MIN QALB 18
*_MQ 18_*
_Mg_
Koda anty zarah tace yazauna suyi breakfast tare baiso karya Mata qwarin gwiwaba amma Dole yace Mata MD yariga yafice tun dazu so karma su jirasa suyi abinsu shima bai tsayaba sbd yau umme tace taredashi zatayi breakfast ya fice ya nufi can tun kafin rashin zuwansa ya shafi Amatu Dan Babu ranarda Bata tsinewa ranar data Fara haduwa da amatun.
Shiru anty zarah din tayi a sanyaye Jin MD baya gidan ya
fice.
Dafa hannunta dake zuba chips Amatu tayi tana murmushi
tace"
Anty karki damu zai hakura inshallah,
Nice nayi laifin Kuma nice zan gyara
Inshallah Allah saina sa Rabin ranki ya yafe Miki Dan haka
ki daina damuwa Amatu zatai Miki handling komai.
Qasa tayi da murya Yana cewa''
Saina Fara sashi yasan dawa yakeyi kafin Nan,
Shine jiya haddasa Dr ya durqusa agabansa Yana wani daddaure
fuska Yana Shan qamshi to zaisan yasa Dr da anty zarah damuwa indai nice Amatu
saiya sani.
Me kike cewa Amahh.
Cika baki tayi da chips da kwai tana cewa''
Bance komaiba anty zarah
Zauna kici abincinki karki Hana kanki abinci sbd soyayya.
Zama tayi tana murmushi tace"
Amah samun Wanda kakeso yanada Dadi hardai idan shima Yana
sinks,
Kinga kamar ke da Dr.
Tea ta kwankwada tana cewa''
Yanxu ni da Dr son juna muke??
Eh Mana gashinan a fili Muna gani musamman Dr bayada damuwa
sai Taki,
Farin cikinki da walwalarki sune nasa
Kina gani yanda baya iya dauke Ido a kanki koyaushe kece
first priority dinsa.
To ni anty banajin wainnan abubuwan da Kika fada nadai San
acikin maza banida kamar su uku shi da kawu da usi,
Yanda kakejin usi hakan nakejin Dr zan iya komai Dan farin
cikinsa da kula dashi.
Bakyajin faduwar gaba duk lokacinda Kika jiyo muryarsa kafin
ya iso gareki??
Sake cika bakinta da soyayyan qwai tayi tana cewa''
Banaji Amma Kinga Rabin ranki Dana jiyo ko qamshin turaran
Nan Masa me qarfi gabana faduwa yake sbd masifarsa.
Tsit anty zarah tayi tana kallonta kafin tasaki murmushi
tana cewa''
Shikenan karki damu zankoya Miki yanda zakiso Dr matuqa
kamar yanda yake sonki.
Anty zarah inason nazama wacce zata bawa Dr farin ciki da
dukkanin wata soyayya..
Bazaki iya basa farin ciki ba sai kin basa dukkanin
zuciyarki da soyayyarki.
Zanbasa sbd shine kadai a duniya cikin maza ya cancanci
zuciyata
Koda zuciyata batasan meye so ba zanbada ita saiya koyar da
ita da kansa.
Taso bawa maganganun amatu nutsuwa Amma ta watsar sbd Amatun
kanta batasan abubuwan datake fadaba Dan haka ba amfanin nazarinsu.
Suna Gama cin abincin Palo suka dawo anty zarah ta zauna
tana waya da ummanta ita Kuma Amatu dakinta Takoma Dan watsa ruwa.
Wanka tayi ta sanya riga da skirt na atampa coffee kala ta
tsaya gaban madubi Yana duba kanta tana sauke ajiyar zuciya sbd ganin Masha
Allah yanxu ita da kanta sha'awar kanta takeyi sbd mulmulewa da jikinta yayi da
hutu da kayan gyara jiki da fata.
