MIN QALB 16
MQ 16_*
Zaune take gaban madubin dakin daya zama Mata tana kallon
fuskarta datayi haske sosai tareda duka fatar jikinta har wani qyallin samun
hutu da kayan gyara masu tsada da mutunci zuwa qirjinta daya ciko shima yayi
daram dam sabanin dah banbancinsa da shafe idan tasaka brazier ne push
up.
Mayarda kallonta tayi Kan cikinta tana miqewa tsaye ta Dan
matse rigarta tana shafa cikin sai tasamu kanta da sakin murmushi karon farko
datai shaawar dama ace cikin gasken ne da ita da zaiyi mata kyau Kuma da duk
wahala da dawainiyar anty zarah baza taje a banxa ba,
Dan sake dafe cikin tayi tana cewa''
To idan ace cikin gske ne to waye zai zama babansa?
Dr??
Girgiza Kai tayi tana cewa''
Ummen sa bazata Bari ba.
Amma dai duk da haka shine zaifi iya bawa babyna kulawa Amma
dai kamanninsa kuwa anty zarah nakeson ya dauko sak sai Kuma......
Shiru tayi takasa qarasawa
Daga bayanta taji ance' sai Kuma me maman bby?
Juyowa tayi tana kallon ZARAH din kafin ta juya ta qurawa
cikinta ido ta cikin madubin ahankali tace'
Sai Kuma inason ya dauko hancin MD.
Zarah dake qoqarin zama bakin gado tsayawa tayi ta kalli
amatun tana karban zancen a baibai saidai kawai tasan duk irin shirme shirmen
Amatun sai kawai tasaki murmushi tana janye Amatun daga gaban madubi tana
cewa"
Zoki zauna zaki gaji da tsayuwa gashi yau zamuje scanning
anjima kadan
MD nake jira ya kirani na sanar Masa zamu fita nayita Kira
baya dauka tun safe bayan fitarsa.
Ki qyalesa anty zarah mu tafiyarmu kawai tunda Dr na can
Yana jiranmu a asibitin tun dazu yake Kira bamu fitoba.
Bazaki gane bane Amatu dokar MD ce baya barina fita Babu
wani babban dalili me qarfi sbd shi mutum ne me buqatar sirrintacciyar rayuwa
Mara hayaniya shiyasa bayason ko iyalinsa ace kowa ya sansu a haka dai zance MD
mutum ne me tsananin kishi.
Dibar zancen na anty zarah tayi ta watsar da baki tana
cewa"
Anty zarah to nidai gskia muje karki tsaya jira tunda yaga
Kiran naki fa na tabbata,
Kuma nidai bazan Bari Dr yayita jiraba tunda Modibbo da Andi
sunsan da zancen fitar muje kawai Dan Allah.
Miqewa anty zarah tayi tana nufar qofa tana cewa'
Amatun 6acin ran MD ba kyau bazan iya take dokarsaba
Zan iya fita yanxu wani Abu yafaru wlh bazan iya daukar
fushinsaba kiyi hkr Bari nasake gwada kiransa kozai dauka....
Takaici yasa Amatun dafe ciki ta durqushe tana cewa''
Wayyo Allah anty zarah cikina marata ciwo sosai
Dan Allah anty ki taimakeni kada cikina ya samu matsala Ina
sonsa banason ya zube.....
Da gudu anty zarah ta dawo tana Kiran sunanta cikin tashin
hankali tana riqota
Ita kuwa Amatu sai wani murqususu takeyi tana sako hawayen
qarya tana Daman cewa''
Anty ki taimakeni banaso cikina ya zube.
Tsabar tashin hankali da firgici tareda tausayin Amatun me
tsanani ZARAH batasan lokacin data fashe da kuka ba tana kamota jikinta tana
qoqarin muqar da ita tana kwalawa hafsatu Kira Dan tazo su kamata suyi asibiti.
Kamata sukayi suka saka mota a gigice anty zarah ta yafo
gyalen jallabiyar dake jikinta ta fada motar ta jasu suka fice tana cewa
hafsatu"
Hafsatu maza Yi sauri ki Kira Dr khalil ki sanar Masa Abinda
yake faruwa gamunan zuwa.
