MIN QALB 17
MQ 17_*
_Mg_
Ana qoqarin turata motar Yan sandan ta hangosa tareda mutane
Yana waya har lokacin kamalarsa na sake fita dabam acikinsu batasan lokacin
data washe baki ba tana cewa''
Anty zarah bazan Bari kije station ba da mutuncinki,
Fizge hannunta tayi daga hannun 'yar sandar mace ta maraice da
fuska kamar zatayi kuka tace"
Officer madam Dena riqeni da qarfi cikine Dani Kuma....
Kallonta anty zarah tayi duk da tsananin baqin ciki da
kunyar datake ciki Bata fatan Abinda zai samu Amatun sbd cikin jikinta
Zatai Magana idonta ya sauka kan MD dasuke qarasowa daf dasu
zasu shiga mall din
Wani mummunan tashin hankali ya shigeta tai saurin fadawa
motar Dan kada ya ganta bazataso mutuncinsa ya zube agurin ba da zarar angano
ita matarsa ce
Barema sanin dokarsa da Abinda yafi tsana shine iyalinsa
suzo budadden gurinda za'a Gama ganesu kamar wasu marasa daraja.
Amatu na ganin haka ta 'dan daga murya tace"
Ku bamu damar Kiran wani daga gida
Sbd daga babban gida muka fito wato ZABEERAS.
Cak ta 'dan tsaya bai juyoba saidata qara Kiran sunan
zabeeras din tana sake Dan daga murya sbd ganin ya tsaya
Kai tsaye ya juyo idanuwansa suka sauka kanta a bakin motar
'yan sandan Babu alamar kunya ko Jin nauyi atare da ita
Kai kawai ya dauke zai tafiyarsa saikuma ya tsaya cak sbd
kamar matarsa ya hango cikin motar
Saiya kasa juyowa tsawon seconds kafin ya juyo cikin nutsuwa
ya kalli cikin motar
Zarah dince kuwa a zaune tana sunkuyar da kanta
take wani irin dacin
Rai me mugun tsanani ya rufesa Amma idanba Wanda yasansa ba bazai iya ganewaba
Rintse idanuwansa yayi dasuka sauya atake yana controlling
nutsuwarsa ta sakan hudu kafin ya budesu ya sauke Kan managern gurin cikin
muryarsa me taushi da nutsuwa yace"
Meyake faruwa anan?
Bayani tsaf manager ya koro Masa Yana qarawa da cewar"
Ranka ya Dade wannan itace asalin wadda tayi satar inaga ita
waccan me ajewa ce wato shugabarta Kuma.........
Hannu ya dagawa managern Yana qara controlling fushinsa da
idan yasakesa agurin fasa gurin zaiyi gaba daya Dan bazai iya daukar
fushinsaba.
Yana daga wayarsa dake ringing yace"
Ku sakesu suje
Abar zancen daganan
Zanyi handling komai da kaina.
Okay ranka ya Dade angama
Officer ku sakesu su tafi
Ke hajiya fito
Allah ya taimakeku MD yasa baki ku wuce karku sake zuwa Nan
sbd next time bazaku samu wannan damarba ta kubuta Dan munsan yanda muke
dealing da qananun barayi irinku..
Zuwa lokacin kuka anty zarah keyi sbd maganganun dayake jefa
musu dakuma sanin yau taqare Mata tsakaninta da MD Dan ita kawai ke iya hango
_rage_ din dake fuskarsa gasu tafito bada izininsa ba,
Takai dare a waje ga wani irin bacin suna da aka ja Masa
Danma ba'a gano ita matarsa bace.
Daqyar take Jan qafa jikinta na mugun rawa ga hawayen datake
sosai ta nufi mota Amatu na binta jikinta a macen itama sbd ganin halinda anty
zarah din ke ciki Wanda Bata taba ganinta acikinsaba.
Suna shiga mota daqyar anty zarah din ta iya tayarwa suka
bar gurin Babu me iya ko dogon motsi a motar har suka Isa Kuma har lokacin
hawayen anty zarah Basu tsayaba.
Suna barin gurin ya daga wayarsa daketa ringin Kai tsaye
yace"
Dr duk Abinda kakeyi ka tabbatarda matarka tabar gidana
acikin Daren Nan.
