MIN QALB 19
*_MQ 19_*
*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN
JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*
*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*
*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida
tsohuwa yarinya*
*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata
ta daban cikin mata*💆🏾♀️🙎🏽♀️
*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki
gami da tada duk wata komaɗa ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯🏽♀️👯🏽♀️
*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*
*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM
http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*
*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*
*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR
WAYAR 08169380189_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*🤞🏾🤞🏾🤞🏾🤞🏾
**********
Doguwar tafiya tayi har zuwa sashensu tana Jin tsananin
azabar radadin da hannunta keyi ta daure ta iso tana rintse ido cikin uwar
azaba ga zufa sai karyo Mata yake shiyasa tana isowa tun a Palo ta zube Kan
kujera tana kallon hannun da harya Fara kumbura
Sanin anty zarah na dayar palon tareda baquwarta yasa ta
sulala tayi dakinta ta kwanta Dan kada ta dagawa anty zarah din hankali saidai
ita kadai tasan uwar azabar datake ciki shiyasama takira usi
Yana daga wayar sai alokacin taji hawaye sun ciko idanuwanta
sai Kuma takasa mgn ta kashe wayar ta ajiye tana gani yanata Kira takasa dauka
sbd karta daga Masa hankali kawai.
Duk yanda take tunanin zata iya riqe ciwon takasa sbd
sosaine tasamu gocewar qashin hannun sai kumbura yakeyi har takai tafara kasa
motsasa sbd tsamin daya dauko.
Har dare tana dakin Taki fitowa sai bayan magrib baquwar
anty zarah ta tafi
Itama anty zaran dakinta ta nufa sai datayi sallar magrib da
ishai tukuna ta fito palon saidai rashin ganin amatu a palon yasa ko zama
batayiba ta nufi dakinta.
A kwance ta taddata Idanuwanta a rufe tanajin anty zarah din
ta tashi zaune tana rintse ido alamar ciwo
Nan anty zarah din ta qarasa bakin gadon da sauri tana dafa
Hannun me azabar Bata saniba
Wani irin zabura Amatu tayi cikin tsananin radadin dataji
tana tana cewa''
Anty hannuna ya karye.
Da sauri anty zarah ta kalli hannun batasan lokacin data
zaro ido ba ganin ya kumbure sul a rude tace"
Amatu meye wannan nake gani?
Garin Yaya hakan yasame ki??
Sai alokacin hawayenta suka gangaro tace"
Anty wannan me son Dr din ce ta tureni na Fadi a hannun.....
Mene??""anty zarah tafada da qarfi tana maida
kallonta Kan cikin Amatun da har lokacin Bata cire cikonba tace"
Ta ture ki batada hankaline bataga Abinda ke jikinki bane ko
so hauka ne Bari nakira Dr yanxun Nan yazo
Ita Kuma Nuratun I will deal with her later wannan ai
ganganci ne.
Dr najin Abinda yafaru hankalinsa ya tashi gashi wani
mahimmin meeting sukeyi sbd gobe shida wasu manyan likitocin asibitinsu zasuyi
tafiya zuwa china gurin wani program na sati biyu.
Tunda zarah takirasa tafada Masa hankalinsa ya rabu biyu
Meeting din kawai suke Amma Rabin hankalinsa na gidan sanyi
daya dayakeji aransa shine SALMAN yananan yadawo kwararren likitan qashi ne
yasan basa buqatar zuwa koina.
Sai guraren 8:40 suka fito gashi Kuma yanada wani Wanda
yayiwa alqawarin ganinsa idan yafito hakanan yakoma office dinsa
Koda ya Isa office din mutumin na kiransa Nan suka Fara
mgnar dazasuyi ahankali yanayi Yana shafa qirjinsa da numfashinsa ke Dan
sauyawa tun safe yakejin hakan Kuma yasan alamace ta ciwonsa zai iya tashi ko wane
lokaci Amma meeting din yasa baisamu damar amfani da inhaler gashi idan yataso
duka Dole saidai oxygen Wanda duk lokacinda aka saka Masa oxygen rayuwarsa tana
cikin mugun hadari ne sbd oxygen din nabawa lungs dinsa matsala sbd dama can
basuda qarfi lungs din tun haihuwarsa shiyasa shida likitocinsa sunriga sunkai
qarshe akan karya taba Bari ciwonsa natashi gaba daya harya tafi qarfin inhaler
ta riqesa.