Shiru Amatu tayi daga kukan qaryan datakeyi jikinta na yin
sanyi da yanda anty zarah ta daga hankalinta sai hawaye takeyi tana Mata sannu
Amma Babu yanda ta iyane itama sbd Dr yace Mata komai zatayi ta tabbatarda
sunxo asibitin sbd yabasu scanning din daya shirya Dan ita din idan basuxo
asibitin ba to tabbas wani likita ummensa zatasa akawo har zabeera din Dan
kawai ayi komai yafito fili
A bangare daya Kuma ga USI da shima zasu hadu duk a asibitin
shiyasa tayi hakan,
Ahankali ta kamo hannun anty zarah din bayan har sun iso
asibiti Khalil ya karbeta sun shige yayi duk yanda zaiyi ya hado scanning din
aka kwantar da ita office dinsa tareda 'yan magungunan vitamins sai alokacin
hankalin zarah yadawo jikinta ganin Amatun tadawo daidai ciwon ya daina.
tana kallon anty zarah din bayan ta riqe hannunta ganin har
lokacin da sauran damuwa a fuskarta itama cikin sanyin murya furta"
Nagode anty zarah,
Nagode da matsayin da Kika bani na qanwa tamkar wadda kuka
fito ciki daya,
Anty zarah wlh kece mutum ta uku da Kika taba qaunata
tsakani da Allah ba qyamata ko wulaqantawa Dan haka kinada babban matsayi a
zuciyata da har abada bazan mantaki ba.
Kasa cewa komai anty zarah tayi sbd har lokacin Bata Gama
fitowa cikin shock din halinda Amatun tashigaba
Dan wato da ace wani Abu yasamu cikin bazata taba yafewa
kanta ba.
Shigowar Dr da USI a bayansa yasata miqewa zaune da sauri
tana washe dukkanin haqoranta cikin tsananin farin ciki takira sunansa tana
qoqarin saukowa gadon Dr khalil yayi Mata gyara murya Yana kallonta
Take ta kallesa tana dawowa nutsuwarta saita waske ta hanyar
cewa"
Anty zarah ga qanina usman.
Kallonta anty zarah tayi irin da gasken Nan kike?
Daga Mata Kai tayi murnarta na sake bayyanuwa ta jawo Usman
din gaban anty zarah tana cewa"
Usi ka gaida anty zarah.
Da sauri cikin girmamawa yace"
Anty mun wuni lafiya?
Ya gida Yakuma qoqari?
Mungode sosai sosai fa anty
Allah ya saka Miki da alheri
Ya biya Miki buqatunki na alkairi.
Murmushi anty zarah tayi tana kallon yanda jikinsa har
mazari yakeyi gurin gaidata Yana fiddo dukkanin girmamawar dayake ji akanta sbd
duk yanda take qaunar Amatunsa tafada Masa shiyasa shima tun baigantaba yake
Jin qaunar halayenta da ganin girmanta.
Kallon Amatu dake cikin dokin ganin usman din tayi tana
cewa''
Amatu me Kika fada Masa yaketa wannan addua haka?
Usman karka ji komai ba komai Amatu tamkar qanwar da kuka
fito ciki daya nake jinta
Saidai kayi Mata nasiha ko zataji Amatu Bata zama kurum
kodan halin datake ciki gashi yauma sbd tasa damuwar fitowa Dole yasa akaso
samun matsala har muka qare kwance a asibiti.
Anty zarah ki ringa doketa kokuma ki Fara hanata kayan Dadi
zata dawo hankalinta.
Dariya sosai anty zarah tareda Dr suka saki harda ita Amatun
tana kaiwa usi mugun duka a baya tace"
Ni zakayiwa baqin ciki usi?
Zakasan dawa kayi sai nasa kawu ya aura maka qanwar maman
junior data maqale maka.
Cab wannan ai koni tafi iya sanin yanda ake sanfewa Dan wlh
koke duk qwarewarki saita sanfeki
Kisa ranarda aka kawota ta sanfe Dan cinikin iyami da kawu
kejin yanzu yafara zamowa sahun masu abun Kai kawu ya kwana ya debewa auren
albarka.