Kashe wayarsa yayi Yana Gama fadar hakan kafin yajuyo ya
kalli P.A dinsa yace"
Faruk handle this for now
Gida zanje gobe zaka bani details din yanda akayi.
Juyawa yayi Kai tsaye ya nufi motarsa ya fada tareda janta
da kansa yabar gurin sai alokacin suka fahimci da matsala sbd yanda yaja motar
yabar gurin.
Suna shiga Palo tayi saurin Shan gaban anty zarah tareda
zubewa qasa da qarfi Kan gwiwoyinta tana sunkuyar dakai cikin tsananin nadama
tace"
Anty zarah kalmar hakurina bazata canza komaiba gameda
tozarcin Dana janyo Miki yau din
Dan Allah anty zarah kiyi hkr wallahi bantaba Jin kunya da
takaicin halinaba sai ayau,
wlh sbd ke yau naji
na tsani wannan halin nawa Dan Allah anty zarah kiyi hkr wlh banyi Dan
tozarta.....
Saukar wani lafiyayyan Mari taji a fuskarta Wanda yasata
qarasa zubewa zaune tana taba fuskarta amatuqar gigice ta dago a zuciye zatai
Magana idonta ya sauka cikin nasa idanun dasuka kada sukai jajir....
Da sauri zarah ta zube qasa itama zatai Magana ya daga Mata
hannu batareda ya kalletaba yace"
For first time ayau naji nayi takaicin amincewa da aurenki,
Hw cud you zarah,
Bakisan mutuncin kanki da Wanda ya ajiyeki bane dazaki fita
in the first place batareda izini ba
Ever this stupid being came here nasan zaayi haka wata Rana
sbd wannan ba mace bane she is just a shame,
Sata rayuwarta ne
Shi aka reneta dashi sbd Abinda tasani shine kawai sata da
yawo cikin maza with no shame,
A hausance banma san sunan dazan kirataba sbd idanma
ankirata da abin kunya an Bata sunan mutunci
Amma ke this is the last thing I expected from you...
Banason hayaniya I prefer rayuwata ni kadai yafi nutsuwa da
kwanciyan hankali so please ku duka just park ur things kubar Nan
Ni kadai nakeson zama anan just I think kowannenmu need a
break.......
Wani irin kuka Mai taba zuciya anty zarah tasaki tana
qoqarin basa hkr ya juyawarsa zai haye sama Amatu ta miqe da saurin Tasha
gabansa tareda sake zubewa tana tsiyayo hawaye masu tsananin 'dacin kalaman
daya furta akanta saidai komai 'dacinsu zata hade bazata Bari laifinta ya
lalata auren anty zarah ba kodan yanda tasan shine rayuwar anty zarah din.
Akaro na farko a rayuwarta datake qwallan cin zarafi da akai
Mata sabanin da ko ajikinta Dan ko damuwa batayi barema ada Babu Wanda ya Isa
ya tsareta ya iya fada Mata haka Bata saka an Masa zanen yorbawa a fuskar ba.
Sabbin hawaye suka gangaro Kan fuskarta ta bude baki
muryarta a matuqar sanyaye tace"
Dan Allah kayi hakuri anty zarah batada lai...
Ko kallon inda take baiyiba ya wuce tayi saurin rarrafawa
zatasha gabansa cikin tsananin 6acin Rai
ya daga qafa zai wuce da ita aka saka hannuwa biyu aka tare qafar
Ya tsaya cak kallon Dr daya riqe qafar tasa cikin tsananin
mamaki da sabon takaici.
Dr daya jima tsaye Yana sauraran duk Abinda MD din ya fada
suna dukan zuciyarsa duka me tsananin daya karya gwarin gwiwarsa.
Baice komaiba sai kawai ya sauke gwiwoyinsa qasa gaban MD
din tareda sunkuyar da Kai cikin tsananin rauni da damuwa me nauyi murya a
sanyaye yace"
MAHMOUD karka hukunta zarah akan laifin amatu na roqeka da
sunan Allah,
Itama Amatu Ina roqonka daka yafe Mata Koda hakan zai zama alfarmar qarshe dazakamin
arayuwata to Dan Allah ka yafe Mata ba laifinta bane laifina ne Dana kasa bar
Mata duk Abinda yakamata nabar Mata......