Qoqarin Kama numfashinsa dake son qwace Masa yakeyi Yana
dagawa mutumin Kai sbd Magana tafara son gabatarda ya dago daqyar ya kallesa
Yana dannewa yace Masa yaje zai nemesa idan yadawo daga tafiya zasuyi Magana.
Mutumin na fita ya dafe qirjinsa cikin tsananin azabar
rashin fitar numfashi idanuwansa sunyi jajir jijiyoyin kansa sunfito sosai
Hannunsa na rawa ya jawo drawer office din nasa ya Fara
laluba baiji inhaler dinsa ba,
Firfito da duka kayan ciki yayi Yana watsowa cikin sauri da
tsananin azabar dayake ciki baiganta ba gashi yafara loosing control din kansa
sbd idanuwansa sun Fara gani dishi dishi
Da sauri ya miqe ya dauki wayarsa da keys din motarsa ya
fito Yana riqeda kurkinsa ya nufi motarsa ya fada Yana tayarwa yafito asibiti
saidai abin yaci qarfinsa gaba daya zuwa lokacin sbd numfashinsa daya dawo gaba
daya bakinsa tuni motar tafara qwace Masa.
Daga government house yafito daga wani guntun meeting dayayi
da deputy governor akan investing dasuke sonyi a sabon ZABEERA LTD dinsa dake
Bangkok,
Shida malam Umar ne a motar shike tukasa
Gaba daya hankalinsa nakan wayarsa dayake duba tarin
misscalls din da akaita Masa Wanda duk yawanci daga mutanen hurdarsa ne sai sauran daga family
wainda yasan dukansu bazai wuce buqatar kudi daga garesaba Wanda Sam shi ko
mamakinsu baida lokacin tsayawa yayi
Misscal din zarah guda hudu ne ya kalla numbernta dayayi
saving da ZB wato zarah zabeera,
Sam Bata gajiya da Kira ita duk da tasan bako yaushe yake
dagawa Amma Sam taqi sabawa da hakan
Wasu mutanen suke aikata Abinda zai 6ata ransu,
Abinda tasani ya koya a rayuwarsa shine kayi rayuwa akan
mizanin dazai baka nutsuwa da ease
Baya tunanin har abada zai iya jefawa ko Kai kansa ga Abinda
zai baqanta ransa ya Bata Masa Rai yayi iya qunci da baqin cikin dazaiyi tun
Yanada quciya Dan haka wannan babin na damuwa akan alamarinda wani zaisaka ya
Dade da wucewa agurinsa
MD ga wannan kamar motar Dr khalil ce Kuma kamar dai ba
lafiya ba Dan.....
Bai qarasa yayi saurin over taking motar Dr din sbd wani
junction dazata nufa ta buga.
MD din ne da kansa yafito ya nufi motar Yana budewa idanuwan
Khalil din na qoqarin rufewa da zafin nama ya fizgosa daga cikin motar tareda
taimakon malam Umar suka kamasa zuwa motarsa da kansa ya qara sanyin AC din
motar tareda fitowa cikin sauri ya zagaya ya bude gaba cikin sauri yabude can
qarqashin sit din driver saigashi yaciro inhaler da sauri ya zagayo ya dago Kan
Khalil din Yana shaqa Masa Amma Ina Sam ko Shiga batayi sbd numfashinsa ya
tsaya gaba daya.
Kasa mgana yayi yafito idanuwansa na sauya ya karbi mukulli
hannun malam Umar ya zagaya ya figi motar cikin mugun speed din dayasa Mutanen
gurin watsewa da sauri sbd gudun tsautsayi shikuma Mal Umar yashiga motar Dr
din yaja yabi bayansu.
Zabeera ya nufa Kai tsaye
Securities suna hango motarsa da yanayin da yake tahowar
cikin speed yasasu saurin wangale Masa makeken gate din da mutum uku ne ke iya
rufesa
Yana isowa yashige gate din Yana qara gudun motarsa yabi
bangaren dama inda tacan gefen hanyar zuwa part din Khalil din yake.
Yanayin parking bakin part dinsa yafito ya nufi wata qatuwar
flower vase dake bakin qofar shiga palonsa inda anan yasan Khalil din na aje
keys dinsa.
Ya a budewa da bedroom dinsa ya nufa Kai tsaye sbd yasan
inda allurar take
Tun daga cikin dakin ya hadota yadawo motar Yana shiga ya
daga hannun Khalil din ya soka Masa tareda dannata da sauri ruwan suka shige
jikinsa take yayi wani irin yunquri tareda Jan numfashi me qarfi da qara kafin
jikinsa yakoma yasaki.
