansa juyawa yakeyi Wanda hakan har akan fuskarsa
ya nuna confusion sai kawai ya miqa Mata ledar hannunsa daya siyo Mata
tarikicen kayan chocolates dasu cookies ya juya baice ko kala ba.
Yana fita Saida ya zauna cikin motarsa ya yamutsa kansa Yana
cewa''
Amatu MD ZABEERA takeso bayan tana matsayin matar khalil
zabeera kokuwa kansa ne bai fahimci yanda abin yakeba????
Kasa yadda yayi yaja motarsa yana qoqarin yakice tunanin
dama duk Abinda kunnuwansa sukajiyo Masa.
Bayan fitarsa kuwa cikin farin cikin abubuwan daya kawo Mata
din tazauna gefen anty zarah suna bubbudewa suna cin wasu suna dauko wata firar
tasu maman junior tana bawa anty zarah din labari suna dariya hankalinsu
kwance.
Sasai Tasha chocolates din Wanda har Saida anty zarah tace
ta daina sbd ciwon Mara Amma haka ta share tunda tasan ba wani ciki ajikinta
sasha kayan zakinta harsai dataji cikinta kamar zai Yi ciwo ta aje sauran cikin
fridge.
Da daddare tana qoqarin zama bayan futowarta daga wanka ta
shirya cikin riga da wando na bacci masu Dan akuri ta saka wularsu sai qamshin
turaren Dr khalil takeyi Wanda yabata datace tanason qamshinsa saiga kiransa
yashiga saidatai wani wuntsilawa sbd farin cikin ganin kiransa sbd dazu yakira
da numbernsa tacan tayi saving.
Tana dauka tafara zuba Masa qirafin da batai Masa dazu ba
sbd gaban anty zarah ne tace"
Nifa ban daina fushiba katafi kabarni zabeera ni kadai.
Murmushi me sauri yayi Yana qara Jin sonta har cikin ransa a
natse yace"
Baga zarah Nan ba.
Shiru tayi kafin ahankali tace"
A cikin zabeera da wajenta a yanzu Babu inda nakejina cikin
tsaro da kulawa idan har bakanan,
Dr kariga ka koyar Dani Jin rashin tsaro idan baka kusa Dan
Allah kadawo da wuri tsoro da fargaba nakeji idan baka kusa.
Nutsuwa maganarta ta qara Masa yaji sanyi Yana qara samun
nutsuwa yace Mata"
Inshallah Amatu idan Ina Nan kina cikin tsarona Babu Abinda
zanbari yasameki sai qaddara.
Nasani Dr""""tafada tana Dan yamutsa
fuska sbd mararta data Fara murdawa gashi dama ita qa'idane duk wata saitayita
baqar wahala idan zatayi period,
Tunda tazo zabeera Dr khalil sbd cikin da akace tanadashi
Yana gano tana ciwon period yake kaita asibiti duk wata tana ganin Dr Fatima
ana Yan dubaru har tagama period din tukuna.
Fira sukeyi tana daddaurewa ahankali sbd ciwon marar gadan
gadan yakeson taso Mata sai alokacin tagane Abinda anty zarah ke nufi data
daina cin zaqi.
Jin kamar tanajin bacci yasa yayi Mata addua kamar yanda ya
Saba duk dare kafin ya kashe wayar saidai hakanan yakejin kamar ba lafiya
takeba.
Lallabawa tayi ta kwanta tana juye juye hardai abin yataso
Mata sosai Nan tafara hawaye tana Kiran sunan Allah.
Bayan kusan awa biyu da Gama wayarsu ya yakasa samun nutsuwa
ya kalli agogo yaga yanzu su can a Nigerian dare yayi sosai sai ya janyo
wayarsa yashiga massage yayiwa zarah text yasan tana tareda MD Amma dai idan har
tagani zataje ta dubo Amatu tagano masa.
Anty zarah na dakinta yau bataje dakinsaba sbd yanda yadawo
tasan a gajiye yake bazaiso a takurasaba shiyasa tayi kwanciyarta dakinta
tanata juye juye cikin tunanin daukar shawarar Amatu Amma tanajin shakku,
Saiga massage dinsa yashigo tana karantawa ta miqe sanyeda
kayan baccinta riga da wando irin na Amatun sak ta nufi dakin da sauri.
Salati tasaki me qarfi tana Shiga dakin cikin tashin hankali
tayi kanta ganin tanata juye juye riqeda ciki tana wani irin numfashi da kukan
azaba.
A rude takira Dr tana fada Masa cikin tashin hankali yake
dama daya duba yaga yaune date din period dinta da sauri yace"
Kira umme Dan Allah ta taimaka Mata takira Mata Dr
Fatima.
Umme Kuma"""
Anty zarah tafada cikin mamaki sbd sanin kowa yasan umme
Bata qaunar Amatu da Abinda yake cikinta.
Shikuma sanin umme ce kawai tasan Amatu batada ciki yasa
yace aje gurinta sbd yasandai bazata tonaba yanzu.
Eh Zarah Kira umme Dan Allah Yi sauri.
Jiki na rawa ta Danna Kiran numbrn umme Saida tayita ringin
kusan Kira biyar sai ana shida ta daga cikin bacci.
Umme zarah ce
Gamunan Amatu batajin Dadi zaki Kira Mana Dr Fatima ne Wai.
Wani qaton ashar ummen ta gundumo tana cewa''
Uban Dr Fatima zankira muku,
Zarah Kika sake kirana cikin Daren Nan saina mugun Bata miki
wlh.
Kallon wayar da ummen ta kashe Mata tayi cikin mamaki da
tsoron Ina mafita gashi idanba idonta yayi Mata qaryaba saitaga kamar jini a
jikin dogon wandon Amatu din.
Wani razanannen qaramin ihu tasaki tareda jefar da wayarta
tana fitowa da gudu tayi sama dakin MAHMOUD cikin sa'a Yana zaune yana aiki a
laptop da cikin tashin hankali da rudewa tace"
Amatu ce ba lafiya kamarma jini cikinta zai lalace.....
Cak ya tsaya tareda dagowa ya kalleta ta daga Kai cikin
rudewa tana kasa Magana.
Kallon agogo yayi batareda ya motsa yaga dare be
Zata sake Magana ya aje laptop din gefe tareda miqewa ya
zura jallabiya Fara qal Kan singlets da short dake jikinsa ya dauki keys ya
sauko zarah din na bayansa.
Kamar bazai Shiga dakinba saikuma ya Shiga daidai tayi wani
juyin azaba zata fado qasan gado ya tareta da hannunwansa biyu
Unfortunately sai idanuwansa suka sauka kan stain din jinin
dake jikinta
Ya rintse ido da sauri tareda dauke Kai Yana shawarar
daukanta saikuma ganin halinda take ciki yasashi daukarta cak gaba daya yafito
Yana cewa''
Zarah ki Kira zamu dawo zuwa da safe.
##mamuh#

No comments