What???Khalil Kama San waye wannan yarinyar kuwa?
Tun farko bansan me kagani na hankali atareda wannan
yarinyarba harka iya sabawa iyayenka ka aureta,
And now kana durqushe a gabana duk sbd ita
Khalil Kama ganin daidaine hakan?
Rintse idanu Dr yayi a sanyaye Yace"
Abinda nasani yanxu arayuwata shine indai sbd itane zanyi
har Abinda yafi durqusawa sbd tsirar Mata da mutuncinta,
Kai Dan uwanane mafi kusanci agareni Wanda kalmomin batanci
mafi Muni suka fito daga bakinka kan macen danafi so da qaunar Kare martabarta
shiyasa na durqusa gaban nake neman afuwarka sbd ita,
Cikin sake kunnasa da Khalil din yayi da maganganunsa
hakanan kawai yaji mugun zafinsu
Yau Khalil ne ke fadar kariya da martabarta
Rintse ido yayi suna qara rinewa ya kalleta
Sautin kukanta na fita ahankali sbd maganganun Dr sungama
sanyata cikin nadama me tsanani
Take zafin zuciyarsa yafara loosing control ya juya zai wuce
Khalil ya miqe tareda Shan gabansa yace"
MD matuqar haryanxu matsayina na Nan a zuciyarka da
rayuwarka inason ka tabashi biyu kabani nida Amatu sbd wlh ni itace tawa
rayuwar,
Zakaimin alqawarin yafe Mata tareda Bata mutunci amatsayinta
tawa,
Idan bakayi Dan ni ba kayi kodan jinina dayake jikinta Wanda
yake shima naka jinin,
MD Ina fatan zakamin wannan alfarma ko bayan idona.
Kasa kallon Khalil din yayi sbd baqin ciki da takaicin duk
akan mace ya zare haka macen ma ba kamar matan mutunci ba haryana kirarin idan
yana qaunarsa saiya qaunaceta
Ra'besa kawai yayi ya haye sama tun kafin shida Khalil din
ta 6aci akan yarinyar.
Bayansa Khalil yabi da kallon harya shige kafin ya saki
numfashi a sanyaye tareda juyowa ahankali ya zauna gefen amatu dake kuka qasa
qasa takasa ko motsi.
Kallon zarah dake nata kukan yayi zaiyi mgn ta miqe tabar
gurin tayi dakinta ta rufo sbd itama kukan takeso tayi sosai ko nauyin
zuciyarta zai ragu.
Cikin sanyin jiki ya maido da kallonsa Kan amatu yafara
lallashinta Yana Mata nasiha hartayi shiru da kansa ya dauko ruwa a fridge
yabata Tasha ya rakata har dakinta kafin ya wuce zuwa nasa part din jiki da
zuciyarsa amatuqar sanyaye.
Sallolinta tayi ta zame ta kwanta Kan dadduma a inda tayi
sallar yau ba Maganar cin Dadi
Amma datayi awanni a kwance taga bacci ba zuwa zaiyiba sbd
yunwa hakanan ta miqe ta fito taje kicin taci fruits dinta da yoghurts ta qoshi
tazo ta kwanta tunanin Dr na dawo Mata bangare daya Kuma damuwar da anty zarah
take ciki.
Washe gari tunda safe Dr khalil yazo sbd yasan shikenan MD
zai Fara rashin 'dan zaman dayakeyi a gidan fita tinda safe dawowa sai dare
qarshema yasan zai iya tafiya yabar qasar yakoma wata qasa sai yaga dama ya
dawo.
MD na ganinsa ya kallesa Yana watsar da tunanin abubuwan
jiya din sbd shi ba mutum ne me aje hargitsi cikin kansa ba Sam ko maganar
batason a tayar sbd kar asashi cuwon Kai.
Kallonsa Dr khalil yayi Yana qaqalo murmushi yace"
Good morning MD ZABEERA.
'dan kallonsa MD din yayi Yana maida kallonsa Kan agogon
hannunsa cikin miskilanci yace"
Morning Dr khalil zabeera.
Murmushi Khalil din yayi Yana cewa''
Sorry MD.