Sai alokacin MAHMOUD ya sauke ajiyar zuciya Yana 'dan dafe
goshinsa tareda lumshe fararen idanuwansa dasuka sauya kala.,
A duniya idan akwai mutum daya dazai iya sadaukarwa Koda
rayuwarsace to shine Khalil,
Khalil ne kawai weakness dinsa a duniyar Nan sbd shikadai ne
yake shiga tashin hankali akansa aduk lokacinda yaga ciwonsa yatashi sbd hakan
na razana jarumtarsa Dan Khalil shine mutum na qarshe dayake baya iya tunanin
ma rasawa,
A rayuwarsa he has only two dear ones,
Na farko mahaifiyarsa da har yanzu take cikin qasan ransa
daya kasa cire kewarta,
Sai na biyun shine khlail,Wanda bayada wani Dan uwa dayake
gani amatsayin jininsa kamarsa.
Tsananin mataki da kulawar daya daukarwa ciwon Khalil din
yasa dukkanin motocinsa da office dinsa yanada ajiyayyar inhaler dayake ajewa
sbd Khalil din Dan Koda ta kwana irin haka.
Ahankali yaji an dafa hannunsa
Saida yaqara rinste idanuwansa yasaki qaramin numfashi kafin
yabudesu akan hannunsa da khalil din ya dafa a wahalce.
Kallon fuskarsa Khalil yayi tareda sakin wani wahalallen
numfashi ganin duk duniya idanba ubangiji daya halacci MAHMOUD din ba Babu me
iya gane kowane yanayi na MAHMOUD da Abinda yake ciki sbd fuskarsa Bata taba
nunawa,farin ciki ko akasin hakan.
Kallonsa yayi da jajirtaccin idanuwansa cikin nutsuwa
yace"
Koma me kake tunanin kanayi zaifi idan kadawo kanka,
You know this is stupidity right??
Menene amfanin aiki da gwagwarmayar idan Babu lafiya you
better come back to your damn senses.
Girgiza Masa Kai Khalil yayi tareda qoqarin fitowa motar
Amma bazai iyaba sbd jikinsa ba qwari Dole MAHMOUD din yakamasa suka fito
yakaisa har cikin bedroom dinsa kafin yayi amfani da wayar khalil din yayiwa
umme txt akan bayajin Dadi.
Harzai juya ya fice Khalil din ya riqo hannunsa Saida ya
fidda numfashi ahankali na marasa lafiya kafin ahankali ya furta"
Thank you.
If you want to thank me be careful about your health,
Next time idan kayi Wasa irin haka yafaru ka shirya rabuwa
Dani sbd i can't take this stupidity,
U're unbelievable Khalil
Kana likita Amma Kaine kake Wasa da lafiyarka har kake
tunanin yin tukin mota cikin wancan yanayin,
Menene cikin kanka dayafi kula da lafiyarka mahimmanci????
Amatu.
Tsit MAHMOUD yayi sbd Jin zancen na Khalil a bazata.
Kallonsa yayi cikin zallar mamakin irin like seriously??
Lumshe ido yayi Yana sake maimata sunan Amatun a gajiye
Yadora da fadin"
MAHMOUD wallahi Amatu itace tunanin kulawa da ita yafimin
lafiyata,
Acikin yanayin danake ciki Babu Abinda nake tunanin cimmawa
kamar na iso gida gareta sbd tana cikin halin buqatata akusa,
Banajin yanayina kawai Abinda nakeso na iso gida alokacin.
Zame hannunsa MD yayi tareda miqewa Yana qoqarin barin gurin
sbd idan baiyi nesa da Khalil ba tsaf zaisa a binciko Masa the best
psychiatrist Dr taduba Masa shi.
Tashi zaune Khalil din yayi cikin dasasshiyar murya
yace"
Amatu amanata ce idan kana qaunar 'dan uwanka zaka kulamin
da ita aduk lokacin da bana kusa
Shine kawai Abinda nake roqanka a matsayin alfarma ta har
iya rayuwa.
Cak ya tsaya tareda kasa juyowa zuciyarsa na juya Abinda
Khalil din yafada Wanda yasashi Jin wani iri saidai kawai ya wuce batareda ya
juyoba Kuma baice kala ba ya ficewarsa daidai isowarsu umme tareda Nuratu da
tuni hankalinta yayi mugun tashi Jin Khalil dinta bayajin Dadi.
Zaune zarah take a Palo tana jiran isowar Khalil din sbd
tayita kira daga bayan nan wayarsa a kashe
Allah ma yasa Amatun tasamu bacci ya 'dan dauketa.