Dariya suka saki gaba dayansu hadda anty zarah da batasan
meye sanfewarba dagasu sai Dr ne kawai suka sani shima sbd yayi bincike sosai
akansu ne Kuma sun zauna dashi su kawu da USI din Basu boye Masa komaiba gameba
rayuwarsu sbd sunriga sun daukesa kamar jininsu.
Ta Dan saci kallon Dr da ita yake kallo shima zuciyarsa na
samun nutsuwa da yanda yake ganinsu cikin nishadi zuciyarsa na sake samun
nutsuwa
Ta juya ta harari usi tareda take Masa qafa da qarfi har
Saida ya zabura tayi saurin dafesa Dan kada anty zarah tagane qasa qasa
tace"
A gaban Dr baban babyn nawa kake tayarda maganar qwarewata a
sata ka shirya kwanciya a asibitin Nan
Dan saina fasa maka baki da haqora idan anty zarah ta fita.
Kallon Dr yayi da Ido Yana cewa''
Ka ceceni matarka zata fasa bakina Wai.
Kamar zaiyi Magana sai ya fasa Yana sakar Mata murmushi sbd
idanun data zuba Masa tana jiran jin Abinda zai ce ta mayarda rigimar kansa.
Ikon Allah anty zarah tayita kallo a tsakaninsu sunata raha
da nishadinsu cikin tsananin qaunar junansu ga Dr da tuni dama yazama 'daya
daga cikinsu gabanta harsu iyami aka Kira da kawu a wayar Dr Nan aka Dora wata
sabuwar hayaniyar sbd labarin fadanda kawu yayi dasu maman basiru ya dauko
motar yan sanda biyu aka kwashe gidan kaf harda alhaji mande daya iya shigar
sani infika.
Dariya sukeyi sosai musamman da iyami ke fadawa Amatu
kawunta ya zabure yanzu tunda yaga ya 'dan tsayu hakama insfector Garba na Nan
Yana bibiyar kawun akan maganar aurenta.
Nishadi sosai suke saka anty zarah tayi zugum tana kallonsu
suna burgeta hakanan taji inama acikinsu take itama data samu farin ciki
kamarsu,
Abu daya tasani shine Koda take cikin wadata ta taso cikin
tun tana gidansu Basu San wani Abu Wai sakewa cikin nishadi kayi rayuwarka ba,
Tun a gida sun Saba bin umarni ne kawai da oda suka sani
Iyayensu basa jansu ajiki Wai da sunan tarbiya da kadasu
lalace
Shiyasa yawancinsu Basu wani cikin walwala saidai kawai suyi
rayuwa cikin daular Amma Babu wani walwala saigashi wainnan bayin Allan sunada
duk wani nishadi da walwala suna rayuwarsu hankali kwance,
Tabbas shi nishadi da farin ciki ba siyansa akeyiba Allah ne
yake baka
Gashi ayau duk da tarin daular datake ciki rayuwar wainnan
talakawan tana burgeta harma tanajin inama acikinsu take.
Anan sukai kusan Rabin yinin sai yamma suka fito gabaki
dayansa tana Jin kewar usi dasu kawu tun Usin be tafi Amma hakanan suka rabu
shida Dr suke tafi a motar Dr sbd yakaisa gida itakuma suka tafi a motar anty
zarah da hafsatu.
Suna tafe suna tana kallon titi cikin nishadi sbd tunda
tashiga zabeera tsawon wata biyu sai yau tafito,
Gskia dai ma Ashe wani lokacin masu kudin rayuwar takura
kawai sukeyi kullum a killace Wai sbd kar mutane su dameka,
Ita Sam batason akoma gidan yanzu yawo takeso tadan sakata
ta Wala.
Qaramin tsoki taja a fili Wanda yasa anty zarah kallonta
tana cewa''
Yaya dai Amatu?
Bata fuska tayi tana yamutsawa tace"
Anty zarah Dan Allah muje blue fox na taba yin aiki acan
Muje kibiya madam dinmu kudi yau da kanta zata wanke min Kai
da qafafu tasan Nima bayan ta koreni aiki nayi gaba ba bataba.
Murmushi tayi tana cewa''
Amatu ba dama.