Kallonsa ya 'danyi kafin yaci gaba da duba wayarsa.
Bai kamata nama Magana irin yanda nayi maka a jiyan kayi
hkr.
Karka damu I can't even recall Abinda yafaru a jiyan.
Numfashi Khalil ya sauke Yana gyara tsayuwa kafin yace"
Amma akan Amatu inakan duk Abinda nafada Dan haka Ina riqon
alfarmarka sbd abin dake cikinta please kabata damar dazan gyarata kodan
'yayana su samu uwa ta gari.
Gaba daya MD din ya dago ya kallesa wannan karon tareda 'dan
lumshe fararen idanuwansa yasaki wani sahirtaccen numfashi kafin yace"
I hope you know wat u're doing.
Motarsa ya fada tareda cewa''
Mu yini lfy Dr.
Murmushi Khalil yayi Yana cewa''
Zan dauki wannan amatsayin amincewa da roqona thank you.
Ciki ya qarasa gurinsu sbd Suma yanason mgn dasu musamman
zarah bayason tasamu matsala da Amatu akan wannan alamarin sbd ita kadaice
yasan Amatu is safe a gurinta.
Cikin sa'a kuwa Zarah din na dining tana qoqarin jera
breakfast tayi 'dan adonta duk da ba walwala sosai a fuskarta duk sbd taqara
bawa MD hakuri.
Cikin sakin fuska yakira sunanta
Ta juyo tana yaqen Dole suka gaisa
Suna cikin mgn saiga Amatu ta fito jiyo muryarsa
A sidade ta qaraso tana kallon fuskar zarah a raunane.
Ganin yanda tayi din sai anty zarah din taji rashin Dadi ta
saki 'dan guntun murmushi tana cewa''
Amatu Zo
Kinci abinci jiya da daddare kuwa?da maganinki ma kinsha??
Wani sabon girma da qaunar anty zarah dinne suka rufeta
batasan lokacinda ta qarasa gurinta da sauri ba ta rungumeta tareda sakin wani
siririn kuka tana cewa''
Anty zarah Dan Allah ki yafemun wlh nayi nadama me tsanani
akan Abinda na ja miki.
Karki damu Amatu qaddarane Kuma yariga ya wuce tunda kince
bazaki sake ba.
Zama tayi gefen anty zarah din ta share hawayenta tana
sunkuyar da Kai tace"
Anty zarah kunyarki nakeji haryanxu sbd tun yanxu nafara
saka Miki da Abu Mara kyau akan alkairi da qaunar da kike mini,
Ayau naji gida nakeson komawa inda nafito,
Cikin mutanenda nafito,
Cikin rayuwar damuka saba da qanqancin da muka Saba dauka
sbd nafara gane ban cancanci zama cikin mutane masu mutunci da daraja kamarku
ba,
Anty zarah daukar abin wani yazama tamkar qaddaratace sbd
saimun dauki abin wani muke iya ciyar da cikinmu abinci wata Rana,
Rayuwa da mutanen cikintane suke tilastamu ga aikata wasu
laifukan wata Rana,
Nida usi muntaso cikin bola muka rayu acikinta mukayi wayo,
Acikin bola muka Fara sanin yanda zamuyi fafutuka mu gudanar
da rayuwarmu,
Bayan Tasha shine gurin kwananmu
Shine muhallinmu a lokacin,
Tun munada shekarun da bamu Gama sanin bambamcin jinsuba aka
lalatawa usi rayuwa ta hanyar Masa fyade,
Fyaden da shine sanadin farko na qarin tabarbarewar
rayuwarmu,
Alokacin mukasan ba tausayi atareda mutanen cikin duniya,
Munkoyi data Danmu ci mu tsira mu rayu,
Anty zarah bamu qara fuskantar qasqancin halin rayuwa da
mutanen cikintaba sai alokacin da nida USI aka kamamu a gaban idonsa aka yaga
tsumman sutura dake jikina za'ayi mini fyade Wanda yayi sanadin haduwarmu da
mutum na farko daya Fara yima kallon muma 'yayane Kuma mutane 'yan Adam,
Kawu ya gabatar Mana da sabuwar rayuwar almajiranci wadda
nayita acikin maza da siffar maza ta hanyar rayuwa usman namin aski,