Yana shigowa ta dauka Khalil dinne tayi saurin miqewa zatai
Magana saitaga MAHMOUD ne fuskarsa daukeda wani yanayi na kasala da sauri ta
qaraso gabansa tana cewa"
Sannu da dawowa¿
Kallonta yayi tareda kallon agogon dake palon yasake maido
da idanuwansa kanta yayi Mata kallon minti biyu cif ahankali ya daga Mata Kai
alamar amsawa cikin sautinsa me sanyi yace"
Haryanxu kina zaune a Palo
Akwai matsala ne?
Kallonsa tayi wani irin sanyin Dadi na kwaranya cikin
zuciyarta harsaida murmushinta ya bayyana ta kalli cikin idanuwansa ya dauke
Kai sbd Sam bayason ana kallon cikin idanunsa ahankali tace"
Dr nake jira nakirasa tuntuni yanzu Kuma wayarsa akashe
Amatu ce ba lafiya taji ciwo sosai a hannunta.....
Cak ya tsaya daga tafiyar dayakeyi batareda ya juyoba
saikuma ya tafiyarsa Yana cewa'"
Shima bayajin Dadi bazaiso damuwa ba yanzu shima Kuma gobe
tunda safe zaiyi tafiya so just handle her situation for him.
Wucewa yayi yabarta tsaye dafe da goshin tunanin mafita da
abin Yi.
Ganin Amatun tasamu bacci haka ta lallaba itama taje ta
shirya tayi dakin MD din saidai duk Rabin hankalinta na qasa gurin Amatu.
Dr Khalil kuwa asubar farko lafiya kalau yatashi da qarfinsa
kamar baisamu attack din ba ajiyan,
Qarfe Bakwai na safe jirginsu zaitashi Dan haka qarfe shida
da rabi yafito a shirye driver din umme zai kaisa airport
Yaso ganin Amatu Amma yasan lokacin Basu tashi ba hakanan ya
hakura ya wuce bayan yayiwa zarah text tareda transfer din kudi masu kauri na
kulada duk Abinda amatun ke so kafin sati biyun yadawo,
Hakama bai wuceba Saida yayi Magana da Salman akan zaije
yaduba Amatu yasan matsalarta da Abinda za'ayi Mata.
Tun qarfe hudun asuba ta tashi tayita juye juyen azaba tun
tana daurewa harta kasa tafara hawayen azaba tana juye juye Dan haka Koda gari
ya waye anty zarah tashigo tuni idanuwanta da fuskarta sungama kunburewa sbd
kukan azaba aikuwa tana ganin anty zarah din ta sake sabon kuka
Da sauri zarah ta rungumeta tana rarrashinta da Mata sannu
kamar zatayi kuka.
Hannun har wani qyallin kumburi yakeyi shiya qara daga
hankalin zarah ta kamota suka fito Palo tana cewa''
Dr yayi tafiya Bari nafadawa MD zamuje asibiti.
Tana qoqarin juyawa saiga qwanqwasa qofar Salman tareda usi
bayansa Wanda Dr khalil ya roqesa akan yadaukosa aje dashi yaduba Amatu sbd tun
jiyan data kirasa taqi Magana hankalinsa yake atashe.
Aikuwa amatu na ganinsa tasaki sabon kuka
Da gudunsa yayo gurinta hankalinsa a mugun tashe Yana cewa''
Amatu??
Zama yayi kusa da ita Yana kallon hannunta sai kawai yaji
shima idanuwansa sun ciko da hawaye kamar mace saigasu suna gangarowa.
Dr salman zabeera sai suka basa dariya ya zauna Yana duba
hannun Yana cewa"
Zarah kina ganin mutuniyarki tasa oga Usman kuka saikace ba
namiji ba,
Usman dama jarumtar taka a baki take kenan.
Matsa hannun nata yayi da qarfi take tasaki wani razanannen
ihu tana damqe hannun dataji akusa da hannunta dake Kan hannun kujera
Shikuma da saukowarsa kenan basusan dashiba ba yazo wucewa
yaji an damqe hannunsa ya tsaya cak batareda ya juyoba sbd ko bai juyoba yasan
itace sbd zafin ciwo ta riqesa batareda tasani ba
Saidai Kuma samun kansa yayi da tsayawa batareda ya qwace
hannunba yana gane radadin datake ji ta
hanyar yanda ta mugun matse hannunsa.
##mamuh#

No comments