A blue fox wani shaqiyanci ta dinga yiwa madam bell din tana
cewa ga Abinda da Abinda takeso
Haka dai suka ringa yimata Abinda tace sbd ganin wadda
sukazo tareda ita din she's from zabeeras.
Gyaran Kai akai musu itada anty zarah din tareda kyan qafa
da gyaran fuska take suka koma tamkar wasu amare musamman amatun da Bata taba
irin wannan gyaran ba take suka hau wani irin sheqi.
Daga nan restaurant din blue fox din ta matsawa anty zarah
suka shiga Nan tayi odar kayan dadin dataci harta Bar saura sbd sunfi qarfin
cikinta suka fito nanma matsawa anty zarah
tayi suka nufi wani qatoton shopping mall datace tanada kwadayin son
shigarsa.
Suna shiga mall din me hawa biyu batasan lokacin data saki
tsallen murna ba tana rarraba idanu cikin gurin farin cikinta a bayyane.
Sama suka hau gurin kayan babies antyn na cewa kayan baby
kawai zasu siya
Nan anty zarah tadan
zaba kayan babies suka sauko Amatun nata zare Ido tarasa abin dauka sbd duk
kayan Dadi da maqulashen dake gurin akwaisa a gida hakama sutura Bata buqata
sbd Dr kusan kullum cikin kawo Mata su yake hakama anty zarah
Idan turarukane duk tanadasu a gidan hakama takalma,
Ita Kam da a dah ne tazo wannan gurin da saita sace kusan
kayan dubu dark saidai suje station
Amma ko yanxu ba damuwa Dan saita yiwa Dr tsarabar dazai
ringa tunata.
Wani tsadadden agogon Rolex tagani Yana qyalli take ta hango
kyanda zaiyi a hannun Dr
tasaki murmushi tana kallon anty zarah dake qoqarin Ciro
card dinta tabayar gurin payment ta faki idanuwansu ta zaresa tareda sakawa
cikin aljihun doguwar English gown din dake jikinta tana waskewa tahau 'yan
juye juye tana latsa wayar anty zarah dake hannunta.
Suna Gama payment din suka fito har zasu shiga mota aka
tsayar dasu da sauri ana cewa su dawo ciki anason ganinsu.
Tsayawa anty zarah tayi tana kallonsu cikin mamaki kafin ta
kalli time har anfara Kiran sallar magrib tace"
Lafiya?
Sauri mukeyi munyi dare fa.
Dayan ne me sanyeda suit kamar ma shine babbnsu yace"
Haj wani Abu mukeson kugani da idanuwanku kafin muyi mgn
please.
Qaramin tsoki tasaki tana cewa''
Amatu ku jira a mota Ina zuwa.
Aa hajiya da ita zakuzo duka muke buqatar ganinku.
Ba musu suka koma ciki har office din managern gurin suka
zauna take aka kunna musu Abinda footage na CCTV camera
Mutuwar zaune anty zarah tayi cikin mamaki da kunya
Amatun ma cikeda kunyar anty zarah ta dago ta kalleta kafin
tayiwa manager kallon takaici
Bataji kunyarsa ba ko kadan ita anty zarah ce kawai abin Jin
nauyinta itama dandai na farkone datayi a gabanta.
Bude baki anty zarah tayi Yana Mata nauyi zatayi Magana
kenan saiga Yan sandan da aka Kira mota guda har sun iso Nan take aka gargadosu
zuwa mota anty zarah tsabar rudewa da tashin hankali ko magana ma takasa Yi.
Wata baqar Mercedes-Benz beymach30745 2020 ce tashigo
harabar gurin tayi parking
Tareda wasu motoci guda biyu manya na asalin me mall din
dasukazo Dan duba gurin zai siye tareda estate din dake bayan mall din.
saidaya dauki lokaci
Yana qarasa wayar dayakeyi kafin yafito
Lokacin su alhaji bayo din yafito tareda P.A dinsa dukkanin
ma'aikatan gurin sunyo gurinsa suna Masa barka da zuwa hakama ganin MD ZABEERA
taredashi yasasu qara bada girmamawa suna Masa barka da zuwa barema daman sunji
shine zai siye gurin.
##mamuh#

No comments