Munyi almajiranci na wahala Wanda yasamu baqin jini acikin
almajirai Yan uwanmu,
Munyi kukan sarari munyi na fili saidai bamuda tudun dafawa
har Saida rayuwar wahala da garari ta aure mu kafin kawu yasake kallonmu da
idanuwansa na rahama da jin qai ya zamo uba garemu,
Ya bamu uwa me qaunarmu tamkar 'yayanta iyami,
Mezamu ce arayuwar Nan bayan wahala da rayuwar garari a
jininmu take shiyasa ko a gidan kawu tsanani da Matsin rayuwa be qare Mana,
Muna kwana da yunwa mutashi da ita Kuma muyi rayuwarmu,
Munshiga masifu iri iri da rayuwa ta jefamu aciki saidai
Babu wani mahaluki 'daya daya taba kallonmu da zuciya me kyau
Kowa nada buri Mara kyau akanmu Wanda ya dangantamu da irin
wannan rayuwar da ake qyamarmu sbd ita,
Rayuwa ta zabar Mana gwagwarmayar samun Abinda zamucu kota
halin Yaya alokacinda 'yaya kamarmu suke makaranta suna karatu shin anty zarah
bawa shi yake zabarwa kansa qaddarane??
A tsawon shekarun ban bantaba Jin nadamar daukar abin waniba
sai a jiya Dana jawa macen data Soni tsakaninta da Allah batareda ta hada komai
daniba,
Anty zarah a shirye nake Dana bar Nan sbd zamana anan masifa
zai janyo Miki ba alhe.......
Rungumeta anty zarah tayi da sauri Yana sakin sheshekar
kukan datakeyi na tausayin Amatun da usman tareda su kawu dasuka taimakesu
bayan Suma taimakon suke nema.
Tabbas Amatu sbd Allah nakesonki tun ranar da kikazo Nan,
Kinmin laifi Amma ban riqeki a raiba sbd sanin ajizanci irin
na 'dan Adam,
A da Ina zaune dake amatsayin matar Dr dakuma Amana da aka
bani Amma daga yanxu zan zauna dakene amatsayin qanwa da muka fito ciki 'daya.
Zamewa Amatun tayi da sauri tana share hawayenta ta saki
qaramar dariya tanason kawar da kukan anty zarah din tace"
Anty da gaske?
'daga Mata Kai tayi tana share hawayenta itama.
Anty zarah karfa wata Rana kice aa alqawari kikamin munzama
kamar ciki daya muka fiyo.
Dariya antyn tayi har lokacin hawayenta Basu Gama tsayawaba
tace"
Amatu nayi alqawari ba canzawa
Amma kema kinsan kinyi alqawari zakiban babynki idan kin
haihu"" tafada cikin tsokanar Amatun.
Da sauri ta kalla Dr dayayi mutuwar zaune da tsananin
so,qauna, tausayi tareda ganin girman Amatun
Ta dafe cikinta tana cewa''
Dr kaji anty zarah Wai zamu Bata babyn.
Yana kallonta cikin tsananin shauqi yace"
Idan har kin amince zaki Bata ni Kuma idan har nine dadynsa
nayi alqawari da hannuna zanbatashi.
Murmushi yasaki tana shafa cikinta ahankali tace"
Inama inada cikin wlh Dana baki anty zarah.
Qasa yayi da murya daidai kunnenta yace"
Karki damu watanni kadan ne yarage mufita wannan dilemma din
zamu bawa antynki da MD baby.
Kallonsa tayi da sauri tana boye dariyarta Dan batasan
yajitaba ganin yakasa daina murmushi yasata miqewa da sauri tayi hanyar dining
tana cewa''
Anty zarah mijinki yagama ci muzo muyi namu party din a
dining Dan wlh har yunwar jiya saina fanshe abuta.
Murmushi sukeyi suna Mamakinta ganin tabbas Bata aje
al'amarin duniya a ranta sbd karta wahalar da kanta a banza sbd me gatane ke
tsayawa kuka da damuwa Dan a lallashesa suda basuda ko daya sunyi futo na fito
da kuka da damuwa tareda abin kunya Sam baya damunsu.
##Mamuh#

No comments