Akan cikinta dake shafe kamar bashi yake daukar uban kayan
Dadi da abincin datake zuba Masa ba ta shafa ahankali tana gyara tsayuwa
Hakanan kawai yanxu tsananin son cikinta ya shigeta duk da
tasan ana Magana ne akan Abinda Babu kwata kwata saidai ita zancen yashigeta
musamman idan tayi tunanin ganin babyn a hannunta tana Masa Wasa Yana murmushi
irin na Dr.
Dankwalin kayan jikinta ta zare tareda nadawa ta saka cikin
rigarta daidai cikinta saita saki rigarta cikin yataso ya zauna daidai tareda
qarawa tsayinta kyau sai tayi kamar sabuwar amarya me qaramin ciki
Batasan lokacinda tasaki murmushi ba tana shafa cikin saiga
anty zarah tashiga tana cewa''
Amatu baki gama Shirin bane gurin Modibbo zamuje gaisuwa
tunda kikazo bakije kin gaishesaba hakama umme sune fa iyayen mijinki....
Tsayawa tayi da maganar lokacinda idonta ya sauka kan 'dan
matashin cikin na jikin Amatun take dukkanin farin ciki da Jin Dadinta ya fito
fili ta qaraso da sauri tana cewa''
Kinga Amatu yanxu cikinki yafito sbd kinsaka riga da skirt
dogayen rigunan Nan boye cikin sukeyi gaba daya..
Kallonta Amatu keyi tana murmushin ganin yanda ganin fitowar
cikin kawai yasaka anty zarah wannan farin cikin to ranar da aka haifesa fa ta
daukesa a hannunta.
Anty zarah Inshallah kema zaki dauki ciki ki haifi 'yayan
kanki Dana Rabin ranki.
Allah yasa Amatu
Sbd babbar adduata a yanxu shine samun haihuwa tareda MD sbd
haihuwa ce kawai zanyi na tabbatarda MD ZABEERA yazama nawa,nasamu muhalli
acikin zuciyarsa da rayuwarsa.
Gyale coffee ta yafa akanta suka fito zuwa sashen Modibbo,
Kamar Wasa saigasu sun 'dan jima agurinsa sbd yanda Amatun
ta zage tana basa labarin qanxon kurege na aurensu da Dr daya sake tambayarta,
Hakanan sai ta 'dan shiga ransa sbd Jin yanda sukayi
gwagwarmaya itada mahaifiyata baba Jamila.
Daganan sashen umme suka nufa Kai tsaye Amatu nata sake bude
idanuwanta da zabeera din koina kallo takeyi cikin burgewa tana sake tantance asalin
girma da wadatar Zabeera din.
Kwankwasa qatuwar qofar shiga palon umme sukayi
Tsawon mintuna hudu kafin me aikinta tazo ta bude musu suka
shigo Amatu na santin kallon qayataccen palon da qamshi tareda sanyin AC suka
cikasa.
Zama zukayi jiran saukowarta saidai shiru shiru Bata saukoba
Nan Zarah da aka Kira tayi baquwa ta tafi tabar Amatu na zaman jira.
Saidata shafe awa kusan biyu a zaune kafin ummen ta fito
cikin shigar alfarma tana waya Kuma dagaji da Dr take wayar sbd yanda take
amsawa da Dan sauran haushinsa dabai Gama sakinta ba
Saidata shigo tsakiyar palon ta lurada Amatu dake zaune tana kallo tana Kira ruwan
lemu da aka kawo Mata hankalinta kwance Dan wuce guri da volume bai ishetaba ta
dauko remote taqara tana shigaba da kallonta remote din a hannunta sai
murmushin Abinda take kalla takeyi.
Ko sallama da Khalil din batayi ba a wayar ta kashe tana
cewa"
Uban waye zaune har cikin palona?
Juyowa Amatu tayi tana aje cup din hannunta da murmushi Kan
fuskarta tace"
Haj Mama nice Amatu matar khalil nasan zuwa yanzu
kinmantani.
Cikin quluwa ta daka Mata tsawa tana cewa"
Uwar matar khalil din ce ba matarsa ba
Zoki fice kafin nasa kiyi nadamar zuwa Nan.
Matsowa Amatu tayi da sauri gabanta tana cewa''
Umme Dan Allah kiyi hkr da Abinda yafaru ba laifina bane
bakuma laifin Dr bane qaddarane Kuma nidai na karba qaddarar nan da hannu biyu
ta zama matar Dr wlh inaso.....
Ganin tafara loosing patience dinta batason tayiwa Amatun
komai yanzu sbd tanadin datai Mata tukuna shiyasata fixgota a wulaqance ta jeho
ta waje daidai isowar Nuratu wajen ta
tareta daga faduwar dazatai saidata dago taga Amatu ce aikuwa ta saketa amatun
tayi muguwar faduwa akan hannunta na dama take ta samu kurdewar qashi tasaki
wani razanannen ihu tana qoqarin tashi Amma takasa dafawa sbd azaba take wani
zufa ya karyo Mata ta kalli Nuratu a masife tace"
Ita waccan data jeho ni nasan dalilinta kekuwa da kikaimin
haka meye naki dalilin??
Dalilina shine cikin jikinki""tafada cikin
tsananin tsana da takaicin ganin cikin jikin Amatun.
Miqewa tayi da qyar tana dafe hannun cikin azaba tace"
To ke meye ruwanki da cikina kokuwa kema cikin 'yan koren
uwar Mijina ce sbd dai bakida alama da 'yan zabeera daga Ina malama???
Baqin ciki maganar Amatun tai Mata tana sake quluwa
tace"
Ni ba matsiyaciya bace kamar ki wadda Babu Wanda yakeda
tabbacin ba karuwa bace Khalil ya fada tarkonta ta auresa sbd kudi
Wama yakeda tabbacin wannan cikin nasane Kona wani
qa........
Wani gigitaccen Mari ya sauka akan fuskar Nuratun dayasa
gefen bakinta 'dan fashewa
Ta dago da sauri tace"
Ni Kika Mara???
Zuciya data gama ciyota kukan kura tayi tai Kan Amatun zata
mareta aka riqe hannunta ta bayanta ta fizge zata Kuma Yi Kan Amatun ya sake
riqe hannunta tareda zagayo gabanta kyakkyawar fuskarsa ta jinin zabeera tana
fidda sheqi
Tace"
SALMAN????
Sakeni,
wlh saina koyawa wannan mummunar karuwar hankali..
Saukar wani Marin ne a fuskarta yasata qarasa zaucewa tana
qwacewa tace"
Wlh yau sainaga ubanda ya tsaya wannan tinkiyar...
Sakinta Salman din yayi tareda kallon Amatu da mamakinta
yagama kashesa yana cewa"
Lallai Nima zanso ganin Wanda take dashi daya Bata wannan
qwarin gwiwar me ban mamaki da burgewa
Ina buqatar saninsa Dan basa jinjinawa ta musamman.
Kallonsa Amatu tayi ganin Yana qarawa wutar masifar fetur
tace"
Amatu itace tsayayyiyar kanta Bata buqatar tsayawar wani
gurin nunawa kowa matsayinsa,
Ki zauna ki nanatawa tosashiyar qwaqwalwarki ni Amatu nariga
Masha gabanki
Idan har akwai Amatu har abada Dr khalil zabeera bazai taba
kallonki ba
Kai da kake Dan uwanta saika taimaka Mata gurin fahimtar
hakan
Amatu ba tsarar yinki bace.
Tana Gama fadar hakan ta wuce Yana shafa cikinta Dan qara
qular da Nuratun
Cikin mugun baqin ciki da takaici nuratu ta juya a zuciye
tabar gurin tana fidda huci kamar zuciyarta zata tarwatse idanuwanta har wani
cikowa da hawayen baqin ciki suke
Dama can Kuma halinta ce saurin fusata.
The great ORTHOPEDIC Dr Salman zabeera kuwa gabaki daya
Amatu tagama basa mamaki lokaci daya da burgesa sbd sanin darajar kanta datayi takuma
nuna batareda tsoro ba,
Koma wacece Amatu shi tagama burgesa shiyasa yakasa dauke
Ido daga kanta harta bace.
##Mamuh#

No comments